Showing 198001 words to 201000 words out of 366611 words
Chapter 67 - AUREN SIRRI Book 2 Complete by Aisha Bagudu.txt
ba?
... wayyo Ni nablah me zancewa mahaifina dayace kada nazo aikatau ..?
Me zancewa yan'uwana da suka tattara dukkan wata yardarsu da amanarsu gareni" tare da amincewa dani ,?
Wayoyyy wayyyyyoo Ni nablah wazan ce yayi min ciki......? Kuka take hade da sambatu iri iri .
,tausayinta ya sake kama doctor saira ya mamaye zuciyata sosai har batasan sanda hawayen tausayin yarinyar yashiga tsiyayo mata ba .
, ahankali ta zare dan siririn medical glass din dake manne da fararen idanunta ta goge Hawayen dake tsiyayo mata tare da maida medical glass dinta tana cigaba da kallonsu , ...
Mikewa nablah tayi da kyar tana layi... yayinda gafe daya km tasoma ganin juwa juya.
batare data juyo ta hankalta da irin kallon tausayin da doctor saira ke mata ba.
" ta fara tafiya cike da damuwa da rudanin rayuwa....
DEENI ya zabura ya Mike tsaye ya biyo bayanta da sauri yana Kiran sunanta tare da kokarin dawo daita amman taki sauraronsa ,sai ma fizge jikinta datayi daga nashi tacigaba da "Daga kafafunta da kyar ..
tafiya daya biyu zuwa uku tayi DEENI yayi nasarar sake damkota gareshi Ina zaki a hk...?
Ki natsu man musan abinda yakamata a yi duk wannan kukan naki bashi ba sulotion atare dake .....
zubewa tayi ajikinsa tare da sakin wani irin gigitaccen kuka.
ahankali tasa hannuta ta dafe daidai tsaitin zuciyarta datake jin yana mata zafi tamkar zata tarwatse..
" ta manne ajikinshi tana sakin numfashi da kyar tare da lumshe shanyayyun idanunta hawayenta Na tsananta zubowa, yayinda zuciyarta ke dada karyewa sbd mummunar halin data tsinci kanta ciki ..
Ahankali ta bude shanyayyun idanunta data lumshe ,tasoma ganin dakin Na jujjuyawa daita ...juwa take Gani sosai Domin zuwa lokacin bata ganin komai dake 'cikin dakin hatta bakin dake cikin idanunta yasoma yin sama da kasa alamun juyewa .
DEENI ya dake rungume daita a jikinshi yana kallon yadda idanunta ke son kakkafewa Yayi saurin yin kasa daita , kafin ya ankare tuni ta saki wata irin naunauyen ajiyar zuciya me karfi gaske .
Yayi saurin saka hannunshi duka yana jijiga fuskarta da iyakacin katfinsa tare da Kiran sunata a rude na..bee..lah.. na..bee..lah dan girman Allah Kada ki min Haka please.... ki natsu musan abin yi tukun yana cigaba da girgirzata Can yaji gabadaya takarasa sakewa ajikinshi .....ya tsayawa cak ..... yana dubanta da rikitattun idanunsa....
Gani Yayi bata numfashi ya dago fuskarta da sauri yana dubanta sannan a rude yasa byn hannushi a hancinta .
Amman kwata kwata bai ji wata alamun
numfashi a atare daita ba .
'Cikin wani irin tashin hankali da matsanancin fargaba ya Mike tsaye daita.
Yayinda , jikinshi ya dauki wani rawa yana Kiran sunnan doctor .......
kai tsaye kan dan madaidaicin gadon marasa lfy ya nufa ya kwantar daita yana sake Kiran sunan Doctor.
,yayinda doctor saira itama tazagayo daga inda take tsaye.
da mugun saurinta tare da kallon abin mamaki yadda DEENI ke sake ya rudewa akan wannan yarinyar dabata gama Sanin kowacece gareshi ba .
da dan hanzarinta takaraso inda nablah ke kwance tamkar wata matacciyar gawa dan bbu inda ke motsi a sansar jikinta..
