Showing 42001 words to 45000 words out of 112612 words

Chapter 15 - BABBAN GORO BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY SUMAYYA TAKORI.doc

da kika yiwa Imam har ta kai ga saki? Saki ukku?? Wanda bazai gyaru ba, wanda Allah baya so???
Ba ta iya karya ba, ta gaya mata dalla-dalla. Mami ta yi shiru tana nazari, ta ce,  Ai shi kenan, tunda hakan kike so& .... Sai hawaye sharrr! Data yi tunanin watakila sakamakon hakan Imam zuciyarshi ta buga ya mutu ne, ko ya haukace.
Hankalin Safah ya kara tashi, yau ga mahaifiyarta na kuka saboda bakin cikin ta. Ta ci gaba da rokon Mami ta yi hakuri, amma Mami kuka take haikan tun daga karkashin zuciyarta. Sai da ta share hawayenta da tafukanta ta ce.
 Haka Allah Ya so, na kuma yarda da kaddara, idan Allah Ya rubuta ke ba matar Imam ba ce a duniya yaya zan yi? Halin da yake ciki, a ina yake? Shine abinda ke damuna.
Ki tattara ki koma makaranta, don in ina ganin ki cikin gidan nan ba zan rabu da bakin ciki ba. Wanda zai iya zamowa barazana ga lafiya ta .
Cikin kuka ta ce,
 Mami baki yafe min ba kenan?
 A a, na yafe miki, Allah Ya yafe mana baki daya. Ki je ki nemi afuwar Daddy shi kika batawa ba ni ba. Cikin sha aninki yanzu kam ni  yar kallo ce .
Jikinta babu kwari ta taso ta fito daga dakin Mamin ta nufi sama sassan Daddy.
Kishingide yake da jaridar New Nigeria da medicated glass dinshi yana dubawa, ta yi sallama ya amsa ba tare da ya dubi hanyar da ta bullo ba.
Ta isa gabanshi ta kwantar da kai a kan kafafun shi tana kuka tana rokon shi da kalaman da ta roko Mami.
Shiru ya yi mata kamar ba da shi take ba. Da ya gaji da kukan ta ya ce,  Me kike so in ce miki Safah? Kin nuna min ban isa dake ba, na yi hukunci kin tozarta ni, na ce ga abinda nake so sabida kyautatuwar rayuwarku gabadaya ko bayan raina kin ce bakya so.
To ya bi umarnin ki ya rabu dake ba sai ki yi abin da kika ga dama ba?
Ta ce,  Don Allah Daddy ka yi hakuri, na yarda na yi kuskure na yi nadama .
Ya yi murmushi ya ce,  Nadama ko? Tukunna ma. Yanzu me kika yankewa rayuwar ki?
Ta ce,  Makaranta zan koma gobe in Allah Ya kaimu .
Ya sa ido yana kallon ta ya ce,  Aure kuma fa?
Ta sunkuyar da kai ta ce,  Zan yi Daddy in Allah Ya kawo mijin . Ya kyabe baki.
Ya ce,  Tashi ki je ki yi shirin tafiyar .
Ya janyo brief case ya rubuta mata chekue din kudi masu yawa, ta karba ta yi godiya ta fito.

Safah na tuki a kan titin da zai kaita Zaria daga Kaduna, cikin kankanuwar motarnan kia-optima, wadda Zahradden ne ya zabar musu ita. Ba yadda Mami bata yi da Daddy a kan direba ya kaita, amma ya ce shi ya daina sangarta  ya ya, motar ma daya barta ta dauka zai tura a dawo masa da ita. Ta shiga Adaidaita sahu ya daidaita mata sahu.
Yanzu zata san yaya dalibai suke neman ilmi a jami a, a tsaye ba a kwance ba irin wanda suka samu, ta shiga cikin hostel ta zauna tayi rayuwa daidai da dan kowa, a kyale ta ta fara koyon darasin rayuwa. Domin batasan Annabi ya faku ba .
