Showing 78001 words to 81000 words out of 112612 words

Chapter 27 - BABBAN GORO BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY SUMAYYA TAKORI.doc

Gaskiya ai daci ne da ita .
Malam ya yi murmushi ya ce,  To yanzu in ya tattaro matan nasa ya kawo miki shi ya tafi shi kadai me za ki yiwa matan nashi?
Za ki ije musu larurar aure ne ko za ki dauki nauyin su?
Ta yi shiru, don ta rasa amsar da za ta bashi.
Ya ce,  Da girmanki, da mutuncinki kika share mazauna kika zauna ana gaya miki gulma a kan mutanen da basu da hakkin ki.
Wallahi ki ji tsoron Allah, Allah ba azzalumin kowa bane. In kin ki ji ba kya ki gani ba . Ya karkade babbar rigarsa ya fita.
Kwana bakwai din da suka biyo baya, babu waya daga Lamido ko ji daga gare shi. Don haka Malam Abdulkarim ya yi shiri ya bi dansa don hankalinsa ya gaza kwanciya.
Ta jirgi ya taho, dan haka cikin dan lokaci ya isa Abuja, ya yiwa Isaac waya ya je filin jirgi ya dauko shi.
Suna tafe a hanya Isaac yake gaya mishi ai Oga yana asibiti yau sati guda, mai yiwuwa ma yau a sallamo shi.
Malam jiki a sanyaye ya ce,  Me ya same shi?
Isaac ya ce,  Mu kanmu ba zamu ce ba, lafiya na dauko su a filin jirgi shi da Maman su Fa ik, muka shigo gida lafiya. Ta dade a Sydney sai ranar ta dawo.
Ba a fi awanni biyu da shigarsa gida ba sai Madam karama ta soma ihun kirana. Wallahi wani abu aka luma masa a tsakar ka kamar bullet saboda zurfin da ya yi.
Dan Allah ya rubuta yana da sauran shan ruwa a gaba da ba za a same shi ba. Har yanzu likitoci suna hasashen Allah yasa kwakwalwarsa ba ta samu matsala ba, za su tura shi wani asibitin a Miami, likitan kwakwalwar da babu kamarsa a Africa da Turai ya duba shi sosai, Dr. Al-ameen Bello Makarfi (Siradin Rayuwa).
Don haka duk da bai fada ba, sai dai in a tsakanin Madam babba da karama ne wata ta yi mishi wannan aika-aika wallahi, don mu dai bamu ga kowa ya zo ba, kuma babu wanda ya shiga, don babu wanda ya isa ya karya security din gidan nan kwamfuta bata nuna shi ba .
Malam ya girgiza kai, tuni ya gano bakin zaren al amarin.
Ya samu Lamido ya ji sauki sosai, sai dai asibitin cike yake da ma aikatansa da abokan arziki har da mataimakin shugaban kasa.
Lamido ya ji dadin ganin mahaifinshi. A lokacin aka sallame su suka nufi gida motoci bila adadin biye dasu.
Lamido mutum ne na jama a, kowa son shi yake. Shi ba dan siyasa bane amma yanada siyasar sa akan- karan kansa, wadda ke sayo mishi kauna daga al ummar Nigeria kabilu da hausawa. Yana rike da hannun Malam, Safah na biye dasu rike da jakar Malam din karama, basu tsaya ba sai falonta na kasa.
Lamido bai ambato Danejo ba balle ya ce ita ta yi mishi wannan aika-aika, cewa ya yi tsautsayi ne wanda ba a sa mishi rana.
Malam din ma bai takura sai ya kure shi ba, shi dadi ma ya ji Lamido zuciyar  yan Aljannah gare shi, ya rufawa iyalinsa asiri shima Allah Zai rufa masa.
Malam don haushin Danejo ko zancen zuwanta Taraba bai masa ba. Ita tana can ta hada shi da mahaifiyarsa da  yan uwansa, shi ga shi yana rufa mata asiri, don ya tabbatar bai yi aure don baya son Danejo ba, ko don ya wulakanta ta ba.
Washegari Malam ya yi sammako ya yi komawarsa. Bayan ya saka musu albarkar hidimar da suka kwana suka yini yi da shi kamar sun hadiyeshi shi da Safah.
Da ya dawo gida ma bakinshi ya ja ya yi gum bai ce dasu komai ba. Ta zauna gidan in ta zama  yar ta adda kar ta kashe masa rabin zuciyarshi Lamido.
Tambayar duniya Haj. Nadeeya ta yi Malam ya ki ce da ita komai. Da ta dame shi da tambaya sai ya ce.  Dana bai ce min ga laifin da Danejo ta yi masa ba .
Ta ce,  Rashin arziki ne kenan ka gani ko? Don haka gobe a sai mata tikiti ta koma dakinta .
Ya ce,  Bani da hali .
Ta ce,  Ni ina da shi zan bata .
Ta shuri kwanukan abinci ta fita.

