Showing 291001 words to 294000 words out of 366611 words

Chapter 98 - AUREN SIRRI Book 2 Complete by Aisha Bagudu.txt

29 Dec 2025

8187

deeni taga Yana kokarin sanyo Kai cikin gidan. Ahankali karasa yashigowa jikinsa sanye da farar jallabiya fara kal da alamun daga masjid yake.
Take wani irin sanyin dadi ya zirayarci ilahirin jikinta da zuciyarta.ta dinga jinta wani Iri wani iri.
Amman ta kauwar da kanta da abinda take ji tacigaba da saukowa ahankali jikinta naciga da rawa wanda har yar karamar Jakarta hannuta rawa yake.
gaban deeni ya buga da matsanancin karfi ganin umminsa rike da jakar matafiya .
Wanda duk sanda kaganta da ire iren jakunkunan Kasan tafiya zatayi.
har tazo ta gifta ta kusa dashi idanunshi akanta yana kallonta da mamaki a saman fuskarsa.
ganin tana shirin bude kofar yasa da sauri ya riko jakar hannuta Jikinsa na wani irin rawa ..muryarsa cike da in... Inna... yace u'm.... ummi ina km zaki tafi hk ?
Meyasa ummi zaki mana hk ?
ummi please.......

ummi kada kiyi hk Dan girman Allah kiyi hakuri ki yafemin ya zare Jakar hannuta ya ajiye agefe daya tare da tsungunawa agabanta gwaiwa biyu biyu ya daura tafin hannusa duka bisa kafafunta please ummina kiyi min afuwa bisa ga laifin abinda na aikata miki bazan sake ba.
na tuba ummi nabi Allah da manzonsa na biki. ummi karki kujemu.idan kika gujemu rayuwarmu zata tagyara zamu shiga wani hali dagani har zeenat dinki......
ahankali ta zare kafafunta zuciyar na wani irin bugawa jikinta yayi sanyi.
Take zuciyarta tashiga shawagin barin tilon danta da diyarta zeenat .. Taku daya tayi zuwa biyu taja ta tsaya hade da juya masa baya tana jin wani irin matsanacin kunyar deeni .har zeenat ahalin yanzu kunyar hada ido
take dasu.
Batason km hada idanunta danasu.
tarasa ina MA zataje ta saka ranta taji dadi da
wa zatayi hirar ta rage zugin da zuciyar ke Yi akan abinda ya faru zeenat kadai gareta diya Mace gashi itama tagujeta ta juyawa rayuwarta baya akan abinda ya faru...
Jikinsa na rawa da rarrafe ya samu ya matso inda take.
yace kiyi hkr ummina karki tafi ki barmu bamuda kowa a nan sai ke idan kikabarmu yaya kike son rayuwarmu takasance?
Ummi taja naunauyen ajiyar zuciya da numfashi ta sauke da kyar.
Kana tayi dauriyar juyowa tana kallonsa duk da har lokacin zuciyarta cike take tab da jin kunyarsa da kunyar abinda yayi mata gaban big dady da gaban dandazon daginsa sbd common Mace.... Mace ma wace itace da kanta ta tsaya tsayin daka ta aura masa ita ,yana kukan bai sonta....
"muryarta a dake tace Ai wannaN bakomai bane idan na barka deeni.. karka manta yanzu kana da madadina wacce tafi agurinka .
har kake kokarin yimin tawaye akanta you give me double surprise deeni akan Macen da nice na tirsasaka ka aureta ba dan kana sonta ba..
ni... ni deeni ta nuna kirjinta da dan yatsanta Amman babu komai karku damu duniya ce.
sai dai kasani ayau din nan zanbar muku kasarku da danginku gabadaya na koma tawa kasar .
dama dan wa Nike zaune?
Dan kai da zeenat ne Amman ayau kun nuna min ni din bakowa bace agareku km nasan ko babu ni arayuwarku zaku cigaba da rayuwarku yadda kuke so.... Takarasa fadar hk tana kuku .
deeni ya rude ya gigice hankalinsa yayi mugu mugun tashi ya sake rungumo kafafunta please ummi karki ce hk kice komai mu kice rayuwarmu kece farincikinmu kece jigon komai agurinmu karkiyi mana hk ummi yana mgn yana kuka yana rokonta tayi hakuri tayi masa aikin gafara ko a'lamura zasu daidaita gareshi.