Cike da natsuwa doctor saira tasoma dubata suma tayi doctor saira ta fadi hk tana duban Inda DEENI ke tsaye rike da hannun nablah yana mammatsawa ko zata dawo haiyacinta..
suma ... DEENI ya furta hkn da karfi jikinshi Na sake daukar rawa duk jikinshi bbu inda baya tsatsafowa da ruwa gumi tsabar tension din dake zariya a gabobin jikinsa.
,Ok please doctor taimaka min kibata taimakon gaugauta please.
Abinda nake kokarin son yi kennan ..
DEENI ya saki yatsun Hannu nablah da kyar .
ya shiga zariya acikin makeken office din yana furta duk wata addu'a dayasani Dan neman sausauci a gurin Allah.
da taimakon Allah dana doctor saira aka samu numfashi nablah ya dawo daidai yasoma sauka ahankali ..
doctor saira ta sauke ajiyar zuciya ganin numfashin nablah ya dawo daidai ,shima DEENI sai lokacin hankalinsa ya dan kwanta ..
Doctor tace muje mr DEENI Ina son magana da kai, ya gyada mata kanshi kawai batare yace mata komai ba sai ma zuwa yayi ya zauna kan kujera yana furzar da huci me gauraye da tashin hankali.
Doctor saira ta zagaya ta zauna tana dubansa Na wasu Yan dakiku sannan ta saki numfashi kana tace .
"yanzu Mr DEENI yakake ganin za'a bulowa Lamarin yarinyar, kaga dai yadda ta daga hankalinta akan 'cikin jikinta ?
Jikinsa a matukar sanyaye yayinda gabadaya yanayinsa ya sauya 'cikin lokaci daya da kyar ya iya bude bakinsa gurin cewa ki barni daita kawai zansan yadda zanyi handover din koma ta yadda komai zaizo da sauki .
Wlh yarinyar tayi matukar tabani tausayi sosai yanzu kowaye mutumin da Yayi mata 'cikin ?
Nima abinda nake son sani kennan DEENI yabata amsa da hkn.
A gsky idan ba,zaka damu ba zanso nashiga 'cikin lamarin binciken Wanda Yayi mata 'cikin jikinta ...Wannan ba damuwarki bane ba km hurunmin ki bane da son sani Wanda Yayi mata ciki DEENI ya katseta ta hanyar ce mata hk ...
A dan kausashe yacigaba da kaina zan nemo duk Wanda Yayi mata hkn sannan Na zartar da hukuncina akansa ..
Ok hk ma Yayi
Amman kasoma da rarrashin ita yarinyar firstly ko zata tuna Wanda Yayi mata haka kafin ka zartar da komai.
Yace uhm alamun yaji ....
Cike da natsuwa Ta tsura masa ido kawai tana sake dubansa da nazarinsa sosai kana tace dan Allah in maka wata tambaya Inda bazaka damu ba ....
Ya dago rikitattun idanunsa ya zuba 'cikin nata kana ya sake ce mata uhmmmm...
Ina son sanin matsayin yarinyar nan a gurinka? ..Yayi tsaida da ranshi tare da yin shr yana nazarin abinda zai ,daga karshe da yace mata cousin's muke daita . Ok shiyasa naga duk hankalinka ya tashi to Allah kiyaye gaba .. doctor saira nagama fadar hk ta Mike tsaye tana gyara farar rigar jikinta ta nufi kofar fita Domin son zuwa duba peticent dinta ..
Kusan awa daya da fitar doctor saira sannan nablah ta farka ... da wani matsanancin kuka har da shesheka deeni dake tsaye akanta ya matso sosai kusa daita ..yana shafa sumar dake baje a kanta.
Ahankali ya dinga jero mata sunnu babu kwaukwautawa.
, shr kawai tayi tana kukanta batare datace masa komai ba.
Yasa hannunshi ya dagota tare da jinginar daita .sannan ya zauna kusa daita ganin yadda ranta ke a jagule da bacin ran halin datake ciki.
yasashi Mikewa tsaye 'cikin tsanyi jiki Ya nufi dan karamin fridge din doctor saira ya dauko ruwa mai tsanyi ya zuba mata a cup ya kara mata cup din a daidai lip's dinta, yashiga bata ruwan da kanshi .
