Showing 36001 words to 39000 words out of 112612 words

Chapter 13 - BABBAN GORO BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY SUMAYYA TAKORI.doc

kuma ta yi biyayya, ai ko bata cancanci jin tausayi ba, ta cancanci rarrashi. Babu abinda zai ragu daga jikin ka don ka yi hakan. Ni na gaya maka idan har za ka jure da hakan wallahi za ta sauko .
Murmushi ya yi yana mamakin a ina Shahida ta san duk wannan? Wannan ba abin mamaki bane domin Shahidah  yar siyasa ce. Sai dai bai tambaye ta ba, bai kuma ce ya karbi shawarar tata ko bai karba ba? Saidai can a karkashin zuciyarsa ya yarda cewa kowanne irin ilmi da irinnasa amfanin.

A kokarinsa na son kawar da tasirin da zantukan Shahida suka suka soma yi a yanayin sad a zuciyarsa kada ta fahimci hakan sai ya ballo sabon zance. Ya ce,  Ke kuma aure sai yaushe Shahidah? Duk wadannan Alhazan da ke yi mana sintiri a gida kullum ta Allah ina lura dasu fah, me zai hana ki fidda daya ki aura idan hankalinki ya kwanta da shi? .
Ta ce,  Wallahi Ya Imam duk suna da iyali, ni kuma ba zan auri mai mata ba .
Ya ce,  Allah ya yi zabin alheri, amma ya kamata ki san cewa kin girma fa (at 26) ya kamata a ce ne a yanzu kina da yara biyu .
Dariya ta yi ta fita tana cewa,  Tunda kai ga shi ka riga ni yi sai in jira naka  ya yan mu raba, idan ban samu mara mata ba .

Shi sam ya mance da wani sako da ya shigo mishi, Shahidah ta tafi da hankalinsa sosai. Sai da ya gama hada kayanshi tsaf, sannan ya dauki wayar, a take kiran shugabansu Mr. Ben ya shigo. Ya tambaye shi har yau bai taso bane?
Ya ce,  Zan taso anjima kadan .
Ya zauna bakin gadon shi ya bude sakon, bai san lambar ba. Ya karanta kamar haka:

 Za ka tafi, baka ce da Daddy komai ba .

Nan take ya gane mai lambar, ya yi murmushi ya koma ya kishingida da pillow a karkashin hakarkarin sa, ya tura mata gajeren sako.

 Ban san mai lambar ba .

 And you want to know waye ne koh?

Da alama a kufule tayi reply din. Ya yi murmushi ya kai hannu cikin sumar kanshi yana cakudawa, a yayin da numfashinsa ke racing yake fita da sauri da sauri.
Ya yi kokari ya yi replying amma ya kasa danna alphabet s din, saboda yadda wata irin kasala ta saukar mishi. Wani zazzabi-zazzabi ya soma kokarin rufeshi nan take sabida azabar soyayyar da yake dandana.
Gashi dai fada take yi ba kalaman soyayya ba, amma ji yayi kamar rungumeshi tayi tana blowing kisses on him. Gaskiyar Shahidah ne wannan dutse ce mai babban daraja like a diamond& & bazaka iya sayensa da sauki ba!!! Kowanne  acting dinta akansa burgeshi yake mai dadi ne ko mara dadi.
Da kyar ya samu ya rubuta kalmar
 Eh .
Ta ga nema yake ya yi yawo da hankalinta, sai ta kashe wayar gaba daya, ta koma gadonta ta kwanta abin tausayi. Ta rasa abin da ke mata dadi.

