Showing 12001 words to 15000 words out of 143522 words
Chapter 5 - DAHUWAR 'KAHO BOOK COMPLETE Hausa Novels By Ameera Adam.pdf
ne?" Kallon yanayin da yake ciki ya sake turnuƙe ta, a fusace ta ce.
"Ta ina za ka san abin da ya faru? Tun da ka saka mace a ɗaki kamar a kanta ka fara sanin
mace." Ko kaɗan bai ji daɗin furucinta ba, saboda ko babu komai yaransa suna tsaye suna
kallonsu.
Rai a ɓace ya ce, "Wai me yake damunki ne Bilkisu? Wacce irin maganar banza kike yi haka a
gaban yara ne?"
"Ƙarya na yi? Ba macen ka saka a gaba ba? To duk jarabarka sai ka fito ka kai yara
makaranta."
Bilkisu ta faɗa cike da kishi. Waigawa ya yi ya hangi yaran duk sun yi zuru-zuru, kallo ɗaya za
ka yi musu ka fahimci a tsorace suke. Ga su sanye da uniform da kulolin abinci, girgiza kai ya yi
a ransa ya ayyana tabbas Bilkisu ba ta cikin nutsuwarta.
"Dama suna zuwa makaranta ranar asabar ne? Ko kin manta yau asabar?" Shiru Bilkisu ta yi
cike da kunya, jin hayaniya ta yi yawa ya sa Amina ta ɗan turo ƙofar ta leƙo. Kanta babu ɗan
kwali ta sha ƙananan kitso mai kyau, ta yafa zanin rufa a jikinta.
"Ina kwana Aunty."
Ta furta a sanyaye, wani mugun kallo Bilkisu ta wurga mata kamar tana jira ta ce.
"Kada ki sake ce mini Aunty, ni ba yayarki ba ce. Me na haɗa da ke? Ai ƙanwata ba za ta taɓa
auren mijina ba." Waigawa Hafiz ya yi ya ce.
"Koma ciki."
Babu musu Amina ta koma ciki, ya riƙe hannun Bilkisu ya kai ta ɗaki ya zaunar a kan kujera.
Ƙasa ya yi da murya ya ce.
"Haba Bilkisu, me ya sa duk maganar da nake yi miki ba kya ji ne? Don Allah ki kama
girmanki, ba na son ki dinga abin da yarinyar nan za ta zo ta raina ki. Yanzu don Allah me kika
yi haka? Kin fa san yau weekend, yaran nan ba sa zuwa makaranta."
Idon Bilkisu ne ya ciko da ƙwalla ta ce, "To ai mantawa na yi." Hannu ya saka ya goge mata
hawayen, zai miƙe ta sake cewa.
"Yanzu shi kenan kuma ka daina sona." Shiru ya yi cike da damuwa, ya girgiza mata kai ya ce.
"Idan ana mata ɗari ko fi, duk wacce zan auro ba zan daina sonki ba Bilkisu. Don Allah kada
ki sa wannan a ranki, kin taɓa ganin namiji ya zauna da macen da ba ya sonta?" Girgiza masa
kai ta yi ta ce.
"To amma ai ga shi nan ka je ka kwanta da wata, shi kenan ta gama gane mini sirrinka."
Murmushi ya yi don ya san kishi ne duk yake damunta, ya matsa kusa da ita ya ce.
"Ke ce fa uwargida, ko kin manta ni da ke auren saurayi da budurwa muka yi? Duk wacce zan
yi mu'amala da ita fa a bayanki ne, kuma da kike faɗin haka ita ma fa matata ce. Ba wurin
macen banza na je ba, ko kin fi son na fara biye-biye a waje da na yi auren?" Girgiza kai ta yi,
ya zauna ya cigaba da lallashin Bilkisu har sai da ya ga hankalinta ya ɗan kwanta sannan ya tafi
ɗakin Amina.
