Showing 39001 words to 42000 words out of 95666 words

Chapter 14 - MASIFAR SO COMPLETE BOOK by Rahamat Muhammad .pdf

11 Mar 2025

7218

me tattare da tausayi

Yace toh yanxu mubar musu gidansu dan banaso na ha'du da kowa acikin Su.....
Dan xuciyata namin xafi ganina suncutar min da mata daga jiya xuwa yanxu
Tace to bara imma XARAH sallama da ha'do kayana sai kawai mutafi
Yace mekike nufi
Kina nufin kiqara shiga cikin gidan nan
Saiya girgixa kai alamar inaaaaa
Yace kin barsu kenan har sai igiyar aurena tahau kanki
Taturo baki Tace nabarta fah tana kuka
Yace Allah yasa kukan mutuwa takeyi
Baxakije gareta bah mijinta ya lallasheta

Gya'dakai tayi kawai yajata suka shige motarsa ya ficce daga gidan

Shuru bame magana acikinsu dan dukkansu da abinda suke kissimawa aranshi. Ita dai
LABEEBAH tasaka aranta koxata mutu baxata auri KAMAL ba
Duk da MASEEFAR SOON da take masa

Yayinda xuciyar YUSUF take kukan yanda akayi Yayan nasa ya ankare da lamarin LABEEBAH
Sannan xuciyar tashi tacika da tsoransa dan yasan yayan nasa sarai kan abinda yakeso
Sam idan Yace yanasan abu tokomiye xaiyi dan yasami wannan abun
Idan kuma yaqi abu tabbas yaqishi har abada
Yanada wasu baiwa Wanda idan ya tunkari abinda yakeso todole wannan abunma yasoshi.

Shiyasa yake katange LABEEBAH dashi
Yasani yayan nashi aikata abu yake abaiyane Sannan baya tsoran takwabe
muddun abin nan bai sa6ama shari'a bah sai yasan yanda yayi yamishi abin

YUSUF ya shafa kansa da sauke ajiyar xuciya yanasan ya ka'daice yayi kuka kuxai samu 'dan
nutsuwa a xuciyarsa.
Shidai Yana MASEEFAR SOON LABEEBAH kuma Yana ji aransa idan ya rasata mutuwa kawai
xaiyi
Dan tatara duk wani Abu da namiji akeso agun mace LABEEBAH ta ha'du yakar ha'duwa

Direct gidansa na wuse two and utako
Yayi
Gidan me bala'in kyau da tsari kamar na XARAH
Yace nutsuwata ga toilet nan kishiga kiyi wanka bari naje nanemo miki abinda xakici ko
Tace toh idan naci saimu tafiko
Yace baxan maidake gidan Momy yanxu bah sai magrib kannan fuskarki tasauka dan kar Momy
taxargi wani kingane ai
Ta'daga mai kai
Yace natuna akwai wasu riguna biyu da muka manta jiya amota bari na'dauko mikisu Tace toh
Tana tsaye anan yakawo mata Sannan ya futa

Wanka tayi tashafah mai da saka turare Sannan tasaka 'daya daga cikin dogayan rigunan daya
bata yanxu
Tayane kanta da 'dankwalin rigar
Tayi kyau sosai tafitoh falo tana jiransa

Bata wani da'de da xama bah yashigo. Tsayawa yayi yana kallanta kawai dan inda ace Matarsa
CE ba makawa shiyasan irin tarbar da xai mata
Yayi gyaran murya dan ya lura tashiga tunani
Ta kalleshi da sakarmai Murmushi Tace kadawo Yace nadawo nutsuwata kinga yanda kikayi
kyau kuwa
Tace kaima kayi kyau sosai
Yace toh gashi saiki gyara nabaki
Tace hmm xanci da Kaina ya kalleta ka'dan Yace baxan iya barinki kici da kanki bah gyara plx
nabaki
Tako matsu kusa dashi yadinga bata tanaci tana xubamai qaramar shagwa6a. Shi kuma yana
qara jin tausayinta da santa

Sanda ya tabbatar da taqoshi Sannan yabarta. Tace tokaima tsaya nabaka
Yabi bakinta da kallo abin sha'awa dashi me santsi da laushi ya gya'da mata kai. Tadinga Bashi
Suna hirar soyayya lokaci lokaci
Ahaka suka gama
Yace toh xanje Nadawo plx kikula da kanki
Tace. Toh Amma kakiramin XARAH

Ya ta6e baki yaxanyi dake. Ya fa'da yana me danna numbar XARAN
Tace mexance mata
Shuru yamata
Can XARAH ta'dauka
Yace matar yayana Tace na'am katafimin da LABEEBAH ko Yace Ashe kin gammu
Tace eh futanku nagani
Yace gani da nutsuwata ina tattalinta da lallashinta haka kawai kun burkitamin ita dan
mugunta.......

