Showing 156001 words to 159000 words out of 366611 words

Chapter 53 - AUREN SIRRI Book 2 Complete by Aisha Bagudu.txt

29 Dec 2025

8176

tashe yake duban fk....

Kukan dana tarar kanayi aciki mafarkika ya Nuna min yadda ka afka 'cikin tafkin kogin soyayyarta please tell me wacece wannan yarinyar may sa'a data yi winning din xuciyarka Haka?
deeni yashare gumin daya rufeshi sannan muryarsa a kasalance yace dan Allah mlm karabani da zance wata yarinya nace maka bansani ba.
km wlh karka sake Damuna da zance wata yarinya can .
yana gama mgnr ya Mike yashige toilet din dake manne da office din sa yabar fk tsaye da mamaki .

Fk ya dade a gurin yana saka da warwara Tare da tunanin iri iri numfashi ya sauke Tare da yin ajiyar zuciya sannan ya bar office din cike da zargin DEENI.


Karfe hudu daidai motar deeni tashiga 'cikin estate din Tare da motocin escort dinsa dake biye dashi a baya .

sule ya daidaita tsayuwar mota yayi parking kana ya fito da sauri ya bude gidan baya Inda oga deeni ke hakimce abunsa hankali kwance Sai da yagama shan kamshinsa sannan ya yunkura ... fitowar nan dazai yi idanunshi suka masa arba da abinda ya kusan tarwatsa zuciyarsa da gangar jikinsa .
abinda yake ji ajikinshi ba iya zucitarsa kadai ya tsaya ba har cikin kwalkwaluwarsa .. idanunsa akansu kyam nablah ce tsaye da kB may wanki .. tsaye suke murmushi kmr wan karan tare da mgn Wanda baisan abinda kB din yake fada mata ba Wanda koda yaushe idan yagansu tare take yawan murmushi da farinciki..

cike da karfin zuciya yakarasa fitowa daga 'cikin motar yana gyara suite din jikinshi yasoma bada step 'cikin kunar zuciya yayinda gabadaya Hankalinsa ya tattara garesu.....


Can bangarensu nablah kuwa ahankali suka cigaba da hirarsu yayinda kB din ke kokarin fahimtar daita sirrin dake zuciyarsa ta hanyar ce mata gsky mlm nablah kina matukar birgeni da yadda kike kama kanki a 'cikin estate din nan.
sabanin yadda naga sauran ma,aikatan estate din sukeyi .
Tayi murmushi kawai tare da cewa Nagode da yabawa
...uhm Ai godiya kadai bazata wadatar da zuciyata ba facce.
Idan
ki amince min da abinda zuciyata take son sanar dake ..
Ta sake yin murmushi har wushiryarta ta bayyana Wanda hakan yabawa asalin kyawun fuskarta fitowa fili . sannan tace meyye shi abinda zuciyarka take son fada ?
Yayi murmushi sosai sannan ya gyara tsayuwarsa da kyau ta yadda zai sake birgeta sannan ya samu damar amayar da abinda ke ranshi .
kalma daya ce tak mara wuya gata da saukin fada a baki .
idan har ta miki zaki fahimceta da saurin km tayi tasiri a zuciyarki gabadaya nablah ta tattara duk wata nasuwarta gareshi yayinda zuciyarta ta bukatu kwarai da son jin abinda zaice mata tare da addu'ar Allah Yasa ba abunda take tunani bane yake son sanar daita ..uhm Ina jinka daidai lokacin da bai fi taku biyar deeni ya iso garesu ba km duk kusan mgnrsu takarshe acikin kunnenshi suka fadawa.

kB yacigaba abinda zuciyata take son fahimtar dake sai km harshensa ya harder yasoma in inna yace Ina ...Ina sonki......


zafin zuciya da buguwar zuciya ne suka tasowa DEENI alokaci guda..

deeni ya runtse Idanunshi gam yana jin yadda zuciyarsa ke tafarfasa dan dama tuni ya yafara zargin Haka atsakaninsu tun kallon da yaga yaron yana mata a kwanakin baya .

