Showing 39001 words to 42000 words out of 112612 words

Chapter 14 - BABBAN GORO BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY SUMAYYA TAKORI.doc

brother (not a sweeeeetieeee& ...). Russunawar da zuciyarta tayi tausayi ne da kaunar jini kawai kawai. Ta hakura da Zahraddeen, ta kuma tabbatar ta rasa shi har abada, amma ba za ta iya rayuwar aure da wanda zuciyarta bata yi amanna da hakan ba.
Abinda take ji akan Imam a yau, ba iri daya ne da wanda ta ji a Zahraddeeen ba; sympathy and pity (na Imam) infatuation (na Zahraddeen).

Kanshi ya kwantar a kan sitiyari, idanunshi a runtse, ya rasa inda zai sa kansa, ya rasa inda zai tsoma zuciyarshi ya ji sanyi. Bai san me zai yi ya sayowa kanshi soyayya a zuciyar Safah ba. Da gaske ne ba ta son sa, kuma har abada wanda ya ce baya son ka ba zai dawo ya ce yana son ka ba.
Yau ya yarda ba a sayen soyayya, duk tsadarta yau da ya sayo! Wanda ya furta a fili da boye, zahiri da badini baya yi da kai LET HIM GO! Da sannu zai gane amfanin ka, da sannu zai gane muhimmancin ka a gaba, da sannu zai gane wanene mai son sa, wanene mai kaunarsa, ka barshi ka yi da mai yi da kai. Ardhullahi Waasi a (Duniyar Ubangiji fadi gareta). Idan wani ya ki ka da wuni, wani da kwana zai so ka. Kuma babu mai sanyata sai sarki ALLAH, not eben physical or material attachement.
A yau ya ga alamomi da yawa, wadanda a da can idonshi ya rufe da soyayya har baya gani, tunda ga shi har ta hada kanta da hawan jini kawai saboda ba ta son shi, an aura mata shi akan dole.
Karamin misali dubi yanzu jini ne ke zuba daga jikinsa, yana karar da hayyacinsa, yana hajijiya da kuzarinsa tana gani ko a jikinta, kwayar idonshi bacewa take neman yi dauriya kawai ya ke yi, idan da tana son sa ko kadan, kamar yadda Shahidah tace lallashi zai sayo, ayau da ya gani ko kadan, ko a kwayar idonta, sanda zata nuna damuwarta ko kulawa akai ma bazata sani ba.
Shi nata ciwon gigita shi yayi, ya fitar dashi daga hayyacinsa, ya janyo masa asarar tafiyarsa neman abincin sa, aalah kadai ya san iya matsalar da zai fuskanta da shugabansu akan hakan, domin bature babu abinda ba zai jura ba, amma banda saba alkawari. Wanda ma ba fitar jini ba kenan abu mai daga hankali.
Wanda ita tayi sanadinsa, baya jin ko ciwon hauka yake zai iya mintsinin Safah duk irin laifin da ta yi masa, balle ya huda jikinta ta hanyar day a san zata cutu, kawai don ya rike hannunta a matsayinsa na mijin aurenta na sunnah bama da wata manufa ba.