Sauke ajiyar xuciya XARAH tayi Tace dan Allah kabani ita inasanjin muryarta ko hankalina xai
kwanta Wlhi tashiga tashin hankalin da niban shigaba

Yace naqi bayarwan dama nakira ne dan kisan muna tare kuma xanturo Sagna ta tattara
kayanta dana Sumayya gobe tace xata tafi dan baxata iya jure tashin hankalinki bah
Tace dan Allah Yayah YUSUF dan Annabi kabata wayan kaji dan Allah
Yace kinci sa'a gata kuma kikayi wani abunda xaisamin ita kuka Wlhi saidai kijita a Kano dan
sallama awaya mah baxaki jita bah

Tace naji bata
Yamiqama LABEEBAH Tace XARAH
Sauke ajiyar xuciya XARAH tayi Tace haqiqa 'Yar uwata ina MASEEFAR SOON Ki
Kishare batun 'daxo dan nayi tunanin kona gaxa tawani gunne yasashi San qara Aure na yima
kaina alqawarin xagewa takowane fanni in faranta mishi dan inmantar dashi ita
Inasan Mijina kuma xanso naga wacce yakeso inga abinda yagani agareta Wanda bandashi
Ina SON KAMAL LABEEBAH dan yatara abubuwa daba duk namijiba yayi takota ina inasan shi
ina kishinsa plx kitayani da addu'ar Allah ya karkatomin da hankalinsa kaina

Sannan ina rokwanki dakarki tafi gobe
Inaso muqara ha'duwa ko tayayane

Hawaye ya xubuma LABEEBAH YUSUF yamatsa kusa da ita Yana goge mata
Taqer LABEEBAH ta iya CE mata toh jibi ma tafi
XARAH Tace Yauwa ki kwantar da hankalinku fah Tace toh Karki damu......
Sai XARAH takashe wayan

Plx nutsuwata kisoni Ki qaunace danni mesanki
Na miki alqawarin baxaki ta6a Allah wadai dani bah.
Xan baki farin ciki Wanda xai baki mamaki
Kina sona
Takama hannunsa ta sumbata Tace inasan ka kuma kai xan aura
Murmushi yayi Yace toh xumu fitta muxaga gidan ko
Tace toh
Haka yakama hannunta suka fito daga falan

Fasa futar yayi yanemi duk wani abu da yasan xaiyi dan yaga dariyar LABEEBAH shi yadinga
cakalowa
Har ita kanta tagano yanasan tasake tamanta abunda yafaru.
Dan haka sata sake ka'dan


KAMAL ko Yana xuwa office 'dansa ya dasa tunanin LABEEBAH aransa
Duba mutane kawai yakeyi Amma kowa ya duba saiyaga mutanan suna juyemai da kamar
LABEEBAH dan haka yace bayajin da'di duk wanda yaxo nemansa yayi hakuri

toh yanxu haka yayi nisa Cikin tunani Auwal yashigo office 'din nashi da sallama Amma ko kusa
KAMAL baisan da shigowarsa ba
sanda yata6a shi Sannan ya ankare dashi
Auwal Yace meyake dumunka KAMAL kashiga dogwon tunani haka
Kai tsaye Yace mai MASEEFAR SOO.......

MASEEFAR SOO Auwal
SOO maseefane SOO damuwane SOO ba da'di bane SOO
Tun farkwan ganina da ita xuciyata tacika da bugawa.
dan kowane kallo namata bugawa takeyi har gobe
Natattara duk tunanina nagane yanda nakeji haka takeji itama
Na kamu da MASEEFAR SONTA akwana 'daya
baxan ta6a rabuwa da itabah dan saina Aureta

Tana MASEEFAR SONAH Amma nawa MASEEFAR SOON yafi natah
Wlhi Wlhi Wlhi Auwal idan nabarta ina tabbatar maka ba wata mace da xataji 'da'dina ina
tabbatar maka ba wata mace daxanso ina tabbatar maka na ture babun Aure arayuwata dan
Itace macen da nake so
itace macan da nake qaunah
Itace idan naji kukanta hankalina yake tashi
itace wacce Komai nata yayimin arayuwa.........