A wannan ranar Hafiz ya ɗauka Bilkisu za ta yi abincin safe da su, bayan da suka yi wanka ya
fito ya tambaye ta kai tsaye ta ce ba ta girka da su ba, tun da ba ita ce da miji ba. Gudun tashin
tarzoma ya sa shi fita ya sayo musu shayi a waje, saboda ba a haɗa gas ɗin Amina ba. Sai da
suka karya sannan ya ɗauki silindarta ya tafi da ita ya ciko mata, a lokacin da ya dawo
'yan'uwan Amina sun zo da wasu tsirarin danginsa. Bilkisu kuwa tana ɗaki ko ƙurarsu ba ta bi
ba, don gabaɗaya dangin Hafiz ya shafa musu kashin kaji.
Yamma liƙis Hafiz ya kawo kayan miya ya ce Bilkisu ta gyara, a nan ma ta kafe kai da fata ta ce
ba za ta yi girki ba. Idan kuwa ta sarrafa ba za ta ba shi da amaryarsa ba, babu yadda ya iya
haka ya kai wa Amina. A lokacin da ya shiga ɗakin, zafi ya ji a jikinta na zazzaɓi saboda rashin
ƙwarin jiki, tausayi ta ba shi sosai. Don haka ya rage kayan jikinsa ya gyara kayan miyar ya ba
wa yara suka kai markaɗe, da kansa ya ɗora miyar ganin haka ya sa Amina ta miƙe cike da
rashin ƙwarin jiki za ta taya shi ya ce ta je ta kwanta. Cikin lokaci ƙanƙani ya ƙarasa miyar, ya ce
Bilkisu ta dafa taliya sai da ƙyar ya samu ta dafa ta miƙa musu.
Tun daga wannan ranar Amina ta karɓi girkin rana da na dare, na safe ne kawai kowa yake yin
na sa. Abin da Bilkisu ta tsira a cikin kwanakin amarcin Amina sai gari ya waye sai ta yi wa
yaranta wanka da sassafe ta saka su, su shiga ɗaki wurin mahaifinsu. Wani lokacin ma idan
suka shiga suna kwance a kan gado, haka Amina za ta sako hijabi ta janyo su falo. Babu wata
dama da suke samu ta kulawa da juna da safe ko da rana, matuƙar yaran suna gida. Idan kuma
yaran ba sa nan Bilkisu ta dinga yi musu habaici ta cewa Hafiz ya cika jaraba, ko ta ce ya auro
makira mai karuwancin cikin gida. A haka suka cigaba da tafiya tun abin ba ya damun Amina
har abin ya fara damunta, saboda akwai lokacin da rana Hafiz ya dawo suna ɗaki duk da sun
tura ƙofa sai ji suka yi yara sun shigo ɗakin da suke kwance.
"Lah Abba."
Sayya mai kimanin shekara uku ta faɗa ganin mahaifinta yana mu'amala da Auntynsu.
Ummou Aslam Bint Adam
07062062624
[17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko
ɗorawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma,
don haka a kiyaye.
Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka
arashi ne.
Alhamdulillah! Shin kunada labarin MG’s Beauty Lounge zai buɗe a ranar Litinin, 2nd June 2025
– daidai lokacin Sallah!
‘Yan mata da mata masu son kyau a Kaduna, lokaci yayi da za ku haskaka a wannan Sallah!
MG’s Beauty Lounge ya buɗe da kwalliya, tsafta da ƙamshi irin na sarauniyar zamani!
Ga abin da zaki samu idan kika ziyarce mu:
Gyaran gashi da kitson zamani
Kwalliyar Sallah mai ɗaukar ido
Wanke ƙafafu da pedicure mai sanyaya rai
Kayan gyaran fata na gaske
Lalle mai kyau da salo na zamani
Tura-turai, humra, incense da ƙamshi masu daɗi
Shirin amare da na musamman
Ba kawai gyara muke ba – kulawa ce ta musamman ga kowace sarauniya.
Zo ki ji daɗin wanke ƙafa, lalle, kwalliya, ki saya kayan kyau da ƙamshi – komai a wuri guda mai
kyau.