Gudu take sosai hawaye na sauka a kan kuncinta. Ta kan kalli gefenta mazaunin Marwah ne. Da tana cikin motar da yanzu ta kunna c.d na wakar India kabhi khushi kabhie gham, tana bin wakar tana rawa da daga inda take zaune. Allah sarki! Tuna Baya Shine Roko.
Wai yanzu ita da Marwah suna duniya daya, amma muhalli daban-daban saidai a ga juna da shauki lokaci-zuwa lokaci. Wani irin nutsatstsen al amari game da IMAM na sauka a zuciyarta, wani irin ni imtaccen feeling ne da ba za ta iya fassarawa ba.
Allah ne kadai ya kawo ta Zaria lafiya, cikin kiyayewarsa da alfarmarsa, amma fa ta sha zagi daga motocin gabanta da bayan ta.
Ba ta sha wahalar samun daki a hostel ba da taimakon wata  yar ajinsu Jamila Sarki. Su biyu ne a dakin ita da Jamila.
Ita Jamila  yar Kano ce, tana da aure amma ba ta haihu ba. Mijinta Mus abu ma aikacin M.T.N ne yana reshen Bauchi, ita kuma take karatu a nan Zaria.
Duk gayun Jamila sai ta ke raina kanta a duk lokacin da ta daga ido ta dubi Safah Dan-Kasa, ita ba  yar gayun bace (ba mai sa kyale-kyale ba), non-transparent (ba mai daukar ido ba), asali ma sai ka kura ido sosai sannan zakaga kyawun bakar fatar data mallaka da nata salon gayun na halitta, komai nata natural babu kari da na kanti ko daya, daga fata, gashi, kyawun sura duka Safah ta mallake su amma in an extraordinary manner.
Haka kawai Safah take burge Jamila, gata yarinya danya sharaf, don Jamila ta girme ta da wajen shekaru biyar. Sannan gata kwaruwa a fannin karatu, sam ba ta wasa oberall ce, abinda ya kawota kawai ta sanya a gaba.
Sai dai a dan zaman da suka yi na tsayin lokaci Jamila ta fahimci Safah Dan Kasa na cikin matsananciyar damuwa da ba ta san ko ta mece ce ba.
Tana so ta tambayi Safah abinda ke damun ta take yawan zama shiru silent sannan isolated, wato ta kebance kanta daga son shiga jama a.
Ta rufe wayoyinta gaba daya ba ta amsa wayar kowa. Tun fil azal kuma dama bata cikin kowanne  social network . Wayar ma data dan rike na dan lokaci soyayyace ta rinjayeta, ita kuma tayi biyayya a gareta. To tunda ta zama tarihi suma wayoyin su zama tarihi kawai. Sai dai kuma Jamila ba ta so ta zamo mai shisshigi cikin abinda bai shafe ta ba.
Don haka ta kawo ido ta zuba mata, cikin zuciyarta tana taya ta da addu ar Allah Ya yaye mata duk irin matsalar da take ciki, sabida ita tsakanin ta da Allah take kaunar Safahn, ga Safahn kuma bata damu da kowa ba sai abinda ya kaita.
Saidai duk wani hakkin Jamilah dake kanta na makwabci mafi kusanci tana saukeshi. Lokacin a zauna ayi hira ne ko jin tarihin juna da ire-iren hakan bata dashi.

A zahiri damuwar itace, Safah ta fada wani hali na soyayya wanda ita kanta ba ta san cewa soyayyar ce ke dawainiya da zuciyarta ba, soyayyar tsohon mijinta dan uwanta Imam, wanda a halin yanzu ba ta san a halin da yake ciki ba, ba ta san inda yake ba. Yana raye ko baya raye?
Wani zubin kwana take tana kukan nadama ba tare da sanin Jamila ba. Tana ganin ta gama kashewa kanta rayuwa tunda ta rasa shi.
Soyayyarshi a zuciyarta a kullum kara karuwa take, kamar ana iza wuta. Kamar azal. A lokacin da ya riga ya zama haramiyar ta. Tunda daman babu iddarshi a kanta, kuma tuni lokaci ya mika.
Kuka take sosai a duk ranar da ta tuno rabuwarsu ta karshe......  Na tabbata dan halak, ba shege bane ko& .?
