Showing 12001 words to 15000 words out of 95666 words

Chapter 5 - MASIFAR SO COMPLETE BOOK by Rahamat Muhammad .pdf

11 Mar 2025

7227

'dinta yanxu
dai-dai kofar gidan nasu......
KAMAL Yace gud qanwata yanxu ke my luv saiki sakemin Mara inyi futsari tunda wacce kikayi
furucin dominta tabaki dama.

Cikin yanayin tausayin LABEEBAH
XARAH Tace shikenan Allah ya tabbatar da alkairi
Dai-dai nan LABEEBAH tasaka kanta Cikin gidansu xuciyarta na bugawa


Tana shiga taci karo da mamah. Cike da mamaki mamah tasaki kayan hannunta tarungumeta
Tace yanxu muke shirin tahowa da innanku ashe jikin da sauqi ke dawa kuka tawo
Cikin shagwa6a LABEEBAH Tace naji Sauqi dan farkawa nayi kawai najini garau. Nida XARAH
da KAMAL ne
Cikin farin ciki mamah tajata xuwa 'daki sun xauna kenan Innah tashigo da farin ciki
Tace eh gaskiyane jiki yayi kyau. Mamah Tace kinganta nan muna qoqarin xuwa saigasu
Tace aikowa jiki yayi kyau kome suka bata oho......
XARAH CE tashigo da magunguna ahannunta Tace gashi injishi wai dan Allah kidaure kisha
zakiga Komai arubuce
Tace toh takar6a
Mamah Tace Allah ya saka mishi da alkairi. Duk sukace AmEEn

Kwana biyu ta warware dan kam batayi sawa dashan magungunan bah


Mustafah Yaxo ga LABEEBAH da gaskiyar xan cansa nasan Auranta
Amma tarufe ido Tace bata san shi.
Abinda ya baqanta ran XARAH kenan har tace ixuwa yanxu nafara tsanar KAMAL 'dinnan ke
nama tsaneshi
Cikin 6acin ran meyasa xatace tatsaneshi LABEEBAH Tace dama kindena dan abin sanki ne

KAMAL ya turo da magabatansa ga Mahaifin XARAH kuma sunyi bincike sun tabbatar KAMAL
daga gidan mutunci yafito
Dan haka take Su manyan suka bada sadaki da saka ranah nanda wata takwas. Asha biki


KAMAL da Auwal a kofar gidansu XARAH. Fa'di Auwal yake plx kakira 'daya daga cikinsu
mana lokaci na tafiya.
KAMAL yayi Murmushi toh agogo sarkin aiki. Inban mantaba yanxu muka dawo daga wajan
siya musu waya koka mantane
Auwal ya dafe goshi Yace ya Allah
Wlhi namanta shaff...
Bai qarasa furucinsa bah Su XARAH suka fitoh
Sunyi kyau sosai Cikin shigar dogayan riguna kamar kasacesu kagudu

_Zuciyar Auwal fa'di take sarki ya tabbata daga Allah yake LABEEBAH sarauniyar kyawawa.
shidai gani yake Aisha-Labibah tafi Fatima-zarah kyau Yayinda xuciyar KAMAL take qaryata
hakan danta shagaltu da soyayyar TEEMANSA_

Tatuqi yake Cikin gwanin cewa
Ga wayoyunku 'yan gatan KAMAL. Auwal yafa'di hakan da dariya
Suma dariyar sukayi
Wayoyin sunyi kyau duk *LG* ne kuma iri 'daya
Cikin farin ciki sukamai godiya Yace no karku damu
XARAH takashe mai ido 'daya da cewa
Kanaji damu my luv gaskiya inajin da'din hakan Allah yabarni da sahibina
Kunfi haka TEEMANAH kuma inbanji da kuba dawa xanji
Kinkasance masoyiyata abin alfaharina ina sanki TEEMAH plx kiqara sonah
Nayi rantsuwa xan soka har qarashen rayuwata Xan kyautata maka har sai kace ya'isa Xan
bika har qarshen numfashina. Amma inajin tsoron kar wata rana kaqini kaso wata ka
wulaqantani..........

