Showing 9001 words to 12000 words out of 143522 words

Chapter 4 - DAHUWAR 'KAHO BOOK COMPLETE Hausa Novels By Ameera Adam.pdf

18 Jun 2025

5509

Karima ta yi ɗan jiƙe-jiƙenta, dangin
abin da ya shafi tsimi da sauransu. Dama tun asali Hajiya Karima mace ce mai gyara sosai,
tana da tsafta uwa-uba ba ta wasa wurin gyaran jikinta. Ta yi wannan haÉ—e-haÉ—en na

musamman ne, saboda yadda ta lura da rawar jikin da Daddy yake yi a kan Shukura. Ba ta son
ko kaɗan ya ga gazawarta, ko ta fuskaci wulaƙanci a wannan ɓangaren daga wurinsa. Saboda
ta san duk son da namiji yake wa mace dole tana buƙatar gyara, kuma ko namiji bai fito ya
bayyana ba idan bai samu yadda yake so ba za ta ga alama. Ko lokacin da Alhaji ya shiga ɗakinta, ta gama shan tsumin gumbar nonon raƙumi da ta
sassaƙen ɓaure. Yana shiga ɗakin ta ƙare masa kallo duk sai ta gan shi a firgice, ƙarasawa ya
yi gefen kujerar da take zaune ya sakar mata murmushi. Martanin murmushin ta mayar masa,
ya riƙo hannunta ya ce. "Mommyn Mami kin ga yadda kika yi kyau kuwa?"
Murmushi ta yi ta ce , "Wanne irin kyau kuma, kai da kake da amarya." Ta faÉ—i haka don ta ji me
zai ce.

"Kowa ai da irin nata kyawun."Ya furta mata yana murmushi. Shiru ta yi tana jin daÉ—i har a
ranta, saboda ta ji an ce maza idan suka yi aure haushin iyayen gidansu suke ji. Amma ita sai ta
ji yana yabonta, tana cikin tunani ta ji ya ce.

"Dama zuwa na yi na nemi alfarma a wurinki." Ba ta kawo komai a kanta ba ce.
"Alfarma kuma Daddyn Mami? Wacce iri kenan?"

Gabansa yana faÉ—uwa, ya zaro kuÉ—i daga aljihunsa ya dire a gabanta. Muryarsa tana rawa ya
ce.
"Amm... dama... so nake ki sayar mini da kwanaki bakwai."

Dum! Ta ji kanta a saman kanta kamar an buga mata guduma, wani abu ne ya turniƙe mata
ƙirji. Murya a ɗan sarƙe ta ce.
"Ban... ban gane ba." Kunya ce ta kama shi, amma har cikin zuciyarsa yake jin ba zai iya ɓata
wa Shukura rai ba, uwa-uba ba ya son yin nesa da gangar jikinta. A tattaro mayafin jarumta ya
yafa wa kansa sannan ya ce.
"Ina nufin ki sayar mini da kwana bakwai na ƙara a wurin Shukura." Ya ƙarasa maganar yana
satar kallonta. Haɗe fuska ta yi tamau, rai a ɓace ta ce.

"Ban amince ba Alhaji."

Ransa ne ya fara ɓaci, don haka ya ɗauki kuɗin ya ɗora mata a cinya ya ce.
"Shi ya sa na kawo miki dubu hamsin ga shi nan, kwana bakwai fa kawai zan ƙara haba
Hajiya." Ya ƙarasa maganar a ɗan tsawace. Da mamaki take kallonsa ita ma, don ta sake ɓata
masa rai sai ta ce.

"Ka É—auki kuÉ—inka ba na so, kuma kwana ban lamunce ba."

Da sauri Alhaji ya ce, "Au haka kika ce? Ke wacce irin mace ce ne wai? Shekara nawa muna
tare da ke kawai don na ce ki ƙara mini kwanaki za ki ɗaga wa kanki hankali? Yarinyar nan fa
'yar cikinki ce, don Allah ban da abin mata kishin me za ki zauna kina yi da ita?"

