Showing 135001 words to 138000 words out of 366611 words

Chapter 46 - AUREN SIRRI Book 2 Complete by Aisha Bagudu.txt

29 Dec 2025

8178

,to meyasa kike so ki tursasani yin AUREN SIRRI da kaskantacciya macce?

tsawon lokaci ya dauka yana kwance idanunshi na kallon celing dakin gabadaya tunaninsa a halin yanzu ya ta,allaka ne akan abinda ummi take son ya aikata .
,yana son umminsa bayason abinda zai disashe farincikinta ballanantana har yakai shi Ga bijirewa
umarnita.bacin ran umminsa ,babban tashin hankalisa ne,a gareshi bancin haka da Babu abinda zai kaishi auran wannan yarinyar may idanuwa tamkar Na mage .
" mtssss yaja tsaki a ranshi Dan duk wannan zance dayake yi yana yinsa ne a zuci .

ahankali ya runtse rikitattun idanunshi banda yana jin bacci Sai Dan yana bukatar maido da natsuwatsa dake kokarin barin gangar jikinsa .



Bangaren nablah kuwa gabadaya duk wata surar dake jikinta ta sauya , ta murje ta sake yin kyau daita Sai dai walwalarta da kuzarinta sunka ragu.
sakamakon matsi da takurar da Zeenat din ke yawan yi mata, Wanda ita kanta tarasa dalilin hakan .
km kwata kwata bata dauki takurar da Zeenat din kemata amatsayin wani aibu ba .

Baya ga tunaninta Haka wasu daga 'cikin masu arziki da manyan masu hannu da shuni sukeyiwa marasa shi km marasa galihu irinta .

Duk da yawan takurar da Zeenat din ke mata hakan bai hanata samun farinciki da walwala daga gurinsu laraba da safeena ba . Dan haka ta tattara Zeenat takurarta ta watsar a gefe tacigaba da abinda yakawota iyakarta daita aiki Wanda tasan dolenta ne Tayi shi Dan abinda tazo yi kennan .


Ranar Saturday ' nablah na zaune ita da safeena a main parlour din gidan sanye take 'cikin doguwar rigar material may ratsin pink and popul yayinda jikinta ke rufe da dan karamin hijab kmr koda yaushe.

babu kwaliyar komai a fuskarta kasancewarta ba ma,aboyaciyar son kwalliya bace da kalekalen zamani, sai Dan Whit lip's din data shafawa lebenta.

,rashin kwalliyarta bai hana ainihin sihirtaccen kyawunta fitowa ba.haka ma kayataccen fatar jikinta choculate colour ta kwance luf. luf..koda take sanye 'cikin ' hijab kyawunta bai boyuwa ba..
Sai dai fuskarta Tayi fayau ..wanda ya nuna alamun rama atattare daita km hakan ya sake fidda asalin siffar halittata kyawun jikinta .

Yayinda kallo daya zakayi mata kaji farar daya tashiga ranka Wanda dama tun asali Haka yanayinta yake 'tana da saurin shiga rai duk Wanda ya daura idanushi kanta , da wuya kangata kaji bata tashiga ranka ba .

bbu kowa a gidan daga ita Sai safeena shiyasa ma ta samu dama ta dan sake ta zauna a parlour Dan bata manta gargadin da matar gidan Tayi mata ba .


Ahankali suke hirarsu 'cikin harshen turanci ita da safeena 'gefe daya km hankalinsu nakan TV .


Salamarsa ce da wani wanda batasan ko waye ba ,ta doki dodon kunneta Wanda hakan yayi daidai da faduwar da gaban yayi , Wanda km tarasa dalili .
dan Kusan duk sanda zata gansa ko jiyo sautin muryarsa Sai ,gabanta yayi mummunar faduwa.

Ahankali Ya karasa shigowa parlour gabadaya fk Na biye dashi a baya .
har zata dago idanunta da niyar kallon inda suke tafasa.
ta maida Hankalinta sosai kan TV dake aiki a parlour tare da amsa sallama aciki batare da ta dubeshi ba Shima Dan sanin mahimmancin sallamar datayi ne Yasa ta amsawa.
" Dan Tasha alwashin bazata km gaida shi ba tunda baya amsa gaisuwa.