Parking yayi a Cikin gidan kakarsa inda dama sunxo gaisheta ne
kallanta yayi Cikin kulawa tare da kafeta da wani mirgi 'dad'dan kallo Yace xuciyata tacika dam
da qaunarki. bawata *'YA* *MACE* daxanso bayanki
Karkiyi kokwanto balle shakka. kisaka axuciyarki narike miki alkawari dan Allah kiyarda dani
sannan kicire xargin... hakan axuciyarki
Itama Cikin nata kalan kallan takalleshi Tace karka damu ko 'daya baxargi acikin xuciyata.
nayarda dakai sosai

Da wani shegen kallo Yace Allah yabarni dake
Sam KAMAL-da XARAH sun manta da LABEEBAH da Auwal acikin motar sukaci gaba da hirar
soyayyarsu

Ixuwa lokacin ko LABEEBAH takai maqura dan haka batasan lokacin data da qarqare ba. Ta
fashe da kuka tana rayawa aranta KAMAL da XARAH xasu kasheta kwananta beqareba

Nan suka farga da inda suke. Cikin mamaki da Al'ajabi Su uku sukace lafiya LABEEBAH me ya
faru
Cikin kuka sosai ha'de da shagwa6a Tace kai... Nane.... Yake... Min ciwo.. Muyi sauri mukoma
gida

KAMAL ya kalli Auwal shima Auwal 'din kallansa yayi
Yace my TEEMAH haka MATAR KAMAL ta ke
XARAH tajah numfashi Tace hmm haka take da shegen shagwa6a musamman agun mamah
da innah. Kai ga kowama na gidanmu
Amma nalura ha'duwarta da KAMAL yaqara ta6ara mana ita
Auwal Yace ikwan Allah kenan. toh yi shuru yanxu xamu koma

Cikin wani yanayi KAMAL yamiqa mata hankicif Yace sorry ko. Ga wannan ki goge fiskarki
Kar6a tayi tagoge fuskar tata tana cewa a _axuciyarta ko Ba komai dai na katsemuku
soyayyarku 'yan rainin hankali_

Haka suka fitoh Suna mamakinta. Ga KAMAL ko jin shi yayi wani iri


Tsohuwace me kalar kamala da nutsuwa suka gani afalan tare da Momyn KAMAL har dasu 'yan
biyu wato Safna da Sagna

Da murna sosai kakah ta tarbi su XARAH Tace lale barhaban da xuwanku jikokina
Auwal yayi dariya Yace waya gaya miki anama kishiya lale mar haban
Tace um um Auwalu wannan nayi shekara da shekaru ina jiranta sai yau Allah yayi
Cikin ladabi XARAH da LABEEBAH suka xauna a qasa suka gaisheta
Ta amsa da farin ciki. Safna da Sagna suka gaishesu
Sannan suka gaida Momy
Cikin wani irin *SOO* da qauna ta amsa tana cewa Sannunku 'yan albarka gaskiya naji da'din
ganinku
Kakah Tace wacece kishiyar tawa. LABEEBAH tanuna XARAH
Momy Tace eh lallene sirikar tawa kyakkyawa CE
KAMAL Yace ai nagaya miki
Tayi Murmushi Tace ga 'Yar uwartama kyakkyawa
Yace hmm momy sai shagwa6a ta'ajiye
Tace ai da ganinta
Safna ce ta ajiye musu kayan marmari Sagna ta'ajiye abinci

Ganin kan XARAH aqasa yasa Safna Tace Aunty XARAH Ki 'dago kanki man naganki
Shuru tamata tana wasa da hanunta

Momy ta qurama LABEEBAH ido. haka kawai taji qaunarta nashigarta

KAMAL Yace yaushe kika xone Momy
Kakah Tace yan xun nan shigowarsu kenan sai gaku

Tashi Momy tayi. Tayi wani shashi na falan tana Murmushi xuciyarta cike da qaunarsu XARAH

Kakah tasake sai jansu take da hira LABEEBAH na biye mata
Al'amarin daya bah KAMAL da Auwal mamaki kenan ganin bata da'de da gama musu kukan
shagwa6a bah

Can sukace xasu tafi. Nan take fuskar kakah ta sauya
Auwal Yace Xan da'da dawo miki dasu Tace toh Allah yasa Yace AmEEn kakale

Safna tagayama Momy xasu tafi nan tafitoh hannunta 'dauke da kayan kwalliya taba Sagna
takai musu mota Sannan tamusu fatan alkairi
Kakah ko har Mota tarakasu tana samusu albarka. Suka tafi
Safna Tace kai Amma budurwar Ya KAMAL akwai kunya da kyau naji Santa Cikin raina da 'Yar
uwarta
Tsaki Sagna tajah Tace hmm Ni 'Yar uwarta tafimin kyau kuma nafi Santa
Safna Tace eh tanada kyau Amma shi XARAN yagani saikije kice ya canja da ita
Tace kinga malama ba magana nanema bah. fa'dar ra'ayinki kikayi. Nima nafa'di nawa wani
abune. Ta qarashe da mata kallan tuhuma.
Cikin takaici Safna tayi ciki batare da tace mata komai bah
Sagna tajah tsaki ha'da da kara wayarta akunnanta


