Showing 21001 words to 24000 words out of 112612 words

Chapter 8 - BABBAN GORO BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY SUMAYYA TAKORI.doc

Sai ka zauna kai kadai cikin daki?
Ya yi shiru bai yi magana ba. Ta ce,  Ina mukullin motar ku je asibiti?
A nan ne ya yi magana da kyar, ya ce,
 Nura samo min paracetamol kawai, ba sai mun je asibiti ba,  its just a tension&  . Nura ya juya ya fita.
Inna ta ce da Rabi a ta hada mishi ruwan wanka, ita kuma ta fita ta kawo mishi abin kari, kunun gyada da masa mai laushi da zafinta da miyar ganye, taji naman kaji zuku-zuku.
Bayan ya fito daga wankan Inna da Rabi a suka sa shi a tsakiya da roko da lallashi, Inna ta samu ya ci kadan.
Nura ya dawo da maganin Rabi a ta dauko gorar ruwan  faro mara sanyi a karamin firjinsa, ta tsiyaya a tambulan ta mika mishi.
Ya karba ya sha, ya koma ya jingina da gadonshi ya runtse idonsa. Nura da Rabi a suka fita, amma Inna ta kasa tafiya ta barshi.
Ta ce,  Ni kuwa tun jiya da ka shigo sai nake ganin kamar akwai abin da ke damun ka, ka boye baka gaya min ba .
Ya bude idonshi a hankali yana kallon Inna, ya tabbatar da cewa Inna mutum ce mai kyakkyawan tunani da hangen nesa.
Ba shi da abokin shawara a duniya da ya wuce Innar shi, tana bashi shawarwarin da idan ya bisu yana ganin yakini a ciki.
Amma ya rasa dalilin shi na kasa gaya mata damuwar shi wannan karon. A karshe ya yanke shawarar gaya mata komai, ko babu komi za ta ba shi shawara a kai, ya san abin da zai ce da Alh. Aliko idan ya tambaye shi shawarar da ya yanke cikin kwanaki ukun da ya diba mishi. Don wallahi bai san me zai ce da shi ba.
Ya yi ajiyar zuciya ya dubi mahaifiyar shi Inna Binta, damuwa karara kwance a bamalliyar fuskarta, amma ba ta katse mishi hanzari ba har ya yi tunaninshi mai isar shi.
Ya maida idanun shi ya lumshe ya ce,  Inna kin san  yan biyun Alhajinmu ko?
Ta ce,  Safah da Marwah da ka ce suna karatu a nan Zaria?
Ya ce,  Eh, su. To ina son daya, mun dade muna soyayya, to amma jiya Alhaji ya yi kirana ya tambaye ni abinda ke tsakaninmu, na gaya masa ina son aurenta, shine yake gaya min cewa akwai alkawarin dan uwanta a kanta, wanda ni bata taba gaya min ba, amma ya bani Marwah idan na amince sati mai zuwa in kawo sadaki ya daura mana aure.
To Inna kin ji damuwa ta, Safah nake so ba  yar uwarta ba. Amma ba zan iya badawa Alhaji kasa a ido ba, don na san karamci ya yi min na kuma san yadda yake kauna ta.
Ya kuma gaya min cewa yana son hada zuri a dani ne kawai, gashi ni kuma bana son ta  yar uwarta nake so. Idan na aure ta na zalunce ta, na kuma zalunci kaina, tunda bana sonta, itama ba so na take yi ba .
Inna ta yi shiru tana tuna alherin Alhaji Aliko gare su tun ranar da Allah ya hada shi da Zahradeen. Ta kuma tuno nata burin na son aurawa Zahraddeen jikar Yayarta Anisa wadda ke karatun karamar sakandire a halin yanzu a makarantar Sarauniya Amina.
Amma kamar yadda Zahraddeen ya ce ne ba za su iya watsawa Alh. Aliko kasa a ido ba, idan Anisa matarsa ce ko nan gaba sai ya aure ta, tunda sa ar Rabi a ce, shekarunta sha uku kenan.
