Showing 69001 words to 72000 words out of 112612 words

Chapter 24 - BABBAN GORO BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY SUMAYYA TAKORI.doc

ma wata muguwar soyayyar Zahraddeen ke cinta a zuci.
Duk da ta san ba ta kai matarsa a komai ba, amma ai dan uwanta ne, zamansu waje daya yanzun ba karamin barazana ya zamewa rayuwarta ba.
Anisa kullum sai ta tafi fadama ta wuni don kar ta ga Zahraddeen. A kwanakin ta daina cin abincin kirki, girkin ma da take musu ta daina sai Maman Daddy ke yi.
Zan so ki hango min Marwa Dan Kasa diyar Aliko a gaban murhu suna hura itace ita da Zahraddeen, idanunsu na tsiyaya.
Amma hakan bai sa ta ki yi musu girki mai kyau ba, naman zabbi da kaji gashi nan sai sun ture, don haka take sarrafashi nau i-nau i, wataran grilled (a turmi), wataran minced, wataran soya, wataran farfesu, wataran gashi (baking) a garwashi.
Ta zubar da komai ko a lahira ta zabi ta zauna da mijinta ko da dan kanzo ne, balle ma shi bai daina gayunshi ba ita din ce dai duk ta sakwarkwace, amma ba abin da ya dame su.
Wasa-wasa sai gasu sun kwashi wata biyu a Rugar Ardo, a wani dare Inna Binta da Badijo suna shirin kwanciya, Badijo ta fara shakuwa ta juya tana kallon  yar uwarta.
Ta ce,  Binta ki yi min alfarma ki sa Dini ya auri Anisa, wannan shine burina na karshe a rayuwar duniya .
Inna Binta ta yi zugum tana jinjina maganar, ko ita din ta so haka a baya, amma ban da yanzu da Marwah ta gama siye zuciyarta da kyawawan halaye da kauna ta hakika ga mijinta.
Sun gina rayuwarsu ta zamo mai ban sha awa abin alfaharin kowadanne iyaye, ba za ta so ta zama silar ruguje farin cikin dake cikin rayuwar aurensu ba.
Haka ba za ta iya bijirewa bukatar Yayarta ba, musamman a wannan hali na rai kwakwai-mutu kwakwai da take ciki, ba za ta mance hidimar Badijo ga Zahraddeeni ba a lokacin da yana yaro.
Ita ta karbi haihuwarsa, ta yaye shi, ta yi masa shayi (kaciya) da sauran hidimomin da ba za su lissafu ba.
To amma wane bayani za ta yiwa Marwah da Zahraddeen su fahimta ba ta da hannu ko niyyar shiga rayuwarsu?
Dabara ce ta zo mata yadda za ta fita ko ba sabulu.
Mikewa ta yi tsaye ta ce,  Jirani Badijo .
Ta dauki fitilar aci-bal-bal bayan ta sauke Daddy bisa katifar auduga wanda ke kwance ciny??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????arta yana barci.
Ta fito ta nufi bukkar su Zahraddeen, ba ta shiga kai tsaye ba, su ma sun kunna aci-bal-bal din amma sun rage haskenta tabbacin sunyi shirin kwanciya.
Sallama ta yi tare da cewa,  Kun kwanta ne?
Daga ciki har suna hada baki wajen cewa,  A a, Inna muna dai shirin kwanciyar ne .
Ta ce,  To ku zo dukkan ku Badijo ta yi magana wadda ta girgiza ni, shine nake so ku zo ku tayani jinta don ku tafi shafa ba ni ba .
Gaba daya suka fito suna tambayar me ya samu Badijon? Zahraddeen har yana karo da asabari sabida tsayinsa ya zarta na  yar kofar bukkar.
Ta ce,  Rikici na tsufa da zafin rashin lafiya kawai .
Suka ce,  Har da zafin ciwo .
Dukkansu suka gurfana gaban Badijo wadda ke kwance kan katifar alawayyo.
 Badijo ga Zahraddeenin ki gaya mishi da bakinki tare da matarsa, na shaidesu kan cewa su dukkansu masu biyayya ne a gare ni, idan na furta aikatawa ce kawai tasu ko suna so ko basa so.
To amma bana so in takura musu don suna min biyayya, duk abin da ya shafi Dini ya shafi matarsa, don haka ki gaya musu da bakinki .
