Showing 66001 words to 69000 words out of 112612 words

Chapter 23 - BABBAN GORO BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY SUMAYYA TAKORI.doc

rayu tare, su fadi tare sannan su tashi tare. Fatan ALHERI Safah da Lamido. Takori

****
Daga dukkan bangarorin biyu, wato Taraba da Chikun, ba a samu tangarda ba. Haka binciken da Kawu Sufyan ya yi a kan EFCC Lamido, it probed positibe, ta fannin halaye, asali da sana a. Shekarunsa goma da matarsa ta fari, ba a taba jin kansu ba.
Sai ma wajen binciken ne alamu suka nuna Nasir da Safah  yan uwan juna ne na jini.
Hakan ya faru ne ranar daurin aure, daurin auren har biyu a kayi, wato Safah da Shahidah, wadda aka fara daurawa auren da angonta Ministan yada labarai Hafizu Ingawa, matarshi ta dade da rasuwa wajen haihuwar dansu na fari, yana nan dan shekaru biyar (Muhsin).
Baffa Sufyan ne ya shigo da iyayen ango wadanda suka zo daga Taraba domin su gaisa da Mami da Hajiya Maama.
Ai kuwa dagowar nan da Malam Abdulkarim ya yi sai idonsa cikin na  yarsa Mami. Ya ce,  Zaynaba nake gani ne ko kama ce?
Mami ta hau salati,  Baffan Taraba ashe ka san Lamido?
Sai ya yi dariya ya ce,  Iko sai Allah, to kenan ke  yar uwar amarya ce ko rashin zumuncin naki damu don kar mu raba ki da gidan marigayi mu tilasta ki kiyi aure yasa kike boye  ya yanki. Don dai na san  Yan Biyu na dade da sanin anyi musu aure .
Mami dariya kawai take zuciyarta kamar madara don farin ciki, ta kasa ba da amsa sai Hajiya Maama ce take mishi bayani.
 Ai ita Safah ba ta je gidan mijin ba suka rabu, tana ta karatun likitanci tsayin lokacin sai yanzu Allah ya kawo auren .
Sai ya fiddo waya ya kira Lamido ya ce maza ya zo.
Haka ya tsallake bankwanan da suke da jama arsa ya zaro jiki ya shigo, amma mai tsaron lafiyarshi na biye da shi, inda duk ya cire kafa nan yake mayar da tasa.
Yana shigowa falon bakinsa dauke da sallamar girmamawa, a nutsensa yake tsaf, babu abin da ke firgita shi a rayuwa. Mutum ne mai karfin zuciya da karfin imani.
Wannan ne ke sayo mishi kwarjini na musamman a duk inda ya shiga. Ita kanta Mami sai da ta firgita da BABBAN GORON da diyarta ta samo.
Sai dai firgicin nata bai yi tasirin da ya bayyana a fuskarta ba,  yarta ma BABBAN GORO ce, lallai da ake cewa  Babban Goro sai magogin karfe . (Takori).
Har kasa ya kai gwiwoyinshi yana gai da Mami da Hajiya, ba sai an gaya masa ba, kallon farko ya ga fuskar Marwah cikin fuskarta. Sai ya kara kwanciya sosai kamar zai yi mata sujjada saboda kauna da girmamawa.
Mal. Abdulkarim yana murmushi ya ce,  Ka ganta nan Yayarka ce, da kakanta da kakana na wajen uwa, uwa daya uba daya suke.
An dade da aurenta da Aliko sun zo bikin wata  yar uwarmu da ta yi aure a Chikun, a can ya ganta ya bita gida Yola ya aure ta.
Abin da yasa baka santa ba tuntuni, Aliko baya kaita Yola. Bayan rasuwarsa kuma babu yadda bamu yi da ita ba kan ta koma gida ta sake aure ta ki, da ta ga an takura mata ma sai ta yanke zumunci da kowa, ko  yan Yola sun zo sai ta ki yarda ayi maganar komawarta, ka ji dalilin da yasa baka santa ba .
Cike da farin ciki Lamido ya dago ya sake matsawa jikin Mami kamar ya rungume ta, sai ta daura hannunta a kan kafadunshi ta ce.