Sautin da ke ta yi mata kuwwa a kunne kenan, a duk lokacin da ta zauna ita kadai, wanda ke kara ruruta wutar nadamar ta. Ita da bakinta tace da Imam idan shi dan halak ne cikin UWA da UBA & .to ya saketa& .gashi ya sake tan kamar yadda ta bukata, to amma sakin ya zamar mata jafa i& .da dai wannan halin da ta tsinci zuciyarta da ruhinta a ciki na bege& . da so da kaunar ma gabadaya& & Harshe?
Ya Allah ka bamu linzamin shi a hannun mu, yana kaimu wuta, yana kaimu sa ira, yana kuma kai mu Aljannah. Again, yana lalata mana rayuwa, mu dinga rikeshi ta hanyar tauna Magana kafin mu fade ta. Idan ya furta baya taba mayarda ita komai dadinta ko dacinta.
Harshe (da Hausa), tongue (da turanci), Lisan (da larabci). Wata tsoka ce mai amfani daban-daban da Allah Ya halitta a cikin bakinmu, wadda in muka iya controlling dinta, zamu iya controlling dukkannin al amuran rayuwar mu.Ta kan ce,
 Ina ma ana maida hannun agogo baya?

Me za ta yi ta yi repenting kuskuren da ta tafka a baya? Babu! Imam, foreber and eber (har Abadan) ya zama haramiyar ta. Ko da ace watarana ya dawo daga inda ya shiga. Domin dai ita kyakkyawan zaton yana lafiya take masa ba kamar Mami ba, kawai dai yayi hijira ne don ya raba duniyarsa da tata.
Ta tabbatar ba za ta kara samun soyayyar sa ba. Bazata kara samun damar da ta samu har tsayin shekaru ashirin ba. Kenan ya zama dole ta yi hakuri, ta fuskanci rayuwarta ta gaba, ta baiwa mazan dake rububin ta damar fitowa, mafi yawa daga ciki farfesoshinsu da manyan Dactocinsu, wadanda yawanci hazakarta ce take sayo mata soyayyar, kamewa da kamalarta, ba kamar sauran dalibai  yan uwanta ba, da yake a dan tsukin aka tura su TH, wato  teaching hospital suna koyar ayyuka a aikace, gara tayi maneji da dayansu duk da dukkannin su masu iyali ne.
To amma wa zata zaba wanda zai maye gurbin Imam a zuciyarta? Wa za ta samu ya so ta kamar yadda Imam ya so ta? Yaya za ta yi da dimbin soyayyar shi da a yanzu take dawainiya da zuciyarta???

***










T
ana kicin tana gashin pizzawarma da french bread da take so za ta yi kalaci da shi, ta jiyo sallamar Rabi a a bakin kofar shigowa sassanta.
Ta yi tsaki tsuww! Tana kunkuni,  Yaushe wadannan mutanen za su daina shiga sabgata ne? In abinci ne na ce bana cin jagwalgwalo a kyale ni mana? .
A fusace ta fito ta bude kofar, Rabi a ce dauke da food flasks guda biyu, ta raba ta gefen ta don ta shiga ta ajiye mata tunda bata bata hanya ba, ta yi mata wani banzan kallo ta ce.
 Ke, koma da abincin nan a koshe nake .
Jiki babu laka Rabi a ta fasa shiga ta juya, ta rufo kofarta ji kake garam! Har sai da Rabi a ta tsorata. Ta karta a guje.
Ta maida flasks din kicin ta ajiye. Inna Binta dake kofar kicin din ta ce,  Ya kika dawo da shi? Ko bata tashi ba?
A kufule Rabi a ta ce,
 Inna ki yiwa Allah ki daina sa sanwa da matar nan, ba ci take ba asara ake, kullum sai dai in zubar yadda na kai mata haka nake daukowa.
Yau kuma kwata-kwata cewa ta yi in komo da shi ta koshi .
Inna ta ce,  Ke kam kin fiya daukar zafi a kan abinda bai kai ya kawo ba, don ta ki ci ba cikinta ba? Hakkina ne in ba ta a matsayinta na diyata kuma makociya mafi kusanci dani .
