Showing 306001 words to 309000 words out of 366611 words

Chapter 103 - AUREN SIRRI Book 2 Complete by Aisha Bagudu.txt

29 Dec 2025

8411

mugun tsanyi da canzawa .
gabadaya ma ta sauya ta daga zeenat din da suka sani ta dawo musu ruwan tsanyi.

Tun sanda ummi ta sanar da zeenat zance haihuwa nan jikinta yayi mugun tsanyi .
sannan takara tabbartawa kanta Dan Adam ba'a abakin komai yake ba arayuwa.
sannan km mutun bai isa ya canzawa kanshi kaddararsa ba.
Ita kam ta yarda ta amince kaddararsu ce nablah ita da mijinta.
Domin tayi imani da Allah idan ba Dan Allah yayi nablah zata shigo cikin rayuwarsu ita da mijinta ba.
da tata kaddarar xubda ciki bai shigo ba.
Dole kaddarar zuwan nablah da hahuwar da zata yiwa deeni ya janyo nata kadddarar zubda cikinta .
jikinta ya sake yin wani irin mugun sanyi take km jikinta yasoma rikicewa tasoma rawar tsanyi ta sake rungume anan dake rungume ajikinta tana jinjina girman alamarin ubangiji da kudirarsa domin duk yadda Allah yaso da lamarinsa hk zai Yi .
shekara biyar Kennan tana neman haihuwa ido rufe byn zubda cikinta sai gashi cikn shekara daya tal deeni yasamu ya'ya har biyar .

hk tunani suka dinga zuwa mata iri iri game da rayuwar duniyar suna wucewa .
duk da yadda take jin jikinta hkn bai hanata budar bakinta tacewa ummi yakama ace xuwa yanzu an isa zuwa hospital.
ba sai wasu daga cikin dagin Sun rigamu zuwa ba.
ummi wacce oready tagama mikewa daga zaune datake tace tunanin da nike Yi Kennan barin na dauko mayafina da Jakarta sai na tafi tunda ke bakya jin dadin jikinki ......
A'a ummi tare zamu har yaran ai bawani Abu ke damuna normal nike .