gabadaya jikin ummi yayi tsanyi zuciyarta tayi rauni tausanyi dan nata ya huda kirjinta.
take komai ya kwance mata ita kanta bata kaunar abinda zai nisantata dashi shi kadai gareta sai marainiyar Allah zeenat .
Tana tsananin son deeni Amman soyayyar zeenat dinta daban ce kasancewar kaunar dake tsakaninta da mahaifiyarta .
tsawon lokaci suka dauka ahaka deeni nacigaba da kuka yana bata hakuri.
da kyar yasamu ya shawo kanta hannuta na rawa ta daura bisa kanshi ta shafa sumar kanshi Kana ta zauna ya daura kanshi bisa cinyarta yana kuka yana bata hkr .
yayinda ita km ta cigaba da shafa sumar kanshi muryarta a matuKar sanyaye tace is OK son kukan ya isa hk komai ya wuce Allah yayi maka albarka Allah sanya albarka arayuwarka data iyalinka gabadaya.
bai samun damar amsa mata ba sbd kukan dayake.
shi kanshi yayi muguwar nadamar abinda yayiwa mahaifiyarsa mafi soyuwa azuciyarsa... Ka tashi ka zauna akan kujera deeni ya tsinci muryar mahaifiyarsa..
ya dago kanshi yana dubanta yana girgiza mata Kai first love barni anan .
ya sake gyara zamansa agabanta suna fuskanta juna.
ummi ta numfasa tana dubansa gabadaya duk ya rame yayi dogon wuya data tuno dalilin abinda yasakashi dawowa hk tayi saurin runtse idanunta gam tana kukan zuci da blaming din Kanta.
itace silar fadawarsa cikin Matsala yana zaman zamansa da matarsa.. Da kyar ta bude idanunta tace ina zeenat dina take yanzu tana gidanka ne?