Gadabada idanuwansa sun gama rufewa ya karasa gurin zuciyarsa tamkar zata tarwatse bai tsaya wata wata ba ya dauke kB da wani gigitaccen mari take jini ya balle ta hancinsa ta baki ..
a frigece kb ya dago yana duban daga Inda saukar marin ya fito ogansa ya Gani tsaye a gabansa tamkar mashi wani duba yakewa boos din nasa tare da neman dalilin jin saukar mari .

yayinda Shima DEENI yake binsa da wani irin kallo may cike da tsansar tsana .
kana yace tsayuwar me kakewa mutane anan Dan ubanka gabadaya kb ya rude ya gigice yarasa bakin mgn Sai ma juyawa dayayi da sauri yakama gabansa ahankali' yake daga kafafunshi da oready sun gama sagewa da mamakin may gidan nasa .


Wani irin zafi ne ya caki zuciyar nablah lokaci da deeni ya dauke kb da mari batare da Yayi masa komai..
tayi saurin runtse idanunta hawaye takaici suka zubo mata. wa tunaninta haushinta da deeni yake ji ne ya shafi kB mutumin da bbu ruwansa km yasan martaba da mutunci mutane ba kmr shi ba .
daya kasance mugu . Wanda kowa wulakantace ne a gurinsa.


Bata ankara ba taji ya fixgota da karfin gaske ta dago shanyayun idanunta tana kallon deeni dasu Wanda gabadaya kamaninsa da yanayinsa sun gama canzawa .

Ta bude bakinta zatayi mgn a zuciye ya dauketa da mari wanda yasata durkushewa agurin tana kuka da takaicin kasancewarta a cikin gidan tadoma tirjewa da son kwace hannuta garesa ganin hk yasoma janta yana kaiwa tsakiyar parlour gidan yayi wurgi daita yana fida numfashi Allah yaso bbu kowa akasan gidan .

muryasa a hassale yace dan ubanki an gaya miki kofar gidana wajen dandalin soyayya ne .. ta Mike da kyar tana dafe da gefen cikinta zuciyarta tamkar wuta Dan takaici abinda yayi mata kana tasoma mgn 'cikin daga murya kofar gidan naka wata tsiya ce daba za a iya zama ba
.....Ta karasa fadar Haka tana jin mugun tsaki ..

a fusace ya
nunata da yatsansa wlh Na sake ganinki da wannnan dan iskan yaron a kofar gidana zan kasheki da hannuwana .
ya cure hanuwansa waje daya kana ya waresu tare da Nuna mata yadda zaiyi daita.

nablah ta zaro idanu waje tana kallonsa jin kalmar zai kasheta da hannuwanshi..
Ok baki yarda ba ko try and see..Ta tsaya sororo tana masa wani irin kallo may cike da tsansar tsana ita fa zuwa yanzu tafara tunanin mutumin dake tsaye a gabanta ya fara samun tabin hankali ko km daman can yana da tsohon ciwon hauka Wanda ita bata sani ba ....a zuciye yasa bayan hannushi ya buge mata baki ashe mgnr zuciyata ce ta fito fili ....
Ya daka mata wata razananniyar tsawa da karfi gaske.
Wanda ya kusan tarwatsa zuciyar nablah Dan tsoronsa daya soma shiga zuciyarta .. Ni ne mental ya fadi Haka ya Nuna kirjinsa da yatsansa tayi saurin girgirza masa kanta well...zaki san mental ne Ni Sai ranar dana sake ganinki da wani Kato a kofar gidana .. nabla ta sake durkushewa a kasa ,cikin azaba kuka Amman Haushin wulakancin da DEENI Yayiwa kb yafi radadin marin da Yayi mata da bakaken maganganun sa gareta.