Sai da ya yi wanka ya zuba orange shirt DKNY product, riga mai dogon hannu da bakin wandon jeans, ya taje sumarshi ta kara kwanciya akansa, ya yi shiri tsaf kai ka ce half-caste ne, wato (ruwa biyu). Duk da duhun kalar fatar jikin sa.
Ko da yake ta wani fannin Imam din ruwa biyun ne, Mamanshi Shuwa Arab, Baban shi Bahaushe.
Yana rataye da wata kyakkyawar bakar jaka wadda su komatsen passport, ID card, wayoyinshi da mukullai ke ciki, ya nufi dakin Hajiya Maama suka yi sallama, sannan ya taho dakin Mami.
Sun jima suna sallama ya kasa tafiya, kuma ya kasa tambayarta abinda idanun shi ke son gani. Gane hakan da Mami ta yi, ya sanya ta ce,  Ka je mana ku yi sallama da kanwar taka .
Ya ce,  Kyale ta Mami, ita ya kamata ta fito ta yi min rakiya amma ban isa ba. Don haka kawai ki gaishe ta, ki gaya mata cewa, na tafi .
Mami ta rike hannunshi ta ce,  Idan ita yarinya ce kaima yaron ne da za ka dinga biye mata kuna kunci da juna?
Wannan ba ya cikin tsarin musulunci, sam baya ciki, ko da ace ba ma aurata kuke ba, what is the cause of all these nonesense? .
Ya ce,  ita za ki tambaya Mami, ba zan dinga shiga al amarinta tana harara ta ba, ko ba mijinta bane ni ai gaba nake da ita, amma yarinyar nan ba ta jin kunyar ko a gaban waye ta harare ni .
Mami ta yi murmushi ta ce,  To ka yi hakuri, babba juji ne .
Ya ce,  A a, wallahi ban da ni Mami, yanzu sai in targada ta kuma in kwana lafiya wallahi .
Ta ce,  Je ka ku yi sallamar ka yi hakuri ta ci albarkacina .
Tana rike da hannun sa har saman bene, ta murda kofar anyi sa a ba ta rufe da mukullin ba, suka shiga Imam na bayan ta.
Kudundune take cikin bargo, sai rawar dari take. Mami ta ce,  Lafiya Safah? Duk uban zafin nan da ake kika shige cikin bargo?
Ta bude idanunta a hankali, sun kankance sunyi ja. Da sauri Imam ya karasa ya janye bargon, ta yi hanzarin dunkule jikinta saboda kananun minis dake jikinta.
Daidai kanta ya zauna ya kai hannu bisa goshinta, zafi rau kamar wuta, sai rawar dari take, hakoranta na karo da juna kaf-kaf-kaf!
Ya ce,  Subhanallahi, Mami ba ta da lafiya...
Duk ya gigice ya rude, rudewa da gigicewa irin wanda Mami bata taba ganin yayi ba. Tuni ya hullar da jakar hannunsa. Itama Mamin ta karaso ta dauki kanta ta aza a cinyarta, ta ce,
 Kashe kanki kike so ki yi Safah, ki dinga kulle kanki kina cuta ke kadai cikin daki?
Ba ta amsa ba kwayar idanunta ta mayar ta rufe. Zara-zaran gassun idonta suka bi idon suka yi linkif.
Mami ta nuna mishi doguwar riga a sakale jikin  hanger ta ce dauko ta sa mu tafi asibiti, kai kuma ka tafi kada jirgi ya tashi ya barka .
Wani irin kallo ya yiwa Mamin ya ce,  In je ina Mami? Alhalin bata da lafiya? cikin fushi da haushin Safah Mami ta ce,
 To zaman ka ne zai sa ta warke? Ko me ya same ta ai ita ta jawa kanta. Ayi mutum sai taurin kai da rashin tawakkali? Za ki hada kanki da hawan jini haka kawai? Me aka yi miki? In dai Imam ne tafiya zai yi ya bar miki kasar ma baki dayanta ba garin ba.....
Aure kuwa saidai ki mutu, ko kin mutun zamu sa shi ne kawai ya wankeki ya kaiki kabari ya dawo mu shafa fatiharsa da wata, wadda ta fiki da duk abinda kike takama dashi, ni banda kai ma wa zai kwashi wannan mai bakin halin da bakar zuciyar?
Yayi dariya aransa yace  mami kenan , a fili ya ce,  Mami ni fa ba inda za ni sai Allah Ya bata lafiya
Ta ce da shi,  To gwale ni (gwasalewa), ai dama kai ba a yi ma gwanin ta in dai akan ta ne .
Ya motsa baki, yana so yayi dariya. Ta taimaka mata ta sa rigar ta rufa mata mayafi, Mamin na rike da ita suka fito.
Mami ta ce,  Ni ba zan je bama, kuje sai kun dawo Allah ya sauwake. In kuma jirgi ya tashi ya barka kai ka jiyo .
Har jikin mota ta rako su, ta bude mata kofar gaban motar ta shiga ya tada motar masu gadi suka bude get ya ja motar suka fita.
Mami ba ta koma ba sai da ta ga fitarsu daga get din gidan, ta koma cikin gida tana addu ar Allah Ya nuna mata ranar da za ta ga Safah da Almustapha matsayin mata da mijin dake matukar son junansu, ko yaushe ce wannan ranar? Ko tanada rabon ganinta?? Ko yaushe zata zo??? Ko zata zo din kuwa???? Ko dai mafarkanta na gaya mata gaskiya ne????

