Showing 108001 words to 111000 words out of 112612 words

Chapter 37 - BABBAN GORO BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY SUMAYYA TAKORI.doc

nice person, sannan soyayyar da yake yi mini ba mai fassaruwa ba ce. Sai na so shi a hankali, na kuma fahimci cewa jiran tsammanin warabbuka bai dace da diya mace ba.
Ko kai ka zauna da Lamido na awa daya sai ka so shi, saboda halayensa masu nagarta da karfin addininsa. Sai kuma kaddarori iri-iri suka yi ta fada masa wadanda duk masoyinsa dole ya tausaya masa.
Lamido ya sha wuya a hannun matarsa saboda ya aure ni (ta gaya masa komai). Har ta zamo sanadin ransa.
Don haka dalilai da yawa ne suka yi sanadin soyayyata ga Lamido, amma ba don na daina tunaka ba. Ko na daina sonka.
Ina rokon ka da ka goge wannan zargin rashin son da kake yi mini. I LOBE YOU BERY BERY MUCH....!!!
Sai ya kankameta suka yi ta fadawa juna sirrin zuciyarsu, kowanne maganganu ne na tsohuwar soyayya yake korawa dan uwansa. Wadda a yau ta zamo sabuwa dal! A cikin ledarta.
Tun Mami na jiran fitowar likitar da hakorin da aka banbaro har dai ta yanke shawarar zuwa ta ga halin da suke ciki ko ciwon ya yi (worsen) ne (ya munana) a tafi asibiti tunda ba kayan aiki gare ta a nan ba.
Da budewarta, da shigarta da fitarta duk basu sani ba. Ta koma falo ta zauna ta zuba tagumi tana mamakin yaran zamani dake yiwa Ubangiji abinda suka ga dama.
Tunani ta yi ko ta dauko bulala ne taje ta yi musu sittin-sittin ne?  Yan banzan yara suna son juna amma suna wahalar da zukatansu, ita ma suna wahalar da ita.
Gara kawai ta yi maganinsu, watakila bulalar ba ta hau kansu ba, tunda ba ta ga komi ba bayan runguma. Ita kuma ba ta san hukuncin runguma a musulunci ba.
Tana nan zaune ta saka ta warware duk ita kadai, sai gasu sun fito Safah rike da brief case da mukullin mota.
 Mami zan dribing Ya Imam to office, jikin bai gama murmurewa ba .
Ta balla mata harara, duk sai jikinsu ya yi sanyi.
Ta ce,  Ku zauna mu yi magana .
A gabanta suka zube dukkaninsu.
Sai ta mike taje ta taho da Hajiya Mama, suka zauna dukkaninsu. Ta ce,  Hajiya zauna sosai ayi maganar nan a gabanki.
Yaran nan sun rainani, basa ganin kimata, sai tamaula suke min da hankali don sun ga babu Daddy.....
Nan ta soma kuka. Hajiya ta ce,  Yi hakuri Zainabu, fitar hawayenki a kansu musiba ce ba karama ba garesu. Gaggauta ki yafe musu kome suka yi miki kafin mala iku su rubuta .
Mami ta ce,  Na yafe musu, amma wallahi yau za a yita ta kare ba za su sa min hawan jini ba in ji da abin da ya dame ni .