Shiru Hajiya Karima ta yi har lokacin ba ta daina bin sa da kallo ba, zuciyarta ta fara wassafa
mata abubuwa da dama.
'Kada ki yarda, idan kika amince masa wallahi daga ranar yarinyar nan za ta raina ki.'

'Ki yi haƙuri ki kyale shi ya yi kwanakin da yake so, 'ya'ya gare ki idan kika biye wa namiji ba
kunya gare shi ba. Zai iya aikata abin da zai shafi tarbiyyar yaranki ko kuma ya sa su fahimci
rashin jituwa a tsakaninku.'

Shawarar ƙarshe da zuciyarta ta ba ta, ta ɗauka don haka ta ce.
"Shi kenan babu damuwa, kwana bakwai ai kamar yau ne." Washe baki ta ga ya yi, ya matsa
kusa da ita ya rungumo ta ya ce.

"Yawwa ko ke fa Hajiya, idan kika kwantar da hankalinki Shukura ba baƙuwar zafi ba ce.
Yanzu akwai abin da kika buƙata ne?" Girgiza masa kai ta yi a sanyaye ta ce.

"Babu abin da muke buƙata."

Miƙewa ya yi ya fice daga ɗakin, ya nufi ɗakin Shukura. A kwance ya same ta, ya rungumo ta
ya ce.
"Baby ta amince."

Da sauri Shukura ta riƙe shi ta ce.
"I love you Babyna." Fake ya sakar mata a goshi ya ce.

"I love you too my baby."

Ɗan lumshe ido ta yi ta ce, "To amma idan mun gama yau ina son shaƙatawa, almost six days
kenan fa ina gida Baby." Shiru ya yi ya ce.

"Don't worry baby, idan wannan ne an gama."
Farr Shukura ta yi da ido sannn suka cigaba da hirar soyayya.

Ummou Aslam Bint Adam🌚
07062062624

[17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO*

©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

GargaÉ—i: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko

É—orawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma,
don haka a kiyaye.

Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka
arashi ne.
https://chat.whatsapp.com/IAZVt2Pz4LvIcklCxSTHwo

SHAFI NA HUÆŠU

A daren ranar sai da Alhaji ya fita da Shukura, ba su suka dawo ba sai da dare ya tsala. Don
gabaÉ—aya yaran gidan sun yi bacci sai Hajiya Karima ce ta ji motsin shigowarsu, shiru ta yi tana
mamakin wai ita ce yau Alhaji ya sayi kwana a wurinta. Murmushin takaici ta yi tana jin hawaye
mai ciwo yana zubo mata, ganin tunani zai yi mata yawa ya sa ta É—auki carbi ta kwanta da shi
tana lazumi har bacci ya yi awon gaba da ita.

A washegarin ranar ma da yake Ruƙayya ba ta da lecture ta safe ita da Mommynta suka shiga
kicin suka sarrafa abin karyawa. Kuma a ranar ne Hajiya ta ci alwashin yi wa Alhaji magana
dangane da girki, tun da ta yi mata na kara wato girkin sati É—aya. Tana son ta ji idan raba girki
za su yi, ko kuma haÉ—ewa za su yi. Su Shukura ba su fito ba sai kusan sha biyun rana, a lokacin
yaran gidan duka sun tafi makaranta. Hajiya Karima tana zaune a falo tana kallo suka shiga,
gaisawa suka yi da Alhaji sai washe baki yake yana haba-haba da ita. Shukura ba ta gaida ta
ba, sai ita ce ta gaishe ta. A yatsine Shukura ta amsa mata, Hajiya ta yi kamar ba ta ga irin
kallon rainin da take yi mata.

Kwanciya Shukura ta yi a jikin Alhaji ta ce, "Baby yunwa nake ji." Jin haka ya sa a birkice Alhaji
Ya ce.
"Hajiya ina abincin ne?"

Sauke ajiyar zuciya ta yi ta ce, "Yana kicin." Miƙewa ya yi da kansa ya shiga kicin ya ɗauko
musu ya ajiye, har zai zuba musu Shukura ta maƙale kafaɗa ta ce.
"Mu je can mana baby sai na fi sakewa."