A take wata irin zuciya ta shige shi, mai bada  courage wato karfin zuciya, ga son yiwa Safah duk abinda take so, don hankalinta ya kwanta. IDAN SO CUTA NE, TO HAKURI MA MAGANI NE. Har zuwa lokacin kuka take, kanta cikin cinyoyinta. Ya ce (cikin wata irin murya da ta kasa amincewa cewa tashi ce).
 Safah!
Bata dago ba haka nan ba ta fasa kukan ba, in banda tafarfasa ba abinda zuciyar shi ke yi. Hannu yasa ya fincikota, ya ce,  Fadi duk yadda kike so..... na rantse da wanda raina yake hannunSa& .. a yanzun nan zan yi miki. Ko da hakan na nufin cewa rushewar farin cikin rayuwata ya zo,& . ko da hakan na nufin cewa, ni zan cutu, zan yi farin ciki idan har hakan shine kwanciyar hankalin ki.
Fada min yanzun nan, me kike so in yi miki ki maida kyakkyawar rayuwarki ta baya? Abin nufi, what may be solution to your problem right now?
Ido ta sunkuyar, sabida ta kasa hada ido das hi a yanayin da yake ciki, wanda bata taba ganinsa a cikin kwatankwacin sa ba, amma hakan bai hanata fadin zahirin damuwar tata ba don samun maslaha ga zaman lafiyar zuciyarta. Allah Shi ke sanya so a zukatan bayin Sa, to bai sanya mata soysayyar Imam ba, baya ga ta  yan uwantaka. Sosai ta ce,
 Bana son ka da aure Ya Imam, na furta amma kowa ya ki saurarena, SO daban KAUNA daban, me yasa bazaku gane hakan ba? son  yan uwantaka nake yi maka. Na fada na kara ..... bazan iya zaman aure da kai ba, bana son ka as a husband.... (a matsayin miji) muharramina nake kallonka, majibincin al amurana bayan Daddy, kuma dan uwan da banda kamarsa. Idan kai dan halak ne cikin iyayen da suka haifemu, to na rokeka ka rabu dani in zauna lafiya da iyayena,& & ka yi rayuwarka in yi tawa, ko ana so dole?
Ya girgiza kai, idanunshi sun rikide, sun juye sun shagide, ya cigaba da girgiza kan kamar kadangare yana cewa,
 Gaskiyar ki kam. Ba a SO dole.....to Safah ki je na sake ki.....! Na sake ki!!& ....Na sake ki!!!
Ya maimaita har sau uku.

Ba karamin razana ta yi ba, don ta dauka zai iya yin komai amma banda wannan. Itan kuma ba wai ta fada har zuci bane, har ma da tabara ta wadda miji ya mace a kanta, domin abinda taga yayi akanta yau, tasha mamaki sosai, bayan zuwa lokacin zuciyar ta ta fara saduda, tun daga lokacin da gangar jikin su ta hadu a ofishin Mathew, wasu allurai suka huda kirjin ta suka shige cikin zuciyarta, taji wasu irin sauyuka a zuciya da gangar jikin ta, da bata taba jin irinsu ba a rayuwarta, ta san ba zai taba iya yin hakan ba, shiyasa ta fadi, har da iya shege. Don ta bashi haushi ya fita hanyarta.
Ga Imam din, ya aikata, don ya cika dan halas din cikin Uwa da Ubanshi. Wadanda ke kwance cikin kushewarsu, aka ambato su yau aka yi masa kandagarki dasu sabida ya nuna soyayya shekaru ashirin cif. Wallahi ko zai mutu babu aure, yau ya hakura da Safah, hakura ta har abada muddin ya cika dan halas din.
A lokaci daya tsoro mai tsanani ya shige ta. (Hattara mata, masu amfani da soyayyar da miji ke musu su azabtar da shi). Takarda ya dauko a aljihun motar ya rubuta ya dora mata a kan cinyarta. Ta kasa daukan takardar ta kasa magana, sai ta saki baki tana kallonshi tana kallon takardar a tsorace. Ya ja motar aguje, kamar za ya tashi sama.
Ya ce, (kamar mai tambayar zuciyarsa ba Safah din ba)  & & .Yanzu na tabbata dan halak, ba shege bane ko???
Wani irin kuka ya kwace mata ta shiga girgiza kai tana fadin  Ya Imam da gaske?? Ka sake ni??? Daya, biyu, har uku& & ???? Idonsa na kan titi bai dubeta ba bai tanka mata ba. A lokacin da yai parking a harabar gidansu. Ta dauki takardar ta dunkule a hannunta ta yi cikin gida da gudu, saura kadan ta fadi, gaba daya ta firgice ta rude, rudewa irin wadda bata taba yi ba, hankalinta ya kai kololuwar tashi a lokacin da ta rabe a gefe ta warware takardar tana karantawa;

 Ni Almustapha Zubair Dan Kasa, na saki matata Safah Dan Kasa saki uku. A bisa bukatar kanta, ina yi mata fata da addu ar alherin duniya da lahira .