Zuciyarta cike take da wani irin tsoro da firgici mai yawa a dalilin mafarke-mafarkenta a dan tsukin akan Safah da Almustapha, masu nuna mata ko zasu yi zaman aure, to ba yanzu ba. Sai can wani karni mai zuwa a nan gaba. Lokacin da al amuran rayuwa zasu juye su rikide su chanza da al amura marassa dadi. Ya kuma sa tana da rabon ganin  ya yansu da jikokinsu. Har ma da tattaba-kunne in Allah Ya nufa.
A lokaci guda kuma tana tunanin halin da Marwah ke ciki da nata angon, ko su kuma wace irin wainar suke soyawa? Tunda wadannan har yanzu sun ki daidaita kansu, su san cewa Annabi ya faku. Ba duk abinda kake so a rayuwa kake samu ba kuma ka zauna lafiya. Amma su sun ki gane hakan da gangan.

Littafi na biyu 2, tare suke da dan uwansa.
-TakoriBABBAN GORO& ..2
A
sibitin da  file din gidansu yake can suka nufa, basu sha wahalar ganin likita ba, likitan Bayerabe ne.
Ya duba ta sosai, sannan ya yi mata B.P ya girgiza kai ya dubi Imam wanda ke rike da hannun daman ta duk da halin da take ciki bata fasa zabga mishi harara ba, harara mai zafin gaske, a lokaci guda kuma tana kokawar kwace hannun nata daga cikin nasa, amma bai damu ba, ko kuma bai ma kula ba da abinda take yi din ba, domin lafiyar ta ce ta dame shi a wannan lokacin.
Dr. Mathew ya dubi Imam ya yi murmushi ya ce,  Tunda bata so ka sakar mata hannun, baka ganin yadda kake shan harara ne?
Kansa ya rausayar. Ya ce,
 Kyale ta Doctor, ni ai har na saba, da harara tana tabo na tabbatar da yanzu babu masaka-tsinke a jikina .
Dariya Dr. Mathew ya yi, ya ce,  Mrs. Safah mene ne damuwar ki? Me kike so baki samu ba? Ga irin wannan caring-husband tareda ke?? Mene ne matsalar ki a rayuwa da kika bari har zuzzurfan tunani da damuwa ya janyo miki high blood pressure da kuruciyarki?
Shima likitan hararar aka zabga masa, tana so ta ce,  Wannan ba abin da ya shafe ka bane . Amma ba ta so ma su ji sautin ta. Da ya ishe ta da nacin tambaya sai ta kwantar da kai bisa tebirin shi ta saka musu kuka.
Imam ya tsugunna a gabanta idanunshi sun yi jajir don yadda sautin kukanta ke ratsa zuciyarsa yana dagula masa kwakwalwa, ya dago kanta daga tebirin ya rungume ta, abinda bai taba faruwa tsakaninsu ba, wani irin shock jikkunansu suka karba a lokaci daya, jikinshi???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? yana rawa muryarshi tana karkarwa yake lallashinta. Abinda bai sani bane ko kuma ya sanin yasa kafa ya take sanin da gangan, duk da baya so ya yarda cewa hakan dinne, zuciyarshi da gangar jikinshi aiki suke according to (abisa ga) maganganun Shahidah. Abinda shi kansa bai taba tsammanin ya iya bane wato (lallashin mace).
Muryarshi ta yi rauni ya ce,  Safah nine dai baki so ko? Wannan ne damuwarki? To ki kwantar da hankalin ki zan yi miki duk abin da kike so ko da zai hada da rabuwa ne, in dai hakan shine samun lafiyarki, farin cikin ki da kwanciyar hankalin ki.....