Kamar wanda ake ba wa umarni haka ya yi zumbur ya miƙe zai fita, cikin sauri Hajiya Karima ta
ce.
"Alhaji ina son magana da kai." ÆŠan satar kallon Shukura ya yi sai ya koma ya zauna. Hajiya
Karima ta ce.

"Dama game da girki ne, na ce za a haÉ—a girki ne ko kowa zai yi nasa? Saboda ina son sani
ne don Shukura ta karɓi girkint." Shiru ya yi yana son jin abin da Shukura za ta faɗa, don yana
gudin ya ɗauki wani zaɓin ta ce bai yi mata ba, Hajiya kuma ta ga kamar zaɓin Shukura yake
bi.
"TabÉ—i, gaskiya ba zan iya girkin haÉ—aka ba. Duka yaushe na zo da zan fara girka uwar

tukunya, kowa dai ya yi nasa kawai shi ne magana." Shukura ta furta cike da tsiwa, jinjina kai
Hajiya Karima ta yi tana jin zuciyarta na zafi. Kasa daurewa ta yi ta ce.

"To ai kin san yana da tawagar kika aure shi haka." Kamar Shukura tana jira ta ce.
"Eh saboda shi mijin mace huÉ—u ne, kuma don na aure shi ba shi zai sa na yi wa 'ya'ya bauta
ba."
Hajiya Karima za ta yi magana Alhaji ya ce.

"Yanzu dai duk ba wannan ba, shi kenan kowacce ta yi girkinta ina ganin haka zai fi." Amsawa
Hajiya Karima ta yi ta miƙe ta shiga ɗaki, taɓe baki Shukura ta yi ganin Alhaji zai bi Hajiya
Karima ya sa ta riƙe hannunsa suka nufi ɗakinta.

Alhaji Umar mai leda shi ne cikakken sunan Daddy, asalinsa mutumin Jigawa ne. Neman kuÉ—i
ne ya kawo shi Kano, shi da Hajiya Karima auren saurayi da budurwa aka yi musu, mahaifinta
da mahafinsa duka abokai ne. Don haka aka haÉ—a su aure a wancan lokacin, lokacin da aka yi
aurensu Alhaji dako yake yi a kasuwar singa da ke Kano. Rashin wadataccan ƙarfi ya sa bai
kawo Mommy a lokacin ba, har sai da ya ta haifi Ruƙayya (Mami). Da yake a lokacin ya ƙara
samun cigaba ya zama yaron shago. Daddy mutum ne mai zuciyar nema, kuma a tsaye yake a
kan iyalinsa daidai gwargwado. Ba za ka saka shi a cikin sahun hamshaƙan masu kuɗi ba,
kuma ba zai shiga sahun talakawa ba. Shi mutum ne mai rufin asiri daidai misali, yana da
dukiya mai yawa da kadarori.

Hajiya Karima macece mai haƙuri da zurfin ciki, tun asali ba ta da hatsaniya. Zamanta da Alhaji
ne ya sa a haka ake ganin ta yi baki, duk da wanda bai santa a baya ba zai dinga yi mata kallon
marar son magana.
Haihuwarta takwas da Alhaji Umar biyu sun rasu, sai guda shida da suke raye. Ruƙayya ita ce
babba tana shekara shirin da huÉ—u, sai Haidar yake bin ta. Shi kuma tsiran shekara É—aya ne
tsakaninsu da yake kwanikar haihuwarsu ta yi. Sai Nabil, Nazir, Sadik da kuma Sulaiman É—an
autanta mai shekara goma. Lokacin da Alhaji ya yi aure bikin Ruƙayya saura wata biyu, don
haka take ta Allah-Allah ta bar gidan ko ta rage ganin kayan takaici. Ita da Haidar gabaÉ—aya
suna level 400 a makarantar Maitama Sule University da ke Kano, Nabil da Nazir kuma sun yi
candy neman Admission suke yi. Sai Sadik da yake ƙaramar sakandire, shi kuma Sulaiman
yana ajin ƙarshe na firamare ba.