Fk yakarasa shigowa parlour Sosai,ahankali idanunsa suka , sauka akan nablah dake zaune Kusan minti biyu ya dauka tsaye yana kallon bakuwar fuskar daya gani agidan ,yaso kwarai ya dauke kansa daga dubanta Amman ya kasa yin hakan.
,a zuciyarsa yake tasbihi Ga ubangijin halitai Dan rabon shi daganin kamilalliyar macce mai tarin kyau da kwarjini irinta ya Dade ,kai shi bai ma taba ganin ba .

Gabanta ya tsananta bugawa da sauri yayinda a 'cikin jikinta ta dinga jin ana kallonta km still har lokacin taki ta yarda ta juyo bayanta Dan tasan deeni ne tsaye .
Sai dake dubanta Wanda bata sanshi ba km tayin hakan ne sbd gujewa kanta wulakanci daga gareshi .

haka kawai taji ta takura a gurin takasa sakewa shanyayun idanunta dake kan TV ta lumshe gabadaya hankalinta baya gangar jikinta ta matsu su bar gurin ko tasamu natsuwar zuciyarta.
, Amman hakan ya gagara samuwa Sai gani tayi ma sun samu gurin sun zauna kujerar dake facing dinta suna cigaba da hirarsu.

safeena ta gaishesu suka amsa a tare amman ita nablah takasa bude bakinta ta gaidasu Sai ma mikewa datayi tsaye 'tana gyara hijab din jikinta Tayi hanyar step .

fk yabi bayanta da wani irin kallo .yana tunanin ko wacece ita a kasan ranshi.shima oga deeni tun shigowarsa zuciyarsa ke kanta Amman ganin yadda Tayi musu banza tamkar bata gansu ba.
, yasa zuciyarsa ta sosu kwarai ranshi ya dinga baci , ballanantana da yaga fk din yayi mata kuriiiii da idanu yana kare mata kallon, hakan ya sake hassala zuciyarsa ,haushinta tare da takaicinta suka taru suka mamaye ruhinsa.


'Tana shiga dakinta ta kwanta ruf da ciki 'akan gado tana sauke ajiyar zuciya wayyo.. wayyo.. Allahna wannan wacce irin maseefa ce take shirin ruguzamin rayuwa ?
meke shirin faruwa dani?

hakika wani mummunar abu Na kusanto rayuwata da Al,amurana gabadaya.
,domin yawan faduwar gabar da nakeyi ta yiwa a tun sanda nazo gidan nan wanda narasa dalilin jin hakan .
Ahankali ta dinga maganar zuci da kanta batare tasani ba .

Ahankali taji an bude kofar dakin safeena ce tashigo ahankali 'tana kiran sunanta .


Ya km Muna zaune Muna hirarmu zaki gudo daki ,kibarnk Ni kardai ?

kefa Naga alamun zaman kadaici baya damunki fa Sai ma Naga kmr baki jin dadi ..

nablah Tayi murmushi yaqe may tattare da takaici kana tace wlh bbu komai safeena km bbu abinda ke damuna , kawai dai Ina son Na dan kwanta na huta ne sbd Ina dan jin bacci ,kafin Aunty Zeenat ta dawo .

Ke dai ki fadi gsky ba wannan ne dalilin dayasa kika dawo daki ba . safeena ta fadi hakan 'tana kokarin zama gefen nablah , nifa Sai Naga kmr shigowar bros ne Yasa duk kika rikece kika kasa zama .

