Showing 258001 words to 261000 words out of 366611 words
Chapter 87 - AUREN SIRRI Book 2 Complete by Aisha Bagudu.txt
masa da wani irin matsanancin kuka me cin rai da Daga hankalin .
Jikinta Na matsanancin rawa ta kwantar da yaran daya byn daya akan gadon.
da kyar ta sauko Daga kan gadon datake ta zube masa a gabansa ta dinga kuka Dan Allah deeni karku rabani da ya'yana Ina son su ko zan rasa raina bazan iya rayuwa bbu su ba.
Wallahi bazan iya rabuwa da yarana ba aduk yanayin da suke Wallahi azim bazan iya rayuwa bbu su ba ni Ina son su a Haka .
kuka take sosai tana rokonsa akan kada surabata da yayanta .
Gabadaya jikin deeni yayi Wani irin mugun tsayi km ilahirin jikinshi suka mace murus yarasa abinda ke masa dadi a zuciyarsa .
Ga koshi Ga kwana yunwa.
hankalinsa ya Kai kololuwar gurin tashi gabadaya yarasa abinda yakamata Yayi ahalin dayake ciki .
kukan farinciki zai yi ko haushinta zai ji Na sabon salon iskanci data tsiro ... sai kallon bbys din yake yana kallonta tsugunne agabansa tana risgar kuka tana rokonsa .
shima ajiye bby' girl din dake hannunshi yayi .
ya tsura mata rikitattun idanunshi da kyau yana cigaba da kallonta hade da nazarinta wato dai da gaske mutuwar son yaran take kmr yadda shima yake matsanancin son su .
duk Shi a tunaninsa yafita son su da bukartasu arayuwarsa ..
a zuciyarsa yaji wani irin matsanancin sanyi ya ratsashi tundaga tafin kafafunshi zuwa kwanyarsa , kennan idan yace zai isar da sakon zuciyarsa gareta bazai Sha wata wahalar shawo kanta ba adalilin wayan nan yaran ..
take km burin mahaifiyarsa ya fado masa .
yaya zaiyi da ummi wace oready tagama gaya duniya da shelar cewa zeenat ta haihu ?
..yaya zata ji idan tasamu wannan mummunar labarin ?
Kuka take Sosai ta rike kafafunshi gam deeni kayi hakuri nasan ban kyauta ba akan abinda nayi Amman Ina son ya'yana duk da kasancewarsu shegu wlh ba zan iya kyauta dasu ba kmr yadda nayi maka.. shiiiiii Karki kara kiran ya'ya Na da she.. shegu ni..Ni..ne ...sai km yayi shr ya datse harshensa da hakorinsa gam jikinsa Na wani irin matsanancin rawa idanunta dake cike da ruwan hawaye ta xuba masa tana kallon bakinsa .. zuciyarsa gabadaya gaskiya take son fada mata Dan ta daina danganta ya' yansa da kalmar shegu Amman yana jin matsanancin tsoron tashin hankali dazata shiga fiyye da wanda take ciki ahalin yanzu.. Shi dai yasan xuwa yanzu ya Mika duk rayuwarsa gareta sbd kaunar dayake mata ita da yayanta ...
'Cikin wannan halin zeenat da ummi suka shigo dakin atare turus sukayi ganin nablah durkushe gaban deeni rike da kafafunsa tana risgar kuka da iyakacin karfinta .
Da sauri suka karasa garesu suna tmbyr deeni lafiya meke faruwa ?
'cikin rawar jiki nablah ta Mike tsaye ta nufi gurin ummi tana layi tana kuka muryarta cike da kuka tace Dan girma Allah ummi ku min rai wallahi bazan iya bada ya'yan nan ba kumin abun alkhari nasani km Na gode da karamcinku gareni Amman kada Ku rabani da ya'yana .....
A zubure zeenat ta dafe kirjinta tare da cewa what ke kina da hankali kuwa ?