Zahra u ta shigo ta tadda mahaifinsu cikin tagumi, Zahra u ita ce autar su Lamido. Akwai shiri sosai tsakaninta da dan uwanta da take so fiye da kowa a gidan.
Shekarunta sha bakwai ta gama sakandire tana jiran fitowar jarabawa, don Lamido ya ce Malaysia zai kaita ba yanzu zai yi mata aure ba.
Ta gaida Malam, ta yi masa barka da dawowa. Sai ta koma gefe ta takure ta yi shiru, idanunta suka ciko da kwalla.
Malam ya maido hankalinsa kanta da ya gane cikin damuwa take, ya ce,  Fadima (sunan da yake kiranta) me ya faru ne?
Hawaye ya zubo mata ta matsa kusa da shi sosai, kamar zata shige jikinsa jikinta yana rawa,
 Baba tun muna yara ka hane mu da yin labe (sauraron maganar mutane), kuma wallahi ban taba yi ba .
Ya girgiza kai alamar ya yarda ba ta yi din. Ta ci gaba da cewa.
 To jiya Hajiyarmu ta fita Inna Shatu (mahaifiyar Danejo) ta zo, lokacin ina barci a uwar daka tashina kenan, amma ban fito ba sai na ci gaba da kwanciya.
Sai na ji Aunty Danejo na gayawa Inna Shatu fasa kan Yaya Lamido ta yi da tsinin takalminta .
Ta share idonta da hanci. Ta ci gaba da cewa.
 Ta gayawa Inna Shatu wallahi sai ta karasa shi in dai bai rabu da matar da ya aura ba. Ita ba gado take so ta ci ba, don ita ma ta shirya tafiya lahirar suje can su zauna su biyu, ko hurul ini Allah ya ba shi sai ta rabata da numfashinta .
Malam ya kadu sosai ya firgita. Zahra u ta ci gaba da cewa,  Sai Inna Shatu ta hau yin dariya, ta ce mata ai a lahira ba a mutuwa.
Ta yi hakuri ta zauna su ci gado, ta danne shi da filo kawai ko ta zuba mishi abin da zai tsitstsinka mishi hanji bakinsu alaikum, ba kishiya kuma ga gado daga ita sai  ya yanta, karkari a bawa amarya tumunin takaba, su Malam da Nadiya ma dan abin da za a tsakura musu a ciki bai taka kara ya karya ba& .. .
Zuwa wannan lokacin Malam ya mike tsaye.
 Tsakanin ki da wa kike magana Fadima? Mai sunanki ba ta karya .
Ta ce,  Idan na yi musu karya kada Allah ya sunsuna min kamshin Aljanna .
Ya ce,  Jeki, ki kwantar da hankalinki barni dasu, ba abinda zai samu dan uwanki da yardar Ubangiji.
Mutane na gari Allah yana kare abinsa a ko ina. Balle wadanda albarka da addu ar iyaye ta yi musu lullubi .
***
