Nablah dake kwance taji gabanta ya sake faduwa jin abinda safeena tace dan Haka a sukwane ta Mike zaune 'tana bin safeena da wani kallon mamaki .
Muryarta a sanyaye tace ko daya ba abinda kike tunani bane ,kawai day Ina bukatar natsuwa ne.

to Dan me ma zan rikece nakasa zama Dan Naga yashigorsa .
Ni karfin shigowata daki yana da nasaba ne da banason Aunty Zeenat ta iske ne a parlour,n sbd gargadinta gareni if not me zaisa Na taso sbd wani alhalin ba zamansa nake yi a gidan ba .


Me zai sa nataso sbd wani alhalin ba zamansa nakeyi a gidan ba ...safeena ta sake maimaita mgnr nablah a ranta ,har ta bude baki da zumar zatayi magana Sai km Tayi shr sbd wayarta data dauki tsiwa, ta duba screen din wayar tana picking din call din 'tare mikewa tsaye dan barin dakin .
'Byn fitar safeena nablah tacigaba da zaman shr tare da tunani iri iri Wanda Kusan yawancin tunanin Na ahlin gidan su ne .


Bangaren faruk kuwa nablah Na karasa bacewa idanunshi ya maido da hankalinsa Ga deeni tare da tmbyrsa wacce wannan yarinyar may zafi Haka ?

Wani kallon wulakancin may tattare da haushi deeni yajuyo yana watsawa fk tare da jin takaicin tmbyr da fk din yayi masa.
, kallon gefe ido Shima fk yayi masa kana yacigaba ,dan Allah a Ina ummi tasamota ko tare da safeena suka zo ?

Deeni yayi masa banza tamkar bashi da yake ba ,kai dan banzan yaro ne wlh wani lokacin kana jin mutune kake nakkasasu. Zuciyar deeni gabadaya tagama cakudewa ta cure kanta guri daya 'ta daina kai kawo a gangar jikinsa.
tarasa sukunin kanta kai kawo tsabar takaicin fk .

Sai da fk yayi ta maimaita tmbyrsa sannan deeni ya furzar da iska may zafi ta bakinsa tare da harde hannuwansa guri daya a fadadden kirjinsa ya fara mgn 'cike da dakewa da yatsina fuska yace housemaid din ce ....

fk ya ware iduna yana kallonsa da gaske kai amman gsky yarinyar batayi kama da housemaid ba wlh. wannan Ai kamata yayi ace 'tana aji 'tana daukar darasi domin karatu ne yafi dacewa daita .
,deeni ya gyara zamansa yakoma rigingine akan kujera dayake yana sakin ajiyar zuciya tare da yin shr ....tsawon lokaci fk Na zaune har ya fidda ran deeni zai sake yin magana Sai km yaji sautin muryarsa a sanyaye ,sanadin karantu ne yakawota aiki .
Fk ya saki murmushi sannan yace ayya ..itama tasan abinda yafi dacewa daita kennan.
to me zai hana ka taimaka mata kamay daita Ga iyayenta sannan ka dauki nauyin karatun nata kmr yadda kasaba taimakawa mutane marasa galihu irinta .

Tsab deeni dake zaune yana sauraron bayanin fk yayi masa kallon baka da hankali 'cikin sarkamewar zuciya da rashin tsoro tare da jin zafi furuncinsa deeni yace baza,a takaimaka mata ba.
Yacigaba , wannan bazanr yarinyar da bata da tarbiyya zan dauki nauyin karatunta" yarinyar da kwata kwata batasan me ake Kira da respect ba kana kallon yadda ko kallon mutunci bamu isheta ba ,Ni wlh haushi ma kabani da naga yadda ka tsaya kana kallonta tare da zuzuta wani wai kyau gareta ko me mtssss yaja tsaki .

fk ya kwashe da wata uwar dariya matsalata da kai kennan idan baka son mutun ,wlh har naji yarinyar tabani tausayi .
Mtssss deeni ya sake jan tsaki .

Tabaka tausayi ko to ka dauki nauyin karatunta man ,Ai kaima Naga kana da karfin dazaka iya yin Hakan.
Fk numfasa tare cewa waneni wannan Sai Ku manya ..nan dai suka bar zance nabla suka shiga abinda yakawo fk.