Su XARAH ko suna xuwa gida LABEEBAH tayima kanta gata ta shige gida
Dan mutanan nata sunfara xaxxagama junansu kalaman *SOO*
Sai dai murnarta 'daya bataba KAMAL hankicif 'dinsa bah


Wannan dare baccin farin ciki LABEEBAH tayi
Dan kowane juyi tayi. To saita shaqi qamshin turaran dake jikin hankicif 'din KAMAL
Har washe gari XARAH Tace dama xaki tsaya ahaka mana
LABEEBAH Tace ban gane bah
Yanda kike Cikin farin Ciki yau dama kullun kike haka XARAH tace da ita hakan

Murmushi LABEEBAH tayi tace ba lefi nasamu wani abu na KAMAL wanda duk lokacin da naga
abun jinake tamkar ina tare dashi
Ta6e baki XARAH tayi Tace hmmm qarya Allah dai yakawo miki sauqi *a MASEEFAR
SOO.*
Cikin wani yanayi Tace nafa'da *MASEEFAR SOO*

Yaxanyi 'Yar uwata,
Xuciyata ta cuceni da taso wannan koda ya baiyana agareni baxan ta6a Auransa bah

Da nuna mamaki XARAH tadena game 'din da takeyi takalleta gami da cewa Me yasa.
Bayan kina sansa. Towaima me kenan kikayi
Ya baiyana agunki Amma kiqi auransa sabodame
_saboda ke. Xan'iya kishi da kowa Amma baxan iya dakeba. LABEEBAH tafa'di hakan aranta_
Afili ko cewa tayi. Haka kawai
Shuru XARAH tayi dan jinta kawai tayi


〰〰〰
Yau take jumma'a
Kuma yaune aka tashi ta tirqewar hadari a garin na kano
Tunda Allah ya wayi gari LABEEBAH take Cikin farin ciki dan sanda kowa yagane hakan
Dake yanxu 'yan gidan sunsa mata hawainiya me canja kala akowane lokaci shiyasa bawanda
ya tambayeta farin Cikin me takeyi

Itako yau tashi tayi da MASEEFAR SON ganin KAMAL
Sai xuciyarta tabata hakuri dan ganin gobene ranar xuwansa
Sumayya ce takasa hakuri Tace mamah nifa ina ganin dan Aunty LABEEBAH taga hadari ya
ha'dune shine take farin ciki
Da sauri mamah Tace kumafah gaskiyarki Sumayya
Dan gashi har tayi shirin tarbarsa
XARAH tayi dariya Tace Allah LABEEBAH yau Karki shiga ruwa kin manta shakaran jiya yanda
kika kwana hanci a tushe
Tace kudai kunkasa ganewa ne. dan ba'abinda yafi farin ciki kamar anayin ruwa mutum
yashiga yana juyi aciki.
Wow Wlhi ina tsintar Kaina cikin farin ciki. Kunga nayi kofar gida. Bata jira cewarsu bah tayi
kofar gida abinta

XARAH tagyara kwanciyarta tace da Sumayya yanxu ruwa xai tsinke
Tace aikowa dai

LABEEBAH na fitta taga wata lafiyai yiyar motar tayi faking a kofar gidansu
Tabbas gabanta yafa'di dan har tayi tunanin ko KAMAL ne
Tuni xuciyarta tabata bashi bane dan baicika xuwa awa'dannan ranakun bah
Gilashin motar me duhune dan haka bata gane wanda yake ciki bah

Shaaaaaaaaaaaaaaa
Ruwan sama ya yanke kamar da bakin kwarya
Ai tuni LABEEBAH tayi 'dan kwanan da take tsayawa idan hakan tafaru
Ruwa ne ake zab gawa sosai
Yanda yake sauka a qasa haka yake sauka akan LABEEBAH

Sai tsalle take tana murna tana 'daga kai sama tare da lumshe ido tana Murmushi
Lokaci lokaci kuma take 'dan juyi
Kallo 'daya xaka mata kagane tana Cikin farin ciki