Ke wace irin mahaukaciya ce yaza'a yi kice bazaki iya bada ya'yan ba .....
take nablah ta fuskanceta sosai a fusace tace gaki nan babbar mahaukacirya da batasan abinda takeyi ba da sanin ciwon Kanta ba.
ke kinsan zafin haihuwa ne?
ko kinsa zafi ya'ya ke kinsa wahalar dana Sha akan wayan nan ya'ya?
to nace bazan bayar ba km idan sama da kasa zata hade bazan bada ya'ya nan ba ke ni akan ya'yan nan banki duniya takini ba ciki km har da iyayena wallahi wallahi dana bada ya'yan nan gara narasa rayuwata gabadaya.
ke indai kika ga nabada ya'ya nan sai dai idan bana numfashi a doron kasa .
rassss rassss gaban ummi yayi wani irin matsanancin bugawa da karfi ..Hk ma deeni gabansa ya km bugawa zuciyarsa tacigaba da rawar datake tun kafin shigiwarsu ummi ..
Zeenat tace Wallahi wallahi baki isa ba nablah kinyi kadan km sai kin bada yaran nan tunda tun farko ke kika amince km kinyi alkawarin zaki bada su muryar zeenat Na rawa takarasa fadar hk .
Wani irin kallon tababbiya nablah tayi mata sannan muryarta Na rawa rawa tace to..to.. yanzu nafasa badasu sbd nima Ina son abuna dama can danayi kyautar su bansan zafinsu bane yanzu kuwa sai dai nabawa wasu labari .
Baki isa ba wallahi sai dai kuwa ki rasa ran naki dakike ikirarin rasawa akansu Amman kmr kin bada ya'ya kingama .. Ok zanga wanda ya isa dazai rabani da ya'yana ..
ke nifa nafiki zafin Kai da rashin mutunci akan yaran nan zan iya miki duk abinda yazo zuciyata inji cewa zeenat .
baki nablah ta saki tana kallon zeenat da mamakinta hakan yabawa zeenat damar cigaba da maimaita kalmar dole abasu yara tunda tun farko an rigada anshirya hk da surutai kala kala tayi kan baby's cike takama zata dauka nablah tayi kuka kura ta dire gabanta cike da maseefa tace ubanwa yabaki damar taba min yara ?
Ubanki da km uban Yayi miki ciki a gidan nan .
a fusace ummi tashiga tsakaninsu tana jan zeenat baya.
ummi ta dinga mamakin abinda nablah tayi duk da tasan Yar tatace da fadan rashin gsky Amman batayi tunani nablah zata iyawa zeenat rashin kunya da tsiwa Haka ba .
Ni zaki kawo danyen Kai da ranshi kunya ta fadi Haka tana nuna nablah da yatsan hannuta Dan girma Allah ummi ki matsa Na canzawa wannan Yar iskar yarinyar halitata dama Ina da ciki daita Ina takaici ta wlh.
kallon kasa da sama nablah ke bin zeenat dashi ahankali wanda ke nuna alamun bata isa ba .
Kina takaicina ai sai kixo ki kasheni ki huta banda mijinki daya nace akan zai taimakamin da tuni ban san inda dare Yayi min .
zeenat tayi sororo tabi deeni da wani irin kallo tana jiran taji yakarya mgnr yarinyar .
Amman taji Yayi shr yana binsu da idanu kawai .
my hrt ummi kuna jin fa abinda yar iskar yarinyar kecewa ko.
ummi tace munji ai zance nata duk shirme ne bakya ganin duk abinda take bata 'cikin haiyacinta tasoma jijjga zeenat din kiyi shiru mu yanzu bawannan shirme bane agabanmu yadda yara zasu zama naki shi kawai .kiyi shr ki natsu asan abin yi .
nablah najin Haka ta buga kafarta daya a kasa ta nufi gurin da bbys dinta suke kwance gadan gadan tasa wani irin mahaukatan kuka tana cewa wllahi tallahi ban bada ya'ya Na .
ya'yan guda uku ta rungumesu ajikinta tana sake sakin wani irin matsanancin kuka me ban tausayi da taba zuciyar ma aboci saurare ..