Wasa wasa rayuwar deeni gabadaya tasoma canzawa 'acikin yan watanni nan.
rabonshi daya samu natsuwa da farinciki har ya manta tun kafin zuwan nablah gidan.
Dan duk sanda zai hadu da yarinyar Sai yanayinsa ya sauya hakan ma ko 'cikin baccinsa ita yake ganin zaune a gefen tare da wasu kyawawan yara tana Miko masa" masu tsantsar kyawu sosai har kagara yake gari ya waye ya daura idanunshi akanta .yanzu kam yasoma gasgata tunaninsa na mayya ce yarinyar idan kuwa ba Haka bane to 'tana da alaka da mutane boye.😍😍



Sannu ahankali sule direbansa ke jansa har xuwa , unguwar gatan kowa dake iyanu - paja .



Nisa kadan da gidan da oga deeni yabashi address sule yayi parking ahankali tare da juyowa baya yace may gida mun iso Ga gidan can ya karasa fadar Haka yana nunawa deeni gidan da yatsansa .


Deeni dake hakemce a bayan mota ya sake gyara zamansa yana karewa gidan da sule direbansa ya Nuna masa .
,tsawon lokaci deeni ya dauka yana kallon gaban gidan tare da Allah wadai da wannan aure da zaiyi.

yanzu irin gidan da zai nemi aure kennan gabadaya kofar gidan a rushe yake bbu wata ishashiyar katanga Sai dan kwanun da,aka zagaye shi dashi tsabar babu . Gabadaya unguwar a hargitse take bbu kyan Gani .

Ahankali kalaman umminsa ke dawo dashi 'cikin duniyar tunaninsa yayinda natsuwarsa ke kokarin shirin barin jikinsa domin gabadaya tunaninsa ya ta'alaka ne da yadda zai nemi auren yarinyar a gurin iyayenta. Yanzu shi wani irin aure zaiyi ?Anya kuwa zai iya auren .

Tunda sule direba yayi mgnrsa ta karshe Bai sake yunkurin cewa uffan ba Dan gudun maseefar ogan nasa ,a sukwane sule yaji sautin muryarsa 'cikin kunnenshi fita kayo min sallama da may gidan iya abinda deeni ya fada kennan yaja bakinsa yayi dif...


Sule ya kashe motar Tare da barin AC motar a kunne ,ya fito yana aikin raba Idanu ta inda zaiga yaron aike .

unguwar shr... sakamakon ruwan saman da,a kwana ana sulawa ,jifa jifa mutane ke wucewa Sai da sule Bai yi dacen samu Wanda zai aika 'cikin gidan ba .
dan Haka ya koma ya jingine jikinsa ajikin mota yana addu'ar kar Allah Yasa oga ya fusata har zuwa sanda zai samu dan aike .


Fitowar wani kyakyawan dattijo ne daga gidan yasa sule jin farinciki a ransa yayinda hankalinsa ya kwanta 💯.

Dattijon dake kokarin gefta shi yana faman xuba fada ,sule ya karaso da sauri Tare yi masa sallama yana kokarin tsugunawa dattijon yayi saurin Miko masa hannu suyi musabaha.

suka gaisa sule Na tmbyrsa ,dan Allah baba may gidan daka fito daga 'cikin sa nake nema , dattijon ya saki murmushi Tare cewa Ai nine may gidan .

Sule yayi murmushi yace yauwa daman may gidana ne yake son ganinka yana 'cikin wacce motar dattijon yabi hannun sule da kallo galleleyar motar dake parke nisa kadan dashi yabi da kallo.
Yace to to yaro bbu komai kana iya sanar may gidan naka Gani .


Sule ya juya 'cike da natsuwa ya sanar da deeni ,dake hakemce abayan mota ya ware kafafunsa yana jiran tsammani .
Ce masa yakaraso nan .

Sule sake koma yasanar da dattijon.
, dattijon Bai wani damuba yakarasa kai tsaye har inda motar take sule bude masa sashen da deeni yake ahankali idanun deeni suka sauka akan mutumin dayake kallo yanzu a gabansa tamkar an tsaga kara da yarinyar dake zaune a gidansa .