Mamaki da Al'ajabi gami da Takaici suka cika KAMAL
Dama shine a motar. Kuma tunda aka fara ruwan idanshi yake kanta
Eh tabashi sha'awa
Amma shi mutum ne mesan yaga mutum na tattalin kansa. Kodan gujema kamuwa da ciwuka
Shuru yayi yana naxarinta. Watoh itadai Sam bata da damuwa. yarinta na damunta. bata da
matsala

Zuwa can cak ruwan ya 'dauke
Aiko taturo baki irin bataso haka bah
Yaxatayi dole tafitoh daga gun daniyar shiga gida
Xuge gilashin motar yayi. Yace Laveeba.......
Tun daga tsikiyar kanta taji wani xirrrrr har xuwa babban 'danya tsanta na qafah jitayi wani sanyi
ya shigeta ha'de da birki cewa
Ya lura da birkicewarta
Ta juyo ahankali. Karaf suka ha'da ido. Ya ko dallah mata harara. Tayi saurin sun kwiyar da
kanta
Zonan Yace da ita
Ahankali taje gunsan jiki shaqaf
Yace bakyasan lafiyarki ne
Ta girgixamai kai. Alamar aa
Baki da bakine
Takalleshi tare da qara girgixamai kai
Cikin fusata Yace baxakiyi magana bah
Cikin sanyi ha'de da nuna tsuro tace xanyi fah
Yaqara galla mata harara Yace xan qara ganinki ne
Taturo baki Tace waitoh menayi
Quqarin bu'de motar yakeyi dan fitowa
Aiko tafalle da gudu tashige gida
Abin yabashi dariya
Abaiyane Yace wannan mijinki yanada aiki

In kaine yaxakayi
Xuciyarshi tatambayeshi
Innine maqure xan dinga yi. inyi maganin shagwa6arta.......
Da sauri yayima kansa dariya ha'de da cewa abaiyane. Toh bama nibane.
Tanada aibine
Xuciyarshi taqara tambayarshi
aa
Yabata amsa still abaiyane

Mamakin kansa yafarayi ganin xuciyarshi na mishi wasu tambayoyo masu kama da Wanda
yakesan fa'dawa wani yanayi
Na me kenan
Na SOO
Xuciyar tabashi amsa da sauri
Ga bansane ya bala'in fa'duwa.
Yayinda yayi saurin kawar da tunanin Yana murmushin tsoro
Fatima-zarah & Aisha-Labibah
Yace abaiyane
Tuni yakori tunanin xuciyarsa ya 'dauko soyayyar TEEMAN Sa yasaka agaba hankalinsa
kwance


Kun gani ko taje ta jiqe shaqaf. Cewar Sumayya
Mamah ta galla mata harara Tace Naji kince min kanki namiki ciwo ko mura na damunki
XARAH ma harararta tayi taqara da cewa kokuma ta'ishe mutane da jan hanci bah

Shuru ta musu dan jikinta ya mutu mu'dus ba abinda takeso ayanxu kamar taka'daice tayi
tunanin masoyin nata KAMAL

Ana kiranki awajefah tafurtama XARAH hakan kamar xata fashe dakuka
Sumayya tayi dariya Tace dan an'dauke ruwanne kikesan kiyi kuka
Ta harareta Tace ban saniba
Wa yake kira na
KAMAL tabata amsa Cikin sauri
Kan XARAH taqara magana wayanta ya 'dau ruri
My luv ganinan gareka masoyinah
Haka kawai Tace Tatashi ta ficce
LABEEBAH ta shige 'dakin mamah tana xubar da hawaye
Wane irin soh nake maka KAMAL
Duk lokacin dana ganka saika sani kuka ha'de da burkitani
Take fa'dar hakan axuciyarta
Wayarta ce tafara ringing tana 'dagawa taga KAMAL ne
Nan take mamaki ya kamata. Ta'dauka
Kitemaka kiyi gaggawar canjah kaya dan Allah Yace da ita hakan
Murmushi tayi Tace toh
Yace ban jiba
Tace cewa nayi toh

Kashe wayar KAMAL yayi yamaida kallansa kan XARAH asanyaye
Ya rasa dalilin dayasa yake bala'in jin da'din muryar LABEEBAH
Ashe awayama tana da'di haka
Kaji shuru my Luv kana kallona kamar ka shiga tunani
Yayi saurin kawar da kansa Yace kyanki nake wara gani Wanda yake hanani bacci maye

sirrinne
Tayi dariyar jin da'di Tace bawani Sirri my luv
Yace da gaske yanxu LABEEBA baxata canjah kayan jikinta yanxu bah
Tace karka damu tasaba Amma tunda kamata magana xata canjah
Yace kice inada darajah sosai haka
Tace kaima kamanta ne. sunanka 'dayafah da KAMAL 'dinta. Ai ina ganin idan aka cire
iyayanmu xakafi kowa daraja a idanta
Yayi Murmushi