zeenat tasaka laraba tayiwa yaran duka wanka ita km tasoma da gyara haidar da junior .
Sannan ta shirya Anan tsab cikin wasu kayan redymedy ta shafa mata baby oil akanta ita dasu Haidar sbd har lokacin ganinsu take they are still baby's.
kawai dai jikin girma jiki garesu sakamakon cimar abincinsu da km kulawa da tattali da suke Samu me kyau .
dan ko abincn da ake basu irin na kasar turai ne.
sai kyalli yaran suke xubawa da daukar hankali barin ma yar gata Anan domin gabadaya gidan sun fi ji daita kasancewarta mace.
Ta feshesu da turare me sanyin kamshi tana tushe hancinta dan jin turaren yasoma hawa kanta.
" sannan Itama ta Mike tsaye da kyar ta zaunar dasu akan kujera three stars tace kujirani baby's dina ina zuwa .
murmushi Haidar da Anan suka mata banda miskilili uban miskileye wato junior me halin ubansa sak kana ganinsa babu tmby like father like son .
tashiga dakinta Kai tsaye bathroom tashige gabadaya tasoma yunkurin amai aiko tashiga kwara amai tmkr zata amayar da hanjin cikinta.
sai datayi me isarta sannan tayi wanka ta fito tana fidda numfashin wahala sama sama.
ta shirya kanta tanajiyo sautin muryar ummi tana ce mata tagama fa ita take Jira .
Bata wani Yi shafa ba ko fesa turare ajikinta sbd yanzu kusan duk bata bukatar shakar kamshinsu .
wanda ta fesawasu anan ajikinsu ne ma yanzu yasakata Amai.
daguwar rigar jallabiya ja wace tasha stone work tun daga samanta har kasanta da hannuwanta ta zira ME shegen kyau da daukar hankali .
tayi rolling din kanta da bakin mayafi sak idan kaganta kaga ba indiyar asali .
duk da rashin shafan da batayi ba hkn bai sa fuskarta yin fesss ba farinta bai disashe ba.
sai ma wani fari data Kara Yi na musamman ta dauki farin ledar tsamiyar birinta wanda shansa ya zamemata jiki tasaka cikin yar karamar Jakar ratayawarta.
tayi kasa.. Suka nufi hospital suna isa kai tsaye dakin da aka kwantar da nanlah suka nufa wanda daman deeni yasanar masu .
bakinsu dauke da sallama suka shiga dakin .
Zaune suka tadda oga deeni manne kusa da nablah makale daita tmkr zai shege mata jiki yana bata tea abaki ganinsu yasa ya dan gyara zamansa yana yiwa ummi sannu da zuwa yana cigaba dabata ita km ganinsu yasa ta Kai hannunta tana kokarin karbar Cup din a hannushi.
babu musu ya sakar mata ita km sunkuyar da kanta kasa sosai takasa sha yayinda yaran sukayo kanta suna murnar ganinta .
dan rabonsu daita kusan tsawon wata uku Kennan.
deeni yayi saurin taresu . aiko junior ya saka kuka yana kallon uwarsa da son zuwa gurinta Amman antareshi.
deeni yashiga rarrashinsa yana ce masa momy she's not filling fine.
bata da lfy Kalli yana nuna masa kyawawan baby's dake kwance cikin dan madaidaicin gadon jarirai momy ta haifa maka baby masu kyau kana so ?
duk cikin harshen turanci yayi masa mgnr junior yayi shr yana kallon baby's sai dai basu dauki hankalinsa ba.
shi dai gurin uwarsa yake son zuwa .
muryar nablah asanyaye tayiwa su ummi sannu da zuwa ummi da zeenat suka amsa tana mata sannu da jiki.
zeenat MA ta bude baki da kyar tace sannu nablah ya karfin jikin?
Ta fada ahankali byn ta zauna suna fuskantar juna.
jikin nablah na Dan rawa da bakinta .
da sauki ta bata amsa still muryarta cike da rudani .
Dan wani irin matsanancin kunyarta taji tayi mugun rufeta.
to Allah ya baki lfyr jiki da lafiyar shayarwa ameen tace muryarta kasa kasa.
ummi ta janyo hannun junior ta zaunar dashi kusa da uwarsa tace makale mata ME shegen bakin nacin tsiya ai idan baganinsa yayi akan bed din kusa daita ba hankalinsa bai zai taba kwanciya ba.
ballantana ya Bari ruhinsa yassmu salama.
aiko take deeni da zeenat suka sa dariya wanda itama ummin dariya takeyi gurin fadar hk.
shi dai junior jinsa kusa da uwarsa yasoma murna yana farinciki sauran yan'uwansa suka makale su km jikin zeenat .
zeenat ta mike tsaye jikinta a matukar sanyaye ta dauko baby's ta mikawa ummi daya itama ta rike dayan tana nunawa anan da hadar yayinda kadan kadan junior ke kallonsu yana kallon uwarsa.ummi tace ki karasa shan tea Man kafin yayi sanyi
nablah ta girgiza kai na koshine ummi. Amman dai takai cup din bakinta.
ganin junior bata bin cup din hannuta da kallo yasa tace masa Zaka sha tea?
ya Dan daga mata Kanshi alamun zai sha tasoma bashi da spoon din hannuta ahankali daman ita kanta tea din ya isheta ga km tarin tsarguwa da kunyar aunty zeenat datake jin yayi mata ruf da dugu. ahankali deeni ya koma ya jingina da bangon dakin tare da ciro wayarsa yana lallasawa Amman gabadaya hankalinsa da natsuwarsa sun karkata ga zeeenat wacce take zaune jugun .
sbd idan dai idanunshi ba gizo suke Yi masa ba rama yaga tayi sosai fiyye da kwanakin baya daya ganta .
Kasa kasa yacigaba da kallon wanda hkn ya takurata sosai har yasa zuciyarta dokowa da sauri .
Kusan awa daya da zuwansu sannan sule direba ya sauke aunty Salma da nuratu sai wata kanwar mahaifiyar nablah .
suna shigowa deeni yabar dakin.
sosai aka shiga gaisawa da juna tare da yiwa juna barkar samun karuwa. wuni cur ummi sukayi a hospital din hira sosai ke gudana atsakanin ummi da deeni inda jifa jifa ummi tana saka zeenat cikin Amman ita zeenat sai tabasar dasu .
tayi murmushin yake kawai .
Dan kar nablah tagane akwai wani Abu.
Amman gabadaya ma tafi meida hankalinta akan nablah tana janta da hira.
Sai yamma list sannan suka kama hanyar gida.