Badijo ta ce,  Ai ba sai kin yi haka za ki tabbatar min matar Dini ta shanyeku ta siyeku ba, kamar yadda nake jin labari, saboda su masu arziki ne.
Ta yadda har ba za ki iya yin sirri dani ba a matsayina na shakikiyarki, kuma ba za ki iya yin umarni ga danki ba, sai kin hada da yardar matarsa.
Duk wulakancin da ta yi muku kin shanye kin manta saboda suna da kudi. Kai Dini, saurareni da kyau bar ganina rai a hannun Allah, har yanzu ina nan a Badijo na, mai bala i kuma mai kirki ga wanda ya yi mata kirkin.
Na baka auren Anisa na bawa uwarka amanarta, ko bayan raina ka wulakanta ta marainiya ce Allah zai saka mata, ka karba ko baka karba ba?
Da sauri ya ce,  Na karba Badijo, ni dai fatana Allah ya baki lafiya. Amma in kina so in ji dadi, to ki goge fassarar da kika yiwa Innata da mai dakina.
Baki taba yin kalaman da suka yi min ciwo irin wadannan da kika furta yanzu ba.
Innata mai sonki ce da girmamaki Badijo, babu ranar Allah da za ta fito ta fadi ba ta ambace ki ba. Tun kan ki yi wannan hasashe Innata ta yi a kan Anisa, ni ne na yiwa maganar birki.
Mai dakina kuwa kome kika yi hasashe a kaina game da ita kin yi daidai. Ta shanyeni, ina gudun bacin ranta, tana da arziki, ni bawanta ne kuma mai kula da dukiyarta.
Amma fa ba ta fi karfina ba, sannan karkashin ikona take. Don haka kar ki kara wannan magana .
Kunya ta kama Badijo, sai ta hau kame-kame,  Ai nima na san hakan uwar taka ce ta bani haushi .
Suka mike suka yi bukkarsu, ko kallon shi Marwah ta kasa. Katifarta ta bi ta kwanta ta soma kuka.
A gefen katifar ya zauna kawai kansa a kasa ya harde hannayenshi guda biyu, kukanta na cin zuciyarsa.
Ya juyo ya kama hannunta ta fizge, ya bita ya kwanta a bayanta ya rungumeta ta soma kici-kicin kwatar kanta, amma karfin ba daya ba, sai kici-kicinta ya ba shi damar rungumeta sosai. Ya kanainayeta.
Ta bishi da cizo da duka duk ya shanye bai cika ta ba, sai da ta yi mai isarta ta gaji ta kyale shi. Ta ci gaba da kuka a hankali.
Sai ya yi amfani da wannan damar ya shayar da ita farin cikin da bai taba shayar da ita a rayuwar aurensu ba. Shi hawaye ita hawaye.
Ba kuma don komai yake hawayen ba sai don tunawa da DADDY, da alkawarin da ya yi masa na karin aure, wannan ne dalilinshi na amsa maganar Badijo farat daya, amma ba don abin da ta furta ba (jan idonta ko masifarta).
Sai da ya bari suka samu nutsuwa sosai, sannan ya soma yi mata bayanin hujjarshi da dalilinshi na auren Anisa don ya cika alkawarin Daddy ne ba don maganganun Badijo ba.
Ita dai ba ta yi magana ba, tunaninta Badijo ba ta sonta kawai, kuma wannan yarinyar mai kafirin girman kan tsiya da nuna mata kiyayya, ita ce Zahraddeen ya amsa zai aura.
Duk iya kokarinsa ya yi wajen lallashi, ban baki da alkawarirrika amma Marwah uffan ba ta ce mishi ba. Ita gara ya auro ko mai digiri uku ce da wannan yarinyar  yar rainin hankali.
Ya ce,  To shi kenan, tunda duk bayanin da na yi miki kin ki yarda dani. Wallahi yarinyar nan ko farcenta ba zan taba kamawa ba, don ni kaina karshen raini ne hakan a gare ni.
Gobe zamu bar garin nan tunda Badijo ta bata miki rai .
Wannan karon ne ta yi magana,  Ni na gaya maka? Kai ka bata min rai ba Badijo ba .
 Da na yi me?