Haushi ya kashe Rabi a ta ce,
 Inna ita ba ta dauke ki a matsayin Uwa ba, tunda ta zo gidan nan yau sati biyar ta taba zuwa inda kike ta gaishe ki?
Ni ban taba ganin inda ake haka ba, kawai an kwaso mana wadda ta fi karfinmu kuma ta raina mu, ko  yar Karuna ce ai sai haka.
Ni wallahi ba zan dauki raini ba, ba zan kuma zuwa kai mata abinci ba tana yi min kallon biyu-a-hu. Sai dai ki aika Nura amma ni wallahi ba zan kara zuwa dakinta ba .
Inna ta yi murmushi tana danne nata bacin ran ta ce,  Bana son rashin arziki, ba gaba take dake ba? Ko ba matar Yayanki ba ce? Abinci ba zan fasa bata ba, ko ta zubar ko ta ci babu ruwan ki .
Sallamar Zahraddeen ta katse su. Ya hade cikin bakaken suit kai ka ce bakin Ba-Amurke ne, inda duk ya gifta lallausan kamshin Dior-Addict ke tashi.
Inna ta daga kai a hankali tana kallon sa, cikin sati biyar da yin bikinsa ya rame kwarai. Kowanne ango yana yin kiba harda teba ya yi kyau bayan bikinsa, amma banda Zahraddeeninta. Wanda wuyansa ya koma uwa marikin lema, idanuwa wadanda dama a lumshe suke, suke kara shigewa ciki.
Ya samu kujera  yar tsugunne ya zauna yana murmushi ya ce,  Inna kun tashi lafiya?
A sanyaye ta amsa  Lafiya kalau Deeni, ya ya amarya?
Ya yarfar da hannu, ya dan juyar da kai ya ce,  Lafiyarta kalau .
Duk sai suka yi shiru kowanne da abinda ke cikin ransa, amma kowanne baya so ya furta. Ba ya kuma son da??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????n uwansa ya gane yana cikin damuwa.
A karshe Zahraddeen ya ce,  Inna ko zan samu kalaci? Kaduna zan wuce yanzun nan .
Ta ce,  Ina matarka da kullum za ka zo ka ce in baka abinci?
Ya rausayar da kai ya ce,  Naki nake so Inna, babu inda zan ci abinci in ji na gamsu Inna sai naki .
Ta yi murmushi ta jawo kulolin da Rabi a ta dawo dasu ta tura masa, yana cin funkason alkama da miyar alayyahun data ji kaji zukuzuku suna hira.
Cikin hirar yake tambayar Inna
 Wai Inna ina wannan Yayar taki ta rugar Ardo Lamido?
Ta ce,  Yaya Badijo? Tana nan lafiya, sai dai fushi take dani don na kwan biyu ban je ba. Amma insha Allahu karshen watan nan zan yi kokari na je. Nura nake jira ya samu hutu don shikadai zai iya shiga wannan jejin mai kayoyi da kwazazzabo da mota ba tareda yayimin korafi ba.
Bikin ka ma ban samu na aika mata ba saboda yadda abin ya zo a kurace, laifi kan laifi kam na yiwa Yaya Badijo, sai dai ta dubi Allah ta dubi zumunci ta yafe mini.
To abu ne irin na jeji ko irin wayar zamanin nan basu da ita balle a samu saukin sadarwa. Sannan babu yadda ban yi da ita ba kan ta dawo nan mu zauna tare bayan rasuwar maigidanta ta ki. Ita ba da ba sai  yar jikallen ta Anisa wadda danta Iro ya mutu ya bar mata .
Ya ce,  Ita ce wadda kike gaya min kin sa ta makarantar su Rabi a?
Inna ta ce,  Ita ce, yanzu ajinta uku kenan a karamar sakandire, tare suke da Rabi an, abinda yasa baka ganinta nan in sunyi hutu can ruga take komawa ta yi hutun ta. Ko tazo min nan ana I gobe zata koma ne, yawanci kuma baka nan kana Kaduna.
Amma gashi tun ba a je ko ina ba Yaya Badijo ta fara fadan karatun ya isa haka aure take so ayi mata, wai ta samu miji a can rugar su.