Auwal ya katse shi da cewa wacece wannan yarinyar da burkitaka haka
KAMAL yajah numfashi da tashi ya juyama Auwal baya Yace Aisha-Labibah.....
Aburkice Auwal Yace wacce nasaki 'Yar Uwar XARAH
Ya juyo yace eh ita
itace

Cikin sauri Auwal Yace kuttumar uba


KAMAL ya kallesa Yace kafa'di abinda yafi xagi
Wlhi Auwal bazan ta6a barinta bah

Auwal ya sauke ajiyar xuciya Yace bai dace kaso LABEEBAH bah. Bai kamata bah. Koka
manta yanda suke ne in fa'dama........

KAMAL ya katse shi da cewa bam manta ba
Fatima-zarah da Aisha-Labibah yaran da suka tashi da tamkar ciki 'daya suka fitoh dan
shakuwa yaran da sukesan junansu
Ko ba haka kake san tunatar dani bah. Ya qarashe da kallansa

Auwal Yace hakane Amma Kasan da hakan kakesan raba soyayyarsu. Kasan kishi kuwa
Yace koma dai miye ba kishiba nifah saina auri LABEEBAH. Dan inasanta ina qaunarta ji nake
kamar in kashe kaina akan santa
Jinake kamar na cutar da ita
Meyasa ban gane tana sonah bah
Meyasa da natashi santa nafa'da tarkwan MASEEFAR SOO.
Sam xuciyata taqimin da'di
hankalina yakasa kwanciya
qanqar jinkina yana san ya kasamce da ita

Dama dama dama.
Dama itace XARAH da yanxu take matsayin matata nasan da xan samu nutsuwa
Auwal Yace kadan ne xuciyarka KAMAL karkaxo kayi abunda xai dameku gabaki 'daya
Yace laveeva tarigaka fa'din haka.
Plx kaidai kasani a addu'a dan ina cikin wani hali plx

Tausayinsa Yakama Auwal tabbas ya hango damuwa da tashin hankali agun KAMAL Wanda
baita6a ganinsa cikin hakan bah
Yace toh Allah ya fitar dakai
Yace AmEEn nagode
Nan dai suka ta6a hira wacce duk rabinta hankalin KAMAL nagun LABEEBAH
Yace xanje gida kawai Auwal dan samun nutsuwar xuciyata shine ganin LABEEBAH duk da
nasan yanxu bata gidana

Auwal Yace toh ba matsala Allah dai ya fiddakai daga MASEEFAR SOO



XARAH na kitchen tana ha'da abincin dare kawai taji dirar motarsa. Gabanta yafa'da
Tanaji yayi 'dakinsa ba kamar yanda yasaba idan ya dawo yabi ta kanta bah

Itama batabi takansa bah.
Taqarashe Komai nata Sannan tajera Komai a dining
Taje tayi wanka tasaka qananun kaya wanda suka amsheta da feshe jikinta da turare Sannan ta
nufi 'dakin nasa.
Da sallama tashiga Yana kan gado Yana danna laptop ta xauna gyefansa Tace sannu da

dawowa my luv
Ya 'dauke kansa daga kan laptop 'din yaxuba mata ido
Anan ya 'danga ta'dan xube ka'dan ( *toh kishi wasa ne*)
Saiya ji tausayinta ya kamashi dan koba komai yana santa. Saidai shikansa baisan ya akayi
MASEEFAR SON LABEEBAH tamishi illa haka bah daga kwana 'daya duk tabi ta rikitashi ta
hargitsa tunaninsa ta jefashi cikin damuwa
Wlhi shi yanxu tausayin kansa yakeji bayajin tausayin kowa sai nasa

Bai ankareba yaga hawaye nabin kuncinta Tace dame narageka my luv
Atunanina duk wani Abu da mace take yima mijinta ina yimaka
Meyasa zaka tarwatsa farin cikina da min kishiya ko shekara bamuyi ba
Bakayi tunanin mutane xasu xargeni bah
Meyasa wannan sauyin yaxomin cikin lokaci qanqani
Saita fashe da kuka ha'de da durqusawa agaban gadan Tace ina rokwanka da Allah kabani
wani lokaci xanxage dantse in baka duk wani farin cikin da kake nema.