 Wai Lamidon Hajiya Nadeeya da ka kai karatu Legas shine ya zama mijin Safah? Ni duk zuwan da yake bamu taba gaisawa ba, amma na rasa dalilin da yasa zuciyata ta karbe shi tun ba ta ganshi ba .
Haka dai aka yi ta hirar zumunci da tuna baya, duk yadda Malam ya so su koma Taraba a ranar hakan bai yiwu ba, Mami ta ki, tasa aka share (guest-room) na Daddy suka kwana a can. Washegari suka yi asubanci Taraba ta diba.
Ranar ta kasance ranar wunin biki, a nan harabar gidan aka yi.
Washegari walima ce itama ta mata zalla Mami ta shirya. Dr. Fatima Ja afar Mai-Yadi ita ta wa azanci mata a ranar, a kan darajar aure da wajibtakar sa a Musulunci.
Ta kawo darajojin da Allah ya yiwa matar aure da daukakar ibadarta a kan ta mara aure. Me maza na gari ke so a mace? Meye basa so.
Lacca ce ta yi sabon salo irin wadda ke cakude da ilimin musulunci mai tafiya da zamani. Wanda yawanci ta zakulo su ne daga rubutun (Aisha Lemu).
Banda wannan Mami ba ta yarda da kowane program ba. Ta ce albarka ake nema ba bidi a mara amfani da almubazzaranci ba.
Sai dai shima angon  yan office dinsa sun shirya liyafar cin abincin dare a hotel din NICON wanda za a gudanar bayan an kai amarya Abuja.
A karo na biyu Mami ta yiwa amarya nasihar zaman aure tana kuka tana rokonta ta jure ta zauna a gidan aure, wannan ne kadai kwanciyar hankalinta, da dadi da babu dadi ta horeta da hakuri sakamakon kananun maganganun da ta soma ji daga bakin  yan uwanta na Yola a kan Danejo, suna cewa ma wai kwata-kwata ba ta san anyi auren ba.
Motoci ne in an anbiable-array (a jere reras) har guda goma bakake sidik firda-firda daga Kaduna har Abuja.
Tankareren bungalow na amaryar na nan a unguwar Asokoro. Wani irin American Billa tamkar kana cikin daya daga flats din New York.
Tsayawa fasalta tsarin gidan ma sai ya zama bata lokaci, dan haka babu abin da babu, babun ce kurum babu in ji Malam Bahaushe. Yayin da aka wuce da Aunty Shahida nata gidan a Ministers-hill.
Suna isowa ko zama basu yi ba, sallar magariba suka fara yi zuwa isha suka yi wanka aka sake shiri aka kwashe su zuwa Nicon - Noga, a can ne angon ya tari amaryar da kansa, don shi ya bude mata kofar mota da kansa ya rungume ta ya sumbaci goshinta, ya rada mata cikin kunnuwanta.
 Welcome to the new and wonderful life, full of lobe and happiness . (Ina miki maraba da shigowa sabuwar rayuwa mai cike da farin ciki da so da kauna).
Ina rokon Allah Ya bani ikon rike ki da amana, da soyayyar da bata yin rauni, sai ranar da na bar duniya .
Dago fararen idanunta ta yi ta dube shi, kwayar idanunta narai-narai da hawaye, kwayar idanunsa ta tabbatar mata da abinda ya fada, haka yake har zuciyarsa.
Ita kanta ta yarda ta shigo sabuwar rayuwa, wallahi ba ta san mene ne a cikinta ba, ba ta san ya take ba.

Tunda ta taso cikin gata ta taso, ba kwaba ba hantara, sai nasiha a inda aka ga za ta kauce hanya. Ta taso cikin rayuwar  yanci da sukuni.
Mene ne kalubalen dake cikin rayuwar aure? Shine ba ta sani ba.
Mami ta tsawatar ta tsoratar da ita sosai. Ta ce da ita,  Wata sabuwar rayuwa za ki fara wadda ta bambanta da wadda kika taso a ciki.
Ita wannan akwai hakkoki da yawa a cikinta na wasu mutane masu yawa da suka hau kanki, wato uwar miji da ubansa, yayyensa da kannensa, kishiya da  ya yansa.
Duk dunkulesu za ki yi su zama naki, sannan ne za ki samu zaman lafiya a rayuwar aurenki.