ummi da zeenat zaune abayan mota da haidar da junior anan km rungume ajikin deeni agaban motor kule direban ummi na tukasu ahankali dan deeni Yabar sule a hospital domin ya maida su aunty salma gida .
ahankali deeni yasa hannusa ya tsaita kan morrow motor ta yadda zai ji dadin karewa zeenat Kallo .
Kallonta yake cike da wani irin mamakin ramarta .
jikinta ne yabata yana kallonta dan hk ta dago idanunta ahankali aiko karaf idanunwansu suka sarke cikin Juna take zuciyarta ta buga da karfin gaske .
sosai ya kura mata ido .
ta kau da kanta gefe ahankali tare da lalubar Jakarta taji wayam alamun tsamiyar birinta takare .taja tsaki mara sauti ummi tajuyo tace ke km lfy ta bata fuska ummi tsamiyar birina ce takare ummi ta tabe baki km shine yazama abun tsaki ?

deeni yaki dauke idanunshi akanta kmr minti biyar tsakanani ta km juyowa taga ko ya duke idanunshi Akanta duk da jikinta yana bata still ita din yake kallo. sake tsarkewa idanunsu sukayi cikin juna wannan Karon atake zuciyoyinsu ya buga.
wani tsaki ta sake ja Amman wannan Karon aranta tayi tana me watsa masa wata uwar harara.
wani tsadadden murmushi yasakar mata wanda tasan da wuya kaga yayi irinsa idan bata kure masa ba.
cikin kwantar da Murya sosai yace first love meke damun yarinyarki naga duk tayi wani iri ? Yakarasa fadar hk yana kokarin gyara anan ajikinsa .
ummi ta juyo ahankali ta dube zeenat tace wlh son bansani ba.
kusan ko ni wannan ramar nata yasoma damuna.
Kin km tmbyeta?
nayi tmbyr duniya nan Amman tace babu komai ba km je hospital?
ummi tace bamuje kasan zeenat da kin zuwa hospital ai.
AI kamata yayi ace kuje kuga likita domin asan abinda ke damunta. shima nayi mata mgn kwanaki har nuna mata bacin raina nayi Amman abanza ni abunda ma yafi damuna yadda bata cin abinci sai kayan tsami kullun ita Kennan shan lemun tsami.
ya sake tsareta da rikitattun idanunshi yana kallonta yana cewa ai dole kam yanzu taga likita Dan bana bukatar wanna ramar nata .
idan ma wani abun ne atareshi da wuri.
ko km ni tasanar min da damuwar nayi maganinsa.
ummi tayi murmushi kawai kana tacigaba ai zeenat din da Kasani.
ta yanzu kam gabadaya ta sauya ta canza tazama me shegen zurfin ciki tsiya komai Aka tmbyeta yanzu tace babu komai .
wlh har abun Nata yasoma data zuciyata bana jin dadin ganinta hk yanzu zeenat tafi bukatar mutuwa akan rayuwata ummi takarasa mgnr kmr zata zubda kwalla..mgnr ummi ta taba zuciyar zeenat sosai magana take son Yi Amman takasa bude bakinta sbd yawun dake cike cikinsu.
lura da hkn da deeni yayi ne ya umarci kule ya tsaya ta zubda yawun abakinta .
akan hanya tace kule ya tsaya .
Tayi warning glass din motor tare da kira me sai da kayan fruit dake zaune gefen titi .
Matashiyar mata takaraso jikin motor da sauri ta tsaya tana tmbyr abinda suke so.
abinda ya daurewa deeni kai bai wuce ganin abinda tayi point ba.
Lemun tsami da agwalima wanda bai karasa nuna ba da kyau wanda dagani yasan zaiyi mugu mugun tsami tace akawo mata matar ta hado duk abinda zeenat ta lissafa mata.
ta mika mata ta karba ta zuba ajakarta shi dai deeni sai binta yake da idanu dazata biya kudi ne ma yayi saurin zaro 5k ya mikawa matar duk da yasan kudin kayan basu kai hk ba .
yace kule yaja motar.
mashiyar matar nayi masa Bayanin ai kudin bai kai hk ba .
ya daga mata yatsunsa alamun tabarshi kawai tun cikin mota zeenat tasoma Shan agwalumarta tana lumshe ido sbd dadin dataji ya ratsata.
deeni dake kallonta ta cikin mirrorw ya sakar mata wata uwar harara akayi sa'ar itama kallonshi take.
Take ta rama tana cigaba da tsotsar kwallon agwalomarta .
Muryasa a kasalsnce yace meyye hk zaki kama shan abu batare da kin wanke ba?
Salon wata sabuwar cutar takamaki .
ke nifa ban ma yarda da shan wannan agwalo ....me take da suna da lemun tsamin ba muryarta kmr zatayi kuka tace ummi kingansa ko nifa banson takura da sa ido fa.
ki gaya masa ya fita harkata da abinda nike ya dago hannu zai buge mata baki tayi saurin gocewa kinga shi ko ummi.....
Nifa banason damuwa ni ne ma damuwa zaki gane kinkirani da damuwa wlh .
ummi tayi murmushi kawai tana girgiza Kai
har suka karaso gida zance zeenat da matsalar dake damunta suke tautaunawa da ummi ...