Ya girgiza mata kanshi sannan yace dukansu basa gidana.
Gabanta ya buga yashiga dukan uku uku bakinta na rawa tace ina zeenat Dina take ?
Tana gidan babanta....... ummi tayi dif kirjinta na wani irin lugude wasu sabbin hawaye suka zubo mata tasoma magana cikin harshen indiyanci , akan zeenat ta gujeta ta daina sonta sbd kuskurenta nason ganin rayuwarta ta inganta agidan danta. kuka take sosai tana daura laifin komai akanta.
deeni na rarrashinta da goge mata hawayen idanunta first love ki daina kuka yanzu zanje na dauko miki zeenat dinki bake kadai kika tsinci kanki cikin damuwar da tashin hankalin rashinta ba.
ni kaina nayi nadamar ramuwar gyayar da nayi niyyar mata yacigaba da gogewa ummi hawayenta .
ita km sai girgiza masa Kai take muryata na rawa tace kaje deeni ka... Kawo min zeenat a duk inda take ko zuciyata da ruhina za samu salama. sai da ya sake goge mata hawayen idanunta sannan ya Mike jikinsa a sanyaye ya juya yasoma tafiya hard ya kawo bakin kofa yana daura hannushi kan handle yaji an murda kofar.
ya dan dakata .. ahankali aka bude kofar.... Zeenat yagani tsaye sanye da doguwar riga da hijab lulube har kasa .
ido cikin ido suke kallon junansu kowace da abinda zuciyasa ke sakawa akan dan uwansa.
ahankali ta raba ta gefenshi ta wuce shi batare da tace masa uffan ba .
ya meida kofar ya Rufe ya biyo bayanta ummi na arba da zeenat ta Mike zumbur jikinta na rawa bakinta na rawa gurin fadar ma..ma... na tana me ware mata hannunta duka alamun tazo gareta zeenat ta fashe da kuka takasara tare da shigewa jikin ummi.. Ummi ta rungumeta ajikinta tana kuka.
a she tunani bai zama gaskiya a she zaki kawo kanki gareni byn duk abinda na miki? Gabadaya na ji kunyarki zeenat .
naji kunya akan yadda fasaha ta dauke min na kulla miki gadar zare da hannuna akamiki kishiya batare da saninki ba. ...
ummi ki daina kuka bazan iya barinki ba ummi dake kadai nasaba arayuwa bansan dadi uwa ba sai ke ummi.
ban rayu da mahaifiya ba sake ummina Kin nuna min gata fiyye "dan" cikinki ummi duk inda zanje nayi rayuwa aikin banza ne idan bana tare da ke.. dan bazan iya jurar rashinki ba ummi. ina sonki duk duniya nan banida kmr ki hakika kin raya zumuncin dake tsakaninki da mahaifiyata.
kin duba byn mahaifiyata domin nasan ko tana Raye da wuya tamin abinda kika min kin nuna min gata kinsa ban Yi kukan maraici ba.. takarasa mgnr tana kuka ummi ta yafito deeni da hannuta yakaraso ya zauna kusa daita tayi saurin goge hawayenta kana ta kamo Tafin hannushi ka bata hkr deeni....Ka Tausayawa rayuwarta har yanzu ina jin xeenat araina tmkr fareeda.. Ita kadai ke mayemin kurbin fareeda arayuwa.
ita kadai ke dabemin kewar fareeda a duk sanda hkn yataso min .....takarasa mgnr idanunta na fidda wasu ruwan hawaye.. jikin deeni a sanyaye yace first love tun jiya nake bata hakuri kwana nayi ina kiran wayarki danata Amman akashe .fisrt love nima abin atausayamin ne .ina bukatar tausayawarku ke da zeenat....
Nasani... Nasani deeni Amman Kasan mace tafi bukatar tausayawa akan namiji.
ummi ta hade hannusu gurin daya ta damke cikin Nata sosai .
atake zuciyoyinsu ya buga sbd tuno da rana da suka mallaki junansu amatsayin ma'aurata ranar da ummi tabasu amanar junansu tare da tabbatar musu da su din yan'uwan juna ne mafi kusanci da juna .
atare suka dago suna kallon juna kowanensu zuciyarsa cike da tausayawa...
muryarsa a raunane yace am very sorry zeenat.. I Din mean to hot you .
ummi ta saka baki kiyi hkr diyata... Duk nice silar cutuwarki denni bashida laifi komai. Ki daura laifi gareni zeenst nice na miki laifi bashi ba.
zeenat tashiga girgiza kanta tasa hannuta daya tana gogewa ummi hawaye muryarta raunane tace ummina na yafe miki ...nasan duk abinda kikayi kiyi ne sbd ni... Nasan ko diyar da kika haifa acikin ki irin kulawar dazaki bata Kennan .
ummi ki manta da wani abu makamancin wannan ya taba faruwa arayuwarmu wallahi wallahi ummi na yafe komai .
shima yaya na yafe mishi duniya da lahira Amman ummi akwai wani hanzari ba gudu ba.
Dan Allah kicewa yaya ya sawake min aurensa dake kaina tunda ni baya sona baya son farincikina.
bansan wani irin kiyayya yaya yake min ba wanda ya manta kowa da komai ya manta da irin rayuwar da muka gudanar a farkon aurenmu ya tsugunawa wata Mace agabana yana rokon taso shi ummi....
Idan har nacigaba da rayuwa aure dashi wlh ban kyautawa kaina ba ...
amman dan hakuri na Hakura da komai na dauki kaddarata nima zanje gaba nacigaba da rayuwata.....
Deeni yayi sororo tare da tsura mata rikitattun idanunshi yana kallonta cike da mamaki abinda tace.
ummi tayi gyaran murya tace mamana bazan takuraki ba sbd tun farko aurnku ma ban takuraki ba ballananta yanzu Amman da zakiyi hkr ki rungumi kaddararki dana nafi kowa dake cikin duniyar jin dadi.
burina ba wuce naganku kuna rayuwa tare ba . abinda bakusani ba batun yanzu nake son ganinku cikin inuwa daya ba.
Amman sbd sanin halin deeni danayi yasa naki hadaku tun farko ko lokacin dayazo min da zance aurenki naji matukar dadi Amman ganin ba sonki yake ba alokacin kawai yana son yin auren ne dan na matsa masa yasa naki amincewa .
Amman kikace kinji kin gani zaki iya...