Hajiya ta ce,  To sun gode. Yanzu me aka yi?
Ta ce,  Shi ya ce ba sonta yake ba, ita ta ce min Sulaiman ta zaba ta aura tunda ba sonta yake yi ba. To mene ne dalilinsu na yin soyayyar shan minti?
Ai ba Safah da Imam kadai ba, hatta Hajiya Mama muguwar kunya ta kama ta. Su kuwa kara bajewa sukai a kan kilishi kamar su ce da kasar ta tsage su shige, ko dagowa sun kasa yi. Harshensu ya sarke balle ya furta kalaman kare kai ko jumlar  ba haka bane .
Hajiya Maama ta ce,
 Zaynabu kai! Wace irin magana ce haka mara dadin ji? Na shaidi yaran nan, wallahi ko Imam zai yi ba dai da Safah ba, babu wata kyakkyawar alaka tsakaninsu, sai dai ko da su Barbarar tasa, amma ba dai Safah ba .
Mami ta gaggalla musu harara ta ce,  Gasu nan tambaye su. Me suke yi a daki tun dazu daga zuwa duba hakorin karya? Ra ayal aini na gansu .
 In za su yin su wawayen ina ne da za su bari ki gane?
 Rabu da ya yan yau Hajiya, sun fi iyayensu wayo da zallar rashin tsoron Allah. Don haka na gaji, jibi insha Allahu za a daura aurenku in ya so ku kashe kanku don soyayyar ko kiyayyar ko sakin rashin hankali irin wanda ka saba ka gudu a nemeka a rasa.
Duk shirin da na ke yi da kai daga yau na daina. Sannan ba ni kara kwana uku a kasar nan sai ka maida ni gida, in ba haka ba ku ga tsiya irin tawa, don wallahi bulalar mazinata zan muku tunda nan kasar arnan basa bin shari ah.... Ta ci gaba da kuka.
Ji da Imam ya yi Mami ta dauki zafi sosai, kuma ta soma sakin layi. Sai ya motsa kafarshi ya ce,  Mami ba fa haka bane, wallahi-wallahi ba haka bane. Ki yarda da kanki da tarbiyyar da kika bamu.
Kada Allah ya bani tsawon rai da lafiyar da zan nemi jinina da kazantacciyar mu amala. Ban taba ba, ko da can balle yanzu da na mallaki hankalin kaina.
Babu komai tsakanina da Safah sai rashin fahimtar juna, wadda alhamdulillahi a yau mun gano inda matsalar take, we only misunderstood each other, but today we bury the hatchet (mun manta baya).
Cikin kyautayi da alfarmomin ku da basa karewa a garemu muke mika ban hakuri gare ki a bisa laifuffukanmu da kurakurenmu.
MADALLAH& . dake wannan Uwa da ALLAH Ya bamu, ma abociyar YAKANAH da TAKAWAH. Duk wani duty na UWA -MAHAIFIYA, a garemu kin cika shi.
Ki yi farin ciki, cikin  ya yanki babu lalatacce ko wanda ya karkace daga tarbiyyarki, sai KUSKURE, wanda babu dan Adam din da yake sama da aikata shi .
Jikin Mami ya yi sanyi, ta dago Safah dake ta kuka ta rungumeta a jikinta tana share mata hawaye da tafukan hannayenta.
Hajiya Mama banda albarka babu abinda take sanya musu.