Sai dai kadan Tasha ruwan ta cire bakin daga cup din tare da jan naunauyen ajiyar zuciya.. DEENI ya ajiye cup din a gefe daya , ya tsura mata idanunshi yana kallonta ji yake tamkar ya rungume ajikinshi ya rarrashita ,hk yaji ..'cikin muryarsa kasa kasa yakira sunanta tare ,
Da kamo tafin hannuta 'cikin nashi yana shafa byn hanunta da nashi hannun ahankali ..
bata amsa masa ba ,sai numfashi da take saki akai akai .
muryasa a kasalance ya sake Kiran sunanta nabeelah kallonsa tayi da shanyayyun idanunta.
ido cikin ido suke kallon junansu , gabanta yashiga faduwa da sauri Wanda Shima sai dayaji hkn atare dashi ..
wai garin Yaya hk ta faru dake ne ?
Shr tayi bbu amsa dan gabadaya wata irin kunyarsa ce ta rufeta ta kasa cewa komai sai kallon 'cikin idanunshi da take ..sai da suka dauki sama da minti goma a hakan suna kallon juna ko wannensu ya kasa dauke idanunshi daga kallon dan uwansa , km kowannesu da abinda zuciyarsa ke sakawa ...
DEENI ne Yayi karfin halin janye idanunshi daga 'cikin nata kana yace tmbyrki fa nakeyi ?
Da kyar Ta iya bude bakinta Wanda Yayi mata nauyi Ta dan turo tsukakken karamin bakinta 'cikin wata irin murya Na Wanda yaci kuka ya koshi tace wlh Allah bansan ya'akayi hk ta faru dani ba , takarasa fadir hk wasu siraren hawaye nabin gefen idanunta daya tare da sunkuyar da kanta kasa .
,dariya taso subuce masa Yayi saurin dannewa.. ai kuwa kiyi gaugawa sanin yadda akayi kikayi ciki .Ko km tuna Wanda Yayi miki ..
Ta dago da sauri tana dubansa ta km fashewa da wani gigitaccen kuka Ni wlh Allah bansan inda zan nemo Wanda Yayi min ciki nan ba tana fadar hkn ta km maida kanta ta sunkuyar .
...Ya km danne dariyarsa a karo Na biyu , to yanzu ya za'a yi kennan da 'cikin jikinki ?
Tayi shr kawai tana tunanin yadda zatayi da 'cikin jikinta can km wani tunani yazo mata.. kanta a sunkuye tayi saurin cewa zansha fiya fiya kawai .ko zan rasa raina gara Na rabu da abinda ke cikina akan Na haifeshi .take gabansa yashaga faduwa yana girgirza mata kanshi ..
Ki kashe kanki kike nufi da abinda ke 'cikin ?
Ta daga masa kanta batare da ta dago ba .
,kinsa hukuncin Wanda ya kashe kanshi da gangan, ballanantana ke dake dauke da wani ran ajikinki ..
'Cikin kuka tace eh nasani amman Na zabi mutuwa dana haifi dan dake 'cikin cikina wasu Hawayen suka sake sulalo mata tashiga kuka sosai ...
Ok kinaji yanzu ...ki natsu ki bar kukan nan hk . Sannan kibar komai a hannuna , ki Bari zan yiwa doctor bayani ansan yadda za'a yi da 'cikin idan ma takama a zubar da 'cikin sai ayi hk da ayi asarar rai biyu gara arasa 'cikin tunda shi bawani girma Yayi ba Ni zan taimaka miki ,
nablah najin hk tayi tsai da kukanta cak... tana shasheka ahankali ahankali tare dagowa.
ta xuba masa shanyayyun idanunta da suka gama canza launi tsabar frigici da tashin hankali datake ciki maramisltuwa ..