Tashin hankali wanda ba'a saka masa ranar zuwa .
zaune kawai deeni yake yana kallon sarautar Allah.
Yana mamakin daman zafin kan yarinyar nan yakai hk Shi Bai sani ba ....abu kmr a film yarinya tana kokarin birkice musu da dagula musu lissafi.
hatta ummi tsaye kawai take sake da baki tana kallon ikon Allah da yadda nablah ke nuna reaction dinta akan bby din da batasan taka maimain wanda yayi ma 'cikin su ba .
,to wannan idan km tasan ya'yan deeni ne km jikokinta me zai faru ? Tayi wa kanta tmbyr tana cigaba da kallon nablah rungume da yara tana kuka .
tamkar wata zautaucciya .
Gabadaya Daga deeni har ummi kasa tabuka komai suka yi sai idanu da suke bin nablah dashi ...
Wani irin tausayinta ne me gyaraye da tsansar soyayyarta ke sake huda kirjinsa da mamaye gangar jikinshi da zuciyarsa .
alahakikanin gaskiya Bai taba tunani yarinyar zata canza salo irin Haka ba.bai dauka zata so ya'yan da ta dinga hauka akan acire mata su ba .
Wani irin gumi ne me zafi ya shiga tsaftsafo masa ta koina ajikinshi yazama tamkar wani mutun mutumi a zaune yana kallon nablah kwakwume da bbys ajikinta duk tayi firi firi tafita haiyacinta .
Take zeenat ta dinga jin zuciyarta tamkar zata fashe ta tarwatse kan takaicin nablah.
ita kanta wani irin mugu mugun son bbys din ne yashiga ranta tun sanda suka zo duniya ta daura idanunta akansu taji sun shiga ranta.
duk da duk sanda ta kallesu gabanta Na tsananta faduwa akan tsananin kamanin da yaran keyi da mijinta.
Dan ko mahaukaci ya kalli yaran yasan kamarsu daya da deeni babu wani bambanci launi ko sura daidai da yatsun kafafun yaran dana hannusu irin na deeni ne sak .
bakinsu da hanci komai Nasu irin nasa ne .
sosai take taji wani irin mugun son yara Na sake ratsata har 'cikin zuciyarta tana jin bazata iya rayuwa bbu su ba ....
Amman Ga tashin hankali da uwarsu tazo mata dashi wanda take jin bazata iya jurawa ba .. Amman duk da Haka durkusawa wada ....
gabadayan ilahirin jikinta yayi mugun sanyi jikinta banda kirma bbu abinda yake tsabar tsoro da rudani .
Ga mamaki deeni da ummi har nablah.
suka Ga zeenat ta zube a gaban nablah tana kuka tare da rike kafafunta tana rokonta Dan girma Allah nablah ki rufa min asiri kada ki min Haka wannan ita kadai ce damata da zata min katanga tare da yi min shingi da kishiya arayuwa ta.
Dan girma Allah kibar min yaran wallahi nafiki bukatarsu zan kular miki dasu fiyye da tunaninki .
zan basu gatan duk duniyar nan .
zan kaunace su fiyye da ke kanki da kika kawo su duniya ..
Dan Allah kibar min su Karki fasa kyautar mana dasu kmr yadda kikace ummi Dan Allah kisa baki tabar min su .. my hrt kaima kayi shr kaki cewa komai please kuyi mata mgn kozataji nafita bukatarsu takarasa mgnr tana fashewa da wani irin matsanancin kuka.
kuka zeenat take tana rokon nablah akan tabar mata yaran ... ahankalin deeni ya Mike tsaye Daga zaune dayake yaje har gaban nablah ya mika mata hannunwansa duka alamun tabashi yaran Amman taki .