T
un daga ranar Malam ya daukewa Hajiya Nadeeya wuta a kan zancen komen Danejo. Gargadi ya yi mata mai zafi cewa kada ta sake ya ji ta maida Danejo dakinta sai mijinta ya bukaci hakan, ya kuma zo da kansa daukan nata.
Wannan ba karamin tada ma Hajiya da Danejo hankali ya yi ba, sai dai ita Danejo ta fita tashin hankali, musamman idan ta tuna Lamido na can yana barje amarcinsa da watanta.
Wannan tunanin ba karamin tada mata hankali yake yi ba. Aka debi sati biyu babu Lamido babu wayarsa.
Sai ta soma hada kayanta kawai kamar mahaukaciya a hantsin safiyar lahadi ta fito jaye da trolley, ta samu Hajiya a madafi ta ce.
 Ni zan wuce Abuja Hajiya, jikina na bani Daddy ba lafiya ba, don bai taba yin irin wannan fushin dani ba .
Hajiya ta yi dan jum! Ta ce a ranta,  Danejo kishi ya maida ta mahaukaciya .
Kamin ta ankara Danejo ta fice. A zaure ta hadu da Abubakar, ta ce,  Yauwa Bukar, dauki akwatin nan ka rakani Airport .
Abubakar ya cika da mamaki, ya ce,  Aunty Danejo babu mukullin motar Malam a hannuna, kin san kuma ba zan goye ki a babur ba .
Ta ce,  Tasi zamu hau .
Ya kama baki yana mata kallon wani abu na motsi a kwakwalwarki, sannan ya ce,  Da izinin Yaya Lamido zan dauke ki a tasi in kai ki filin jirgi?
Ta lailayo wani ubansu ashar ta mirgina masa, ta ce,  Shi da Yaya Lamidon su raba, zai rakata ko ba zai raka ta ba?
Da gudu Abubakar ya yi cikin gida ya shige kuryar dakin Hajiyarsu yana cewa,  Hajiya! Hajiya!!
Ta aje ludayin da take damun kunun gyada da shi ta bishi dakin zaninta na kwancewa, ta ce,  Lafiya Abkar .
Ya ce,  Wallahi Aunty Danejo kanta da motsi .
Ta ce,  Nima na ga alama .
Suka dunguma soron suka kama jakar suna lallaminta ta koma gida ta jira Malam ya dawo ya ba da mota sai a kaita.
Sai ta fashe musu da kuka, daidai lokacin Inna Shatu ta sawo kai soron.
Ta ce,  Lafiya?
Hajiya ta ce,  To da sauki dai, Danejo ba ta jin magana, har yau matar Lamido take ba ta gama sanin halinsa ba .
Da kyar suka lallabe ta da taimakon uwar suka koma cikin gida. Hajiya Nadeeya ta ce,  Ki bar ni in bai zo ba karshen satin nan ni da kaina zan maida ke dakinki.
Bai isa ba wallahi, har yau ba a haifi diyar da za ta rabaki da Lamido ba. Ba  yar uwar Malam ba, ko  yarsa ce ta cikinsa .

****
A nasu bangaren, komawar Lamido gida daga asibiti ta zo da sabon sauyi wanda ke nuna lallai Lamido na bukatar ganin likitan kwakwalwa.
Da farko al amuran basu damu Safah ba, don tana danganta hakan da zafin ciwo, tunda raunin bai gama warkewa ba.
Abu na farko, idan Lamido ya shiga wanka baya fitowa sai ya yi awa biyar. Tana mamakin me yake zama yana yi haka?
Rannan dai ta ga zaman jiranshi a bakin gado ba zai yi mata ba, sai ta bishi bandakin ta ga me yake yi kwanan nan a bandaki?
Sanda ta murda kofar ta shiga sai ta ganshi yana matsa (gilette shabing cream) a kan burushinsa, ya hau wanke baki da shi.
A gefe kuma ya tara kumfa a baf ta omon Ariel ya shiga ciki ya soma bathing. Yana ninkaya cikin rowan. Yana mai yin soso da hularsa.
As a proffessional medical Doctor, sai ta soma obserbing kwayar idanunsa, a juye take gaba daya.
Sanda ta fito, zama tayi kan duwawunta a gefen bandakin a dandaryar tayal tasa hannuwanta cikin gashin kanta kamar ta kurma ihu, ta rasa inda za ta sa ranta.
Sai ta ga ya fito daure da tawul ya nufi ma adanar kayanta ya fiddo best dinta fara sol ya soma kici-kicin sakawa amma ta ki shiga jikinsa.
Da ya takura sai ta tsage gida biyu, ya yi ta tsaki ya yar da ita ya dauki wandon farin boyel ya saka, tazugen na reto har kusa da gwiwarsa. sai ya kawo suit baka ya dora. Ya kawo hula zanna-bukar ya saitata a goshinsa.
Ta mike da gudu ta rungume shi ta baya,

 Lamido kada ka karya min zuciya, bayan ta mika wuya ga kaunarka!!! .