Ahankali ummi ta meda idanunta kan deeni bazan takurata mata ba idan kaji kana bukatar matarka Kanason cigaba da zama daita.
kasan yadda zaka Shawo kanta idan km kasan bakada bukatarta arayuwarka sakar min abata.
domin abinda wani yagaji dashi yaga yayi masa tsufa shi wani yake so da dauki ganin ya mallaka.
deeni ya runtse idanunshi da sauri sbd jin haushi da takaicin zance ummi.
Ummi na mgn fadar hk ta Mike tsaye tabar gurin ta nufi dakinta tana goge hawaye .
bathroom tashiga ta zauna kawai tarasa abinda ke mata dadi.

zeenat ma zame hannuta tayi cikin nashi yana kallonta Tabi byn ummi.
a sikwane Yabi bayanta da wani irin kallo .

tana shiga dakin ummi ta fashe da wani sabon kukan sbd har lokacin tana jin mugun kaunar mijinta.
sonshi acikin jinin jikinta yake .rabuwa dashi babban tashin hankali ne gareta Amman zata dakewa zuciyarta ko zata samawar ruhinta salama sosai take kuka tana tuna rayuwarta acikin dakin datake yanzu.
da yadda abubuwa suka dinga gudana daya byn daya suna wucewa da yadda ta rayu da matsanancin kaunarsa batare daya Sani ba.
da yadda ya dinga jiyar daita dadin aure ta dinga jin dama lokacin zai dawo mata da ta sake sabuwar rayuwar me inganci.
ashe daman zai kara aure arayuwarsa shi yasa lokacin datace yayi mata alkwarin bazai mata kishiya ba yace a'a zeenat bani ne da rayuwata ba.
ban isa Na tsarawa kaina rayuwa ba.
Aure nufi ne na Allah idan Allah ya kaddaromin sai nayi.
kedai ki tabbatar da kin tsare min hakina .
babu mamaki idan kika tsaremin hakkina dake kanki ta yuwu gaba naki kara aure .
duk da babu yadda Allah baya juya lamarinsa.
tuno wannan zance nasa ya sake haukatata ta dinga kuka tana datasani arayuwarta.......
ahankali ta mike tsaye tana safa da marwa ...motsin turo kofar dakin taji anyi tayi saurin goge hawayen dake tsiyayowa daga idanunta batare data juyo ba.
ahankali taji an meda kofar an rufe alamun an shigo dakin.
jingina bayansa yayi da jikin kofor tare da rungume dukka hannuwasa akirjinsa.
ya tsurawa bayanta idanu kawai yana kallonta yayinda ahankali ya dinga jin wani irin tausayinta yana ratsa kowani shashi na gangar jikinsa hakika bata cancanci wulakaci ko sabanin hk daga gareshi ba a kullun yana yabawa da tarin kaunarsa gareshi.
cikin wani irin sayin Jiki yakaraso gareta ya rungumeta ajikinsa ta baya yana me juyo daita suna fuskatar junansu.
atare suka sauke ajiyar zuciya .
ya tallabo fuskarta da hannuwashi yana Kare mata kallo ya bakinsa ya tsotse bakinta muryarsa a matukar raunane yace ki bini mu koma gida zeenat mukarashe rayuwar aurenmu tare.

nifa bazan koma ba domin bazan iya cigaba da rayuwa dakai ba...... Daga yanzu kasawa ranka mata daya kacal gareka..no... no.. don't do this to me zeenat . kiyi hakuri please kishirya yanzu mu wuce tare.
ta girgiza masa Kai alamun bata komawa gidansa yin duniya yayi daita Amman taki amincewa ta bisa..

hk yagaji ya Hakura yabar gadan. Kai tsaye gidan big dady ya nufa ya duba yaransa ita kam nablah bai samu damar ganinta ba sbd taki yarda sukaga juna.


Hk ya koma gida ya shirya zuwa office.
koda ya dawo daga office gidan ummi ya nufa rarrashin duniya yayiwa zeenat amman tace Sam ya barta lokacin data aureshi bai matsawa rayuwarta ta aureshi ba Dan hk yanzu bata Yin auren ya sallameta kawai ta aure wani .
kmr ya mutu hk ya dinga ji alokacin datake fada masa hk..
a matukar fasace ya fito tmkr zai tashi sama .
ko gidan Big dady bai je dubo nablah ba. Ya wuce gidansa
dan yasan haukanta ya zarta na zeenat.
sai dai gabadaya bai da salamar zuciya .
Daren ranar da kyar yasamu bacci barawo ya samu nasarar daukarsa cike da matsanancin damuwa.


washegari zeenat gabadaya akwance take ta zube tayi wata muguwar Rama sallah kadai ke tadata koda ko abinci ta manta rabon data sakawa cikinta ummi tayi ta matsa akan ta saki ranta taci abinci Amman furrrrrrr taki.






