Showing 33001 words to 36000 words out of 112612 words

Chapter 12 - BABBAN GORO BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY SUMAYYA TAKORI.doc

sidik mai santsi da sheki.
Yana jin kansa cikin wasu mutane kalilan masu sa ar samun duk abinda suke so a rayuwa, tunda Allah Ya mallaka mishi abin da rai da zuciyarshi ke so, tsayin shekaru goma sha tara. At last, ya samu. Don haka ba shi da abin da zai ce da mahaliccin shi sai godiya, da neman dadin falalarsa da ni imarsa.
Karfe shida da rabi ya shigo garin Gwamna, don haka kai tsaye alwala ya yi a harabar gidan ya wuce masallaci don samun jam in maghariba.
Mami ta kwankwasa kofar dakin da ta ji an kulle da makulli, Safah ta zo ta bude, sanye take da  shirt da wando samfurin polo kalar ruwan zuma, ta matse gashin kanta daga tsakiya.
Mami sai ta ga  yarta ta kara kyau na ban mamaki. Ko da yake hasken amarci daban ne, ta yi murmushi ta ce,  Mene ne na sanya mukulli a kofar?
Ta ce,  Haka nan .
Mami ta sake yin murmushi, ta san don wanda ake kulle kofar. Tunda aka tafi kai Marwah Zaria tun shekaranjiya ko falo ba ta kara lekowa ba.
A dakinsu take hidimominta ta kulle kanta ba ta son yin mu amala da kowa. Daga Mami har angon babu wanda ke shiga sabgarta, shi ba ya garin ma tun wayewar garin litinin ya wuce Abuja, inda yake fafutukar bisar ta da passport dinta da ya amsa wurin Mami.
Ta ce,  Fito maza ki tayani aiki, ai tunda Marwah ta tafi na san na yi rashin mai taimaka min a kichin .
Ta yi rau-rau da ido kamar za ta yi kuka ta ce,  Kai Mami ni bana tayaki?
Ta ce,  Da yaushe da yaushe kike taya nin? Kin ga bana son dogon turanci wuce muje .
Haka tasa ta a gaba har kicin tana cewa,  In ban da Imam din wa zai iya zama dake? Ga kiwa ga son jiki, ga yawan kwanciya kamar mage, bakya um bakya um-um kamar wata jikakkiyar tsumma.
Ayi mace sai ka ce namiji, daga takarda sai biro? Ko huda-huda yana samun lokaci ya shiga cikin  yan uwansa ya yi mu amala mai dadi dasu.
In bakya hutar da idanuwanki in kin tsufa za ki samu matsala dasu kin ji na gaya miki .
Ta rausayar da kai ta ce,  Nice zan tsufa Mami?
Ta ce,  A a, ba za ki tsufa ba tunda hurul-eeni ce?
Ta yi smiling har wushiryarta da jerarrun hakoran suka fito. Ta taimakawa Mami suka hada abincin dare mai rai da motsi suka jera a dining, sauri take a gama ta gudu kada Imam ya zo ya same ta wanda take Allah-Allah ranar tafiyar shi ta zo ya bar gidan ta huta, don bata da masaniyar yaushe zai tafin.
Dan halak din kuma dan gatan Mamin sai ga shi ya shigo cikin takunshi na sassarfa ya shigo kicin din.
Daga bakin kofa ya tsaya yana kare mata kallo kamar bai san ta ba. Daga Mami har ita babu wanda ya san da shigowar sa, hirar su suke suna dariya.
Sai da ya kalle ta son ransa sannan ya yi gyaran murya ya ce,  Mami wane delicious ake shirya mana ne? Irin wannan  aroma haka tun daga bakin get?
Tana murmushi ta ce,  Duk naka ne, na san ka tunda ka bar gida ba za ka tsaya ka ci wani kwakkwaran abinci ba sai shirme wanda baya rike hanji .
Ya yi dariya kadan ya ce,  Mami kina sangarta ni, sai na tafi inda bani da gata in yi ta ragaita.....
