Showing 57001 words to 60000 words out of 112612 words

Chapter 20 - BABBAN GORO BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY SUMAYYA TAKORI.doc

jikinta.
Ta kirayi sunan Allah AL-LADIF domin neman nutsuwa cikin zuciya da gangar jikinta dake rawa. Cikin ikon Allah nutsuwa ta zo mata.
Ta gyara gilashin idonta, a yayin da shi kuma ya zare na shi gaba daya yadda zai ji dadin kallon duk wani motion dinta sosai, yarinya kamar aljana, gaki baka amma tamkar ba indiya, irin bakaken Indiyoyin Punjabi,  yar mitsila dake, amma cikakkiyar likitar hakori, ko su waye iyayenki sun kyauta, I m edteremely impressed!
Abinda yake fadi kenan cikin ransa, wannan kallon da yake ma likitar, kallo ne na sosai, nan da nan hakan yasa matarshi ta tsargu.
Ga alama irin masu azababben kishin nan ce. Domin fizge danta ta yi daga hannunsa ganin yana neman kwala shi da kasa, ta wuce fuuu.... kamar guguwa ta bugo kofar da karfi.
Da hanzari suka bita da kallo daga shi mara lafiyan, da malamar kiwon lafiyan.
A tare kuma suka janye idanunsu daga kofar. Dr. Safah ta koma cikin nutsuwarta, ta kara gyara zaman gilashin idonta, ta bude  file din dake gabanta, cikin harshen Turanci ta ke tambayarsa abinda yake damun sa.
Da nashi hardadden harshen wanda fulatanci da Ingilishi ya sarke yake mata bayani cewa,  Hakoranshi biyu na karshe basa barin shi ya yi barci saboda azaba .
Ta mike daga mazauninta ta dawo gabanshi, ta dauki  yar cocilan ta sa shi ya bude bakin ta kama habarsa ta haska, ta lelleka ta koma kujerarta ta zauna.
Sannan ta daga bakin gilashin zuwa goshinta, ta ce,  Za a cire daya, za a yiwa daya ciko, sannan za a yi flushing, da alama kana shan zaki da yawa....
Yadda ta yi maganar, cikin jarumta ne, da nuna halin ko in kula, amma ilahirin jikinta rawa yake yi. Shi kuma kirjinshi ne yake bugawa babu sassauci. Saidai nutsuwar da yake da ita ta danne komi.
Idanuwan nan farare kal na  patient din nata sun juye sun rikide zuwa lub colour, ta kan ga irin wannan kallon cikin kwayar idon Imam, ya kasa dauke idonshi a kanta, wanda hakan ya kara kidimata.
Bata taba yarda da abinda ake kira lub at first sight ba sai yau. Wato da ya faru akanta. Ta yi maza ta maida bakin gilashinta ta ce,  Ina magana....
Ya yi wani irin murmushi, ya nitsa yatsunshi cikin sumar kanshi  Ina jin ki ai .
 To ya za ayi?
 Ki yi duk abinda ya kamata .
 Ka shirya?
Bai amsa ba, daga mata kai ya yi.
Ta mike ta dawo gaban shi, dole ta zare bakin gilashin, har zuwa wannan lokacin kallon ta kawai yake makale da murmushi a tattausar fatar bakin sa, ta cigaba da bayani
 Za a cire na cirewar yanzu, na cikon da flushing sai a dawo gobe, because you could not endure the two injections concurrently (saboda ba za ka iya jure allurar dadashi guda biyu a lokaci daya ba)
Ya langabar da kai idanunshi a lumshe,  ni na gaya miki? Doctor, ki yi duk abinda ya dace, ina da uzri ba zan iya dawowa gobe ba, yanzu haka a kan hanya nake, Abuja zamu, ciwo ya ishe ni na ci karo da asibitin ku, nikadai nasan azabar da nake sha da hakoran nan, bazan iya isa Abuja dasu basu sumar da ni ba, shine na yanke hanya na shigo .
Ta gyada kai,  Babu laifi, in yi allurar za ka jure?
Murmushi ya yi,  Me ake da  yan mazan?
Itama ta murmusa. Ta mika hannu a hankali ta kama habarsa inda wani lallausan gashi mai santsi na fulanin usli ya kwanta tubus a kan fuskarsa.
Ta jawo kayan aiki, idanunshi ya rufe, ta tsira mishi allurar dadashi ko motsi bai yi ba. Duk da azabar allurar. Nan da nan ta ballo hakorin, ta danne jinin dake fita da auduga, amma kamar ba jikinsa ake bantara ba, hakan ya faru ne a dalilin cewa, ya fada cikin wata rindimemiyar soyayya marar misali.
Har ta kara yin wata allurar, ta yi ciko ta fara flushing bai bude idon shi ba. Sai da ta gama tsaf ta ce da shi,  Na gama .
Sannu a hankali ya bude idanunshi a kanta, ya kai hannu daman shi ya dafe kansa. Ya ce,  Akwai wani ciwon Doctor...
Ta dago da hanzari ta dubeshi, ,  Name kuma?
Ya yi kasa da murya  Ciwon L ne!
Dariya ta kama ta, saboda yadda ya yi maganar kamar karamin yaro. Ba ta yi aune ba sai ji ta yi ya cire gilashinta,
 Dubi kwayar idona Doctor, wallahi ciwon  L ne .
Murmushi ta yi,
 To Allah Ya yi maka magani, don dai mu nan, bamu da maganin wata cuta mai wannan sunan, baya ga hakori, throaght da dadashi, watakila sai dai ko a kasashen da suka ci gaba, in kai sa a sai ka samu......
Ya girgiza kai cikin dariya  Alright! Shawararki abar dubawa ce . Ya dauki kan wayarta dake nan kan tebirinta, kan ta ce komai ya zuba lambobinshi a ciki ya kira, sannan ya yi sabing ya mike, ya rankwafa daidai kanta har suna iya jin hucin numfashin juna.
Cikin sassanyar murya ya ce,  NASIR is in lub.....pld Doctor sabe a soul... . Ya juya cikin kuzari da sassarfarshi ya fice daga ofishin.