Tun da Alhaji ya raba girki kowa ya koma yin nasa, don haka wani lokacin sai a shafe wuni
guda wani bai ga wani ba a cikinsu. A haka kwanaki suka dinga shuÉ—ewa har Alhaji ya dawo
É—akin Mommy, yanayinsa babu yabo babu fallasa. Sai dai ta lura wuni Shukura ta yi tana shige
da fice a gidan tana ɓace-ɓacen rai. Ita Hajiya abin har mamaki ya bata, saboda gani ta yi har
idan kishi ne ai ita ya kamata ta nuna kishinta. Tun da ita ta shafe shekara da shekaru da shi
suna tare. A daren ranar da Alhaji ya dawo É—akin Mommy cikin dare suna kwance suka ji ihun
Shukura, daga Daddy har Mommy rige-rigen fita suka yi don ganin abin da ya faru. A tsaye
suka same ta daga ita sai wata yaloluwar rigar bacci, samarin gidan da su Ruƙayya ne su ma
duk suka firfito. Ganin yanayin da take ciki ya sa su Haidar suka koma ɗaki, kallo ɗaya Ruƙayya

ta yi mata ta saki tsaki har sai da Shukuran ta waigo suka haɗa ido, sannan Ruƙayya ta yi
tafiyarya É—aki.

"Me ya faru kike ihu Shukura?" Daddy ya furta cikin kulawa. Kuka ta rushe da shi ta ce.
"Ina kwance kawai na ji an shigo mini ɗaki, ban yi aune ba na ji an fara jan zanin jikina ƙasa."
Cikin sauri Daddy ya ce.
"Shigowa? ÆŠakin naki aka shigo?" GyaÉ—a kai ta yi tana cigaba da kuka, haskawa ya fara yi ya
ga ko ina a rufe kamar yadda yake. Ya haske saman doguwar katangarsu bai ga alamar za a
iya hawa ba, haka daga ƙofar da za ta sada ka da babban gate a datse take. Cikin mamaki
Dadday ya ce. "Ko dai mafarki kika yi Shukura?"

"Ni babu wani mafarki, bayan ana ji na yi ihu na ji an fito da gudu kuma ba fita aka yi ba a cikin
gidan nan ne."
Wani irin ɓacin rai ne ya dira a zuciyar Hajiya Karima, don ta fahimci sarai makirci ne da tuggu
za ta yi wa yaranta. Rai a matuƙar ɓace ta ce, "Ke yarinya ki shiga hankalinki, wallahi kada ki
kuskura ki saka yarana a cikin makircinki."

"To ni me nace? Na ce 'ya'yanki ne suka shigo? To ko dama can haka yaran na ki suke?"
Shukura ta yi maganar tana narkewa, a zafafe Hajiya Karima É—ago za ta yi magana Alhaji ya
ce.
"A'a Hajiya ki dai bari a gama jin bayaninta, da kike musawa Shukura yarinya ce da za ta yi
ƙarya ne?" Jikin Hajiya Karima wani irin sanyi ya yi, ta zuba wa Alhaji ido cike da mamaki.

GIDAN HAFIZ
Sai da 'yan kawo amarya suka watse sannan Hafiz ya shiga gidan cikin shigar angoncinsa ta
babbar riga. ÆŠakin Bilkisu ya fara shiga, ya same ta a kwance a kan gado idanunta duk sun
kumbura alamun ta ci kuka ta more. Duk sai ya ji tausayinta ya kama shi, zama ya yi a bakin
gadon ya ce.
"Ummu Sayyid." ÆŠagowa ta yi ta dube shi, sai ta ga ya yi mata wani irin kyau. Nan take kishi
ya mamaye ta, hawaye ya fara zuba daga idonta. Hannu ya saka ya goge mata, tana jin
hannunsa ba ta hana shi ba. Cikin tausasawa ya ce, "Zo mu je falo." Girgiza masa kai ta yi ta
ce.
"Ba zan iya ba Abban Sayyid."