Amma ba yanzu ba ki bani lokaci in yi nazari sosai, ta inda hakan ba zai batawa iyayenmu rai ba, ko su yi fushi da dayan mu akan kin yi musu biyayyah. .
Ga mamakin shi sai ya ga ta dago. Ya kai hankicinshi yana dauke hawayen dake zuba daga idonta, ya akayi- ya  aka  yi ya kai ga runguma sosai yana ta faman lallashin ta, abinda ya kaishi ga soma sumbatar dogon wuyanta, ba tareda zuciyarshi da gangar jikinshi dake ingiza shi ga yin hakan sunyi shawara dashi ba.
Shaf! Ya manta da cewa basu kadai bane, ba a gidansu bane, Mathew yana zaune, ji ta yi kamar ya katse gudan jinin da ke gudana a cikin ilahirin jikinta, ta nemi numfashinta ta rasa na wucin gadi, don wani abu ne da babu wanda ya taba yi mata a rayuwarta tunda iyayenta (Zainabu da Aliko) suka haife ta.
Wani  situation ne tamkar  electrical shocking wanda ya tsirga har cikin kwakwalwarta.
Dr. Mathew sai ya yi sanda ya wuce ya fice ya bar musu ofishin. Rufe kofar shi ne ya dawo dasu hayyacinsu, dukkansu suka zube ragwaf, cikin kujera, don jikin kowannensu ya gama mutuwa suna kokarin daidaita numfashinsu. Kamar wadanda suka yi gudun 1000mile.
Amma har zuwa lokacin bai saki hannunta ba, ta yi ta yi ta kwace ta kasa, sai ta kai masa cizo a damtsen sa har sai da ta ji hakoranta na shirin karo da juna amma ko gezau bai yi ba, kamar ba jikinsa ta huda ba.
Jini ya soma zuba amma bai kula ba, karewa ma, sai ya kara fizgota da azama ya rungume yana lallashi, ban baki, ban hakuri da kalamai na soyayya, masu tausasa zuciya. Wadanda a tsammanin sa, ba daga bakin shi Imam suke fitowa ba. Don bai san dasu cikin kwakwalwarsa ba. Gaskiyar Mami ne da tace  & . ranar lallashin bata zo ba ne, Imamu Almustapha& & ..
Sai ta rage sautin kukan ta tana shessheka a hankali, tana shakar lallausar kamshin akba-amara dake tashi a hankali daga jikinsa. A haka Dr. Mathew ya dawo ya same su.
Yana murmushi ya rubata mata magungunan da suka dace da ita, musamman wanda zai kawar da febern, tare da gargadin ta cewa ta cire ko ma meye ke damun ta ko ta nemawa kanta solution tunda bazata gaya mishi ba ya bata shawarar da yake ganin zata amfane ta, idan har tana son ingancin lafiyarta.
Imam ya yi mishi godiya, bayan ya karbi takardar maganin. Mathew sai ya kirashi ya nuna mishi hannunsa da biro. Da sauri ya kalla, hannun na tsiyayar jinni, a lokacinne radadi na azaba ya ziyarceshi. Amma bai tsaya ba balle ya karbi taimakon da ya lura Dactan nason yi mishi, haka ya juya ya fita.
Yana rungume da ita a barin daman sa suka fito zuwa wajen mota, ba ta da karfin da za ta taka kafafunta guda biyu, don haka ne ta yarda har suka fito a hakan.
Dr. Mathew shikadai a ofis takaici kamar ya kasha shi, buga teburinsa yayi da kafarshi ta dama, cewa yayi  shiiiit! Ya antayo zagi cikin yarensa ya dannawa hausawa, a wurinshi wawaye ne da suke nuna suna son mace, ita din banza! Kamar Imam??? Shi ina zai tolerating wannan iskanci??? Suna so su maida kansu Indians wadanda basu da abin yi sai kashewa kansu rayuwa don soyayyah.