Ta ce,  Ga shi kuma Allah ya baka makiwaciyar mata, ya ya za a yi kenan?
Ya kai duban shi ga sashen da take, idanunshi a sanyaye, ta hade fuska ta yi murtuk kamar hadari, kai ka ce tunda aka halicceta ba ta taba dariya ba sai hura hanci take.
Ya girgiza kai ya ce,  A haka zan yi maneji Mami, an ce  da babu.....
Ta karasa mishi  .....Gara babu dadi! .
Ita dai ba ta tanka musu ba, karewa ma ko inda yake ba ta kalla ba ta tsallake su za ta wuce. Muryarshi ta yi kasa so cool ya ce,  Kin gani ko Mami za ta tafi ta kulle kofa saboda ga dodonta ya zo....
Ita ma Mamin ranta babu dadi, tausayin Imam take ji sosai. Ciwon kana so ba a sonka matukar ciwo ne da shi.
Ta ce,  To ya zan yi muku ne Almustapha? Ita taurin kai, kai kuma baka iya lallashi ba .
Ya ce,  Wallahi Mami ba zan zauna ina lallasarta ba, ai sai ta raina ni .
Ta yi dariya ta ce,  Ka daina cika baki IMAMU-ALMUSTAPHA, ranar rarrashin ba ta zo bane, amma tana nan tafe .
Ya ce,  To Mami ke ki lallasar min ita man ko  yar hira ce ta bari mu yi kafin in tafi? Kin san halin rai& ...
Mami ta katse shi da cewa,  Ni nake maka auren da zan je ina maka bambadanci? Tunda ka ce ba za ka yi ba, to ku yi ta zama a yadda kuke, ruwan ku.
Lafiya za ka je ka dawo insha Allahu, ka zo ka same mu cikin alheri da koshin lafiya kamar yadda ka barmu .
Ya tayata da daukar warmers suka fito. Masallaci ya koma don yin sallar isha i, inda ya tarar da Daddy suka yi sallar tare sannan suka shigo cikin gidan suka nufi tebir din cin abinci.
Daddy ya dago yana kallon su ya ce,  Wai ina Safah ne?
Shahida ta ce,  Tana dakinsu .
Ya ce,  Kirawo ta .
Har ta yi shirin barci cikin wasu tausasan nighties bakake wuluk, tana tufke gashin kanta yadda zata ji dadin kwanciya. Shahida ta kwankwasa kofar, daga ciki ta ce,  Waye?
 Idon matambayi ne . Shahida tace a kufule.
Ta bude kofar tana dariya ta ce,  Ki zo Daddy ke kiran ki .
Ta yafa mayafi ta bi bayanta tana kunkuni, ita an dame ta.
Shahida ta ce,  Ki ce ba za ki je ba mana short and simple....
Ta tura baki ta ce,  To ban ce ba .

Daddy ya bita da kallo har ta zauna a jikin Mami, gaba daya ta rame ta yi sanyi, tausayin ta ya kama shi.
Sai dai ta wani fannin ya fi jin tausayin Imam din da ya kallafa burin rayuwarshi da soyayyar shi a kanta tun haihuwarta. Ya rasa mene ne aibun dan shi da ta kasa son shi. Shi kuma ya rantse har bayan ransa ba zai ta da wannan aure ba.
Cikin kulawa ya ce,  Baki da lafiya ne?
Ta girgiza kai,  Lafiya ta kalau .
Daddy ya ce,  Gobe ne za ki koma makarantar?
Ta daga mishi kai.
Ya ce,  Ki yi min magana mana, sai daga min kai kike kamar kadangaruwa...
Ta ce,  Eh, amma  hostel zan koma, ba zan iya zama ni kadai a gidan ba .
Ya dube ta yana kiyasi ya ce,  To mene ne fa idar komawar taki tunda barin makarantar za ki yi gaba daya?