Dattijon ya Mikowa deeni hannun domin su gaisa deeni ba Dan son ranshi ba ya bashi hannun Sai dai fuskasa a dan sake ba yabo ba fallasa .

Yace idan bazaka damu ba kana iya shigowa daga ciki magana ce may mahimmanci takawo gareka .

Dattijon yace bbu wata damuwa yashigo mator batare da an rufe ba Sai da deeni ya numfasa zai mgn sai km yayi shr 'yana may toshe hancinsa da hanky sakamakon wani wari kwata daya bugu yayi nasarar shiga hancinsa .ganin Haka Yasa dattijon janyo kofar motar ya kulle .sannan DEENI yasa samu damar soma mgn.

abinda yakawo gareka Naga wata yarinyarka ne Ina son ka aura min ita bisa sharadin deeni yasa hannunshi yajanwo wata yar karamar jaka may shake da kudi , ya bude zan mallaka maka fiyye da wannan kudin ..

dattijon daya Ga jiya km yaga yau ya kalli kudi masu tarin yawa sannan ya dago ya kalli deeni yana murmushi .
Kwata kwata kasa dauke idanunshi tsohon yayi daga kallon DEENI Sai ma nazarinsa da yake .


Kusan minti goma yana nazarinsa har DEENI ya tsargu kansa sannan dattijon yace yaro kennan wacce daga 'cikin yaran nawa kake so da aure kafin aje ga mgnr kudi.
bbu wata shakka ko tsoro deeni yace nablah....

dattijon yace garama datazama nablah ce Yar albarka duk da inajin haushinta a raina amman hakan ba zai sa nakasa ji dadi aurar maka daita ba .

Deeni ya sauke naunauyen ajiyar zuciya jin abinda tsohon yace hakan ya tabbatar wa kansa samunta bbu wani shamaki sai dai yayi mamakin yadda dattijon yace yana Jin haushin diyarsa ta 'cikin .

Dattijon yacigaba Sai dai ita wannan yarinyar da kake magana akanta bata nan , asalima ban san inda take ba ahalin yanzu ,deeni numfasa sannan yace wannan ba zai zama da wata damuwa ba muddin ka amince zaka bani aurenta.
,nima tafiyace a gabana zuwa wata kasa ,dan Haka auren kawai nake da bukata a daura inyaso idan Na dawo daga tafiyar sai ayi bikin kaga itama nasan zuwa lokacin ta dawo .

Dattijon yaji dadi mgnr Sosai daman yana 'ciki da abinda Salmah Tayi masa Na daukar masa yarinya, takai gidan aikatau 'byn yace Bai amince akai masa ita aiki ko Ina ba.
,yanzu hakan ma daya fito daga gidan yana fada.
" shi da Salmah ne yake ce mata ta dawo masa da diyarsa muddin batason bacin ranta , dan shi baya wani bukatar Taje neman kudin karatu yafi son ta zauna agabansa har zuwa sanda zai aurar da abarsa .

Ahankali dattijon ya dawo daga duniyar tunani daya lula yace yaro zuwa yaushe kennan kake son auren nata .

Deeni yace idan zai yiwu ayanzu Ma zan fi so Haka dattijon yace may zai hana yiwar hakan wannan Ai abune may sauki tunda Sai ka dawo daga wata uwa duniya za'a yi bikin .

Deeni yayi shr kawai yana kallon dattijon dake zaune Kusa dashi yana kokarin amince masa batare da yasan ko shi waye ba .


'Cikin mintina da basu fi talatin ba mlm salisu ya nemo aminnansa guda hudu na nan kusa da cikon shi biyar .

Sai deeni da sule aka daura auren nabeela salisu gulunbe da nasuruldeeni aliyu khaliyal bisa Ga sadaki naira duba dari cassssssssssss. Wanda sule yakasance wakilin deeni yayinda wani aminin mlm


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login