Yayi yayi tabashi yayan taki sai ma matsawa da tayi Daga kusa dashi tana jijiga yaran da zuwa yanzu hayaniyarsu tasoma tayar dasu .
da kyar deeni ya shawo kanta ta hanyar ce mata bbu inda zanje da yaran nan nablah zan kwantar dasu ne kawai ko bakiga yadda kika matsesu ba ajikinki ba kar wani abu yasamesu .
sannan ta Mika masa mace da Na namiji zuciyarta cike da tsoro da fargaba yaje ya kwantar dasu .
ya dawo ya amshi dayan ma ya kwantar dashi kusa da yan'uwasa kana ya janyo hannuta ciki sanyi jiki Ya zaunar daita akan gadonta ya tsura mata rikitattun idanunshi yana kare mata kallon tsanake .
sannan yasoma magana 'cikin sanyi rai da zuciya...
MMN SUDAIS CE
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗
AYSHA A BAGUDO
Dedicated to
HAUWA A USMAN
JIDDARH
Page 100
Nablah ki natsu ki dawo 'cikin haiyacinki muyi mgn 'cikin tsanake da fahimtar juna da farko kin amince da zaki bamu abinda zaki haifa wanda har muka sanyawa rayuwarmu son abinda ke cikinki.
" to meyyasa yanzu kika canza ra'ayinki alhalin duniya tagama sannin wayan nan ya'yan ya'yanmu ne nida matata ?
Ilahirin jikinta da bakinta wara suke gurin cewa nidai kawai ji nake a halin yanzu bazan iya kyautar dasu ba.
. saboda kinsha wahala gurin haihuwarsu shiyasa bazaki iya badasu ko me ?
Kai tsaye taji ya 'aiko mata da tmbyr datasa ta tsura masa shanyayyun idanunta da suke cike da ruwan hawaye taki ce masa komai sai kallonsa kawai take ..
"jikin deeni Yayi sanyi sosai sbd ganin yadda yanayinta ya sauya . yarasa ta inda zai bullo mata.
ta kalleshi sosai Yayi matukar bata tausayi Amman har 'cikin zuciyarta bata jin zata amince tabashi yayanta kyauta .
" tacigaba da dubansa can km yace kina jina ko kiyi hakuri kibar mana yaran nan nida matata nayi miki alkwarin zan raba tarin dukiya biyu Na baki rabbi akansu kije kicigaba da rayuwarki .
Sosai ta sake tsareshi da shanyayyun idanunta tamkar zata cinyeshi tana mishi wani irin kallon rainin wayo.
hakan Yasa gabansa cigaba da faduwar dayake .
shima kallonta yake yana jira Daga gareta tare da mamakin canzawarta a'cikin zuciyarsa .
idan wani ya fada masa zata rikide ta dawo masa Haka wallahi zai rantse da Allah yace karya ne ranta a matukar bace tace Kai dukiya ta dama km take rudarka har kake jin Kai wani ne .
Amman ni bbu abinda za'a bani a duniyar nan da zai Saka Na iya kyautar da ya'yana har UKu ba daya ba.
ko mahaikaciya ce Ni bazan soma yin wannan dayin aikin ba ballanantana Ina 'cikin haiyacina, yakarasa fadar hk tana nuna brain dinta da yatsan hannuta.
kana tacigaba nidai Dan girma Allah Na rokeku daku barmin ya'ya Na Ina sansu nima a duk yadda suke.
deeni ya runtse idanushi gam tare da furta ya Allah akasan zuciyarsa ....yasoma cizan lips dinsa da karfi .
gabadaya komai Na 'cikin duniyar nan yasoma tsaya masa Bai taba tunani sanadiyar yarinyar zai taba shiga 'cikin tashin hankali irin Haka ba.
ya dauka rashin son 'cikin jikinta datake tun farko zai tsaya a Haka ne .
Amman a kalmomin bakinta na yanzu komai ya sauya agareshi yagane shi din bakomai bane a duniya nan .
sannan ya soma fahimtar Bai isa yace zai ma kaddarsa wayo ba .
Yau din nan tazo masa da tarin abubuwa da daya farinciki dake tattare da tashin hankali mara misaltuwa .
Shin yanzu ya zaiyi da kaddarar data fada masa ?
Ya'yan da zai fara samu a duniya sunzo masa da wani irin salo na daban .
yanzu mezai cewa danginsa da yan'uwa ?