Hawayen da take tattali suka kwace, tsoronta Allah, tsoronta kada ace ta bi Imam, ta ce,  Don Allah Daddy a barni in yi karatuna, na yi nisa kuma ina jin dadin sa....
Ya ce,  To, mene ne abin kuka a nan? Kin san dai yanzu ba mu da iko dake sai yadda mijin ki ke so .
Ya juya ga Imam wanda kanshi ke kan wayarshi yana danne-danne kamar bai jin su, ya ce,  Yaushe za ka tashi?
Ba tareda ya dago daga abinda yake yi cikin wayar ba Ya ce,
 Gobe da asubah insha Allahu .
Ya ce,  To in zai yiwu ka kara kwana daya don ku samu lokaci ku yi shawara a junanku .
Ya ce,  Ni Daddy duk yadda ka yi daidai ne .
Ya yi murmushi ya ce,  Saboda kana tsoron ta? To in gaya maka ba a sakarwa mace ragamar kanta, ka zama namijin duniya ma abocin gwagwarmaya da rayuwa kala-kala. Kada ka bari soyayyar da ke zuciyarka tasa ka kasa tankwara iyalin ka.
Ku tashi ku je ku yi shawara a tsakanin ku abin da kuka yanke gobe ku sanar dani .
Da haka taron ya tashi kowa ya nufi dakin sa. Sai dai har zuwa washegari babu wanda ya nemi dan uwansa tsakanin Safah da Imam.
Ita taurin kai da rashin son duk wata alaka da za ta hada ta da Imam din. Sai ta hadu da wanda ya dame ta ya shanye wajen rashin son wargi da miskilanci.
Imam irin mazan nan ne da duk soyayyar da suke yiwa mace, ba za su lamunci ta raina su ba. Sannan bai taba barin ka gane  weakness dinsa akan soyayyah. Shi Imam ko yana matukar son abu, da wuya ka gane sabida rashin son raini ya ratsa. Sai a inda yasan za a yi maraba dashi, da abinda zuciyarsa ta zo dashi ko ta ke kunshe dashi. Mami kadai yake iya gayawa cikinsa. Kamar ba ita ta haifi Safan ba.

Abun duniya ya taru ya yiwa Safah yawa, ga kewar  yar uwarta, ga hukuncin da Daddy ya yanke mai nuni da cewa, in har tana son karatun ta sai da amincewar mijinta.
To ina ta ganshi balle ta tambaye shi? Shi wani irin mutum ya zame mata yanzun mai wuyar sha ani ba kamar sanda yake yaro ba. Ta manta shekaru kan canza mutum. Kana girma ne kana kara sanin ciwon kan ka. Ba ya shiga sabgarta, ba ya zuwa inda take tun daga ranar da aka daura musu aure. Harkokin gabansa kawai yake, hankalin sa a kwance
Ga shi ita ko lambar wayar shi bata sani ba. Dole ta tsaga billenta ta tambayi Aunty Shahida, don ta san agogon dake like a bangon dakin ta, dana swatch din dake daure a hannun ta na hagu, ba karya suke gaya mata ba; saura  yan awanni kalilan Imam ya bar Nigeria da igiyoyin aurenta, da igiyoyin karatun da ta sha matukar wahala akai. Ba da bata lokaci ba ko tambayar dalili Shahida ta bata.
Ta zuba su cikin wayoyin ta da Zahraddeen ya bata, wadanda dasu take amfani har yanzu, don ranar daurin aure ta bawa Badar ta ce ta neme shi ko cikin mutane ne ta bashi, amma ya dawowa Badar dasu ya ce ta ce mata ta rike ya bar mata duniya da lahira.
Karfe hudu na yammacin ranar ta yi zugum rike da wayoyin a hannunta ta rasa ta inda za ta fara mishi magana, kira za ta yi ko tedt za ta yi?
Duk wani tunaninta ya kare ne a kan cewa idan ta yi mishi tedt ko kira, ya tabbata ta dauke shi a matsayin miji kenan.
