Showing 18001 words to 21000 words out of 112612 words

Chapter 7 - BABBAN GORO BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY SUMAYYA TAKORI.doc

kamar ta ba-sarake, Safah da mijinta, kuma ko babu ban ga me za ta ci da Zahraddeen ba.
Bakin rijiya....ba wajen wasan yara bane. Ban da rashin hankali ya dubi Uwargijiyarshi ya ce yana so da aure? Saboda kankanba da neman wuce gona da iri ko saboda mene? Ai BABBAN GORO SAI MAGOGIN KARFE,& & kuma Tuwon Girma& . Miyarsa nama
Daddy ya yi murmushi yana kada kai ya ce,
 Wannan ba hujja ba ce, ku mata ban san irin ku ba wallahi. Ni a wajena Zahraddeen mutum ne har mutum, mai nagarta, daraja da sana ar da za a bawa aure.
Ba don maganar Imam ba, babu abin da zai hanani wanke Safah in ba shi ba tare da na yi la akari da hujjojinki ba. Mutum da karatunshi da usuli da lafiya da addini da aikin yinsa, me ake nema a nagartaccen miji da ya wuce wannan?
Jarumi haziki irin Zahraddeen, mai zuciyar neman na kansa, mai kwakwalwa, kyakkyawar zuciya da halaye na kwarai, gaskia da amana, wadanda suka yi karanci ga matasan zamanin nan, wallahi ba don Imam ba, zan baiwa Zahraddeen Safah ba tare da na ji ko da dar ba .
Mami ta kama baki cikin mamaki. Cikin takaici ta ce,
 Kenan kana nufin babu matakin da za ka dauka? Idan aka yiwa Imam haka anyi adalci kenan?
Ya ce,  Ni ban ce miki na amince ba, hujjarki kawai na soka (criticizing). Na ce dake zan gansu, ki bi komai a hankali, ki cire bacin rai, fushin fari ba naki bane, tunda ba ke za ki yi mata zaman auren ba .

A wannan daren Mami ba ta yi barci ba, yadda ta ga rana haka ta ga dare. Ita kam duk haushin Daddy ya rufe ta, me Safah take nufi? Da wacce fuska za ta dubi danta Almustapha idan Safah ta watsa musu kasa a ido?
A washegari Safah ba ta ga walwalar Mami ba, ta daure mata sosai. Da Marwa take sabgoginta, itama sai ta kama kanta, ta killace kanta a daki tana rubuce-rubucen ta.
Sai dai zuciyarta cike take da tsoron Mamin, idan ta tuna marin da ta sha jiya. Ba ta taba ganin bacin ra??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????n Mamin irin jiya ba.
Har kullum ita cikin kauna take nuna musu komai, ba ta taba tunanin Mamin na da zafi har haka ba. Ta yarda ta amince akan Imam, Mami zata iya batawa da kowa hada dasu  ya yan cikinta kuwa. Don har fadi musu take
 kafin in sameku shi na samu, a lokacinma dana riga na fidda rai da samun  ya ya. Sai ya zamo wani irin nagartaccen Da, mai debe min kewar  ya yan da bani da su. Don haka zuwanku bai rage komi daga kaunar dana ke yi masa ba. Sabida ya maye min gurbin  ya ya goma, a lokacinda banida ko daya!!!
Balle ke kuma na haife ki ne kawai, amma bansan kashinki ba bansan fitsarinki ba, sai shayarwa ta dan lokaci, wadda ciyarwar dashi yayi miki da madara ta fita tsaho .
Karfe takwas na dare Zahraddeen ya zo, Mami na falo cikin seater tana sauya tashar MBC zuwa Aljazeera.
Tun daga jin sallamar shi ta bi ta daure fuska irin yadda ba ta taba yi masa ba. Ya zube gwiwoyinsa a kasa yana gaishe ta, ta kafa mishi ido ba ta amsa ba. Karshe sai ta mike ta shige kafar benen da za ta sada ta da dakin barcinta, ba tare da ta ce da shi komai ba.
Daga shi har Safah gwiwoyinsu suka yi sanyi, ita Safah ma kunya ce ta kama ta. Aka rasa mai fara yin magana a cikinsu.
Daga baya Zahraddeen yai ta maza, ya yi murmushi cikin basarwa ya ce,
 Mun yiwa Mami laifi halan?
Ta yarfar da hannu, ta lumshe ido
 Tun jiya haka take, na kasa gane mata .
Ya yi shiru cikin tunani, can kuma ya ce,  Mai yiwuwa ne ba ta yi na am da al amarin mu ba .
Ta ce,  Babu komi, za ta huce a hankali .