MMN SUDAIS CE
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗
AYSHA A BAGUDO
Page 87
Hannuwanshi duka ta damko 'cikin nata sosai ' tana sakin wani sabon kuka me cin rai tare da cewa idan kuwa kayi min hk deeni bansan irin farinciki da zanyi ba arayuwata ,jikinta har rawa yake gurin fadar hk tacigaba mgn rabuwa da wannan 'cikin shine muradina a halin yanzu. Ni kaina wlh sai yanzu Na tabbatar da 'cikin jikina km duk hanyar da zanbi gurin salwantar dashi wlh zanbi tashiga jijiga hannushi dake 'cikin nashi Tana wani irin kuka me cike daban tausayi .
Jin abinda tace yasa gabadaya gumi yasoma tsatsafowa ajikinshi takoina tsabar tashin hankali da tsinci kanshi ciki .
, dan ko numfashi ma da kyar ya dinga fitarwa ahankali ahankali yana kallon 'cikin idanunta abinda ya dade shekara da shekaru yana nema shine yanzu Allah Ya amsa addu'ar sa yabashi ake kokarin , za'a zubar ......
.da kyar yasamu ya tattaro dan abinda yake son ce mata .
Karki damu tunda har nace zan taimaka miki zanyi ne . sai dai mu bari muga zuwan doctor .. Nagode.. Nagode.. Nagode..deeni bazan taba manta taimakonka gareni ba ,ta sake fashewa da wani matsanancin kukan ..
Cike da sanyin jiki da tausayin kanshi ya Zare hannuwanshi dake 'cikin nata ya Ciro daya Daga 'cikin wayoyinsa ya turawa doctor saira sakon test ..kana ya janyota jikinshi ya rungumeta tsam yana shafa bayanta kusan minti biyu suka dauka ahaka sannan ya dagota cike da kulawa da tausayawa ya tsura mata rikitattun idanunshi is Ok kukan ya isa hk kinji.
" ta daga masa kanta kawai tare da cigaba da kukanta domin ita kadai tasan irin radadin da zuciyata ke ji a game da 'cikin jikinta .
,ranshi a matukar bace yacigaba da kallon yadda take wani irin kuka Wanda yasan hkn zai iya shafar lafiyarta da dan dake cikinta .
"dan hk ya furzar da wani iska me gauraye da huci kana yace haba..meyasa kika fiyye fitina da wahala ne?
Nace miki kiyi shr hk zan San abin yi ko so kike nazare hannun 'cikin lamarin 'cikin jikinki ?
Tayi saurin girgirza masa kai.
Ok ki bar kukan nan hk bana son jin sautinsa kwata kwata .
,nan ta sake girgirza masa kai alamun taji .
Kina jin yunwa ?
Tana jin yunwar Amman ta girgirza masa kai alamun bata ji .
Byn kmr minti goma shabiyar sai Ga doctor saira tashigo office din hannuta rike da wasu file files tana yiwa nablah sannu da jiki .
, nablah ta daga shanyayyun idanunta Tana dubanta tare daga mata kanta alamun da sauki kana ta zarce zuwa mazauninta Tana jiran isowarsu
DEENI bai tsaya jiran saukowar nablah ba. Ya sanya mata hijab dinta ya nade hannun suit dinsa ya dauke cak.. ya rungumeta ajikinshi yana kallon 'cikin kwayar idanunta ji yayi tamkar ya tsotsi pinky lips dinta da suka sake yin ja .
, ahankali yakarasa Inda doctor take zaune ya zaunar Daita kan kujera yana sake gyara mata zaman hijab din kanta sannan shima ya zauna..
Yana maida hankalinsa sosai kan doctor saira .sai daya sauke naunauyen ajiyar zuciya sannan ya soma dacewa doctor wani taimako nake son kiyi min akan cikin jikin yarinyar nan dan Allah idan har zai yiwu Ina son a cire mata 'cikin jikinta ....