*Afuwa afuwa afuwa kuyi hakuri da rashin jina kwana biyu .. hakan ya faru ne sakamakon rashin lfy danake fama dashi Wanda ahalin yanzu sai dai nace alhamdulilllahi domin bangama warkewa ba karfin hali ne kawai Dan Haka zaku daina jina ol the time please Ina bukatar adurku* 😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭




MMN SUDAIS CE
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗




AYSHA A BAGUDO





*I really appreciate all my fans and all washers that called me when am sick thank God I recoved God bless all , and I pray for the people that are sick may Almighty Allah liet there wings up Ameen I so much loved you fans remain bless once again i appreciate all ur effort on me*🤝🏻🤝🏻🤝🏻


Page 75




A zafafe Ya qakaraso har zuwa inda take a durkushe sbd yanayin takaicin da yake ciki.
'dan bakaramin yamutsa masa tunaninsa tayi ba musamman lokacin daya daura idanushi akanta tsaye da kB.
ji yayi kansa nayi masa wani irin Sara tamka zai rabe gida biyu .
zuciyarsa kuwa zafi take masa tamkar zata kama da wuta.

Kuka take Sosai Na fitar hankali.
may taba zuciyar ma'abocin sauraro kallo daya zakayi mata kaji tausayinta ya tsargamaka km duk rashin imaninka idan kaga halin datake ciki wlh Dole ka tausayawa rayuwarta .


A halin da take ciki bata tunanin duk duniya akwai mutumin data tsana da kin gani ......sama da mutumin dake tsaye a gabanta ...

Kukanta da halin datake ciki ko ajikinsa "asalima kwata kwata bai damu ba.
km bai jin ajikinsa Hakan zai zama damuwarsa sai ma tarin haushinta da takaicinta dake daskare a kasan rashin .
gyara tsayuwarsa yayi sosai tare da rungume hannuwanshi duka a saman fadadden kirjinsa ya zuba mata rikitattun idanushi yana kallon yadda take kuka , kusan minti Goma ya dauka tsaye yana aikin kallonta batare da yace mata komai ba.

jin kukanta yaki tsayawa ne yasa zuciyarsa cunkushewa guri daya tasoma dugunzuma tamkar ana diga masa ruwan dalma .
Kafin ya ankare yaji
Ta sake kara sound din kukanta may tsanani cin rai da tsuma zuciyar ma'aboci sauraro tare da dagula lisafi .


Shr kawai yayi yana tunanin abinda yakamata Yayi gabadaya ilahirin jikinsa sun gama sagewa duk da sanyin AC dake aiki a parlour hakan Bai hana zufa keto masa ta koina ajikinshi, so yake yayi magana Amman km yakasa dan bazai iya yi ba, dan ko yace zaiyi mgnr muryarsa bazata fito ba dan hk Ya runtse rikitattun Idanunshi gam hade da Dan kamo lip's dinshi Na kasa yayita tsotsa ahankali yana jinta tana risgar kukanta dayaje jinsa har 'cikin ranshi .
baya kaunar ya bude idanunshi ya kalleta cikin yanayin halin datake ciki .
km bai jin zai iya furta mata daidai da kalma daya ce a yadda yake jin kansa

Dan hk yabarta tacigaba da kukanta wa tunaninsa idan ta gaji dan kanta zatayi shr amman Ina saima ji yayi ta kara sautin kukan sosai .
Ai take haushinta may gyaraye da tsansar takaicin abinda tayi masa Ya sake ya harzuka zuciyarsa .
bazato taji saukar rankwashi a tsakiyar kanta .
Da sauri tasa hannuta ta dafe gurin tare da sakin wata irin razananniyar kara Wanda ya farga da ummi dake zaune a part dinta .

idanunta suka sake kawo ruwan hawaye may dumi .. ya murde mata kunne da karfin gaske ta sake saki wata kara... tare da cewa wayyo Allahna .... Wayyo Allahna ...wlh Allah Ya isa ban yafe mak.....ai kafin takarasa taji Yasa bayan hannushi ya buge mata baki.
da sauri ta sanya hannyenta dukka akan bakin nata tana may zuba mishi shanyayun idanunta Wanda suke cike taf da ruwan hawaye .