Sulalewa ta yi ta zauna a kan dandaryar kasa a corridor din da zai sadata da hanyar cikin gida.... Wani irin gumi (zufa) ya soma bubbugowa daga kowanne sashe a jikinta.
Me za ta ce da iyayenta, daga tafiya asibiti? Sai saki uku ringididis? Da wane ido za ta dubi Mami? Me zata ce da Daddy bayan ta yi masa alkawarin yin biyayya ga umarninsa? Babu irin yabon da baya yi mata, ya yarda da ita da halayenta na kwarai fiye da Marwah. Itace abar misalinsa da alfaharinsa indai wajen halayen kwarai ne, Marwah ce mara kirki kullum, mara kyan hali, mara jin Magana. Ta toshe baki tana kuka, jikinta yana rawa.
Ta dade a wurin bata san inda kanta yake ba, batasan abinda ya kamata tayi ba, zuciyarta ta riga ta kekashe da tabbacin cewa, iyayenta tsine mata zasuyi ko su sanyata a turmi su kirba suyi miyar kubewa da ita muddin ta basu wannan takarda ta kuma budi baki ta gaya musu da bakinta. Don haka ta soma tunanin matsera,& & tun kamin la anar Daddy da Mami su tabbata a gareta& . tana jin sanda ya tada motar aguje ya bar harabar gidan su, tafiyar da ya tabbatar shi da dawowa& & . sai wani babban ikon Allah!!!
****






A
llah ne ya kawo Daddy zai wuce cikin gida
ya ganta a nan durkushe tana kuka, cikin mamaki da tashin hankali ya cira ta, ta mike yana tambaya  Lafiya? Me ya faru? Ina Imam din?
Ya jero tambayoyin a jere don duk hankalinsa ya gama bashi cewa wani abu ne ya faru d a Imam din, don Mami ta gaya masa sun fita tare asibiti.
Safah ba baki sai kuka take tana jujjuya kai, kawai tayi kundumbalar mika mishi takardar dake hannunta. Bai bude ba tukunna ya sata a gaba suka shiga cikin gidan juwa na hajijiya da ita tana dafa bango yayi azamar riko hannunta barin jikin shi.