A cikin ita wannan rayuwa, baki da iko da kanki sai abin da mijinki ya karkata ki a kai, wato ya yi miki izini.
Na san dai ba zai zamo mai tauye miki hakki ba, amma fa ba ke kadai ba ce. Dole ki bi tsarin a yadda kika same shi.
Idan kika ce za ki kawo sauyi, ba lallai abokan rayuwar naki su karba ba. So ki karbi RAYUWA A DUK YADDA TA ZO, ki kasance mai tsarkakakkiyar zuciya a kan kowa. Sauran al amura ki barwa ALLAH!
Hawayen dake makale cikin kwayar idanunta suka mirgino a hankali masu dumi.
Lamido ya gigice, ya riko hannunta sosai yana share mata hawayen da habar babbar rigarsa.
 Na shiga uku ni Lamido!. Taimake ni ki hadiyesu kada al umma ta ce bakya farin ciki don Allah Safah!
Kwanciya ta yi sosai a kafadunsa da suka zamo waigi a gareta daga faduwa kasa.
A hankali ta ce,  Mami....ni dai wajen Mami zan koma& . .
Ya ci gaba da share mata hawayen kamshin jikinsa na sanyaya mata zuciya.
Ya ce,  Wallahi ko gobe kike son ganin Mamin zan kai ki. Ni dai rokona gareki ki mai da hawayen nan kada abokaina su ce bakya so na....
Ba ta san sanda ta yi murmushi ba, shima ya shiga taya ta murmushin. Suka soma takawa zuwa cikin hall din.
Ai kuwa masu mujallar Obasion da Delight,  yan jaridar New Nigeria, Daily Trust, Triump, Leadership, Weekly Trust, Present Nigeria, NTA Abuja, BBC London (Abuja Branch), ma aikatan gidan rediyon tarayya da sauransu suka taru suka ce da wa Allah Ya hada ku ba da mu ba???
Taro ya gudana kamar yadda aka tsara, cikin tsari da ilimi. Babu hayaniya. Karfe goma sha biyun dare garin Abuja hadari ya gangamo, sama ta daure kitikif da bakin hadari aka soma tsawa da walkiya da guguwa mai karfi.
Zuwa lokacin da yawa jama a sun tafi, wadanda angon ya saukar a hotel din duk sun bi matattakala da lifta sun nabba a a dakunansu da aka kama musu.
Mutanen Yola ne da na Kaduna, sai abokan huldarshi na wasu garuruwan, irin Legas, Fatakwal, Bayelsa, Benue da sauransu.
Akwai kuma jama ar sauran kasashe da dama da suka zo takanas domin halartar liyafar cin abinci, duk sun yi masaukinsu.
Angon ne da amaryar kwance a bayan mota  Opel - Astra , wani kurtun soja ne ke janta. Ko murmushi baya yi fuskarsa murtuk kamar hadari.
A gaba mai kula da lafiyar Lamido ne ya sha bakar kwat wadda harsashi baya huda ta sai muzurai yake kamar ya ci babu, yana fama da wareless da na urori kanana.
Wannan lokacin Safah fuskarta a bude take ba kamar sanda aka kawo ta ba, tana kallon yadda wiper ke kore ruwan dake sauka da karfinsa a kan gilasan motar, har da karar kananan kankara, ta ko kasa hada ido da Lamido.
Shima bai takura ta ba, tunda ya fahimci tana cikin yanayin da bai taba ganinta a ciki ba. Kamar bata san shi ba, zuciyarta Imam take tunawa ranar liyafar dinar aurensu da suka dawo yana tambayar Zahraddeen ko zai rage zafi su zaga otal?
Daga baya duk sanda ta tuna wannan maganar sai ta yi dariya ita kadai, idan ta tuno yadda duk tsiwar su bakinsu ya mutu babu wacce ta ce uffan.
Allah sarki, ashe iyakar auren kenan. Daurin aure da saki. To amma waye musabbabin? Ita ce.
 Kina auren wani kina tunanin wani?
Wani bangare na zuciyarta ya tunatar. A take ta soma jan istigfari, sannan ta fashe da kuka tana rokon Allah Ya yafe mata kuskurenta.