Sannu ahankali ya bude idanunshi fesss suka sauka akan Kwakyawar fuskarta may cike da haiba yana mata wani irin kallo may tattare da tsansar tashin hankali . shiiiiiiiiiii kawai ya iya cewa.
ba shiri ta hadiye sauran kukanta Dan wani irin tsoronsa ne taji Ya caki tsakiyar zuciyarta.

yayinda gabadaya ta canza takoma wata kala daita abar tausayi Banda tsine masa da zaginsa bbu abinda take a kasan zuciyarta ...

daidai wannan lokaci ne
ummi da safeena suke saukowa daga upstairs sakamakon jin tashin sautin kukan yaki karewa km har zuwa time din DEENI na nan tsaye rungume da hannuwanshi .

Da sauri ummi takaraso Inda suke tana tmbyrsa lfy ?
ganin irin kukan da nablah keyi.
DEENI yayi shr kawai yaki cewa komai sai ma cigaba da kallon nablah da yake batare da ya amsa tmbyr da umminsa tayi masa ba .

Ahankali ummi ta dago nablah dake durkushe a kasa .
tana tmbyrta lfy nablah make faruwa ? Me yayi miki ? Hk ummi ta jera mata tmby .

shr kake jin nabla dan bbu bakin mgn sai ma kukan da take risga da iyakacin karfinta har da shesheka .

Ummi ta sake juyo inda deeni ke tsaye Wanda xuwa lokacin ya sake gyara tsayuwarsa tare da cire hannushi a saman fadadden kirjinsa ya mai dasu 'cikin aljihun wandonsa yana ciciza lips dinsa .

Deeni....ummi takira sunansa muryata a kausashe. Kasa amsawa yayi tsabar Haushi sai ma idanunshi daya dauke daga kan nablah ya maidasu gareta .
me yasame yarinyar mutane take kuka irin haka?
ko wani abu kayi mata ta jiho masa tmbyr a jere ..?

Kafin yace wani abu sai daya numfasa tukun sannan ya sauke ajiyar zuciya" tare da yatsina fuskashi" muryarsa a marairaice may cike da tsansar shagwaba kana yace Gata nan a gabanki first love ta fada miki abinda akama mata .

ummi ta bata rai sosai tana dubansa sannan tace bafa nason rashin mutunci deeni ....

Kafita idona Na rufe ...abinda kayiwa yarinyar mutane kawai nake son sani ba wanin rainin hankalinka daka sabawa yiwa mutane ba .

Shima hade rai yayi Sosai fiyye da dazu sannan yace haba first lov ya a gaban yarinyar zaki dinga yimin hk "salon kawai ta raina mutane byn nima hk naganta bansan abinda ya sameta ba.

yana gama fadar hk ya cire hannushi daya cikin aljihun wandonsa" yabar daya ciki tare da juyawa ahankali yasoma daga kyawawan kafafunshi yasoma takawa sannu ahankali 'cikin takun nan nasa may matukar daukar hankali , Ya nufi bedroom dinsa .. ummi tabi bayansa da kallon mamaki tana may tabe bakinta a ranta tace rainin km Na nawa...



Yana shiga bedroom dinsa yaje ya zauna 'bakin gado yana fidda numfashi ahankali ahankali tare da tunanin matakin dayaka mata ya dauka akan kb da ita kanta yarinya.
a dazu daya gansu ji yake tamkar numfashinsa zai fuzge ne daga gangar jikinsa sbd wani irin radadin azabar daya shigesa ...

Zuwa lokacin tuni safeena ta kamo hannu nablah dake kusa da ummi xuwa kan kujera tana tmbyrta abinda ya hadasu da bros dinta. yayinda ita km nablah taki cewa komai sai kuka da take .