Daddy na saukowa daga matattakalar bene Mamin biye da shi rike da brief case dinsa ya yi tozali dasu a falon.
Ya yi murmushi yayin da Mami ta kara hade rai. Ya ce,  Dama ina son ganin ka .
Ya mike cikin girmamawa ya bi bayansa suka nufi falon ganawa da bakinsa dake daga harabar gidan.

Daddy na bisa kujera, Zahraddeen na gefensa bisa kilishi.
Daddy ya ce,  Ya sakon da na baka na Wilcod din Abidjan?
Ya ce,  Ya zo ya amsa tun shekaran jiya .
Ya ce,  To madallah .
Sai kuma ya yi shiru, shi ma Zahraddeen kanshi na kasa. Ko motsin kirki ya kasa.
Can Daddy ya ce,
 Zahraddeen .
Ya dago da fararen idanunshi ya dube shi amma bai amsa ba.
Ya ce,  Meke tsakaninka da Safah ne?
Zahraddeen ya rude, ya soma inda-inda, saboda kwarjinin da Daddy ya kara yi masa, har ya soma ganin wautar kansa, da wuce gona da irin sa.
Daddy ya yi murmushi ya ce,
 Zahradden feel free with me. Ka amsa min mana, ni Babanka ne ba bakon ka bane .
Ya yi ta maza ya ce,  Am Daddy, dama.....dama ina son mu samu lokaci ne, sannan in gabatar maka da kaina a matsayin mai neman auren Safah, mun daidaita kanmu .
Daddy ya yi murmushi ya lumshe ido na  yan mintunsa sannan ya budesu a hankali akan Zahraddeen din ya ce,
 Zahraddeen zaka iya hakura da son da kake wa Safah, ka juyar dashi ga  yar uwar ta? Ina nufin, ka auri abokiyar tagwaitakarta MARWAH?
A firgice ya dago ya dubi Daddy, kamin ya yi magana Daddy ya ce,
 Safah da mijinta, tun ranar da aka haife ta, amma idan kana ganin za ka iya auren  yar uwarta sati mai zuwa ka kawo min sadakin naira dubu goma in daura muku aure rana ita yau. Lahadi kenan, zan daura auren Safah da Almustapha tare da naku. Tashi je ka ka yi shawara, ina sauraron ka .
Ya bude baki zai yi magana Daddy ya ce,  Ka je ka yi shawara tukunna, ba zan yi hakan ba sai da amincewar ka. Ina sonka ne Zahraddeen, ina son hada jini da kai, saboda kai mutum ne na gari.
Banda shi wancan alkawari, ba abin da zai hanani baka wacce kake so cikin  ya yana. Amma Safah da Marwah duk daya ne, abin da ya yi Safah shi ya yi Marwah, sai dai bambanci na akida da halayya wanda za ka iya lankwasawa cikin dan lokaci kalilan. Tunda har yanzu yara ne. Tashi jeka ka yi tunani sosai, ka kuma shawarci Innar ka, na baka kwanaki uku ka zo min da abin da ka yanke .