Abin fa ya soma taba ran Lamido, ya rufe wayar hannunsa ya dube ta sosai, ya ce,  Mami dai?
Ta girgiza kai. Ya sake cewa,  Kenan ba a farin ciki da aurena ni wane irin mara sa a ne?
Da sauri ta girgiza kai. Ya lalubo hannunta ya rike cikin nashi, fatar hannunta kamar auduga don taushi, ga wani santsi da take yi. Bai san sanda ya kai fatar bakinshi gare ta ba, ya soma tsotson bakinta kamar zai tsinke harshen gaba daya ya huta.
Irin wannan kissing bai taba yi a rayuwarshi ba. Domin dai Danejo bakinta bai taba daukar hankalinshi ba saboda mayuka da take amfani dasu na canza fata marasa dadin kamshi da cin uban jambaki, sun sanya bai son sakin jiki da dukkan gabbanta.
Amma a nan wani irin cool kamshi ne ke fita a wasu irin soft-thin lips, da aka tausasa da wet-lips mai dadin kamshi kamar yana tsotson hubba-bubba, cingum din nan mai dadin kamshi.
Ita ce ta kwaci bakinta da kyar sakamakon kashe motar da direba ya yi, gilasan motar suka yi kasa gaba daya, wani irin sanyi da kamshin furanni mai ni ima ya bakunce ta a harabar gidan gaba daya, zuwa lokacin ruwan ya tsagaita amma bai daina zuba ba.
Ai suna shiga falon farko bai bari ta kuma takawa ba, daukar ta ya yi ya bi matattakalarsa, bai dire ta ba sai a lafiyayyen gadonsa.
Da kanshi ya hada mata ruwan wanka, tsugunnawa ya yi daidai gwiwoyinta ya cire mata sarka, dan kunne da zoben hancinta irin na Kanuri, ya ajiyesu a gefe.
Ya tayata rage nauyin leshin jikinta, ya zama sai doguwar riga mai santsi mara hannu (shimi), ya ja hannunta har toilet.
Sai da ya tabbatar ta shiga kwamin sannan ya nufi kitchen da kansa, shi kansa kitchen din a cikin falon saman yake.
Ya duba cikin micro wabe ya ga aikin da yasa kukun sa Abraham ya yi ya yi shi da kyau da ban sha awa.
Wato wani Dawisu (Peacock) an gashe shi irin gashin nan mai ruwa-ruwa da ya ji albasa da tumatir, har da dan attarugu.
Sai ya dauko shi baki daya ya dora a katon fadi-ka-mutu, ya dauko cokali mai yatsu, wuka, pepper, chips and scottish salad da ruwa da jusi ya koma bedroom din.
Ya samu har ta fito ta yi shafa i da wutri, ba ta kai ga tashi daga sallayar ba, sai ya ajiye gabanta. Ta dago ta dube shi idanunta sun koma kanana saboda kuka, sai zafi suke mata. Ta ji duk tausayinshi ya kama ta.
A hankali ta furta,  Sannu da kokari .
Sai ya yi murmushi kawai yana tsiyaya lemun Prime Lady cikin tambulan mai garai-garai, ya sa mata a baki.
Karba ta yi ta sha sosai, don ba ta san ma tana jin yunwa har haka ba. Hatta naman shi yake yagowa da fork yasa mata a baki.
Wannan kulawa da kyautayi ga babban mutum irinsa ya taba zuciyarta. Ba ta san sanda ita ma ta zage ta soma ba shi a bakin ba.
Sai da suka tashi da Dawisun nan baki dayansa sai kasusuwa, don kowannensu bai san cewa ya tara yunwa ba sai yau.
Abubuwa da yawa sun biyo baya, wato sallar neman albarkar aure. Hira mai dadi da karin fahimtar juna.
Don haka da al amura suka fara nisa ba ta da karfin gwiwar ko karfin zuciyar da za ta iya cutar da mijinta mai sonta, ashe ita ma tana da muradi irin na kowanne lafiyayyen dan Adam??? Batasan hakan ba sai yau dinnan.
Sai dai a matsayinta na farin shiga, lamarin bai zo mata da sauki ba. Da ta san haka ne ma ai da ba ta yi saurin ba da kai bori ya hau ba.