Shukrah ta tako dabas-dabas da tafiyarta da ba ta gama yin kwari ba, ta hau jikin Mamanta itama tana taya Mami sharen hawayen, tana fadin
 Mami ce ko? Tofo in rama miki .
Sai ga Safah tana dariya. Shukrah na yi, Mami na yi. Yayin da Babanta ya dauketa daga cinyar Maman ya dorata a kan wuyansa.
 Shukrah-Nadiya, Uwa fa bata fi Uwa ba, nima ina son Uwata yadda kike son taki, ba zan bari ki doke ta ba .

****






A
iyaka fasahar da Allah Ya baiwa Almustapha Zubair Dan-Kasa, ya yi tunani iyaka tunani, bincike iya bincike kan hanyoyin da zai bi ya maido  Dan-Kasa Motors gida Nigeria amma ya rasa.
Ci gaban namu har yau bai zo nan ba, abin tambayar anan shine, yaushe Nigeria za ta ci gashin da Allah Ya bata?
Kasa ce mai cike da albarkatun kasa musamman man fetir,  the problem is with our leaders, they don t know how to harness the resources abailable, in ka ga talaucin da ake yi a cikinta (North and South) da dilapidated infrastructure sai ka tambayi kanka, ina shuwagabanninmu ke kai arzikin kasar Nigeria?
Wannan ce tattaunawar da suke yi shi da Saifuddeen Aliyu Dambatta, a wani restaurant da ke cikin masana antar  Dan-Kasa Motors dake Wilshire, Blbd, CA, cikin birnin Los-Angeles.
Saifuddeen ya kai tambulan din sassanyan lemun inibi bakinsa. Ya kurba ya aje akan gilasahin dake gaban su. Ya ce,
 An ce an bamu  yancin kai, amma ba a daina bautar da al ummar mu ba.
Mun fi Bature fasaha amma bamu ishi shuwagabanninmu kallo?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ba, balle su ankara da muhimmancin matasanmu su tallafa musu su samu ingantaccen ilimi.
In ka ga dan Nigeria na karatu mai kyau, to tabbata aljihun iyayensa da motsi, motsin talaka kuma ko oho. Da ya yi, da kar ya yi, duk daya.
Imam ya ce,  Za ka sha mamaki in ka ga bakaken fatar dake aiki a kamfanin nan. 40% Nigerians ne. Idan suka soma zana maka mota wallahi ta fi ta wani Baturen.
Ba zan taba mantawa da wani hazikin Basakkwace ba da muka yi aiki da shi a GM, (general motors), shine ya yi designing din motar nan da ta girgiza Turawa, wato  Chebrolet .
Gashi nan sun rike shi, Nigeria bata san ana yi ba. Banda  yan jarida da suka zakulo shi suka fadawa Hausawa, wallahi da ba zamu taba sanin da shi a Amurka ba .
Haka suka yi ta tattauna al amarin, har lokacin tashi ya yi suka nufo gida. Bayan sun ci delicious din da Mami ta shirya musu, nan falon suka zauna suna sauraren labarun duniya suna ci gaba da tattaunawa.
Shukrah ta tako ta zo ta rungume Babanta, kafin ya dauke ta Saifuddeen ya riga shi.
 What a kissable toddler! Ya fada yana kissing goshin ta. Imam yayi dariya.
Uwar ta fito, ta yi shiri cikin atamfa Ghana wad koriya shar da mayafin da ya dace da ita, da mukullin mota a hannunta don yanzu Imam ya sakar mata mara, nan ta tadda su.
Ta yi smiling ganin Shukrah na ta sharo masa labari.
Ta ce,  Barka da dare, Yaya Saifuddeen ina Rukayyah?
Cikin mamaki ya dubi abokinsa,  How dare she know Rukayyahh???
Ya yi murmushi idanunshi a kanta, ya ce,  Ina zuwa haka?
Ta ce,  Saloon zani, tun kaina bai soma kyankyasa ba. Haka kawai an kama mutum dan Adam an kulle shi a gida kamar wani barawo a hannun mata .
Ta juya ga Saifuddeen,
 Am a bery big fan of Takori. Na karanta ALHERI!
Ya ce,  Haka Rukayyah ke wuni karatun Takorin nan, na rasa wane irin labari take gaya muku, ta zuki ta malle, ku kuma ku hau ku zauna kamar a gabanku ake yi. Zan sa ido a kan zuwanta wajen Rukayya, don na lura duk sanda ta zo, to sai Rukayya ta canza taku. Soyayya kamar ta kashe ni .
Suka dinga dariya har ta fice ta barsu da Nadeeya, tana cewa,
 Bye-bye Mummy .
Kafin ta dawo Saifuddeen ya tafi masaukinsa a Rodeway Inn.
Washegarui ya wuce Lagos su kuma a ranar ne Imam ya dankawa kowacce passport dinta suka soma shiri za su taho a washegari.
Duk dokin Safah na son dawowar da tafiyar ta kankama sai ta ji ba ta son tafiyar. Hankalinta ya tashi sosai da tunanin iyayen Nadeeya za su iya kwace ta, musamman idan suka ji cewa aure za ta yi ta sake dawowa.
Hatta Mami sai da ta ankara da damuwarta. Ta ce,
 Ba a kallafa rai kan abinda ba a da iko da shi.
`Mutuncin yaro shine gidan ubansa, kuma mutanen nan duk wani karamci sunyi miki. Kema ki yi musu, tunda sun nuna hakan suke so.
Ki yi tunani, in rashi ne to sun fiki.  ya ya biyu maza jigon gidansu ne suka fadi. Don haka wannan yarinyar wani nau in farin ciki ce a garesu. Ke za ki yi ta haifar wasu, su kuwa fa?
Ta share idonta da tishu ta ce,  Mami SABO ne!
Mami ta rungumeta,  Zai wuce a hankali idan kika ga kin tara  ya ya .