 Da ka yi maza ka amsa mana babu tunani babu shawara kamar dama kiris kake jira. Ai ko rashin shiga sabgar yarinyar nan da kake na san sonta kake, ita ma kuma munafuka sonka take, in ba haka ba mene ne za ta dauki tsanar duniya ta aza a kaina ni da Daddy?
Ko jiya ina wanka na hangota ta bayan danga tana kwakkwada masa mari don ya zubar mata da ruwa a buta .
Shi dariya ma ce ta kama shi, don bai taba jin Marwah na yin korafi ba a rayuwarta, lallai kishi ba dama ne.
Ya ce,  To ta mareshi ke ina ruwanki tunda ba ke ta mara ba danta ta mara?
Ta zaro ido ta ce,  Sanda nake nakudar haihuwarshi ta taya ni? Na ce ta taya ni? Ta hayayyako masa kamar ta rufe shi da duka. Sai ya fizgota ya makalkale ta,  Cool down, & apple of my eyes, take it easy& .. biyu kyautar Allah& .na tuba, na bi Allah na bi ki&  .
Ta ture shi,  Ku maza wallahi munafukai ne, algungumai marasa alkibla. Sai ka tafi goben don ni ba zamanka nake yi ba, ita ma Badijon ba zamanta nake ba. Inna na rako .
Ya dan yi fuska don jin za ta wuce kima. Bai sake tanka mata ba, ta kara kuluwa sai ta sake fashewa da kuka.
Ko kadan baya son zubar hawayenta, domin tamkar digar dalma yake a zuciyarsa. Kwanciya ya yi a kan cinyoyinta shi da tirtsetsen cikinta da ya zungure shi.
Cikin ya rungume yana sumbata,  Ya Allah kada kasa babyna ta yo KISHI irin na Mamanta, Allah kasa ta yo halin SAFAH.....
Ai kuwa ta kara kunnuwa.......  Dadin abin dai SAI BAYAN RAINA......
Dafe kai ya yi, cikin razana, don jin yadda ta fassara maganarsa da wata manufa daban ta baya da ta riga ta dade da shudewa a zuciyarsa..............
 Ina rokon Allah ya sa ni zan fara mutuwa in barki, idan har tunaninki kenan .
Iyakar abinda y ace kennan. Ya sa kai ya fita daga bukkar ya barta da binshi da harara.
Zahraddeen saboda bacin rai fadama ya nufa ya samu wani katon dutse luwai-luwai da shi ya zauna ya harde hannunsa a tsakanin guiwoyinshi yana tufka da warwara.
Ya rasa mata wadanne irin mutane ne, duk hankalinsu da iliminsu idan aka zo maganar kishi in suka kwaboma wata maganar sai ka ji kamar ka hadiyi zuciya ka mutu don haushi.
Yana nan zaune yana kallon yadda ruwa ke ninkaya da ambaliya a katon kogin, wanda an tabbatar da cewa ya bullo ne daga Riber-Niger, sai ya samu kansa da diban tsakuwoyi yana cillawa cikin ruwan daya bayan daya.
Marwah ta bata mishi rai sosai. yana nan zaune har yamma, sannan ya tashi ya nufo gida, zuciyarsa ta yi sanyi a lokacin.
A hanya ya ga Daddy da yara 'yan'uwansa kowannensu hannunsa rike da katon dodon kodi mai rai da lafiya.
Tsigogin jikin Zahraddeen suka tashi, shi kuwa yaron yana hango shi ya soma fadin.
"Daddy....Daddy zo ka gani mun samo dodon kodi".
Ya karaso ya bubbuge hannunsa dodon kudin suka zube suna ta motsi. Ai kuwa Daddy ya tsinke da ihu.
Ya dauke shi kafarsa ba ko takalmi ya yi gida da shi yana ihu yana zillo sai ya dauko dodonninsa.
Inna Binta ce ta fara jiyo ihunsa ta fita daga bukkar Bajido da sauri don ganin abin da ke sa shi wannan ihu.
Uwar shi na gindin murhu tana suyar zabbi, Inna ta ce, "Anya Dini ba zaka bar mai sunan Alhaji ya yi wasa da tsararrakinsa ba yadda yake so kamar a kanka aka fara haihuwar da? Kai ba irin rayuwar da ka yi ba kenan, me ya same ka?"
Ya ce, "Inna dodon kodi fa suke daukowa?"
Ta ce, "Meye da shi? Ba abinci bane a gurin wasu?"