Karfe hudu da rabi na asubah amma dukkaninsu basu yi barci ba. Da idanunta ta ga Nasir yana share hawaye, ba kuma ta san dalilin zubarsu ba. Sannan ya mata kwarjinin da ta kasa tambayar shi.
Tana daga kwancen take gaya mishi taimakon da zai yi mata; hada ruwan dumi da dettol a jacuzzi, paracetamol da ampicilline a first-aid bag dinta.
Hakan ya yi, sai da ta fito wankan ta dora alwala, ya ba ta fresh milk ta sha, sannan ya ballo maganin ya ba ta kamar yadda ta yi zato ba hakan ce ta faru ba.
Domin ta yi tunanin za ta yi regretting baiwa Lamido budurcin ta, ba ma shi ba, ko wani namiji sabanin IMAM.
Sai hakan ba ta faru ba, har zuciyarta farin ciki ta yi da Nasir ya dauki barginity dinta da ta dade tana tattalawa Imam, domin ya cancanta.
Ta kuma tabbatar abin da ya sa shi kuka kenan. Shi ya ja su sallar asubahi saboda babu masallaci a nan kusa dasu.
Ko da suka koma suka kwanta don rama barci, hakan bai yiwu ba, saboda sabon fejin da Lamido ya bude gaba daya ya kara gigita ta.

Haka ya ci gaba da shayar da ita mamaki, cikin fannonin kauna da soyayya daban-daban, da ba duk maza Allah Ke yiwa baiwarsu ba, don ita kam ko a litattafai da fina-finan Turawa bata taba yin karo da caring and lobing husband irin EFCC Naseer Lamido Abdulkarim ba. Ko kuma don tana son shi ne ta ga hakan? Ba zan iya cewa ba!!!
***MUTANEN RUGAR ARDO
I
na Marwah ne da angonta Zahraddeen har aka yi biki bamu ji duriyarsu ba? To basa nan, suna cikin wani jeji gabashin garin Kaduna, cikin karamar hukumar Lere, suna jinyar Yayar Inna Binta da suka tarar babu lafiya rai a hannun Allah, dauke da cutar kansar nono (breast cancer). Saidai a kwantar a tayar.
Sannan duk wani roko da lallashi sunyi don su taho da ita asibiti amma ta ki, ta ce wa adinta ne ya zo, ba kuma taso ta mutu a ko ina sai mahaifarta.
Sun kasa tahowa su barta, kuma ta yi rantsuwa ko sun dauke ta ba cikin hayyacinta ba sun kaita an yanke mata nono Allah Ya isa ba ta yafe ba.
Idan kaga Marwah da Zahraddeen a wannan jeji sai sun baka tausayi, sunyi wujiga-wujiga dasu. Inna Binta kam a tsaye take kan  yar uwarta. Ba yadda ba ta yi ba su tafi su kyale su sun ki, ko don aikin Zahraddeen.
Ya ce, ai cikin hutu yake, ya dau hutun shekara. Shi Daddy kuwa ba a magana, kafafunshi sunyi futuk da kaushi da faso, saboda yawo ba takalmi cikin rugage.
Ko sau dubu uwar ta sa mishi takalmi sau dubu zai haka rami ya binnesu ya zo ya ce mata bai gansu ba.
Shi kuma Daddy ba don komai yake hakan ba sai don ganin sauran yara na rugar tsararrakinsa da yake wasa dasu ba a sa musu takalmi, to shi don me za a sa mishi?
Bukkar Badijo guda biyu ce, daya ta marigayin mijinta ce, daya tata ita da jikanyarta Anisa, wadda yanzu ta zama budurwa, domin sa ar Rabi a ce.
A daya Bukkar ne Zahraddeen da matarshi ke ciki, dayar da Inna Badijo ke kwance ciki nan Inna Binta, Daddy da Anisa ke ciki.
Sai dai fa Anisa sam ba ta shiri da Marwa, tana kullace da ita a kan labarin da Rabi a take ba ta sanda suna makaranta na wulakancin da take musu. Duk da ita Rabi a abin ya wuce a ranta har ta manta.
Ko dansu Daddy bata kulawa, kiyayyar uwarshi ta shafeshi, kai ita a dan tsukin nan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login