To amma su auro  yar Alhaji Aliko su ajiyeta a ina? A dan gidansu da bai fi dakin injin wutar lantarki ga  yar Dan Kasa ba? Duk da cewa Zahraddeen yana gini a cikin Kaduna, amma tana tsoron anya? Ba za ta fi karfinsa ba?
Sai kuma tayi wani tunani, Zahraddeen baya daga cikin sakarkarun maza, namiji ne sak, da ke tsaye kan kafafun shi. A karshe ta yi tunanin komai na Allah ne, kuma matar mutum kabarinsa. Ta dubi Zahraddeen ta ce,
 Alh. Aliko ya fi karfin komi a gurinmu, in har muna da shi, kuma muna da iko.
Shi mai saka ka yi aure ne ko da ba diyar cikin shi zai baka ba. Sannan duk mai son ka, saboda halayenka, ba karamin masoyin ka bane. Balle wanda zai yi maka kyautar diya sukutum ba tare da la akari da kai wane ne ba, wato mene ne matsayinka gare shi?
Saboda haka sanya hannu bibbiyu ka karbi kyautar uban gidanka, ka yi fatan Allah ya hadaka da alherin dake tare da ita, ya rabaka da sharrin dake gare ta.
Sau da dama abin da muka kallafa rai ga son shi ba alheri bane a gare mu, wanda bama so din shine alherin.
Amma ka yi istikhara har zuwa lokacin da ya diba maka, nima zan taya ka. Idan ka ji zuciyarka ta kwanta da al amarin to akwai alheri a ciki .
Shine kuma za ka kwantar da kanka ka hau ciwo a kan  yar wannan magana da ba ta fi karfin ayi aiki da hankali da tunani wajen warware ta ba?
A a, bana son hakan. Tashi ka shiga hidimominka kaji Deeni? .
Zahraddeen ya yi murmushi, ya yunkura ya mike. Har wani sabon kuzari ya ji. Inna ta ce,
 To ko kai fa?

Kwana uku Zahraddeen da Inna Binta suna ta istikhara tare da neman zabin Allah, idan auren diyar Alh. Aliko alheri ne a garesu, to Allah Ya tabbatar. Idan babu alheri Allah Ya wargaza ba tare da ran kowa ya baci ba.
****
C
ikin jerin gwanon masu saukowa daga matattakalar jirgin Birgin Atlantic har da Engineer Imam Zubair Dan Kasa. Sanye yake da jibgegiyar bakar kwat mai kauri wadda tsayinta har gwiwoyinsa, ya saya kwayar idanunshi cikin bakin space saboda hazo.
Dogon wandon  Armani ne baki a jikinshi, a ciki kuma  American-Suit ne launin toka-toka wato grey. Saukarsu kenan a filin jirgin Heathrow din London daga Glasgow, inda yawancin fasinjoji a nan za su sauka (transit). Inda jirgin zai sake lodin masu tashi zuwa Ikkon Najeriya a asubahin washegari.
Imam bai gayawa kowa cewa zai zo ba, haka nan zuciyarshi ta tunkudo shi ga son tahowa saboda yawan mafarke-mafarken da yake yi a dan tsukin duk a kan Safah.
Don haka Mami na kicin ta jiyo ihun Aunty Shahida wadda ita ma saukar ta kenan daga Benin inda ta kammala bautar kasar ta.
Da sauri Mami ta fito da ludayin miya a hannun ta, a daidai lokacin da Surajo mai yi musu wanki ke aje manya-manyan jakokin da Imam din ya zo dasu.
A lokacin yana bangaren Hajiya Maama bai idasa shigowa falon gidan ba. Murnar tsohuwar ta kasa boyuwa ta ce,  Oyoyo! Maigidana, yanzu kake tafe shine ko waya balle in yi girkin karbar ka?
Ya zauna kusa da ita har kafadunsu na gugar na juna, kaunar da yake yiwa Kakarsa Hajiya Maama, Allah kadai Ya san iyakarta, ya ce,
 Kai, tsohuwar nan da ran karfe kike, kin ki margayawa mu samu mu ci gumba, na ce bana yi da ke, baki yi min ba amma kin nace sai ni .