Hakika Komai yagama dagule masa ahankali ya juya saitin da zeenat take tsaye surusuru tana aikin barin jiki da marairaice wa .
yana aika mata da wani irin matsiyacin kallo me frigita zuciyar wanda akawa sannan muryarsa a fusace yace kinga ni ko ?
Kinga irin abinda sakacinki ya haifar mana ko ?
Me kike tunani zai faru gaba idan har taki amincewa tabada yaranta ?
Zeenat da jikinta ke mugun kirrrrrrma ta sake fashewa da wani irin matsanancin kuka tana yarfe hannuwa .
yanzu dakin yi hakuri kin haifi wanda Allah yabaki da duk hk Bai faru ba.
da km baki samu 'cikin tsaka me wuya ba. Amman bbu komai duk 'cikin wannan lamarin ni akafi cuta yakarasa mgnrsa yana jin kunar rai acikin zuciyarsa yayinda kirjinsa ke wani irin buguwa da karfi .
Shi kanshi kuka yake son yi ko zai daina jin radadin azabar ciwon zuciyarsa keyi .
banda kuka bbu abinda zeenat keyi ita kanta tasan ta cuci kanta da kanta.
Ta ruguza rayuwarsu sbd sakacinta da son zuciyarta ta Mike Daga inda take ahankali tana layi ta rungume ummi ajikinta tana matsanancin kuka.
Ummi kiyi hakuri a rayuwa nasan Na cutar daku Amman ko daidai rana daya ummi baki taba kina ba .
Sai ma sabuwar kulawa da kike bani hakika ke uwace guda har da rabi samun irin Ku ahalin yanzu zai yi wuya ummi kiyi hakuri abida nayi ki ya femin Na cutar dake domin ba irin tarbiyya da kika bani ba kennan ta sake tsanata kukanta.
ummi itama ta rungumeta sosai tana zubda hawayen tausayin diyarta arayuwa ta tsani abinda zai saka zeenat dinta zubd hawaye matukar tana da yadda zatayi.
kasa cewa komai tayi Sai aikin rarrashita datake tana shafa bayanta ..
Ahankali deeni ya dauke idanunsa akansu ya juyo sosai tare da gyaran zamansa yana fuskantar nablah da kyau ya kaskantar da kanshi da muryarsa agabanta yana nuna mata shin din bakomai bane facce me nema agurinta .
a wannan fani har ya mance dako su waye tsaye akansa.
Domin Bai San sanda ya kamo tafin hannunta 'cikin sanyi jiki ba yana kallon 'cikin kwayar idanunta muryarsa cike da rauni zuciya tare da mayyen sonta ya Kira sunanta.. nabeelah ...kiyiwa Allah ki mallaka mana bbys din nan.
badanmu ba Sai saboda Allah ki duba tashin hankali da zanshiga akan yaran nan .
sannan ki duba halin da mahaifiyata da matata zasu shiga ki tausaya nablah ki duba yadda mahaifiyata tagama gayawa duniya akan nida matata muka haifi bbys din nan .Kinsa idan akaji sabanin hk zatashiga tashin hankali da rudin rayuwa ..
nablah nasan kina da saukin Kai da sanyi hali hade da hakuri akan komai Na rayuwa .
Na rokeki da Allah kibarwa zeenat bbys din nan .
Allah zai duba lamarinki ya sake baki wasu da yardarsa ...
a fusace ta fizge hannuta 'cikin sauri Daga nashi tana jin takaicin mgnrsa . ..
Kana ji har mara hankali matarka ta kirani dashi akan ya'yan dani kadai nasan kalar wahalar dana Sha akansu tunda Daga cikinsu har zuwa haihuwarsu.
idan har nabar mata yaran nan wallahi azim Na tabbata mahaukaciyar gaske deeni .
zeenat ta bar jikin ummi tamatso gareta sosai tana kuka tana rokon nablah.
ZUCIYAR deeni tasoma rawa yasoma jin Wani irin ajikinshi hakika ya tausayawa zeenat duk da yasan itace silar rugujewar rayuwarsu da yi musu katangar karfe da burin ransu km farincikinsu