Mami na zaune a falo tana waya, shigowarsu haka yasa ta katse wayar, itama tambayar da ta yi shine  Lafiya? Ina Imam din?
Dukkansu babu wanda ya bata amsa.
Daddy ya zauna kusa da Mamin, ya ciro medicated dinsa cikin brief case dinshi ya sanya, ko kadan zuciyarshi bata kawo mishi wani abu makamancin wannan ba, sannan ya soma warware dukunkunanniyar takardar ya soma karantawa.
Mami sai gani ta yi Daddy ya sulale kasa, kamin ta yunkura ta mike ya sume. Da gudu ita da Safah suka isa gareshi.
Safah hannuwa ta daga ta dora aka tana ihun a zo a taimake su. Da gudu Hajiya Maama da ma aikatan gidan dake kusa suka shigo, kowa kokarin shafa masa ruwa yake har aka samu ya farfado.
Ya shiga bin kowa da kallo a hankali, kamin ya dire idanunshi a kanta, tana gefe sai kuka da makyarkyata take yi, kamar wadda aka sanya cikin sanyin kankara.
Ya maido idon shi ga Mami wadda kansa ke bisa cinyarta, sannan ya maida idon shi ga mahaifiyarshi wadda ke ta faman yi mishi firfita da mayafinta.
Tana cewa,  Ni Salamatu me ya faru ne Aliko?
Duk sauran ma aikatan suka fita, ya rage sai su hudu.
Ya mike da kyar ya zauna, ya dauki takarda ya bawa Mami ya ce ta karanta kowa ya ji.
Mami ta bude takarda ta karanto. Itama sai ta fashe da kuka.
Ta ce,  Haka kika zaba ko Safah? Haka kike so kuma ya yi miki. Ai shi kenan ki je ga duniyar nan ta ishi kowa riga da wando.....
Hajiya Maama ta katseta,  A a, Zainabu yi hakuri kada ki yi mata baki, ku yi hakuri gaba daya ayi tunanin hanyar gyara, dukkan su kuruciya ke diban su.
Shima Imam mene ne na saurin saki, ko me za ta yi masa ai yarinya ce....
Mami cikin kuka ta ce,  wane gyara za ayi cikin saki ukku?  Yar shekaru 19-20 ce yarinya? Allah kadai ya san irin rashin mutuncin da ta yi masa....amma ni na san Imam sarai.....haka kawai ko giyar wake ya sha ba zai yi wannan aika-aikar ba.
Ga gidan nan ki zo ki zauna, mu jera kafada ni da ke....idan na yiwa mijina kwalliya ki bini da ido....wannan ce dai rayuwar da kika zaba ko? To zauna mu yi ta. Allah Ya baki sa a .
Shi kuwa Daddy tunda ya farfado neman Imam yake yi a waya, amma gaba daya layukan shi a rufe suke. Alamar yana cikin jirgi.
Tana rabe a bayan kujera sai kuka take, Daddy ya mike ya wuce ta gabanta ba tare da ya dubi inda take ba, bai ce mata komai ba, ya bi matattakala zuwa dakin sa. Mami ta mike ta bi bayansa tana ta sharbe hawaye da majina da gefen mayafinta.
Hajiya Maama ta zuba mata dundu da iya karfinta ganin yadda take kikkifta ido na rashin madafa, tace,  Yar banza, mai munafukan idanu, kukan me kuma za ki yiwa mutane tunda burinki ya cika? To Zahraddeen din mijin  yar uwarki za ki aura ko Ubanki? Bace min da gani tun ban yi miki Allah Ya isa ba.... Ta fada tana nuna mata hanya.
Sum-sum-sum Safah ta wuce ta nufi dakinta, ta kwanta a lallausar gadonta, amma yau sai ta ji kamar ta kwanta a kan kaya.
Wata irin nadama ta sauka a zuciyarta a sannu, filla-filla take tariyo majigin rayuwarta tun haihuwarta, da kaunar da Almustapha ya wanzar da rayuwarshi a nuna mata.
Shin mene ne ya shiga kanta ne da ya makantar da idanunta ga soyayyar dan uwanta? Me Almustapha ya yi mata? Mene ne aibunsa? Me take nema a da namiji da babu a Imam? Zuciya ta gama zaluntar ta, ta kaita ta baro, da ta yi mata hudubar banza ta yi mata silar kubucewar mai kaunar ta da gaskiya, kaunar da ta tabbatar har duniya ta nade, ba za ta samu makwafinta ba, indai daga da namiji ne ba daga iyayenta ba.
Me yasa ta fi baiwa soyayyah muhimmanci fiye da kauna? LOBE is not the only thing we are to go for in marriage..& . There are other important aspects; sacrifice and debotion. (Abin nufi anan, bamu zo duniya don muyi auren soyayya kadai ba. Akwai wasu abubuwa da yawa da suka fita muhimmanci cikin aure, kauna da sadaukarwa)& &
Ta yi tumus cikin nadamar da AL-AMEEN BELLO MAKARFI ya kira NADAMA MARA AMFANI. (Duba SIRADIN RAYUWA, littafin Takori na farko, tare suka fito, an sake buga shi a karo na biyu ga wadanda basu karanta ba)
Ga shi ta bata goma daya bata gyaru ba. Ta yi asarar mijin kwarai irin ALMUSTAPHA ZUBAIR DAN-KASA. Bata ga tsuntsu bata ga tarko.
Ta bata da iyayenta da Kakarta da ke tattalin ta da so da kauna, amma  yar kankanuwar biyayya ta kasa yi musu a rayuwa sabida soyayya. Wace rana haihuwarta tayi wa iyayenta, tunda basu isa su zaba mata abinda suke ganin shine alkhairi a gareta ba. Ta sanya su cikin baki-ciki da takaicin da watakila har su mutu, bazasu yafe mata ba. Idan ba Imam ne ya dawo garesu ba.
Mene ne makomar rayuwarta a halin yanzu? Wa za ta aura? Ko zama za ta yi ta yi a gida gaban iyayenta tana sa musu ido kamar yadda Mami ke cewa?
Rashin sanin hakikanin wadannan amsoshin ya sanya ta rushewa da kuka mai cin rai, kuma mai cakude da NADAMA MARA AMFANI....c
ikin kwanakin da suka biyo baya, rayuwa ta yi zafi ga Safah, wata irin rayuwa take agidan Ubanta tamkar ta wadda aka saki uwarta aka bawa kishiyar uwa mara mutunci rikonta. Mami ta daina kula ta, ta daina shiga sabgarta.
Ba a maganar Daddy, wanda ko inda take ba ya kallo, da ya kalleta gara ya ga bakin kumurci, da yana da karfin zuciyarma da korarta zaiyi daga gidansa taje ma duk inda zata, amma zuciyar iyaye data muslunci ta rinjayi komi.
Har zuwa yau din kuma bai taba ce mata komai akan al amarin ba, hankalinsa ya tafi ga binciken inda Imam ya shiga a fadin duniyar nan, domin an tabbatar masa bai bi jirgin da yayi booking ba zuwa Glassgow, wani daban ya hau, wanda ba a tantance na ko ina ne ba a nahiyar Birtaniya, har assistant dinsa Mr. Kalakari mutumin India na waya yana tambayar Daddyn dalilin rashin isowarsa a washegarin ranar daya je daukoshi a filin jirgi..
Duk wannan tarairayar da Daddy yake yi mata ada ya daina, ido kawai yake binta da shi idan ta zube agabanshi wai tana gaisheshi.
Wajen Hajiya Maama kadai take samun sanyi wani lokacin, duk da kullum itama ta tuno Imam sai ta zage ta. Ta kukkunduma mata ashariya, ta kai mata hauri ta kai mata duka da mangara, sai kuma ta koma kuka tace
 annamimiya, wallahi kin yi asara, kuma sai kin nemo min Almustapha . Tayi ta kuka.

