Showing 90001 words to 93000 words out of 112612 words

Chapter 31 - BABBAN GORO BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY SUMAYYA TAKORI.doc

sulusin dare tana zaune a gaban gadon Lamido a kan kujerar mutum daya ta roba, da karamin Alkur ani a hannunta tana tilawa tana gyangyadi, har ta kai ga bingirewa a gaban gadon, Alkur anin na neman subucewa, sai ta ji hannun Lamido cikin gashin kanta.
Ai sai ta kara rike Alkur aninta ta ci gaba da barcinta tana cewa cikin ranta, in mafarki take kada Allah yasa ta farka yanzu.
Wasa-wasa sai ji ta yi hannuwan Lamido biyu sun jawota sun kankame ta, sai ta bude idanu tangararau tana yiwa Allah tazbihi.
Zuwa asubah sai ga Lamido a kan kafafunsa ya shiga toilet don ya dauro alwala.
Tare suka yi sallah, sannan ta hada masa ruwan wanka mai dumi a jacuzzi ta taimaka mishi ya yi wanka sosai irin wankan da rabon da ya yi irinsa yau watanni takwas, sai dai na goge jiki da tawul da Safah din ke masa.
Sau biyar tana canza ruwa, tayi mishi gyaran fuska, ta hada mishi tea mai kauri ya sha, sannan ta ballo magungunansa na kwakwalwa da har zuwa lokacin bai daina sha ba.
Ya karba ya sha tare da wadanda yake sha na tofin addu o i (tawaida) da Malam ke masa kullum.
A lokacin Malam ya koma Nigeria, sai Ishak (mai bin Lamido) dake tare dasu. A lokacin shi yana Hotel bai ma shigo asibitin ba.
Karfe bakwai daidai na safe likita da Nurses suka shigo domin lokacin shan maganinsa da gashin kashinsa ya yi.
Nan suka ga abin mamaki, wato patient din ya yi matashi da cinyoyin sahibarsa suna ta hira cike da shaukin juna.
Doctor Tonnies kwararren physiothearapist ne da ake ji da shi a Bienna (Austria).
Warkewar Lamido wata irin warkewa ce ta bazata (ta karfin addu ar al umma), a lokacin da basu taba zato ba.
Don haka har a Bienna weekly journal ta wannan satin da ake ciki ya saka labarin, domin Bature baya raina abin mamaki.
Gashin kashi basu fasa yi mishi ba har zuwa wani lokaci mai tsawo da sauran treatment dinsa da shan magani. A ranar da ya sallamesu ko kwana daya Lamido bai bari sun kara ba, suka taho gida Nigeria.

Gidansu Lamido babban gida ne me sassa daban-daban, don kowa a gidan yana da dakin kansa. Duk sun fito daga cikin mace daya wato Hajiya Nadeeya  yar asalin garin Jazeera ta kasar Sudan.
A ranar da su Lamido suka sauka a Taraba ana sunan jaririn da kanwarsa Talatu ta haifa wanda ya ci sunan Lamido wato (Naseer).
Don haka duk dangi sun hallara, su Zahra u na ta karbar baki sai ganin Yaya Lamido su kai ya sanyo kai falon Hajiya, idanunshi rufe cikin glasses masu ruwan kasa yana rike da hannun santaleliyar matarsa Safah.
Don haka wadanda basu santa ba ma yau sun ganta sun yaba sun yi tofin albarka (classy wife) in ji Zahra u. Perfect match (in ji Abubakar). Classikue (in ji Aliyu& & .). Duk cikin zuciyarsu suke fada, basu san cewa a fili suke yi ba.
Nan da nan gida ya kaure da ihun murna, addu a da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login