In yace baiji tausayin XARAH ba yayi qarya
In yace xuciyarsa batayi rawaba yayi qarya
Amme yafijin tausayin kansa fiye da ita da LABEEBAH

Tashi yayi ya 'dagota tare da xaunar da ita kan jiyarsa Yace banasan in yaudareki XARAH
Ina sanki Sannan xuciyata takamu da Santa
Na miki alqawarin baxaki sami matsala da nibah inhar kika fahimceni
Plx kimin rai ki namince min Auranta dan Allah

Na shiga uku ni XARAH idan ka Aureta baxa kamin adalci bah dan tun yanxu nagano soyayyar
da kake mata ta danne tawa. Bansan ya akayi xuciyata tanarke da MASEEFAR SONKA bah
Kayi tako ta ina kowace mace xataso mallakarka amatsayin mijinta
Katemaken xuciyata dan tanamin xafi hankalina na tashi da xaran na hangoka da wata mace.
Plx katemaken kabani lokaci Wlhi Xanyi duk wani qoqari dan mantar da kai wata *'YA MACE*
Taqarashe da rushewa da kuka
Rungumarta yayi shima hawayan yaxubu mishi Yace am sorry najiki xanyi qoqari inga koxan iya
barinta Amma gaskiya TEEMAH da kamar wiya............




YUSUF da LABEEBAH ko sai kusan biyar suka yi gidan Momy
Zuwa lokacin LABEEBAH tasake dan kam YUSUF yayi qoqari wajan sata farin ciki
Anan taga kayanta dana Sumayya da sagna ta 'dauko a gidan XARAH



Can wajan qarfe 8:00pm na dare KAMAL ya shigo gidan direct 'dakin Momy yayi

Nan yaganta da Safna Suna linke wasu sababbin Kaya Momy nace mata maxa jeki kiramin
LABEEBAH Tace toh xata fita
tagai sheshi ya amsa cikin kulawa Sannan ya gaida Momy
Taxumai ido dan ganin yanda yaxama wani iri bayi da maraba da mara lafiya
Cikin tashin hankali Tace mexan gani haka KAMAL meya sameka meyake damunka kaga inda
kaxube kuwa........
LABEEBAH CE ta shigo da sallama idanta ya sauka akan KAMAL gabanta yafa'di.
Momy ta'amsa sallamarta KAMAL ko Sam baiyi gigin kallanta bah
Ya kalli Momy Yace ba wani abunda yake damuna Momy sai soyayya. Na kamu da Santa
Momy plx inasan inqara Aure.........

Wiwi wiwi wiwi LABEEBAH tarushe musu kuka Wanda duk Wanda yaji kukan toko xai gane
bana shiri bane

Dukkansu suka xuba mata ido na wani lokaci candai Momy takamo hannunta tana cewa
menene AISHA meke kuma ya sameki
[1:50PM, 28/09/2016] Rahamat Nalele💋: Tace dan Allah dan Annabi Momy ki roqeshi yabar
XARAH ita ka'dai
Tana sanshi akanme xai tarwatsa mata farin cikinta dan Allah Momy Karki bari ya mata kishiya
plxx momyna

Momy tayi Murmushi dan tahango tsoro qarara a idan LABEEBAN kuma tagane tana taya 'Yar
uwarta kishine

(Hmm Momy kenan LABEEBAH takanta take)

Tace kwantar da hankalinki ba zai mata kishiya bah
KAMAL Yace karki mata haka Momy. Dan Ki kwantar mata da hankali kigaya mata kawai dan
nidai Aure ba fashi

Momy ta harareshi Sannan tamaida kallanta kan LABEEBAH data qara volume 'din kukanta
Tace kidena kuka maxa share hawayanki baxai qara auran bah kinji
Ta 'daga mata kai alamar taji
Sannan Momy ta nuna mata wasu Kaya Tace maxa 'dauka nakine wannan wancan na
Sumayya jeki jerasu a akwatin naku
Tace toh Allah amfana takwashe tafuta

Sumayya takaima kayan Sannan takoma falo tana jiran fitowar KAMAL dan tabashi hakuri ya
barta