Ita kuma yarinyar bata so tafi son ta yi karatu, sai dai kwakwalwarta bata ja, gashi tana son karatun kamar me, amma Allah bai bata kwakwalwa ba.
Rabi a ta ce ita ke daukar na karshe a ajinsu, sai dai hakan baya damuna don tun farko ba a dora ta akan turbar karatun ba, banda ma n adage na kafe aid a ko firamare bazata bar tat a je ba, sai kiwo da tatsar nono .
Zahraddeen ya yi dariya ya ce,  Duk sanda za ki Inna ki yi min magana zan kai ki nima in sada zumunci, bazan taba mancewa da kaunar da Badijo ta nuna min ina yaro ba, ita ta yaye ni, a wajenta nayi jinyar shayi (kaciya) . Inna tayi dariya tace  ashe baka manta ba .
Ya mike ya zuba hannun shi cikin aljihu ya zaro mukullin motarshi ya nufi hanyar fita yana cewa,  Ni na yi nan Inna, Kaduna za ni hutun da Alhaji ya diba min ya cika, yau zan koma ofis ayi mana addu a .
Inna ta ce,  Addu a kullum ina yi maka Dini, Allah Ya ji kan mahaifinka, ya baka  ya yan da za su share ma hawaye kamar yadda kake share min. Ya kare min kai daga sharrin makiya da mahassada, ya kai ka lafiya ya dawo min da kai lafiya .
Har ranshi ya ji dadin addu ar Inna, ta wanke bacin ran da ya kwana da shi. Cikin sukuni yake tukinsa a kan titin da zai sada shi da garin Kaduna.
Isarsa ofis ya tadda jibgin ayyuka na jiransa, don haka ya zamo busy a satin gaba daya. Sai da ya gama dukkan ayyukan shi sannan ya rubuta (resignation letter) wato takardar ajiye aiki da  Dan Kasa Holdings da hujjar tafiya karo karatu, ya tura ofishin Daddy.
Alh. Aliko ya dade yana juya takardar Zahraddeen a hannunsa, wadda sakatariyarshi ta shigo mai da ita. Wadda ta ciro yanzunnan a kwamfuta.
Kafin ya ce wani abu Zahraddeen ya yi sallama a ofishin cikin sallama, daga mishi kai kawai Daddy ya yi, amma ya kasa amsa sallamar shi.
Binsa kawai yake da kallo kamar yau ya fara ganinsa. Zahraddeen ya zauna ya sunkuyar da kai shima ranshi babu dadi.
Shiru ta ratsa a ofishin na tsayin mintuna biyu, sannan Zahraddeen ya yi ta maza ya gaida Daddy ya amsa, sannan ya sassauta mamakin sa ya ce.
 Da gaske kai ka aiko da wannan takardar?
Cikin matsanancin ladabi ya ce,  Na am Daddy ni na aiko da ita .
Ya ce,  Kuma don za ka je karo karatu sai ka ajiye aikin gaba daya?
Idanuwanshi na son zubo da hawaye yana kokarin maida su da karfin gaske, ba kuma na komai bane na  sabo ne da kaunar da yake yi ma Alh. Aliko, Uba mai cin tudu biyu a yanzu; siriki/ubangida.
Ya ce,  Hakan na ga zai fiye min kwanciyar hankali Daddy, ka yi hakuri kada ka kullace ni, ko ka yi min wata fahimta sabanin kyakkyawan kudirin dake zuciyata.
Daddy ban yi haka don raini ko don na bata maka rai ba, ko don ka yi min wani laifi ba, ina da sha awar zurfafa karatuna ne kawai .
Alh. Aliko sai ya yi murmushi don shi babba ne, tuni ya hasko abinda yasa Zahraddeen yin wannan zuciya.
Ba shakka ya fahimci rainashin da Marwah ta yi shine dalilinsa na yin hakan. Sai ya ji yaron ya kara burge shi, ya kara shiga ransa.
Ya ce,  Ina bayanka Zahraddeen, Allah Ya shige mana gaba. But I ll miss u so much& ..(zan yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login