Kokarin rabata yake da jikinsa, bayan ya bata kyawawan mari guda biyu a kuncinta na dama. Zafin marin ne yasa ta yi baya ta yi taga-taga ta fada gado.
Ya fice yana ce da ita,  Ki yi maza ki dama min koko da  yar tsala, irin wadda Hajiyata ke mini ina tafiya dasu makaranta .

Fitowarsa ke da wuya Isaac ya jawo mota har gabansa, haka mai tsaron lafiyarshi na tare da shi suka nufi office, kowannensu fuska muzance da shigar da Ubangidansa ya yi. Amma wa ya isa yayi Magana?
Isaac na tuki yana sharar hawaye, lallai maganar likitocin sa ta tabbata.
A cikin office abubuwa suka ci gaba da gudana abnormally, a fuska dai Oga lafiyarsa kalau, amma abubuwan da yake yi sun sha bamban da wadanda yake yi a baya.
Abu na farko da ya fara yi shine, transferring gaba daya kudin dake cikin account dinsa zuwa account din Safah (na bankin GT kenan). Na First bank zuwa account din Malam Abdulkarim. Na kadarorinsa kuwa zuwa account din Fahad da Fa ik.
Sannan ya rubuta wata latter ya tura ta zuwa email din mataimakin shugaban kasa mai dauke da cewa a sauke shi daga mukaminsa zai koma kasar Saudiyya da zama, a nemi wani a bashi kujerar shi ya yi retire.