Sun sauka ranar Asabar a Abuja, kai tsaye gidan Shahidah suka sauka, mai  ya ya uku a lokacin, biyu maza mace daya.
Shahidah ta rasa ina ta-ka-saka-ina-ta-ka aje da iyaye da  yan uwanta. Nan suka shiga hidima dasu ita da maigidanta. Kwana daya sukai suka karaso gida.
Gidansu na nan kulle yadda suka barshi, da yake maigadi yana nan da mai kula da shukoki, kuma Imam na biyansu ta banki. Gidan ma fes suka same shi, sun gyare shi fes.
Kwana biyu sukai suna hutawa sannan suka wuce Chikun gidan Baffa Sufyan, family house din su Alh. Aliko kenan.

Washegari Baffa Sufyan wanda ya manyanta wanda ya kasance kani ne ga mahaifin su Alh. Aliko, ya daura auren Almustapha Zubair Dan-Kasa da Safah Aliko Dan-Kasa a kan sadaki mai albarka, wato mafi kankanta.
Mal. Abdulkarim da sauran kannen Lamido maza sun halarta. Karshen karramawa Imam ya yi musu. Da za su koma tikiti ya yankar musu suka juya har da Shukrah-Nadeeya.
Don haka gaba daya amaryar yau an kasa gane mata. Duk ta birkice, kuka take tana karawa.
Ba don bata son auren ba, sai don rabuwar Da da mahaifi. Dan ma dan kankani who need an edtreme mother care..... kamar Nadeeya.
Ita take kalla ta tuno Lamaido. Ta yi masa addu a, ita take kalla ta ji sanyi irin wanda iyaye ke ji a kan  ya yansu.
To ya za ki yi? Amarya sai hakuri (Takori).
Mami ta yi waya da mutanen Malta, ta sanar dasu daurin auren  ya yanta a karo NA BIYU.
Shima Imam ya yi waya da Zahraddeen, sunyi murna sosai, sannan basu ce za su zo ba. Ana tsakiyar walimar da Mami ta shirya a nan gidansu sai gasu dukkansu kamar an koro su. Zuwa na bazata, wanda ya kara armasa al amarin.
Inna ma ta zo washegari ta yiwa Mami Allah ya sanya alheri, ita da Rabi a da Umma. Washegari suka koma.
Zahraddeen da iyalinsa ma kwanaki uku suka yi. Rana daya suka bar Kaduna da ango da amaryar. Su suka hau mai zuwa Holland, su kuma suka hau na inda suka fito.

A cikin jirgin amaryar da angon like suke da juna. Duk da cewa jikin amaryar a sanyaye yake na angon ma haka.
Har kullum wannan abin na yawo a zuciyarsa yana tokare mishi a kahon zuci. Abin nan dai da Hajiya Maama ta gano.
Don haka daga shi har ita idan ka lura babu walwala da nishadi na sabbin ma aurata a tare dasu. Dari-dari suke da juna.
Ita gani take kamar aurensu akwai kwaruwa a ciki, a matsayinsa na wanda bai taba dandana aure baa, ya auri wadda ta dade a cikinsa, har da haihuwa. Kawai sai ga hawaye suna zuba daga idonta.
Hannunsa kawai ta kama ta ce,
 Don Allah Ya Imam kaima ka yi irin na Zahraddeen ka auri Samry ko Barbara ko wata budurwa mu zauna tare. Gani nake na kwareka .
Sai ya kama dariya ya rungumeta sosai, ya ce,  Ni din ko? Ashe saurayi ne tuzuru ba? Kar ki damu, na fiffige  yammata har ba adadi, wannan abin ba zai dameni ba. Nima Bazawarin kan titi ne in ji Hajiya Maama........
Ta hau dukan kirjinsa da hannayenta biyu tana shagwabar da bai taba gani a diya mace ba.
Don haka a daddafe Imam ya jure nisan wannan tafiya ta Paris suka shigo, tafiyar 11 hours daga Paris.
Sanda suka iso Beberly Hills inda gidansa yake karfe goma sha biyu ne na dare. Bacci ne dankam a idanun kowannensu.
Don haka dakinta na da ta nufa, shima ya nufi nasa. Wanka kawai suka yi da yake babu yunwa a tare da kowannensu, sai kawai kowa ya bi lafiyar gado.