Zahraddeen ya mike ya fita, kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki, ya nufi motarsa ya bude ya shiga ya zauna ya kwantar da kai a jikin sitiyari. Bai yi aune ba sai jin danshi ya yi a kan fuskarsa, ya mika hannu ya shafo su, hawaye ne, shi kansa bai san dalilin zubarsu ba.Ya fi minti talatin a hakan, kamin ya ja motar masu gadi suka bude mishi get ya fita. Ya yarda ba zai samu Safah ba, amma ba ya jin da ranta zai iya auren  yar uwarta-shakikiyarta. Karewama wadda suka fito duniya tare a lokaci daya.
Ba aure ya damu ya yi da wuri ba. Kasancewarsa saurayi da bai taba aure ba, ba kuma shashanci yake yi ba, balle ya tantance yanada bukatar mace soon ko a ah. Safahn kawai yake so, soyayyarta ce ta sanya mishi son yin auren. To amma ya zai yi ya budi baki ya ce da Daddy baya son  yar cikinshi, wanda shi a ganinsa karamci ne ya yi mishi?
Me yasa Safah ta boye mishi cewa akwai alkawarin dan uwanta a kanta? Tayi masa wasa da hankali da zuciya& ..Har ya iso gida bai san inda hankalinsa yake ba. Kuma tambayar da yake so yayi mata kenan, hakika tayi mai wasa da zuciya, don bazai iya cewa ta yaudare shi ba, don ya yarda son da take masa na gaske ne, na tsakani da Allah ne.

Alh. Aliko na zaune a falon shi, ya kira Mami ya ce ta turo mishi Safah.
Tana zaune a bakin gadonta ta yi tagumi, Marwah na jera kayansu da aka kawo daga wanki cikin wardrobe.
Mami ta yi sallama ta shigo dakin. A hanzarce Safah ta dago kyawawan idanunta ta dube ta. Kallo daya za ka yi mata ka san cewa cikin damuwa take, damuwa mai tsanani.
Mami ta balla mata harara ta ce,  Taso muje .
Ta mike babu kuzari ta bi bayan Mamin har falon Daddy. Jikinta a matukar sanyaye, don ta tabbata Mami ta fasa kwan.
Daddy yana ta aiki cikin takardu da farin gilashi a idanun shi lokacin da suka shigo.
Ya janye takardun gefe ya kuma cire gilashin ya bi Safah da kallo a lokacin da take zama a carpet. Kallo daya ya yi mata ya karanto matsananciyar damuwar da take ciki. Don duk ta zabge cikin kwana daya kacal.
In banda alkawarin da ya yi, da matsayin Imam a wurinsa, da ba abinda zai hana shi baiwa wannan soyayyar goyon baya, ba ya son Zahraddeen ya kubucewa gidansa, don haka ne ya yanke shawarar wanke Marwah ya ba shi in har ya amince. Ya tabbata ahankali zai sota, sabida tanada nata kualities din itama. Duk da ya san ita din mai dagawa ce (ba kamar Safah ba), amma abu kadan yana tankwara ta.
Sannan ba zai taba dauke alkawarin Imam ba, sai in har shi da kansa ne ya ce baya yi, wanda ya san har abada hakan ba za ta faru ba.
Ya kai duban shi ga Hajiya Zainab ya ga yadda ta hade fuska ta yi murtuk, sai ya yi murmushi ya ce.
 A lokuta da dama ku mata kuna bani mamaki, kina kin Zahraddeen ne saboda kawai yana karkashi na. Ba kya duba asali, halayya, addini da dabi a.
Manzo (S.A.W) yaron Nana Khadija ne, kuma ya aure ta, ta kuma so shi saboda nagartattun halayensa da amanarsa.
Ba za ki yi la akari da wannan ba ki kuma duba cewa soyayya hadin Allah ce, ba yin mutum ba?
Ya maida duban shi ga Safah, wadda kalaman mahaifinta ke sanyaya mata zuciya, har ta soma hango alamun nasara cikin al amarin ta.
Idanunta suka cicciko ta ce,
 Don Allah Daddy ka bawa Mami hakuri, ina son Zahraddeen shima yana so na. Mami Zahraddeen ma mutumin kirki ne wallahi.
Ni ban ce bana son Ya Imam ba, amma bana yi mishi soyayya ta aure, Zahraddeen nake so Mami ba zan iya auren Ya Imam ba.....
Ai kuwa ta kara harzika Mamin, daga dan sanyin data yi da nasihar Daddy, ta buge bakinta ta ce,
 Ashe baki da kunya Safah? Ni kike gayawa kina son wani bayan Da na da na raina na yi mishi tarbiyyar da nake so? A gabana kike cewa ba za ki iya auren Almustapha........
Sai ta soma kuka,
 & .Tunda ka daure mata gindi ku tozarta alkawari, shi kenan zan bar muku gidanku, don bani da idanun da zan dubi Imam, alhalin tana auren wani can. Ka aura mata duk wanda kuke so...
Daddy shiru ya yi yana kallon su, ya dubi Mami da har ta kai bakin kofa ya ce,  Zainabu .
Sai ta dakata, amma ba ta juyo ba.
Ya ce,  Kin ji hukuncina ne kamin ki yanke naki hukuncin? Dawo ki zauna .
Ta koma ta zauna.
Ya ce,  Ba tsoron ki nake ji ba, ba kuma so nake in yi miki abin da kike so ba, illa nima na san muhimmancin alkawari, kuma ni da bakina na yi wannan alkawarin ba ke ba.
Don haka na yanke cewa zan baiwa Zahraddeen Marwah....