Bayan ta gama cewa bata son shi a matsayin miji, kuma haka abin yake har gobe a ranta, sannan ba ta san irin karbar da zai yi mata ba, don ta lura green snake ne, ta ruwan sanyi suke ladabtar da zuciyar diya mace, ba ta lallashi da tarairaya kamar Zahraddeen ba.
Da ta ga duk wannan ba zai mata ba, ga lokaci yana ja, kuma ta ji yana gayawa Mami jirgin  Cathay-Pacific zai bi karfe takwas na dare, ga shi yanzu karfe biyar na yamma. Sai ta saduda ta soma yin tedt din fuskarta kamar ta fashe da kuka.
Yana hada kayan shi cikin troller a lokacin da ya ji alamar shigowar sako cikin wayarshi. Mami ta aiko Shahida da kilishi da dambun nama mai yawa ta ce ya hada a kayan.
Hajiya Maama kuma gireba ce bokiti guda ta kawo mishi, don yana son gireba sosai.
Yana murmushi ya karbi sakon Mami ya yi masa mazauni kusa da na Hajiya Mama, ya ce da Shahida,  A ce da Mami, na gode! .
Har ta kai bakin kofa ya kira ta, ta dawo ta zauna. Ya ce,  Safah me take yi yanzu?
Ta ce,  Wallahi ban sani ba, rufe kofar take yi .
Kamar ba shi ba, saboda yadda muryarsa ta yi kasa sosai, ta nuna wani mutum mai azabtuwa a cikin soyayyah matuka. Yanayi ne da Shahidah bata taba ganin dan uwanta a ciki ba (rauni) Ya ce,
 Shahidah don Allah, a matsayin ki na mace mai shekaru fiye da kannenki, kuma shakikiya agareni wadda nake da tabbacin bazata gaya min karya don inji dadi ba ta boye gaskiya don na cutu ba, ina da wani aibu ko wani hali mara kyau ne da Safah ta kasa so na?
Tausayin dan uwanta ya kama ta, ta ce,  Wallahi-wallahi ka ji rantsuwar musulmi kenan, baka da shi .
Ya ce,  To a ganin ki mene ne matsalar?
Ta runtse ido ta ce,  Ya Imam shi SO ba a nan yake ba. Dubi Zahraddeen ai bai kai ka ba, ka fi shi komai, amma ta so shi.
Shi ya sa tun farko na yi fatan a ce ina ma MARWAH ka nema, don ita ce mai yi maka soyayyar aure ta gaskiya& .....
Ya bude baki yana kallon ta ya ce,  who told you? (Wa ya gaya miki)
Dariya ta yi  Na san komai, kada ka manta kannena ne, tare muke rayuwa, kuma na fi su hankali, sannan duk wani takunsu a kan idona suka yi shi tun haihuwar su har girmansu. Abobe all, (sama da komai) I m far more sociologistic than a political scientist.
Marwah ce take yi maka e-mail ba Safah ba. Marwah ce take baka greeting cards da sunan Safah, Marwah ce take yi maka asirtacciyar soyayya wadda babu son zuciya a cikinta, domin ta yi juriyar da har yau,  yar uwarta ba ta taba ganewa ba .
Ya ce,  Me yasa tun a lokacin baki gaya min ba?
Ta ce,  Ta yaya zan gaya maka alhalin lokacin idon ka ya rufe da soyayya? Baka ji ba ka gani balle ka gane inda ake maraba da soyayyar taka? Ta yaya zan shiga tsakanin  yan uwa biyu? Karewa ma wadanda suka fito duniya tare a lokaci daya?
Ya yi murmushi kadan ya ce,
 Ni ban sani ba, kuma ko da na sanin ba abin da zan iya. Safah kawai nasan rai da zuciyata ke so a fadin duniyar nan, kuma ita za su ci gaba da so har duniya ta nade.