Xuciya da abinda takeso ai ko minti 'daya LABEEBAH bata qaraba ta canja kayan jikinta tana
'dan Murmushi dan kulawar da KAMAL yabata tamata da'di hakan ne ya kori kukan da takeyi











MASEEFAR SOO
〰〰〰〰〰〰
Rayuwa kenan
Yau taxo maka da da'di gobe taxo maka sa6anin hakan
Haka watanni suka shu'de masu XARAH da KAMAL & LABEEBAH

Toh yau Allah yayi saura sati biyu bikin XARAH-da-KAMAL
Tun yanxu suka cika da shagalul lukan biki

'Din kunane baje akan gadan Innah na XARAH da LABEEBAH Wanda KAMAL yakawo musu
Ko wacce kala goma goma

Shiri suke dan tafiya sweet-faty
Sanyi kyau sosai Cikin shigarsu ta doguwar Riga ta materiyal jah me ratsin ash Colo sunyi kyau
sosai
dan kam kallo 'daya xakama shigarsu kagane sunyi shigar alfarma dan tsadar kayan
Aikin KAMAL ne

Qawayansu na islamiya dana skull ne sunkai Su ashirin kuma kowacce tayi shiga takerema sa'a

Jamila 'daya daga cikinsuTace kai habah LABEEBAH lokaci na tafiya yaushe kukaje make-up

kuka dawo har mutafi

Au namanta anqara awa 'daya ban fa'damiki ba. LABEEBAH tace da ita hakan

Sumayya Tace kunga kutashi mufara gaba tunda dama daga canne xasu hucce
Sukace toh sukayi can

Su XARAH na fitowa Auwal Yace 'yan gatanka sunfito
Cikin sauri yakai kallansa Kan XARAH nanko suka ha'da ido tasakarmai Murmushi
Yace wow. Kyau haka tunkan ayi make-up ya dire kallan nashi akan LABEEBAH
Wacce tunfarko tayi qasa da kanta tana wasa da xoban hannunta
Tace toh munji. Yanxu dai muje mutane sunfara qorafi
Yace aikowa dan muma yanxu muka gama bada hakuri dan haka ku shiga da sauri


Hiyana make-up beauty sukaje
Nan tagyara amarya XARAH tsaf ha'de da LABEEBAH
Duk iya hangenka qaryane kagane wacece amarya tsakanin XARAH da LABEEBAH
Tun amota KAMAL yaketa satar kallansu
Wani abokinsa Jameel Yace dan Allah XARAH kiban 'yar uwan nan taki plx dan Allah
Tace wa ni😳
Rabani da LABEEBAH karkasa saidai inga tana yima wasu dariya bani
Da mamaki Yace ban gane bah
Shuru tamishi
Yayinda LABEEBAH tayi fuska kamar ba akanta ake maganar bah
Jameel ya maida kallansa kan KAMAL kamar xaiyi kuka Yace tayimin shuru
KAMAL yayi Murmushi yace wacce acikinsu
Yace XARAH da ita 'din mana
KAMAL Yace hmm. ai indai MATAR KAMAL CE baxaka ta6ajin ta bakinta bah
My XARAH ko bata da abin cewane shiyasa yin shuru
Cikin sauri yace MATAR KAMAL. Kana nufin ita'din matar Aure ce. kuma mijinta ya barta haka
KAMAL Yace aa fah. Ba haka nake nufiba
Sunan saurayin natane KAMAL me sunana

Jameel ya ta6e baki danuna kishi Yace yabada sadakine
Bana tunanin hakan Amma ban saniba. KAMAL yabashi amsa ataqaice
Yace wow Allah Nagode mah dani xa'ayi
Cikin sauri XARAH Tace hmm Allah yasa
Shima da saurin Yace AmEEn
LABEEBAH najinsu ita jin da'dinta 'daya yau XARAH da KAMAL sunkulle bakinsu basuyi
kalaman so ba bare susa mata damuwa da tashin hankali

Wajan shaqatawane qayataççe Jameel abokin KAMAL ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login