Duk kokarin Daddy na neman layukan Imam ya kasa samun shi, don haka ya soma shirin tafiya Glasgow ya gani da idonsa da gaske Imam bai koma bakin aikinsa ba, don watakila sun hada baki ne da Mr. Kalakari ya bugo ya nemeshin don Daddyn ya debe tsammanin kasancewarsa a can, in ba haka ba ina Kalakarin ya samu lambar wayarsa? Shirinsa yake ba tare da ya gayawa kowa ba. Saidai kuma ya samu tsaikon tafiyar sakamakon tsohon pasport dinsa da ya nema ya rasa cikin takardunsa.

Mami na zaune a gefen gadonta tana sauraron muryar Ahmad Sulayman cikin Suratul-Tagabun daga cikin wayarta, ta idar da sallar la asar kenan, a lokacin ma tunanin Imam take, da halin da yake ciki. Jikinta na bata amatsayinta na UWA, Imam baya cikin kwanciyar hankali, yana cikin wani hali da yake bukatar mai kaunarsa akusa dashi ya rage masa maraicin da baiyi a kuruciyarsa ba sai a girmansa, tasa gefen hijabinta tana tsane kwallar idonta, ta yi sallama dakinta ta amsa ciki-ciki. Tunda amsa sallama ya zama wajibi ga musulmi, da bazata amsa ba.
Ta samu gefen kafafunta ta zauna, ta dora kanta a cinyoyin Mamin tana rero kuka a hankali. Mamin bata katseta ba bata rarrasheta ba saida tayi iyakacin wanda take ganin zata iya ta samu sassaucin zuciyarta sannan cikin rishin kuka ta ce,
 Don Allah Mami ku yi hakuri ku yafe min, na yi nadama na gane na yi kuskure wanda bazan iya repenting ba, wallahi sharrin zuciya da sharrin shaidan ne.
Ban taba zaton  yar maganar da na gaya mishi zai sa shi furta saki ba. Ko kadan ban kawo haka ba, sakin ma har guda uku? Mami idan kowa ya juya min baya na jure, ba zan iya jure naki fushin ba, domin dafi ne mai barazana ga rayuwata . Ta ci gaba da kuka.
Mami ba ta katse ta ba sai da ta yi mai isar ta. Abinki da da da mahaifi, a hankali ta ji zuciyarta na yin sanyi. Abinda take so ta ji, bazai yiwu ba idan bata saurareta ba.
Daga can karkashin zuciyarta ta ce,
 Ni me kika yi min Safah? Amma saboda Allah ki gaya min abin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login