A razane Safah ta dago ta dubi Daddy. Ya girgiza mata kai ya ce,  Ki yi hakuri Safah, gara ka auri wanda ke sonka, a kan ka auri wanda kake so!.
Bana kin al amarin ki da Zahraddeen, ko kadan bana ki, sai dai ba zan iya daga alkawarin Imam a kanki ba. Na yi kokarin neman mafita mafi maslaha na kasa sai wannan din. Wato bana so Zahraddeen ya kubuce mana.
Ki sowa  yar uwarki abin da kike sowa kanki. Ki yi min alfarma Safah in cika wannan alkawarin nawa, ni kuma in yi miki duk abinda kike so a duniya. Alfarmarki nake nema, Safah, zan samu?
Kuka ya ci karfinta, tausayin mahaifinta ya lullubeta, ganin yadda ya karyar da murya ya kwantar da kai yana rokonta kamar ba shi ya haifeta yayi ta wahala da ita har ta girma, ya kawo Zahraddeen din cikin rayuwarsu har ta ganshi ta ji tana so. Ta ce cikin rishin kuka,
 Ka yi duk yadda kake so da mu Daddy....har abada mu masu biyayya a gareka ne. Na yarda da hujjar ka. Na yi maka wannan alfarmar Daddy.... Ta ci gaba da kuka a hankali.
Zuciyar Daddy ta karye, ya ce,
 To amma Safah, kukan na mene ne haka? Kukan ki, na nuna min cewa..... na zalunce ki .
Ta yi saurin toshe bakinta da mayafinta, ta hadiye kukan da karfi ta ce,
 Babu zalunci tsakaninmu daku Daddy, sai kauna marar misali, kai Allah Ya baiwa ragamar zaba mana mijin aure.
Matsalata yadda zan lallashi zuciyar tawa, ta hakura, ta daina son Zahraddeen, ta amince da hukuncin ka Daddy....
Ya yi murmushi ya ce,
 Da dai ba Almustapha da Zahraddeen zan aura muku ba, shine zan tsaya ina lallashin ku.
Amma na san hannun da zan bada ku, hannu ne da ba zan taba yin dana sani ba .
****





















Y
adda Zahradeen ya kwana bai runtsa ba, haka Safah ta kwana tana juyi a gadon ta. Inda duk ta juya maganganun Daddy ke yi mata kuwwa a kwanya.
Ta yarda ta saduda ta amince Zahraddeen, ya haramta gare ta, soyayyarsu ta zama mafarki mai dadi, irin wanda dan adam kan yi, ya farka yana mai cizon yatsar kasancewarsa reality, tunda har Daddy ya yi wannnan hukuncin. Dreams are conceibed, but not all dreams are born alibe. Some are aborted. Others are stillborn!
Ta tuno da kalaman noble - laureate - Zaynab Alkali.