Ta kai masa duka da maficinta ya kauce yana yi mata murmushi, wanda da ka gani ka san na kauna da kewa ne ziryan.
Ta ce,  Yo borancin me zan yi? Tunda wadda ka kallafawa ran ba son ka take yi ba, ai ba zan ji tsoron yin kishi da ita ba.
Ina nan za ka zo ka same ni kana  yar murya idan ta wulakanto ka .
Ya sunkuci kwanon furar ta ya yi waje dashi, shi da Shahida suna yi mata dariya. Saidai kuma wannan kalma da Hajiya ta ambata BA SON KA TAKE YI BA ta taba zuciyar Imam ba dan kadan ba.
Marwah ba ta gidan ta je shopping sai  yar mulkin ita kadai a falo tana kwance cikin kujera da littafinta a hannu, ko karatun take ko tunani take oho, ita ta barma kanta sani.
Wani irin lallausan kamshi da mutum daya rak ta sani da shi a duniya wato na turaren  burberry - brit cakude da  akba-amara ya bakunci hancinta. A lokacin da ya russuna daidai kanta ya zare littafin daga hannunta.
Ta juyo tana kallon shi da idanuwanta narai-narai da hawayen dake son zubowa, don a ganinta (mai takurawa rayuwarta ya zo), ba ta ce komi ba.
Shi kuwa murmushi ya yi, yana mamakin yadda Safah ta kara girma, ta kara kyau, ta kara gogewa. A tsayin watanni tara da ya yi bai ganta ba, bai ji muryarta ba.
A haka Mami ta fito kicin tana kallonsu basu ankara da ita ba. Da sauri ta koma kicin din tana mai tasbihi ga Allah a zuciyarta.
Ba ta taba ganin perfect-match na miji da mata da suka dace da juna irin Safah da Almustapha ba, ga shi kamarsu daya, kamar an tsaga kara. Haske kawai ya fita. Hasken ma bana fata bane, na zaman kasar sanyi ne kawai.
Safah ce ta fara dauke idonta sannan ta hade fuska sosai ko kalmar sannu da zuwa da take mishi a da, yau bai samu ba. Karshe ma mikewa ta yi ta bar mishi falon.Ya yi dariya ganin yadda ta cika, ta yi tam, kiris take jira ta fashe.
Shahidah kuwa dake gefe tana kallon su ciwo ta ji sosai na halin ko in kula da Safah ta nunawa dan uwanta, wanda ya taho tun daga tsakiyar duniya don ya gansu, abin mamaki akan idonta ko kunyar kwayar idanun ta yarinyar nan bata ji ba, a take ta ji ta fara tsanar Safah, duk da cewa ita dinma  yar uwarta ce, amma ai wata kusan& .. hausawa suka ce  ta fi wata , amma ta ga shi bai damu ba, dariya ma yakeyi sabida rashin zuciya.
Mami ta fito fuskarta yalwace da murmushi, ya isa gareta ya amshi tray din da ke hannunta. Hannun shi ta kama suka isa dining tare, ita ta yi serbing din shi da kanta.
A lokacin da Daddy ke saukowa daga matattakalar bene, ya yi arba da Imam ba zato ba tsammani.
Ya ce,  What a surprize? Cikin satin nan nake shirin cewa ka zo, to kuma sai ga ka. Amma me yasa baka sanar dani zuwan ka ba?
Yana dariya ya ce,  Nima tafiyar ban shirya mata ba Daddy, kamar wanda aka tunkudo haka nan na ji duk hankalina yayo gida....(nostalgia)
Marwah ta shigo da ledoji biyu a hannunta ta yi arba da Yayannasu, ta watsar da ledojin ta rugo da gudu kamar za ta rungume shi, amma sai ta tsaya a gabansa ta maida hannuwanta baya ta sarke su tana dariya.
Ya mika mata hannu ya ce,  Come on.... my dear Sissy, na yi kewar ku da yawa .
Ba ta mika mishi hannun ba ta yi dariya ta ce,  Har dani Ya Imam a wadanda ka yi missing? Ban yarda ba .