Binsa ta yi da kallo tana murmushi har ya fice daga ofishin, wannan shine Da namiji na uku da ta ji shi har cikin zuciyarta. A yau kuma take addu ar Allah Ya sa kada shima ya kubuce mata, kamar yadda ta rasa Imam da Zahraddeeni. Bayan ta dandani wahalalliyar soyayyarsu mai wuyar fita daga inda tayiwa kanta muhalli cikin zuciyar da ke cikin kirjin ta.
Har zuwa lokacin kamshin sa bai bar ofishinta ba, ta sauke idonta a hankali a kan tulin  files din dake gabanta wanda take tantamar anya za ta iya ci gaba da duba su? Ba ta da wannan kuzarin.
Sai ta tattarasu ta ture gefe, ta dau wayarta ta kira Dr. Garba Bilal ta ce ya zo don Allah ya taimaka mata za ta wuce gida ba ta jin dadi.
Ta tattara  yan komatsanta ta jefa a jaka, ta fice ko gabanta ba ta gani sosai.
Mami sai ganinta ta yi ta dawo da wuri, ta ce,  Ya na ganki yanzu?
Ta yamutsa fuska  Bana jin dadi ne sosai Mami .
Ta ce,  To ki sha magani ki kwanta ki huta, duk ke kika ga za ki iya ai, wannan aikin wahalar da har cikin dare baka tsira ba .
Ta murmusa ta wuce dakinta ba ta ce komai ba. A ranta ta ce,  Allah na tuba in ban yi aiki ba me zan yi? Imam ya tafi ya barni, bai yi min uzri da kuruciyata ba, bai kara waiwayoni ba, wanda ke nufin ya daina so na...!
Ta yi juyi a lallausan gadonta, kwalla ta cika idanunta. Tabbas duk wanda bai yi biyayya ga iyayensa ba, yana tare da nadama& & yau shekarunta ashirin da bakwai babu aure& & ko sai yaushe? Ko Imam zai dawo? Ko zata samu ya yafe mata? Ko zata samu ya maida ita ta goge kuskuren ta na baya? Ko wani auren zata yi? Ta ma manta cewa Imam, ya haramta gareta kwata-kwata. A yanzu kam ta tabbatar Soyayya aikin banzace, domin abuce mai gushewa, zata iya gushewa a kowanne lokaci kamar ba a yi ta ba, ba kamar KAUNA ba.
Musamman idan zuciyar da gangar jikin suka samu abinda sukeso, amma banda albarkar iyaye.
Ga dai Marwah can da ta yi biyayyar mukus da ita a dakin mijinta, da ba soyayyar ce ta hadasu ba, har sun fara tara zurri a, ina soyayyar da Zahraddeen ke mata? Da ya kunshe matarshi a daki ya manta da ita? Yake bata  ya ya daga jikin sa da yayi mata alkawarin nata ne ita kadai? Meye ribarta cikin soyayyah da jayayya da iyaye akan soyayya?