Shi ya bude kofar motar ya zaunar da ita ya rufe, sannan ya zagaya ya shiga mazauninsa. Tafiya yake sannu-sannu, kamar bai son ya daina tukin. Amma kansa zagayawa yake jiri na dibarshi. Sanyin na urar sanyaya mota na ratsa jikkunansu, wanda ya hade da kamshin jikin kowannensu, tare da kamshin air fresh din motar na turaren  oud-abyad . Ya saukar da nutsuwa da aminci a zuciyar Imam har ya soma jin zai zai karbi Safah da duk abinda ta zo da shi albarkacin kaunarsa gareta, a nata bangaren itama tata zuciyar sanyi take yi sabida yanayin,ya wanke zuciyar SAFAH daga daci da kuncin dake cikin ta. Ta fara tunanin solution kamar yadda Mathew ya ce. Ba ta hanyar nuna kiyayya ba.
Har ta soma jin kiyayyar ta ga auren da aka yi mata da dan uwanta rabin jikin ta Almustapha ba da son ranta ba na decreasing gradually da 50%. (raguwa a hankali da kaso hamsin cikin dari). Ta riga ta yi amanna da cewa ZAHRADDEEN MAITAMA& .. ya haramta gare ta. Babu soyayyar shi ko daya a halin yanzu cikin zuciyarta, tun daga ranar da aka daura auren sa da  yar uwarta rabin jikinta. Ba kuma wani daban take hangowa ba take son neman maslaha da Imam sabida shi ba. Zahraddeen is her past, and her husband (Imam) is her present& & then why the hatred? (Kiyayyar ta mecece?)
Ta soma kalubalantar kanta da cewa,
 Me ya hanata son dan uwanta? Me ya hanata karbar soyayyar mijinta dake sonta da dukkan zuciya, ruhi da gangar jikinsa? Amsar mai wuya ce idan aka tirketa aka ce sai ta fadi. Domin ita kanta, ba za ta ce ga dalili ba.
Abinda ta sani kawai shine, ba ta son Imam da soyayyar aure, saboda ya nuna mata soyayyar ne a lokacin da bai isa a ce ta san menene bambancin so da kauna ta  yan uwantaka ba.
Gashi ta dandana SO akan wanin sa, ta san dadin sa da dacin barin sa. In bacin hakan ita kanta tasan Imam banda soyayyah ta Allah babu abinda zai ci da ita. Tunda ba fin sauran mata gashi aka ta yi ba.

Shekarunsa goma yana karatu a Birtaniya, wadanne irin mata ne bai gani a duniya ba? Amma ya tsallako su ya dawo, sabida ita, ita kadai ranta. Alhalin ba wani abu ta fi sauran mata ba ba kuma kyau ta fi kowa a duniya ba, sai soyayyah ta lillahi da haduwar jini. Wadda yake kimsa ta a zuciyar bayinSa ba tareda yayi shawara dasu ba.
Menene laifin mai son ka?

Ji ta yi ya tsayar da motar a gefen titi, ta yi saurin dagowa ta dube shi da idanun bidar dalili cikin kokarin boye sabon tunaninta da rauninta. Kallonta yake, da idanuwa masu sanyi, wadanda ke cike taf, da so da kauna, kallon ta yake da idanuwa masu cike da soyayyar da biro ba zai iya rubutawa ba.
Amma hakan bai sa ko kadan zuciyarta ta russuna ba, daga matsayin da zuciyartata ta bashi; bloody

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login