Adireshi: Block 21, Nnamdi Azikiwe by Makarfi Road, bayan gidan Indomie, kusa da Sorera
Restaurant, Kinkinau, Kaduna.
Tambaya/Booking:
WhatsApp: 08062991549
Kira: 09016108092 / 08064532391
Ki zo ki gani da idonki – ki ji daɗin sauyin MG’s Beauty Lounge.
Bi mu a IG & TikTok: @MGsBeautyLounge
SHAFI NA BIYAR
A razane Amina ta ja bargo ta rufe jikinta, haka shi ma Hafiz cikin sauri ya janye jikinsa daga
jikin Amina haɗe da rufe jiki. Ya haɗe fuska tamau cikin tsawa ya ce.
"Fita daga nan."
Ganin yadda mahaifinta ya birkice lokaci ɗaya ya sa ta fita da gudu tana kuka, miƙewa Hafiz ya
yi yana suturce jikinsa. Bai yi aune ba sai ji ya yi Bilkisu ta banko ƙofar ta shigo cikin masifa
tana faɗin.
"Uwar me Sayyada ta yi miki kika dakar mini ita take kuka, baƙar munafuka kin san ba kya
ƙaunarsu kika maƙale saboda kwantan da kika yi kika auri mahaifinsu." Ganin Amina ba ta falo
ya sa Bilkisu ta faɗa ɗakin za ta yi magana ta ci karo da su suna gyara jikinsu, wani baƙinciki ne
ya maƙure ta. Cikin zafin kishi ta ce. "Wannan wacce irin jaraba ce da rana tsaka salon ku ɓa ta mini tarbiyyar..."
"Fita ki ba ni wuri ba na son rashin hankali."
Hafiz ya katse ta a zafafe, yadda ya hautsine mata ya sa ta ja ƙafa ta fita don ta lura ransa a
matuƙar ɓace yake.
Amina da ke zaune a gefen gado kifa kanta ta yi ta fashe da kukan takaici, jiki a sanyaye ya
ƙarasa ya rungumo ta ya ce.
"Don Allah ki yi haƙuri Amina."
"Habibi na gaji, wallahi na gaji da abin da matarka take yi mini. Yanzu wanne irin abu ne a ce ni
da ɗakina ba ni da sirri, ina kwance da mijina dubi yadda 'yarka ta zo ta same mu? Wanne irin
kishi matarka take da shi, da har ta gwammace gara ta ɓata tarbiyyar yaranta? Wallahi matuƙar
ba za ka ɗauki mataki ba ba zan cigaba da zama a haka ba." Amina ta ƙarasa maganar tana
zubar da hawaye. Ya sani sarai Amina tana da haƙuri, don akwai abubuwa da dama da idan ya
ga Bilkisu ta yi mata ya san idan ita ce ba za ta yarda ba. Cikin lallashi ya ce.
"In Shaa Allahu haka ba zai sake faruwa ba, don Allah ki yi haƙuri babyna." Hawayenta ta
share tana gyaɗa masa kai, bakinta ya sumbata. Ya janyo ta yana yi mata raɗa a kunne, turo
baki gaba ta yi a shagwaɓe ta ce.
"Ni a'a, ba yanzu ba." Marairaicewa ya yi kamar zai yi kuka ya ce.
"Please, ai ba laifina ba ne da za a hukunta ni. Kuma kin san dai ba zan iya..." Sai kawai ya
kashe mata ido ɗaya, ɗauke kai ta yi ta alamar fushin wasa ta ce.
"Kuma hakan za ka haƙura ka bar wa dare, wai dama haka idonka yake a buɗe amma kafin
aurenmu kullum sai ka yi ta sunne kai ƙasa." Dariya ya yi sosai ya ce.
"To wancan lokacin da yanzu akwai bambamci ai, ni dai gaskiya ki san yadda za ki yi da ni."