"Don Allah ki daina kukan yana damuna." ÆŠagowa ta yi ta zuba masa ido ta ce.
"Yanzu fa wurin wata za ka tafi ko? Dama Hafiz za ka iya mu'amala da wata macen bayan
ni..."

"Don Allah ki daina wannan maganar Bilkisu, ki taso mu je please." A sanyaye ta zuro
ƙafafuwanta ƙasa, ta ɗauki hijabi ta saka tana goge fuskarta. Ɗakin Amina ya shiga ita ma ta

kira ta, Bilkisu tana ganinta gabanta ya shiga faÉ—uwa. Nasiha Hafz ya fara yi musu, jin ba za ta
iya danne abin da yake cikin zuciyarta ba ya sa ta miƙe fuuuu ta shige ɗaki. Girgiza kai Hafiz ya
yi, ya ce Amina ta koma É—akinta, sannan ya shiga É—aki wurin Bilkisu. Yana shiga ya hango ta ta
cusa kanta cikin ƙafafuwanta, ƙarasawa ya yi gabanta sai kawai ta ɗago ta rumgume shi ta saki
sabon kuka. Riƙe ta ya yi sosai, musamman yadda ya ji jikinta yana rawa. Murya a dashe ta ce.

"Mutuwa zan yi."

"Ki daina faÉ—in haka Bilkisu, ke fa musulma ce don Allah ki É—auki wannan auren a matsayin
ƙaddara."Hafiz ya furta cikin lallashi, sannan ya ajiye mata ledar kazarta da lemuka. Sallama ya
yi mata har ya juya zai tafi ta ce.

"Au da gaske wurinta za ka je?"

Shi maganar ma dariya ta so ba shi, don ya lura wani abin da Bilkisu take yi kamar ba ta cikin
hayyacinta. Ya waigo ya ce.
"Eh." Sai hawaye ya cigaba da zuba daga idonta cikin kuka ta ce.
"To ka je duk abin da ka yi mini, Allah ya yi maka Hafiz kuma ka zo ka É—auki tsinanniyar
kazarka ba na ci." Ta ƙarasa maganar tana yin jifa da ledar da ya ajiye. Hafiz bai kula ta ba ya
wuce ɗakin Amina, sai da ya ba ta haƙurin jimawar da ya yi sannan suka shiga gabatar da abin
da yake gabansu.
Kamar wata wacce aljanu suka kama haka Bilkisu ta dinga ɓurumtu tana shige da fice a tsakar
gida, kusan yadda ta ga rana haka ta ƙarasa ganin darenta. Da asubar fari ta ji Hafiz ya haɗa
musu ruwan wanka ya kai banɗaki, jin haka ya sake ɗaga hankalin Bikisu. Da ƙyar ta lallashi
kanta, ta samu ta gabatar sallar asuba.
Tun asuba ta shiga É—akin yaran ta dinga jibgarsu tana tashinsu sallah, abu kaÉ—an za su yi za ta
fara zaginsu tana duka. Tsakar gida ta fita, ta cigaba da kwaramniya da kwanuka tana fafutukar
É—ora abinci. Su dai yaran shiru suka yi, duk suka takure wuri É—aya. Tsoron mahaifiyarsu duk ya
kama su, sun san dai ranar asabar babu makaranta. Kuma sun ga sai shiri take yi tana musu
masifar su yi su ci abinci kada su makara, tsoron kada ta dake su ya sa suka gagara faÉ—a mata.
Don haka a ranar tun bakwai da rabi ta gama shirya su, ta ƙarasa ƙofar ɗakin Amina ta shiga
bugawa da wani irin ƙarfi.

Tun da Hafiz ya yi sallar asuba bayan ya leƙa Bilkisu da yara, ya koma ɗakin Amina ya kwanta
suka koma bacci. Suna tsaka da bacci suka ji bugun ƙofa a tsakar kansu, a hargitse ya fito
daga shi sai gajeren wando yana faÉ—in.
"Lafiya Bilkisu me ya faru

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login