Gabadaya komai ya cukudewa deeni guri daya takowani bangare babu sauki da sausauci gida da office baida natsuwa tafiya kawai yake Amman zuciyarsa tap take da damuwa da tsantsar tashin hankali da tunani mara misaltuwa.
daga office kai tsaye gidan ummi ya nufa yashigo gidan bakinsa dauke da sallama ummi kadai ya tarar tana zaune ta amsa masa tana kallonsa.
dan ramar tasa ta yau tafi ta kullun nunawa ahankali ya zauna tare da ajiye jakar system dinshi yace first love mun yini lfy.
lfy lau son ya aiki .
yayi dan jim sannan yace alhamdullahi kusan minti goma yayi zaune baiji motsin zeenat ba wanda abinda yasani ne matsawar ummi na guri dole ka isketa kusa daita.
jikinsa a sanyaye ya fito da system dinsa cikin wata karamar bakar jaka yasoma dudubawa yana son karasa tura sakwanni .muryarsa akasalance yace first love ina zeenat?
Ya fadi hk batare da dago ba.
Ta mike tsaye tare da bashi amsa tana sama yanzu ta tashi .
OK turo min ita first love .

koda ummi tasanar mata da sakonshi bata mutsa ba taxo a parlour ta sameshi zaune kan daya daga cikin kayatattun kujerun parlour'n ummi na alfarma system dinsa akan center tablet agabanshi yana latse latse jikinsa sanye cikin wani farin yadin volya fari kal me shegen kyau hasken yadin da kyawunsa, su suka tona asirin tsadarta kashim turaren nan nasa na yau da kullun yana nan. yacika gurin batare daya dago ya dubeta ba ya nuna mata kujerar zama da hannusa cikin harshen turanci yace have a sit.
ba mutsu jikinta a matukar sanyaye ta zauna kusan minti goma bai ce daita komai ba yanata danne dannesa ta dago idanunta tana duban agogon dake manne a parlour muryarta a sarke cike da matsanacin tsoro tace nifa gsky ina son komawa daki dan ina da abin Yi.
ya dago rikitattun idanunshi ya dubeta..ya lashin lips dinsa na kasa kana yace Kibani minti biyar local in kammala muhinman aikina.
Taja numfashi hade da kawar da kanta gefe .

ahankali ta sake kallon agogon minti biyar din tacika tana shirin sake yin mgn taga ya ture system din dake gabansa ya mike ahankali ya zagayo gefen datake zaune kafafunsa babu takalmi ya janyo wata yar karamar akujerar stood dake daf daita ya zauna ya rusuno sosai kusa daita har suna jiyo numfashin junansu.
Muzeenat........ ya Kira sunanta cikin laulausar muryarsa .
ta tsuke fuskasta sosai batare data amsa masa ba .
bai wani damu da yanayin yadda tayi ba yacigaba da mgnrsa.
muzeenat meyasa kika Xabi rabuwa Dani ki auri wani?


alhali nasan kina mugu mugun sona?


da sauri ta dago idanunta ta sauke cikin nasa gabanta ya buga da karfi take ta kawar da idanunta tace daba lokacin ban san ciwon kaina ba Amman yanzu gsky bana wani sonka.
Uhmmmmm ya sauke numfashi tare da yin murmushin yake.
nasan kin fada ne kawai sbd girman laifi da kike tunanin miki Amman in da gaske kin daina sona ki dubi kwayar idanuna ki tabbatar min da ba kya Sona ......
cike da rashin tsoro wanda duk daurace kawai ta aro tasanyawa jikinta ta Kalli cikin idanunshi tace yaya deeni na daina sonka.
bana kau... Yayi saurin katseta ta hanyar daga mata hannu tare da runtse idanunshi gam zuciyarsa na wani irin harbawa da suya muryasa a raunane tamkar zaiyi kuka yace naji na yarda kin daina sona Amman ki duba wasu abubuwa kafin kiyi tunanin barina na farko Ki duba rayuwar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login