Hararar wasa ta yi masa, sannan suka cigaba da ba wa juna kulawa.
A tsammanin Bilkisu tun da ta katse musu yanayin da suke ciki ta wargaza musu na wannan
lokacin, ta ɗauka Hafiz zai fito ya same ta da maganar ta yadda za ta ja shi da faɗa har ya ɓata
lokacin a wurinta. Jin shirunsu a ɗaki ya sake ɓata mata rai, don haka ta koma ɗaki ta cika fam
da ɓacin rai. Tana nan zaune ta hangi Amina ta fito ta shiga banɗaki, tana wuce babu jimawa
shi ma Hafiz ya rufa mata baya. Cikin suɓutar baki ta ce.
"Kan babban bala'i, wato ni za a gwadawa bariki ido biyu da rana. Hafiz saboda ya wulaƙanta
ni har wankan ma tare za su shiga?" Tana rufe baki sai hawaye ya fara zuba, don rabonta da
shiga banɗaki tare da Hafiz tun Sayyid yana ƙarami. Tana nan zaune ta ga Amina ta fito, bayan
wani lokaci shi ma Hafiz ya wuce ɗakin Amina. Sai da ya shirya cikin ƙananan kaya sannan ya
fito hannunsa riƙe da wayar caza, ya ƙarasa ɗakin yaran da suke wasa. Hannun Sayyada ya
kama duka biyun ya riƙe wuri ɗaya, ya shiga zabga mata wayar cajar a ƙafa da sauran jikinta.
Nan take 'yan'uwanta duk suka takure wuri ɗaya cikin jin tsoro, don sun ɗauka yana gamawa
zai koma kansu. Jin kukan Sayyada ya sa Bilkisu ta fito fuuu a fuskace ta kai hannu za ta janye
ta. Da wata irin muryar ɓacin rai ya ce.
"Idan kika taɓa mini 'ya ina dukanta wallahi sai kin tafi gidanku a yau." Janye hannunta Bilkisu
ta yi, saboda duk abin ta tana matuƙar son Hafiz, koda wasa ba ta son wani abu da zai raba ta
da shi. Kiran sauran yaran ya yi ya haɗa su wuri ɗaya, fuska a haɗe ya fara magana.
"Daga yau sai yau duk wanda ya kuma shiga ɗakin mamanku ko ɗakin Aunty amarya, ba tare
ya yi sallama ba sai na farfasawa mutum jiki. Sannan zan haɗa ku gabaɗaya, na kai can bolar
bayan gari na watsar. Idan ya so nan gaba sai mamanku da Aunty amarya su haifo mini wasu
yaran." A tsorace duk suka gyaɗa masa kai, cikin tsoratarwa ya buga musu tsawa da cewar.
"Kun ji me nace ko? Kuma idan kuka yi sallama sai kun ji an amsa an ce ku shigo, idan ba
haka ba wallahi dukan da zan yi wa mutum sai ya fi wannan." Baki yana rawa yaran suka amsa,
ya ɗauko alawa ya damƙa wa kowa a hannu sannan ya lallashe su cikin nasiha ya tashi ya fita.
Ɗakin Bilkisu ya shiga, saboda tun da ya yi mata magana ta yi zuciya ta fice ta tafi ɗaki. A
zaune ya same ta ta haɗe fuska, shi ma fuskar ya sake haɗewa ya ce.
"Bilikisu!"
Shiru ta yi masa ba ta amsa ba, ya dube ta ya cigaba da cewa.