A rayuwar da Safah ta yi da Lamido, bata taba cin wani abu wai don neman karin ni ima ko something associate, other than wanda likita ya yarda da shi kamar fruits, fresh milk, honey (zuma), farfesun kifi ko na kaji ko zabi, yawan shan ruwa, cin cukwi, dabino da kwakwa, ta duk hanyar da za su sarrafu.
Don haka yanzun ma ba ta manta ba, balle a inda suke da abubuwan tantsan fiye da namu. Wato ko kayan marmarinsu bula-bula (riped)ne nunannu da suka bambanta da namu sun wadaci mai cin su.
Tana jin sanda Imam ya shigo dakin don ganin ko ta tashi da safe, ta yi lamo a kan pillow kamar mai barcin gaske. Tana jin sanda ya sunkuyo ya sumbaci goshin ta, ya mayar mata da gashinta da ya bazo a kan fuskarta baya, sannan ya fita.
Sai bayan fitar tasa ne ta tashi ta yi wanka, da yake ta samu ta yi sallar asubah tuntuni. Walha ta gabatar domin hantsi ya dubi ludayi.
Ta shirya cikin suit din Marc Jacobs mai dogon hannu da dogon siket bakake wuluk da kwalliyar silber. Sai ta dora mini hijab fari sol dan Saudiyyah, ta zabo farin flat shoe ta saka bayan ta tabbatar akwai kudi isassu a katuwar bakar jakarta samfurin Gucci.
Sanda ta fito dattijuwa Suzana na ta goge-goge, suka gaisa ta yi musu sannu da dawowa, sannan ta kawo mukullin mota  sportist camry  ta bata, ta ce in ji Oga ko za ta bukaci fita.
Ita da har ta shirya public bus za ta je ta hau ko ta yi shatar tadi saboda kayan da za ta sayo.
Don haka ba karamin dadi ta ji ba da Suzana ta bata wannan sako, sai tasa hannu cikin jaka ta fiddo kudi ta bata, ta ce ta yiwa yara sayayya in ta gama aikinta ta tafi. Suzana ta yi ta godiya.
A zamanta na shekaru uku ba kadan a LA (Los Angeles) waje dai-dai ne bata sani ba, don haka kai tsaye ta nufi babbar kasuwar kayan abincin LA da ake kira Farmers Market.
Ita wannan kasuwa, kasuwa ce ta kayan abinci zallah na kowanne ethnic group, wanda manoman California ke shigowa dasu. An bude ta a watan Yuli, 1984.
Akwai food stalls, sit down eateries, prepared food bendors da sauransu. Kasuwa ce mai tsohon tarihi a LA, kuma bangare ce na tourist attraction. Babu irin kayan abincin Amurka da babu, tun daga American Cuisine, Latin-American, African da kuma Asian Cuisines.
Tana nan ne kan titin Fairfad Abenue cikin kauyen Fairfad din Los-Angeles. Duk abin da take so ta samu har ma da kari. Kankana rusa-rusa, cukwi irin nasu (rake), kayan yaji su kanimfari da ma wadanda ba ta zaci samun su ba tunda na surkukin Africa ne.
Ba ta iso gida ba sai bayan la asar. Ta nika na nikawa, ta cakuda na cakudawa. Ta ki cin komai ta maidasu abin cinta da shanta. Ta jera su cikin firji a kicin.
Karfe shida daidai Imam ya dawo a yunwace matuka, yana ajiye bakar brief case dinsa ya cire kwat ita ma ya ajiye, kai tsaye kicin ya dosa.
Ya bude firij ya ga an cika shi da gyararrun kayan marmari, ya dibi iya wanda zai iya sha ya nufi falo.
Ya gane ta fita kenan tunda da safe da ya fita bai gansu ba, shi kuma bai aiko kowa ya kawo mata ba. Suzana ba zama take ba da ta gama ayyukanta tafiya take yi.
Sai da ya ji sassaucin yunwar cikinsa sannan ya nufo dakinta, sai ya same ta a kan sallaya tana sallar la asar da ta risketa a hanya.
Gadonta ya haye ya yi dai-dai, daga shi sai dogon trouser din dake jikinsa baki na Jeans, ko sallame sallar ta kasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login