Ya dan fiddo ido  Na yi karya kenan, gemai-gemai da ni ko?
 A a, ni ban ce ba . Ta fada cikin dariya.
 To ki yarda dani, I missed all of you a lot .

Marwah ta ji dadi, yau ne rana ta farko da ya taba yi mata kalami na kulawa tun tasowar su.
Mami ta ce,  Kyale Marwa ka ci abincin nan Imam .
Ya ce,  Bari Mami in fara shan furar uwargida na
Sai da ya shanye furar Haj. Maama, sannan ya aje jug din ya soma cin abincin Maminsa, cike da nishadi da kewa mai yawa. W ata tara ba kwana tara ba.
Ya ce,  Gaskiya ne da Bature ya ce,  No place like home . Mami na yi missing girkin ki yadda bakya zato, kullum na zo cin abincin gongoni sai na tuna ki Mami, na tuna girkin ki mai sawa mutum ya manta sunan sa.
Ba don kowa da inda Allah Ya tsaga mishi hanyar abincinshi ba, da babu inda zan je in barku Mami .
Ta yi murmushi ta ce,  Imam kenan, nima kullum sai na tunaka, sai in ce da Imam yana nan da kaza ta faru, da kaza bata faru ba .
Marwah ta shiga dakinsu da ledojinta, sai ta tarar da Safah tana sanya kayan barci, ga dukkan alamu kwanciya za ta yi.
Ta girgiza kai ta shiga toilet ta yo alwala, a ranta tana cewa da wannan banzan yaron ne ya zo da yanzu tana nan tana shafe-shafe da murje-murje.
Ta yi alwalarta ta yi sallar isha i, ta fice falo inda ake ta hira ta barta a nan.
Kwanan Safah uku a daki ba ta fitowa don kar su hadu da Yaya Imam din, ko yunwa take ji sai dai ta yi waya kichin a kai mata abinda take so. Shi ma Imam din ya share ta baya shiga sabgarta, ga shi ga dukkan alamu a yanzu kam ya fara amincewa da gaske Safah ta ke ba ta son shi.
Idan a da yana yi mata uzuri da kuruciya a yanzu fa? Shekarunta goma sha tara, ta isa ta bambance abinda take so da wanda ba ta so. Wato dai ta isa ta yiwa rayuwarta ZABI ba tare da an tursasa ta ba.
Shi kuma ya amince ba zai aure ta bisa tursasawar iyaye ba. Zai yi mata yadda take so muddin ta furta da bakinta cewa ba ta son shi.
A dakin Hajiya Mama yake a safiyar yau suna hira, ta ce,  Ban da abin kuruciya irin na Safah ga dan uwanki jinin jikinki, wanda ya san ciwo da darajarki, amma ki nace sai wani can da bai san zafin ki ba?
Sai kuma ta tuna da wa take magana, ta yi hanzarin gyara subutar bakinta, ta ce,  Au, wanda yake son Safah shi Alhaji zai baiwa Marwah .
Imam ya yi tsai da ranshi yana duban ta a tsanake. Ji yayi tamkar aradu ta rikito kansa. Amma ya nuna maganarta ba ta taba zuciyarshi ba.
Ta hanyar cewa
 Shi wanda take so din a ina yake?
Hajiya Mama ta ga babu amfanin yiwa jikan nata rufa-rufa, kallo daya ta yi mishi ta karanci matsanancin KISHI a kwayar idanunshi.
Duk sai ta ji babu dadi, ta kuma yi Allah wadai da surutun ta. Koda yake dole kuma ta gaya mishi yadda abun yake, tunda kuma Daddy ya kashe maganar.
Ta ce,  Ma aikacin Alhaji ne, wa yake da suna? Ni sunan wuyar fada yake mini .
Ya ce a nitse,  Kutama ko Peter ko Maitama?
Ta ce,  Kai, ba haka na ji sunan ba .
Ya mike ya zura takalmin shi yana cewa,  Idan kin tuna ki kira ni, kin san baki san sunanshi ba kika fara gaya mini?