Ahankali ummi takaraso kusa dasu ta zauna itama.
" tmbyr duniyar nan bbu irin Wanda ummi da safeena basuyi mata ba Amman Sam nablah taki cewa Ga abinda aka mata sai hawaye ne kawai ke fita daga idanunta ..

tun tana kuka a zahirance har ta dawo kukan zuci .. yadda taga ummi duk ta damu ne.
Yasa duk jikinta yayi tsanyi Sosai ta sausauta kukanta tare goge Hawayen idanunta .. jikinta a sanyaye ta bude bakinta Da kyar tamkar may koyon mgn takira sunnan ummi ...

ummi ta amsa tare da juyowa ahankali ta zuba mata idanun kawai tana kallonta hade da nazarinta ... sannan tace uhm nablah Ina sauraranki mekike son cewa ?
'cikin muryata may matukar sanyi da ban tausayi tace da Allah ummi Ina son zuwa gida naga mamana da sauran yan'uwana, takarasa fadar haka hawaye da yayi saura a idanunta yasamu nasarar silalowa kan kuncinta .

ummi tayi shr for the mean time tana cigaba da nazarinta sannan daga baya tace shine daman abinda Yasa ki kuka hk ?

Nablah ta girgirza kanta da sauri tana duban kasa.

to fada min meyye abinda yasaki kuka ? Ko km waccen babban kobon ne yayi miki wani abu?

muryata a raunane tace a,a ummi bbu komai fa Dan tasan koma ta fada mata , abinda yayi mata ba komai za'a yi masa ba ya rigada yacita bulus..

Shikennan amman zanso ki kara yin hakuri.
zaki je gida inshallahu Amman ki Dan bani lokaci kadan da kaina zan kaiki har gidan naku kinji .

kinga yanzu shirye shiryen zuwa India nakeyi tare da safeena zamu wuce har da Zeenat.

ke .. zaki cigaba da kula da al,amuran gidan .
Da zarar Na dawo duk da ba'a gidan nan zan sauka ba ,zan koma gidana zaki je gida kiga family dinki kinji .

gaban nabla yayi wani irin bugawa da sauri hankalinta yayi mugun tashi jin abinda ummi tace ta dago ahankali tare da zubawa ummi shanyayun idanunta kawai dan takara tabbatar da abinda taji tace .
Ahankali ta 'cikin hijab dinta tasa hannu ta dafe daidai saitin zuciyarta dake harbawa da sauri da sauri .

bata jin zata iya zama ita day ranta acikin tanbatsetsen gidan irin hk may cike da abubuwan ban tsoro "duk da tasan bada laraba za'a ba . amman ,hankalinta yayi mugun tashi .
Sake kafe ummi tayi da shanyayun idanunta tana kallonta da kyau yayinda sauran Hawayen idanunta suka cigaba silalowa . kadan ya rage zuciyarta batakarasa bugawa ba.
sbd rudanin da take ciki muryarta Na rawa tace Dan girman Allah ummi kiyi hakuri kibarni Na tafi tunda kuma tafiya zakuyi bazan iya zama Ni kadai raina acikin gidan nan ba wlh ni tsoro nake ji takarasa fadar hk wasu Hawayen nakarasa zubowa tare da hade hannuwata guri daya ta curesu may nuna alamun a tausaya mata .....

safeena dake zaune ta kamo tafin hannuta 'cikin nata tana murmushi cikin hadadden turancinta tace Kai nablah badai tsoro ba wlh.
kiyi hakuri kiyi zamanki kmr yadda ummi tace bbu abinda zai sameki inshallahu.
Ga laraba nan tare zaku zauna.
duk kinbi kin wani frigice daga jin za'a barki a gida.
nifa Na dade da gane wayonki so kike ki gudu wlh , safeena ta karasa fadar hk tana murmushi tare da duban saitin da ummi take ..

Murmushi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login