Wata zuciyar tace da ita  Baki ga komai ba, yanzu zaki fara rayuwa Safah! Rayuwar aure ba??? Ga diya mace ba abu ce mai sauki ba, ba abinda ya kaita samun kalubale, musamman wadda ba a ginata tun farko da albarka da biyayyar mahaifi ba. Don shi Allah Ya baiwa damar zabarwa diyarsa budurwa mijin aure.

Mu sauke numfashi, mu bi Dr Safah Dan kasa cikin rayuwar auren ta, musamman da muka leka muka hango kamar ta samo wani BABBAN GORON, ko zata tauna? Ta ji shikuma yaya yake? Ko kuma tsohon GORON zata cigaba da yiwa jiran tsammanin warabbuka? Mu bi ta a hankali.
****
Ta bude dakinta ta shiga ta kwanta a gadonta na alfarma. Daga kwancen da take ta mika hannu ta dauki remote din A.C a kan side drower ta karo karfin iyakwandishin din, sannan ta lumshe ido ta fada duniyar tunani kala-kala.
Wayarta dake gefe ta yi kabbara, cikin melody mai dadi, wannan shine tune din wayarta.
Ta mika hannu ta dauka ta duba, bakuwar lamba ce ta kamfanin Glo, ba ta san lambar ba, kuma a ka idarta ba ta daukar wayar da ba ta san ko ta waye ba.
Sai da wayar ta ci kukanta ta koshi Safah ba ta ko kara bin ta kanta ba. Ta yi zurfi a tunanin abin da ya kamata ta yi wa rayuwarta tunda sauran kuruciyarta.
Duniya gaba take kara yi kullum ba baya take yi ba, duk wani burin rayuwa da dan Adam ke nema babu wanda Allah bai bata ba.
Me ya rage mata a rayuwar duniyar nan banda AURE? Da Imam zai dawo tsayin wadannan shekarun ya isa ace ya dawo kowanne irin fushi ya yi da ita kuwa.
Idan ita ta yi masa laifi me Mami da Daddy suka yi masa da zai nisancesu har tsayin wannan lokacin?
Gara ta yiwa kanta fada ta hakura da Imam ta kama daya cikin dimbin masoyanta ta yi aure, ta ginawa kanta rayuwa irin ta kowacce diya mace, wato rayuwar iyali mai albarka.
Hakan ba yana nufin cewa ta daina son Imam bane, amma gara ta wankewa Mami da Hajiya Maama zuciya haka ta yi aure, ko ba dan komai ba sai don cikar mutunci da kimarta, da kuma farin cikin mahaifiyarta da kakarta.
Zuwa wannan lokacin wayarta ta yi ruri har ba adadi, sai kuma ta jiyo alamar shigowar sako (tedt message).
A kasalance ta dauka ta bude.

 Ki dauki waya ki ji mai zan ce miki, rashin daukar wayar ba zai sa ba, kuma ba zai hana ni yin kiran ba .