Zan yi maneji haka Shahidah, kuma ina ji a jikina watarana na zuwa da zata so nin, musamman idan muka haihu tare, wuyarta mu kasance karkashin inuwa daya, shine mai wuyar kuma ya tabbata. Nidai na san bazan tsaya ina lallashin ta ba ta so ni, ai sai ta raina ni, Shahida dariya ce ta kama ta tace a ranta  Ya Imam ho! Son girma kamar gyambo. Wane raini ne kuma ya saura tsakanin miji da mata? Ai da daban, yanzu daban babu zancen discipline sai unity and cooperation. A fili kuma ta ce,
 Yayana! .
Ya dago ya dube ta.
 Safah fa ba kai ne ba ta so kwata-kwata ba, I m sorry to say....... kai ma kana da laifi, mutum ne kai, tough& &  .
Ya saki rigar da yake ninkewa ya dan fiddo ido ya ce,  Ni din?
Ta ce, (cikin dariya)  Kwarai, baka lallashi, tarairaya da nuna zahirin soyayyar ka.
Ba haka Zahraddeen yake ba, mutum ne dan soyayya wallahi, wanda ya iya nunawa mace so har ta ji tamkar babu wani da namiji da ya saura a duniya bayan nata.
Da wadannan makamai Zahraddeen ya yaki zuciyar Safah, kuma ya samu. Dalili shine, mu mata muna da indibidual differences a fannin soyayya.
Wata tana so a nuna mata kauna a zahiri da badini, wata tana so amma a boye, wato daga ita sai mijinta.
To Safah tana daga cikin rukunin matan da ke so a nuna musu so da zuciya da gangar jiki a zahiri da badini, idan suna tare, soyayyar da yake yi mata bata boyuwa, amma kai akidarka daban ce. Ban jin ko kalaman soyayyar ka iya.
Ka daina treating dinta kamar sauran matan da ka sani. Ka yi la akari da bambancin kabila da al ada, matan Turawa da kuke tare dasu basu san darajar kansu ba balle su san martabar da Allah ya yi musu, shi yasa suke hauka a kan ku, suke binku kamar jakai, su suke nuna muku soyayyar ba ku kuke nuna musu ba.
Unlike namu matan da aka halitta da kunya, kawaici, da bin al ada. Musamman Safah in kayi duba ga yanayin rayuwarta, za a iya cewa kanta a duhu yake, banda karatunta batasan komai ba sai wanda aka koyar da ita. Abin nufi, she s not edposed to modern society& . not interested to social networkings& .. She is just acting according to her edperiences wato yadda aka tafiyar da ita a baya.
Bata wani san cewa yanzu mata ke bin maza ba. Batasan wai mata tarairayar namiji suke ba& & Safah fa ko talbijin bata kallo& & Ba kawa ba abokiya balle aminiya. & .Bata karance-karance sai wanda ya shafi karatunta. Wannan ce kake cewa bazaka rarrrasa ba sai dai ita ta kwantar da kai ta so ka? To a wane dalili? Rannan fa ina ji kana cewa wai Mami ta rarrasheta haba Ya Imam! Wannan dutse ce mai babban daraja like a diamond& ..bazaka siye ta da sauki ba!!!
Sannan an halicce mu mu mata da juriya fiye da ku, ta yadda ko muna son mutum zamu iya jurewa mu danne. Har sai ya sauke kai ya nemi soyayyar tamu don kashin kansa.
Ta wace hanya ka taba neman soyayyar Safah asanda ta soma mallakar hankalin kanta? Kwanciya fa kayi kana harkokin cigabanka, sabida tabbacin da kake dashi kawai na cewa taka ce! Babu wanda ya isa ya kwace, anya?
Don haka Ya Imam nake baka shawarar ka cire rawanin girman nan ka lallashi matar ka, ka nemi soyayyarta& .. (a hankalce), ka mantar da ita Zahraddeeeeni& .duk da nasan ta zuciyarta ta Marwah ce bazata kuma darsa mata wani abu akan mijin Marwah ba. Ka ji tausayin ta mana, an rabata da wanda ta mikawa zuciyarta sabida kai,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login