Sako ya shigo  Economic and Financial Crime Commission cewa ga mai girma Deputy zai shigo ma aikatar yanzu.
Nan da nan kowa ya mike tsaye aka karbi mai girma Deputy. Bai tsaya ba kai tsaye ofishin Lamido ya nufa. A lokacin Lamido kuka yake yi, ya kifa kai a teburinsa.
Har mai girma ya shigo bai san ya shigo ba, sai da ya fiddo waya yana magana da Mr. President sannan ne Lamido ya dago.
Ko gurin zama bai bashi ba, shi ya yiwa kansa mazauni a kujerar dake fuskantar Lamidon.
Ko gaishe shi Lamido bai yi ba balle ya mike tsaye don girmamawa. Kallonsa kawai yake da juyayyun kwayar idonsa, shine ya sassauta murya ya ce.
 Lamido baka gane ni bane?
Ya ce,  Idan na sanka sai me za a yi? Aikinku ne na ce bana yi, to me ka zo ka yi min?
A daidai lokacin da jiniyar sojoji ta cika ma aikatar, sai ga mai girma Mr. President ya zo da kansa. Suka kulle kansu su uku a office.
A Turance suke magana a tsakaninsu da mai girman da mataimakinsa. Nasir sai harararsu yake, ya soma tunanin ma bari kawai ya gwara kansu dukkansu munafukai ne.
Ai da suka ga ya mike ya nufo su a fusace daya ne ya bi ta kan daya ya cimma kofa. A nan ne kuma likitan Lamido ya danno kai, sai Mr. President ya bi ta kansa ya yi gefe guda shi da jakar aikinsa, bai tsaya ba ya tsallake shi ya cimma jama arsa a kofar ofishin yana haki yana zazzare ido da kokarin nuna komai is normal.
Don haka Lamido kan Mr. Deputy da Dr. Mohammed ya hada ya gwara da bango, sannan ya nuna musu kofa ya ce,  Habe your way here . (Ku bi nan).
Deputy bai tsorata ba, haka Dr. Mohammed, sai ya rungume Lamido yana kuka sosai, goshinsa yah aye yayi suntum, ba tare kuma da ya damu da naushin da Lamido ke kai mishi ta ko ina ba.
Shi kuma likita yayi gefe bisa tebir yana ta rubuce-rubuce cikin file din shugaban EFCC Nasir Lamido Taraba.
Da lallashi da ban baki Deputy ya ciyo kansa ya yarda ya shiga mota suka maida shi gida, suka samu Amarya abin tausayi, ta ci kuka har ta gode Allah. Ko kayan barcin jikinta ba ta cire ba, tana zaune cikin kujerun falonta ta yi tagumi, fuskar nan data sha mari ta kumbura duk da ta mulketa da manthaleta.
Da saurinta ta mike ganin sun shigo da shi a rirrike. Yau ce rana ta farko da ta taba yin ido da ido da Deputy Sulaiman Yakasai, sai dai ta ji shi a bakin Lamido ko hirarsu in suna waya.
Ba wannan ne a gabanta ba, ta ce da Dr. Mohammed  Am sure Lamido is not well . Ta gaya mishi abubuwan da ya yi a yau.
Allurar barci Dr. Mohammed yai mishi, bai kai minti biyar ba ya yi barci. Cikin dan lokaci manyan Psychiatrists sun cika gidan, har da jar fata.
A can bangaren Deputy da Mr. President tuni sun kammalawa Lamido da Safah shirin tafiya MIAMI. An dora wani a kan kujerarsa an kuma tafi dauko Malam Abdulkarim daga Taraba.
Wanda ke can yana mamakin alert din da ya samu cikin wayarsa mai nuna cewa Lamido ya yi masa kyautar kudin da bai taba jin adadinsu a rayuwarsa ba.
Sai ga sako ya cimmasa Isaac ya zo, aka bude mishi dakin ganawa da bakin Malam. Can Malam ya je suka gaisa, ya gaya mishi an turo shi ne ya dauke shi. Bayan wannan bai ce da shi komai ba. A daren suka tashi zuwa Abuja.
Hankalin Malam Abdulkarim ya kai kololuwar tashi da ganin wai Lamidon shi ne riga daban wando daban, yana kallonshi cikin ido amma bai gaishe shi ba. Safah na gefe dukunkune cikin lafayya tana ta kuka mai ratsa zuciya.
Addu a malam ya soma karantowa yana tofa mishi, sai ya soma kunkuni yana cewa,  Gaskiya ni ka daina tofa min miyau .

A wannan dare da ya zowa Safah da sauyika da dama a rayuwarta, har garin Allah ya waye ba ta daina kuka ba, ba ta san tana son Lamido har haka ba sai yau da rayuwa ta juya masa baya.
An sauke Lamido daga kujerarsa an mayar da wani a gurbinsa. A cewarsu, dakatarwa ce ta rashin lafiya a bisa shaidar motsuwar kwakwalwa da likitocinsa suka bayar.
A washegari suka tashi zuwa MIAMI su hudu, Malam Abdulkarim, Safah da Lamido, sai Dr. Mohammed (personal Doctor ) dinsa da iyalinsa.

****S
MUTANEN PARIS
un sauka a Paris karfe goma sha biyun dare, motar Hotel din da Zahraddeen ya yi booking tun kamin su taso tana tsimayen saukarsu, suna sauka chauffer din ya kwashesu.
Babu komi cikin wannan zama na Zahraddeen da mai dakinsa sai so da kauna zallah.
Hutu suke mai suna hutu da tsimayen isowar jaririnsu ko jaririyarsu. Sun manta da wata Anisa da al amarinta wadda suke kallo a matsayin wata wadda ta yi musu karan tsaye a cikin rayuwarsu.
Sai dai Marwah zuciyarta babu mugunta. Da ta samu nutsuwa ne ma ta soma tunanin hanyoyin da za tabi ta janyo hankalin Zahraddeen da su ya kaunaci amaryarsa, in dai ba zai kusance ta ba ita bata damu ba, ko duniyar ne ya tattara ya bata.
A ranar da suka yi kwana uku ta kira Inna ta sanar da ita sun sauka lafiya, kuma tana samun kyakkyawar kulawa daga likitocin ta.
Inna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login