Tana zuwa gida wanka da sallah tasoma yi sbd lokacin sallah tayi ta dawo parlour'n kasa ta zauna .
tana nan zaune ummi ta sauko taci abinci ita da yaran ta mikasu gurin deeni.
ita km takaraso gaban zeenat ta zauna tana kallonta tare da cewa bazaki ci abinci bane?
ummi banajin cin komai yanzu wlh ni kaina ina son cin abincin Amman da zarar na zauna gabadaya sai naji ya fita akaina.
ummi ta tsura mata ido sosai tana kallonta tana nazarinta sannan daga baya ta numfasa.
ummi batasan sanda tace ko dai ciki gareki zeenat?
Zeenat tayi murmushi kai kai haba ummi wani irin ciki km .
byn every month ina yin period dina kawai dai hk nike jin kaina yanzu Amman wlh banida komai .
OK yanzu meyye amfanin zamanki zeenat agida kiyi hkr ki koma gidanki shine gatanki da rufin asirinki.
duk yan'uwanki suna zaune gidajen mazajensu lfy lau ,da dadi da babu duk da nace bazan matsamiki ba Amman wlh komawarki shine kwanciyar hankalina.
zeenat taja numfashi da kyar ta fesar Kana tace ummi kiyi hkr da abinda Zance gsky bafa zankoma gidan deeni ba adduata bai wuce ya sauwakemin .
Allah ya hada kowa da rabonsa mafi alkhari . ahankali ummi ta dinga mata fada cikin zafin rai da kunar zuciya ki zauna saunanci har wannan karamar yarinyar ta dawo ta kwance miki miji gabadaya.
,ki kara rasa gane kanshi gabadaya tun yana binki yana baki har yazo ya tattaraki ya watsar .
sosai ta dinga mata fada ta inda take shiga ba tanan take fita ba daga baya ta dawo nasiha.
ta kamo hannuta cikin nata hb mamana ki tashi tsaye ki karbi mijinki.
ni nasan kina matukar son mijinki.
zeenat ta zaro ido waje tare da cewa kai ummi wanna ai zance da Kennan.
wai ina son yaya ?
wlh kina sonshi sai dai idan kin ce min bakamar da ba na yarda.
km ko ni zanji dadin hk Dan zakewarki akanshi yasa tun farko ya dinga nuna miki ko inkula Amman abinda nake so dake yanzu ki natsu ki shiga hankalinki kiyiwa kanki fada kishiga ilimin ta natsu ki koma dakinki .
Zan yiwa hjy turai mgn tasamomin me
gyara min jikinki ciki da waje .
ta yadda kema zaki zama abar alfahari agidanki.
km akwai sakon danabada akamin daga India suma duk na gyara ne .
zeenat tayi dariya sosai wanda rabonta dayin irinta tun kafin hargitsin daya faru.
tace kai ummi ina kyawun sona?
dole ne mamana akanki babu abinda bazanyi ba matsawar zaki samu farinciki uhmmmmm ummi Kennan kina son dai nakoma gidan yaya alhalin kinsa baya sona shikenan hk zan koma gidansu yacigaba da wulakantani agaban matarsa ummi ki bar zance komawar nan tawa bashi da wani amfani wlh ...
Yana da amfani mamana kema wanann Karon dole kiyi hkr ki zage ki kwato yancinki agidanki abinda baki sani ba matar Fari da mujin fari suna da wuyar rabuwa duk runtsi km ko Sun rabu wlh kowannensu zaishiga damuwa da tashin hankali mara misaltuwa koda kuwa rabuwar tasu bata arziki bace.
aganina yakamata ace ..... Cak ta dakata da mgnrta ganin saukowa deeni ......kunnenshi makale da waya yana hira da sanyi idanunshi Yakaraso inda suke ummi tace ina yaran ?
yayi mata alamun duk sunyi bacci da hannushi. ya zauna kan kujerar da zeenat ke zaune akai har cinyoyinsu na gogar juna damm gabanta ya buga shima hkn ce tafaru dashi ta Dan saci kallonsa ta kasan ido suka hada ido ya kashe mata ido daya yana cigaba da wayarsa .
ta kawar da fuskarta gefe tana Kallon ummi .