Momy takalli KAMAL Tace kaiko wace irin soyayyace wacce xata sakaka qara Aure nan kusa
Yace hmm Momy kenan Kinsan abinda ake kira MASEEFAR SOO
Tace eh kai
Yace toh Wlhi ni tawa maseefar tafi ta MASEEFAR SOO

Tace innalillahi garin yayah kabari wannan MASEEFAR ta kusantoka
Yace nima bansani bah Momy
Kwanciyar hankalina shine in sameta in Aureta shine farin cikin ruhina.....
Momy taja numfashi Tace YUSUF Yana cikin damuwa namishi tambayar duniya yaqi cemin
Komai kasan shi da xurfin ciki
Gashi kai kaxo da MASEEFAR San wata
Shin wai ya kukesan nayi da raina ne. So kuke damuwa ta illatamin ku. Yaxanyi ne
Addu'a
KAMAL yabata amsa kai tsaye tayi shuru candai takama hannunsa tace katemaken ka
kwantar da hankalinka KAMAL dan nasanka baka iya shiga tashin hankali ba dan Allah kamin
rai nasami nutsuwa ko daga garekane
Tausayin mahaifiyar tashi ya kamashi nan Yace toh naji Momy Amma gaskiya samun AISHA
shine samun farin cikina shine kuma samun nutsuwata
Tace sunanta kenan. Yace eh
Tace toh kabani lokaci inyi tunani sannan gobe kakawomin XARAH
Yace toh da miqewa
Harya kai 'kofah Tace kaje part 'din YUSUF ka kiramin shi
toh Yace mata ya fitta
Afalo ko yaci karo da LABEEBAH sai kaiwa da kawowa take tana hawaye
Wucceta kawai yayi
Yayi shishin YUSUF
Aiko tabi bayansa tana mai kuka.
A falan YUSUF suka yada xango tsabar jin yanda kukan nata yake mishi xafi aransa yama
manta YUSUF yaxo kirama Momy
Sai kawai yaxauna kan kujera

Aiko LABEEBAH tamai xaman dirshan agaba ta tankwashe 'kafah tabu'de mai shafin kuka

Gefah guda YUSUF na kwance kan kujera tunanin LABEEBAH da Yayan nashi yake yaxaiyi
dasu
Sai kuma yagansu yanxu yako xuba musu
yanda ya fuskanta sam basu mah lura da shiba

(wai ance hankali shike gani. Toh na KAMAL da LABEEBAH yatafi jos gun Mrs Rufa'i dan
takawo musu agaji

Xuba mata ido kawai KAMAL yayi axa hiri kallanta yake aba'dini kuma tausayin kansa yake dan
shi yama tafi duniyar tunanin ganinsa da ita amatsayin ma'aurata

Qarama kukan nata da tayi volume ne yasashi ankarewa da itafah 😳

Yace dan Allah dan Annabi Baby kibarni naji da MASEEFAR SONKi da kika jaxamin kibarni
haka kukanki bala'i yake qaramin
Cikin kukan tace dan Allah kajanye soyayyarka gareni XARAH tayi tako ta ina kajuye wannan

soyayyar kaqara akantata
Ina San 'Yar uwata dan Allah karka tarwasa mata farin cikinta
Yace Wlhi baxan barkiba baby
Taqara rushewa da kuka Tace bana sanka dan akwai wanda nakeso yanxu shi kuma xan aura

Yace ai habah yaushe kika fara sanshi
Tace Dada 'dewa mana. Ni dai baxan aureka ba
Duk da KAMAL Yana cikin wani hali hakan bai hanashi yin Murmushi ba
Yace kinyi kuskura sona da kika farayi

Baby naganki da yarana cikin mafarkina.
kina nufin atiti xaki haifamin Su ba tare da Aure bah
Takalle shi afurgice taqara rushewa da kuka
Tace ai mafarki ba gaskiya bane
Kuma ba Ni ka gani bah XARAH kagani
Kama hannunta yayi Yace Wlhi kice Babyna plx Ki fahimceni mugina wata rayuwa me da'di da
santsi da gar'di
Nasan xaki bu'de mana wannan rayuwar muyita cikin kwanciyar hankali
Cikin kuka shgwa6a ha'di da harararsa Tace bana sanka nacema ko
Yasaki hannunta ya kama fuskarta ya fara lashe hawayanta Yana cewa ni inasanki nagaya miki
ko. Yafa'da yaname kwaikwayan muryarta
Tana hawayan yana lashewa. Nashi hawayan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login