Doctor saira tayi shr Tana sauraronsa har sanda ya dasa ayar mgnrsa , sannan tace gsky mu hospital din nan bama abortion domin doka ce me karfi idan aka kama mutun da laifin aikata hakan.
nablah najin hk ta zamo kasa da sauri Tana marairaice fuska da murya ,yayinda hawayen dake makale a idanunta suka soma ambaliya suna tureneniyya gurin fitowa ta hade hannuwanta duka guri daya tasoma rokon doctor
,dan girman Allah doctor ki taima min ki cire min 'cikin jikina, dan girman mahammadu rasulillahi s.a.w ki agazawa rayuwata ki rabani dashi , idan ba hk ba wlh mahaifina zai kashe Ni takarasa fadar hk Tana sakin wani irin kuka me sotsa rai gefe daya km jikinta ya sake daukar kirrrrrrma tasoma rarrafowa Inda doctor ke Zaune.
A dan hassale DEENI yace wai meyye hk kike yi ?
bakiga magana Mukeyi daita ba ta yadda za'a rabaki da 'cikin jikinki ba. wlh idan kikasa wasa sai kin haifi 'cikin jikinki da izinin Allah.
ta juyo da sauri ta rarrafo zuwa gurinsa ,tana kuka dan girman Allah kada kamin hk DEENI.... karigada kayi Niyya taimaka min dan girman Allah kada kafasa ..
To wlh Inda har kina bukatar taimakona
to ki natsu kibar kukan nan hk tun ban hassala dake ba, Na canza ra'ayina ba ,tasa byn hanunta da sauri tashiga goge Hawayen dake siyaya a idanunta .. kayi hakuri gashi Ina gogewa .
To ki natsu sosai dan Ina bukatar natsuwarki a halin yanzu ta Mike ahankali Tana kakkabe jikinta da sake gyara zaman hijab din jikinta..kana tace zan natsu kaji ..gabadaya ta gigice ta rude , ba DEENI ba" hatta doctor saira sai da tausayin yarinyar ya dinga ratsa jinin jikinta .
DEENI ya maida hankalinsa sosai kan doctor saira tare da ce mata doctor ki taimaka please kisan yadda zakiyi ki rabata da 'cikin jikinta Doctor tace Ok shikennan zan taimaka.
nablah tayi saurin cewa yauwa doctor Nagode sosai Allah Yasa kifi wannan matsayin . Doctor saira bata bi takan nablah ba tacigaba da mgnr dan ta lura yarinyar bata 'cikin sense dinta.
ta Mike tsaye tashiga wani daki a duk acikin office dinta taje tattaro duk wasu abinda tasan ana amfani dashi gurin abortion tazo ta zubesu gaban nablah.
tace yanzu dai zabi ya rage naki ,kinga wayannan abubuwa ?
nablah tashiga duban abinda ta zubesu gabata tare da dagawa doctor kanta , sizos ne zube 'cikin wani dan madaidaicin tire da wasu karafe birjik . Doctor tace kinga wayannan abubuwa to dashi ake cire ciki .
idan kin amince za'a cire miki ,Amman 'cikin dayan biyu ,rayuwa ko mutuwa wane kika zaba ?
. nablah tayi shr kawai Tana tunanin abinda zata zaba yayinda gefe daya km dade ya rufe DEENI zuciyar deeni tunaninsa ko taji tsoro ne yasa yaji tayi shr Amman Ga mamakinsa sai ya tsinci sautin muryata 'cikin dodon kunnenshi muryarta cike da kuka tace ,bbu komai doctor nazabi kowane daga ciki Ni dai burina Bai wuce kicire min wannan 'cikin ba .
doctor tayi shr tana dubanta hade da nazarinta. DEENI ya dinga aikawa nablah da wani irin kallo me cike wahalar fassarawa kallon mara hankali yake mata .
a fusace yace doctor bada wannan a sake samo wata dabarar yi.
ita km nablah ce take doctor ki taimaka please ... Ke kiyiwa mutane shr da bazan 'bakin nan naki duk kinbi kin cikawa mutane kunne .
Doctor ki taimaka iya abinda yace kennan yayi shr tare da xubawa nablah idanunsa .
,take km wani dabara yaxo ma doctor saira
Tace kada kadamu zan taimaka mata akwai wasu kwayoyin da za'a iya mata amfani dashi yanzu Wanda zai saka 'cikin ya hade guri daya zuwa