Ya ce, "A'a, ban da ni wallahi, kuma idan ba zai zauna a gida ba daure kafafunsa zan yi".
Inna ta kama baki. Marwah na jinsu tana ta dariya a boye, dan yajin da ya yi mata tun safe ba ta ganshi ba, yasa duk ta damu, sai yanzu da ta ji muryarsa. Dadi ya lullubeta.
Ta saci kallonsa yana ta wankewa Daddy hannu da omo, kafarshi futu-futu da yashi. Sai ta ji kamar ta lashe shi don so. Ta manta da wata sa'insa da suka yi da safe.
Ta cika ruwa a buta ta je gabanshi ta tsugunna ta soma wanke mishi kafafun ba tare da ta bari sun hada idanu ba.
Anisa na gefe zaune a kan katon kunkuru (tortoise) tana satar kallonsu kamar ta shaketa ta mutu don kishi.
Da ta ga za ta yi kuka sai ta yi maza ta shige bukkar Badijo, sai kau da kai yake wai shi ya yi fushi. Ita kuma tana binshi da kallon ka yafe ni.
Ita kanta Inna sha'awa suke bata, da ta ga Marwah ta manta da suyar ta sun shige bukka da dansu a hannunsu, sai ta fito tana karasa mata.

Yau da dare Rugar Ardo ta yi tsit, duk al'ummar rugar sun ya da hakarkarinsu kasa, shakuwa ta damu Badijo.
Har ta tashi Inna ta bude randa ta debo ruwa ta kawo mata shimfidarta, ta tallafo ta tana ba ta ruwan, sakamakon aci bal-bal din an rage ta, ba ta ankara da cewa ruwan dawowa yake yi ba.
Tuni Mai kowa da komai Ya amshi abinSa. Da ta ji shiru tsammani ta yi ta koma barci, sai ta kwantar da ita ta koma shimfidarta.
Anisa ma ta tashi tana zaune dungurgur ta rasa me ke damun ta? Ta rasa inda za ta sa kanta da soyayyar dan'uwanta.
Ita ma Inna kasa komawa baccin ta yi, ta dauro alwala ta zo ta soma nafilfili tana rokawa 'yar'uwarta sauki wajen rabbil izzati.
Asuba ta yi sannan ne Anisa ta yo alwala ita ma ta fara bada farali. Ita kuma Inna Binta sai kawai ta dora sallar asubahi.
Gari ya soma haske ya yi dan shaaaa! Haka, basu ji maganar Badijo ba ko gyaran muryarta.
A ka'ida kuma duk asubah sai ta tashi kowa ya yi sallah, har karfe shida na safe. Inna Binta ta yanke shawarar tashin ta.
Kallo daya ta yiwa 'yar'uwarta ta tabbatar mai kowa da komai ya amshi abinsa.
Ta ce, "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un!"
Sai ta janyo mayafinta jikin kofar bukkar ta yafa tana hawaye ta nufi gidan Liman ta sanar da shi.
Sannan ta dawo kofar bukkar su Marwa, "Dini kun tashi ne?"
Zahraddeen dake sanye da short - nicker din (Adidas) da farar singileti fara sol saboda zafi, ya yayibi zanin matarsa ya rufa sannan ya ce, "Ni ne dai na tashi".
Ta ce, "To ita ma tashe ta ku fito jana'izar Badijo wa'adi ya cika".
"Daga Allah muke kuma gare shi zamu koma".
In ji Zahraddeen. Ya yi hanzarin zura kaftanin shadda a jikinshi da dogon wando, sannan ya soma jan yatsun matarsa.
Cikin barci ta ce, "Na fa yi sallah, don Allah ka barni in dan runtsa".
Ya ce, "Watarana dukkanmu haka zamu tsinci kanmu a kabari daga barcin safe".
Ta girgije ta ce, "Me kuma ya kawo zancen kabari saboda Allah?"
Ya ce, "Badijo ta rasu....'
Kafin ya rufe bakinsa ta kai kanta bukkar Badijo daga ita sai rigar barci ko kallabi babu a kanta.
Ta tarar Inna Binta da Abuwa matar Liman suna yi mata wanka, sai ta sulale a gefe za ta fara kuka.
Inna ta ce, "Kul! Tashi maza ki je ki kintsa ki zo mu yi mata karatu kafin maza su taru".