Ta shiga mamakin wannan karfin hali, ba ni na neme ka ba, kai ka neme ni sannan ka ce za ka yi min gadara?
Kawai sai ta kashe wayar gaba daya ta yi kwanciyarta.
Wunin ranar zungur a daki ta yi shi, ga shi tana fashin sallah, ba abin da ke tayar da ita daga gado sai shiga bandaki.
Washegari haka ta tashi sukuku, Mami ta rasa gane kan diyar tata. Gaba daya ta birkice mata tana ta kuka.
Tambayar duniya Mami ta yi Safah ta ki cewa komai. Addu a kawai take ita ma Allah ya dau ranta ta bi Daddy ta huta da azabar zuciya da nadama.
A wannan lokacin babu wanda Mami ta tuno sai DADDY, magana daya mai sanyi zai gayawa Safah ta warware daga bacin ranta.
Ita ma sai ta saka kuka ta ce,  Safah mutuwa kike so nima na yi? Kukan ki na daga min hankali, idan ba ki ji tausayina ba bai kamata ki kara min damuwa a kan wacce nake ciki ta rashin IMAM ba .
Cikin kuka ta ce,  Ki yi hakuri Mami, nima shi nake son gani. Mami na kasa son kowa, Mami shi kadai nake so, ki taimake ni ki nemo min shi .
A yau har na fara yin tunanin yin aure, sai kuma nake ganin idan nayi hakan ban kyauta masa ba, zai kara tabbatarwa da cewa shine bana so din muddin na auri wani. Ya dawo ya tadda ni a gidan aure .
Ta ci gaba da kuka sosai.
Zuciyar Mami ta karaya sosai, ta yarda al amarin Safah ba da wasa bane. Watakila hakki ne yake tambayarta.
Ta jawo ta a hankali ta rungumeta, ta ce,  Da da akwai abin da zan iya a kan ganin Imam da na yi tun kafin ki furta.
Kina gani ba irin neman da Daddy bai sa anyi ba, zancen dai daya ne ya bar Glasgow, babu wanda ya san inda ya koma.
Ina so ki tuna cewa Imam ba yaro bane, duk abin da zai yi yana sane, ba zai kai kanshi ga halaka ba duk rintsi. Sannan babu sauran maganar aure a tsakanin ku koda ace ya dawo. Ki dawo cikin hankalinki kisan abinda kike ciki.
Don haka ni kullum cikin mafarkina lafiya nake ganinsa. So ki cire Imam a ranki haka, ki zabi mutum guda cikin maneman ki ki yi auren ki ki huta, ko don muma mu huta da surutun mutane a kan rashin auren ku ke da Shahidah.
Don Allah Safah ki rufa min asiri ki yi aure ko na samu sukunin zuciyata ,
Ta share fuska da mayafinta ta ci gaba da cewa.
 Kin ga Shahida ta fidda miji, da ke wata mai kirki ce sai a hada bikin ku a huta. Ku ku huta, muma mu huta .
Ta rungume mahaifiyarta. Ta ce,
 Mami insha Allahu ina ji a jikina lokacin aurena nima ya zo .

****
A washegari ba ta je office ba, don haka ba ta je ba sai ranar Laraba. Inda ta cimma aiki jingim, don ma wai a hakan Dr. Garba ya taya ta.
Abu na farko da ta fara yi shine, kunna wayarta. A take kuma sakonni bila-adadin suka soma tittidowa.
Duk rabi daga wannan lambar ta Glo ne. Ba ta tsaya karantawa ba duk ta goge su. Don ta dauki mai wannan layin a dan rainin hankali kawai, sannan tasa wayarta a boicemail.
To amma kwakkwafi irin na zuciya, sai ta dame ta da son sanin waye wannan? Meye dalilin shi na wannan kira haka da wadannan ssakonni haka??
Ta bude file na farko dake gabanta kenan aka turo kofar ofishinta babu sallama, aka maida kofar a hankali aka rufe.
Ba ta dago ba don a zatonta patient din ce, tana ci gaba da rubutunta ba tare da ta dago din ba, ta ce,  Habe a seat plz . Ta ci gaba da rubutunta.
Tsayin minti biyu sannan ta dago don ta ji alamar patient din bai zauna ba ko bata zauna ba. A lokacin ne idonta yai arba da patient dinta da ya yi mata karan-tsaye a zuciya kwanaki biyu da suka wuce.
Sanye yake da caftan na wani lallausan yadi fari sol. Dogon Bafillacen, a idanunshi siririn farin tabarau ne wanda ya kara kwarzanta kyawun halittar sa, ya fiddo ilhamarsa, bai kuma boye kwayar idanunshi ba, wadanda suka canja kala daga farare kal zuwa brown, suke kuma cike taf da wani babban al amari da ba ta hango iyakarsa ko karshensa ba.
Ta dan bude baki tana murmushi mai nuna sanayya, ta kasa magana amma har cikin zuciyarta murmushi take. Sai kuma duk ya cika mata ido, ya yi mata kwarjinin da ya sanyata mikewa tsaye (alamar girmamawa irin ta Bature).
Sannan ta ce a hankali,  Habe a seat plz .
Bai zauna din ba dai, kallon ta yake da idanuwa narai-narai kamar za su zubo da hawaye saboda maikon su (oily eyes) masu dauke da  tensions da rigingimu masu yawa.
 To shi kenan .
Ta fada

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login