Ta ce,  Dawo ka zauna zan tuna a hankali .
Ya ce,  Kada ma ki tuna, bana son ji .

Karfe sha biyu na rana Zahraddeen ya shigo gidan, cikin shadda edcelcior maroon colour, kanshi babu hula wanda hakan ya bayyanar da kwantacciyar sumar kanshi ta Mallawan usli, sai sheki shaddarshi take tana maiko tana nuna tsadarta.
Kiris ya rage suyi karo da Imam dake fitowa daga kofar cikin gida. Dukkansu basu san juna ba sai a suna.
Imam ya kan ji sunan ZAHRADDEEN MAITAMA a bakin Daddy ba tun yanzu ba, ta yadda yawan ambaton Zahraddeen din da Daddy ke yi Imam ya fahimci shi din wani hadimi ne mai muhimmanci ga Daddyn, domin adadin kaunarka da mutum adadin yawan ambaton sa a bakin ka, Zahraddeen kan ji dana ALMUSTAPHA a bakin Daddy, amma basu taba ganin juna ba.
A take Zahraddeen ya yankewa zuciyarshi wannan ne Almustapha, tunda ga kamannin Safah nan a kyakkyawar fuskarsa, ta wani fannin kuma da Daddy yake kama.
A take ya ce,  Imam.....
Shi kuma ya ce,  Maitama....
Suka yi hannu suna murmushi. Amma fa zuciyar kowanne na zabalbala da kishin dan uwan ansa, amma fa tsabtataccen kishi na masu aiki da hankali da tunani, ba kallon juna suke don son hango aibu ko nakasun junan su ba ko makamancin hakan a ah, kallo ne na son hango how much lucky are you??? Kowannensu ganin dan uwansa yake a matsayin wanda yafi kowa sa a a duniya. Imam ya fasa fita ya yiwa Zahraddeen jagora har main parlour.
Yau kadaran-kadahan Mami ta yiwa Zahraddeen karba ta mutuntawa. Tunda ya zama dolenta.
Ta ce,  Zahraddeen ga Almustapha fa .
Ya ce,  ai na canka Mami, from the first glance... (daga kallo na farko)
Ta ce,  Imam. Ga Zahraddeen din Daddy .
Ya ce,  Nima na canka Mami, ko daga tsagin Mallawan .
Duka suka yi dariya. Suka zauna tare cikin kujera, daga nan kuma sai hira rai-rai-rai kamar sun dade da sanin juna.
Cikin dan lokacin Mami ta soma fahimtar Zahraddeen mutum ne mai dadin mu amala, kuma dole mutumin da ke alaka da shi ya so shi, saboda saukin kansa. Nutsuwarsa da yadda yake fidda kalamansa a ilmance, duk wata kalma data fito daga bakinsa mai ma ana ce, daga yadda yake Magana zaka fahimci zurfin ilminsa, ga kyau da kwarjini, gashi mai wayayyen kai. Safah bata yi laifi ba don tayiwa kanta sha awar auren Zahraddeeen domin ta ko ina yayi a rayuwa.
Ta tabbatar Daddy na da hujjar shi na son Zahraddeen, kuma bai yiwa diyarta zaben tumun dare ba. Auren gata yake so yayi mata.
Sai ta russunar da kwayar idonta kasa ahankali cikin saduda. Sai azahar Daddy ya shigo yana baiwa Zahraddeen hakurin bata mishi lokaci da ya yi.
Zahraddeen ya ce babu komi. Saima halayen Alhajin dake kara masa ganin kimarsa. Bai dauki kanshi a bakin komi ba. Suka nufi masallacin Daddy dake wajen gidan suka gabatar da sallar azuhur.
Kamin su dawo Mami da Marwah sun shirya dining, ita  yar mulkin tana daki ko fitowa ba ta yi ba. Tana jiyo muryar Zahraddeeeeeeeen dinta& & , cikin tausasan lafuzzansa. Ya na yiwa Imam bayanin nasarorin da  Dan-Kasa Holdings ta cimma a wannan shekarar. Bata san cewa hawaye ke zuba tarara daga idanunta ba.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login