Anisa tana ta suma ana yayyafa mata ruwa tana farfadowa, amma in ta ga gawar Badijo sai ta sake sumewa. Don haka aka fita bukkar da ita.

Ta taso ba ta san iyayenta ba sai Badijo, wajen haihuwarta uwarta ta rasu, babanta shine da daya kwal da Allah ya baiwa Badijo. Ita ta raine ta da madarar shanu har Allah ya kawo ta yau inda ta ke.
Ba ta san dangin mahaifiyarta ba saboda Fulanin tashi ne ba zaunannu ba. lokacin da suka aurar da mahaifiyarta gaba suka yi basu tsaya ba tunda ta tubure tana son Haruna, alhalin ba dan rugarsu bane.
Sai da ta yi wayo babanta shima ya rasu, sakamakon wata saniya da ta soka masa kaho a ciki wajen kiwo.
A haka Anisa da kakarta suka rayu, basu da kowa sai Inna Binta, ita ta sata a makaranta tare da Rabi'a, akwai shakuwa ta 'yan'uwantaka tsakanin Rabi'a da Anisa.
Tun bayan auren Rabi'a Anisa ta dauke kafarta daga Zaria, tana nan tana jinyar Badijo.
To yau hukuncin Allah ya cika a kan Badijo. Jama'a sosai suka halarci jana'idar ta, bayan an kaita makwancinta suka ci gaba da karbar gaisuwa har kwana uku.
A ranar sadakar bakwai Inna Binta ta yi umarni ga dattijan rugar Ardo suka daura auren Zahraddeen da Anisa.
A kuma ranar ne suka hada kayansu domin barin rugar. Motar Zahraddeen dake rufe cikin tamfol ta yi kura futuk, yashi ya rufe rabin tayoyinta.
Haka ya zage yake wanke motar da kansa ciki da bai dinta, yasa karfi ya banbarota daga cikin yashi da kwanjinsa, ya yi mata ful tank da fetir din da tuni yayo guzurinsa a but din motar ya soma diban kayan amfaninsu marasa nauyi yana zubawa a boot, irin su mujallu da computer (Ipad), da makullan gidansu, amma ko kayan sakawar da suka yi amfani dasu a bukkokin basu dauka ba.
Zannuwan gado, filallika, barguna da takalmansu duk basu dauka ba sadaka suka barwa iyalan Liman.
Sai da ya gama zuba dukkan kayansu ya dubi Anisa dake gefe kan kunkuru tana mike da kafafu wadda ke nuna babu abin da ya dameta yanzu.
Ya harareta ya ce, "Ke ba za ki dauki komai ba?"
Ta ce, "Komai kai".
Ta mike ta je ta kinkimo katuwar akwatin karfenta da take amfani da ita tun a makaranta da Ghana Must Go shake da sutturunta ta dire a gabansa.
Sannan ta kinkimo katon kunkurunta shima ta dora a kan akwatin, ta ce, "Suke nan basu da yawa".
Zahraddeen don haushi bai san sanda ya ce,
"Kin ci ubanki bakauyar banza!"
Ta ce, "A'a-a'a! Ubana yana kabarinsa ban san halin da yake ciki ba ka daina zagar min shi".
Ya kama baki, "To ki rama mana".
Ta zumbura baki ta turo dankwalinta goshi dogon gashi ya zubo kamar na Larabawa, amma wallahi bai burge shi ba, ganinta ma ya yi ta koma kamar tunkiya.
Daidai sanda Inna da Marwah suka fito yafe da mayafansu, Inna rike da hannun Daddy, suka tadda diramar da ake tsakanin Zahraddeen da amaryarsa.
Ya ce, "Wallahi Inna ba zan saka wannan akwatin karfen mai kama da akwatin ajiyar gawa a boot din motata ba, balle wannan jakar buhun cike da tsummokara, bare kuma kunkuru da ransa".
Ai kuwa Anisa ta balle da kuka, "Ni wallahi ko ba za a dauki komai ba, ba zan bar kunkuruna ba.
Ni na raine shi tun yana karami, na ci da shi na sha da shi har ya zamo abin da nake zama a kai in ji dadi, in dube shi in ga kamar na ga wani dan'uwana a raye".
Gaba dayansu sai jikkunansu suka yi sanyi, Marwah ta ce,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login