"Ba zan zura ido ki lalata mini tarbiyyar yara ba, saboda kishin rashin hankalin da kike yi, daga
yau sai yau idan kika kuma tura mini yara ina ɗakin Amina ba tare da ƙwaƙƙwaran dalili ba sai
ranki ya ɓaci. Ni ba hana su shiga ɗakinta zan yi ba, amma ke ma ki san lokacin da za ki dinga
tura su. Wai duk wannan abin da kike yi na mene ne? Ba dai don kana da na yi mu'amala da ita
ba ne? To me ya yi saura yanzu? Na fahimci duk karar da nake yi miki da mutumtawar da nake
yi miki ba kya gani. Bari ki ji, yadda kike matata haka Amina take a wurina duk matsayinku
ɗaya, yadda kika san ni a matsayina na mijinki haka ita ma ta san ni. An faɗa miki kishi hauka
ne? Ke wanne irin abu ne ba ki yi ba a lokacin da yayanki zai ƙara aure, ba ke ce amara ba har
da ɗauko auko? Amma a kaf dangina wa ya taɓa zuwa gidan nan ya nuna miki yana farinciki da
auren da zan yi, duk suna yi ne don su yi miki kara ba wai don ba sa so ba ne.
Wallahi tun wuri ki dawo hayyacinki, ina faɗa miki haka ne tun ba ki ƙure yarinyar nan ba. Idan
kika buɗe mata ido nan gaba ba za ki ji daɗin zama da ita ba."Hafiz yana gama magana ya fice
daga ɗakin rai a ɓace.
Wannan faɗan da Hafiz ya yi wa Bilkisu da yaransa su Sayyada, shi ya sa Amina ta samu
'yanci sakata ta wala a ɗakinta. Don idan Hafiz yana nan, tana samun damar saka ƙananan
kayanta masu jan hankali da rigunan bacci. Saɓanin a baya da take saka manyan kaya, gudun
kada yaran su shiga su ga shigar da ba ta dace a jikinta ba. A ranar da Hafiz zai koma ɗakin Bilkisu tun safe take cikin annshuwa tana walwala. Hatta
Amina da ba wata hirar suke yi ba, ta fahimci walwlarta. Tana zaune bayan la'asar ta ji sallamar
Aunty Murja da Na'ima, duk da Amina ba ta sansu ba amma fuska a sake ta amsa sallamarsu
tana yi musu sannu da zuwa. Fuska a sake su Aunty Murja suka amsa mata, suna cikin
gaisawa Bilkisu ta leƙo a fusace ta ce.
"To tsaiwar me kuke yi Aunty Murja ku shigo mana." Ƙarasawa suka yi ɗakinta, sai da suka
gaisa Aunty Murja ta ce.
"Oh ashe kuma haka abu ya faru Bilkisu, ni ai ina zaune rannan katsam Abban Sajida yake
faɗa mini wai Hafiz zai yi aure. To daga baya kuma na ji an ce ba za ki yi wuni ba, don dama
cewa na yi zan zo ƙafa da ƙafa. Da muka ji ba wuni sai kawai na cewa Auntyn yara ta bari ma
zo daga baya." Taɓe baki Bilkisu ta yi ta ce.
"Tsinanniya gata can ai, an kawo ta baƙar daga. Sai ta zo ta ci uwar da nake ci." Aunty Murja
murmushi ta yi, ta tuna irin habaici da cin kashin da suka dinga yi mata. Sai kawai ta ce.
"Allah Ya haɗa kanku, ya sa zuwanta alheri ne."
"Haba Aunty Murja, kin taɓa ganin zuwan kishiya ya zama alheri?" Bilkisu ta faɗa cikin sauri,
sunkuyar da kai Na'ima ta yi. Aunty Murja ko kaɗan ba ta ji daɗi ba saboda Na'ima tana wurin,
don haka ta miƙe ta ce.
"Mu bari mu wuce yawon namu da yawa, za mu leƙa barka matar yayan Auntyn yara ce ta
haihu."
Mamaki ne ya kama Bilkisu ganin yadda Aunty Murja ta ɗauki kishiya kamar wata ƙanwarta.
Har soro ta raka su, Na'ima ce ta fara fita. Cikin sauri Bilkisu ta kamo hannun Aunty Murja ta ce.
"Aunty Murja wai kishiya kike yi wa wannan haba-habar? Salon kina zaune ta zo ta raba ki da
mijin? Ai wallahi ni da kishiya sai dai kallon banza." Murmushi Aunty