Ta juya kallon ta ga gadon  yar uwarta Marwah, barcin ta take cikin sukuni da alama ba ta da matsala a rayuwa. Kuma bata san menene SO ba.
A ganin ta yau ba mai sa a a duniya kamar Marwah, tunda bata taba dandana zakin so ko dacin sa ba (a tsammaninta). Gashi dai ta fita rawar kai, amma bata taba yin kankanbar sanya kanta cikin soyayyah ba, balle ta zo ta zame mata ciwo mai kama da cancer; ; it starts from one cell, and spread to other cells, tunda ta faro ne daga zuciya kawai, amma ta kurda har cikin kashi da bargo, jijiya da jinin jiki, har ma da  nerbous system bata tsaya anan ba, saida ta cigaba tayi attacking sukuni da farin cikinta.
Wayar ta dake karkashin filonta ta soma ruri cikin tune din da ta tabbatar Zahraddeen ne. Ta yi har ta tsinke ta kasa dauka, don ba ta san me za ta ce da shi ba, zai kara luguiguita zuciyarta ne kawai.
Ta yarda ta amince tunda har Daddy ya yi furucin aure tsakaninsa da  yar uwarta da suka fito duniya a tare, suka sha nono daya, to ta yanke duk wata alaka ta soyayya dake tsakaninsu, da karfin tauhidi ba da nata karfin ba.
Ya kira ya fi sau goma amma ba ta dauka ba. A karshe ma kashe wayar ta yi gaba daya, ta kifa kanta cikin filonta, ta lumshe ido cikin halin tausayin kanta.
Don Zahraddeen ba abin tausayi bane a ganinta, tunda anyi masa toshiyar baki da cancadediyar budurwa da ta fi ta kyau mai daukar hankali.
 To kema ai anyi miki toshiyar bakin da zankadeden miji na nunawa sa a, na fita tsara, na nunawa sarki& ....., wanda da ana likawa da zaki iya likawa a goshi, kiyi tinkaho da zamowarsa miji a gareki, wanda ba don jinin  yan uwantaka ba, da ba abinda zai yi dake inda a hanya kuka hadu, a mataki da matsayin rayuwa irin nashi
Wani bangare na zuciyarta yace....
 Kayya! Ba a nan take ba!!! .
Itama ta yi gaggawar kalubalantar zuciyar tata da cewa,
 & .soyayya yin Allah ce, ba yin mutum ba. Ba ruwanta da sura, nasaba, asali, matsayi, ilimi ko mukami. Zahraddeen take so, kuma a halin yanzu ta hakura da shi tunda ya zama rabon  yar uwarta.
****
A ZARIA
Har karfe goma na safe, Zahraddeen bai fito ya gaishe da Inna Binta ba, kamar yadda ya saba in har yana gidan.
Inna ta ce da kanwarsa Rabi a  yar kimanin shekaru goma sha uku,
 Anya lafiya har yanzu Yayan ku bai fito ba?
Rabi a dake tuyar masa ta tsame hannun ta tana wankewa cikin tukunya ta ce,
 Bari in je in dubo shi .
Nura ya ce,  Yau da asubahi ko masallaci bai je ba .
Inna ta damu sosai, ta ce,  Bar min tuyar tashi jeki ki gano .
Ta mike bayan ta wanke hannun ta nufi sashen Yayan nasu.
Ta kwankwasa ta yi sallama bai amsa ba, ta sake daga murya ta yi sallama amma shiru. Don haka ta murda marikin kofar, anyi sa a bai sanya mukulli ba.
Ta shiga dakin nan ta hango shi can tsakiyar gado kudundune cikin bargo yana ta rawar dari. Ta karasa ta ce,
 Yayanmu lafiya har yanzu baka fito ba?
Cikin dasasshiyar murya ya ce,  kara rufa min bargon can Rabi a sanyi nake ji .
Ta ce a raunane,  Sanyi Yaya? A wannan uban zafin da ake zabgawa? Ko dai baka da lafiya?
Ya kasa ce mata komai, sai ya lumshe idonsa. Ta karaso ta daura hannun ta a goshinsa, zafi rau! Ta taba wuyanshi kamar an yarfa mishi wuta.
Da sauri ta fita tana gayawa Inna Binta. Tare suka dawo dakin har da Nura, Inna ta zauna a gefen shi duk ta rude.
Ta ce,  Ka san baka da lafiya shine ko waya ba za ka yi ka fadi ba?

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login