muryasa a sayaye yace nablah bazafa ki taba ganewa ba ke yarinya ce bangaren nablah kuwa cewa tayi tayaya zangane kuwa.. Allah abban anan kayayyakin sunyi yawa ne sosai shiyasa kaji nace hk hatta aunty salma ma sai datayi mgn akai .
Ina aunty salma take?
gata OK kibata wayar kawai .
jin hk yasa zeenat tasan da nablah yake waya hkn km yasa zuciyarta tayi wani irin harbawa da sauri .
da sauri tashiga kokuwa da numfashinta dake neman daukewa.
take km tasoma karanto addua acikin ranta .
nablah ta mikawa aunty salma wayar yayi mata bayanin abinda yake so ayi .
tace ai abun ne yayi yawa wlh bai Yi ba aunty. komai nayi mata ta cancanci hk daga gareni to to shikenan angode Allah kara budi .
yace ameen sannan ta mikawa nablah wayar suka Yi sallama daita tare da cewa zai kirata zuwa anjima karta Yi bacci tajirasa yakarasa fadar hkn ba ta yadda zasu ji ba .
ummi ta mike tsaye tana cewa yakama kazo ka koma gidanka hk fa.
kar fa daginka su sani gaba da kanan zance .
bangama fita cikin wance surutan ba ka sake jawo min wani... ajiyata ce agidanki first love ki bani ita kawai nakama gabana yana gama fadar hk ya waske tmkr bashine yayi mgnr ba take ummi da zeenat suka gane abinda yake nufi..
ummi taji sanyi sosai aranta domin yanzu tana jin dadin yadda deeni yake nuna kulawarsa akan zeenat da damuwa da lamarinta.
tayi murmushi sosai tace wlh deeni ka rainani dayawa to yazanyi first love abubuwa sun min yawa most especially matsalar zeenat first love Kalli ki duba yadda zeenat ta dawo kullun sake ramewa take bata rasa ci da sha ba da komai Amman takasa damuwa aranta.
Wlh ji nike tmkr xuciyata ta buga akan hk .
ummi tace hkr zakayi komai zai Wuce Inshaallahu yazama labari .
zeenat ta furzar da iska tana sauke naunauyen ajiyar zuciya aranta km tace kaji shi.
da iyayin tsiya yana yin wani abu dan ace ya damu da lamarin mutun ...
alhalin ba hk bane ackin zuciyarsa .
nan ummi tabarsu tayi Dakinta tana adduar Allah ya daidaita lamarin komai atsakaninsu.

ahankali ya janyo system dinsa yasoma operating yana tura sakonni ayanar gitso ta mike tsam itama zata bar gurin batare daya dago kanshi ba yakira sunanta tare da cewa ta hado masa coffee juyawa tayi zuwa hanyar kitchen ta hado masa coffee.
cinki daurewar fuska takaraso ta'ajiye masa batare data kalleshi ba .
ta juya abunta aiko bazato ba tsammani taji ya fezgota zuwa fadadden kirjinsa ya rungumeta tsam ajikinsa yana sakin numfashi tare da ture system din


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login