Showing 3001 words to 6000 words out of 95666 words

Chapter 2 - MASIFAR SO COMPLETE BOOK by Rahamat Muhammad .pdf

11 Mar 2025

7211

har nagayama Baban naku
yace aa bayaso yamishi Auran dole
Shuru Labibah tayi tana jin haushin yayan nata ganin yanasa iyayan nasu Cikin damuwa akan
yayi Aure kawai.....
Shigowar shine ya katse mata tunanin nata
Ya gallah mata harara ya xauna gefan taburmar
Yace watoh memakwan Ki tausasa xuciyarta shine harda wani cewa wai tasa Babah yayimin
Auran kawai innaga haka naso Auranko
Taturo baki Cikin shagwa6a kamar zatayi kuka
Tace nidai yau kayarda da maganar Auran dan Allah
Ya 'dauke kallansa daga kanta yamai dashi ga mamah Yace
Wallahi mamah yarinyar nan tacika shagwa6a da yawa
Ki dubafah kamar xatayi kuka
Tace naji ina ruwanka. Yanxu kaji rokwantane koya
Yace nayarda mamah Amma saidai banda wacce Xan Aura
Mamah xatayi magana Labibah tarigata da cewa ga Rukayya yayah tanafah sanka sosai
Yace Kinsan ba kulata nakebah. Kuma yanxu da kunya naje Nace nadawo gareta

Tace aa ba kunya Xan rakaka gunta anjima indai yanxu kana santa xancima albasa
Mamah tayi dariya Tace toh Uwar 'yan xumu'di kibarshi da ita yasan yanda xaiyi
Yace Allah mamah inajin kunyarta
Kuma dagaske xanso Labibah tarakani gunta Tace aishikenan. Yace toh kishirya bayan sallar
isha'i kirakani
Cikin murna Tace toh Allah ya kaimu Yace AmEEn
Nan yasha fatan tsakin yafita.



Bayan isha ko nayi suka fitoh danxuwa gun Rukayya
Labibah Tace bara nakira zarah
Yace toh
Da sauri tashiga gidansu zarah tana kwalla mata kira
Innah Tace ikwan Allah yau Usman yaga takanshi dan yaha'du da 'yan rakiya.
Dariya Labibah tayi Tace Innah kenan Tace agaskiya nafa'da
Zarah taxura hijabinta itama
Tace toh saimun dawo Innah
Tace adawo lafiya
Har sunkai soro sumayya takwallama Labibah kira tana cewa ga ishirin 'dita dan Allah kisiyamin
rake adawowa

Dawowa tayi takar6a Zarah najah tsaki suka fitoh
Usman ya kallesu Yace 'Yan biyu kenan
Wacece hassana acikinku mah
Zarah tayi saurin cewa kasandai nice ya Usman
Yace hmmm inawai xakikai san girmane
Labibah Tace tambayetadai yayah

Suna xuwa kofar gidansu Rukayya
Saiko gata tafitoh kamar tasan da xuwansu
Zarah Tace toh Auntynmu ya Usman ne Yace mukira mishi ke
Taqarashe xancan da nuna matashi da ido
Basuyi mamakin farin Cikin data nunabah dan sunsan haka xata faru
Tayi gunsa Cikin farin ciki Amma ta'danjah ajinta ka'dan dankarya gano farin Cikin nata

Labibah Tace tunda sun ha'du saimu tafi
Zarah Tace aikowa dai ya samemu agida

Suna Cikin tafiyarne Labibah Tace ya mutuminmu na'daxu
Zarah tayi Murmushi Tace ohofah. Dan tunda nashiga gida ban qara fitowa bah saiyanxu. Kuma
bai turobah daga ganinsa xaiyi jinkai

Murmushi Labibah tayi Tace bana tunanin haka dan baiyi kama damasu jin kamba
Zarah Tace hmm kinsan wani Abu Tace aa
Tace naji sanshi araina kuma naji ajikina kamar shine xaixamo miji gareni

Wani ciwo Labibah taji axuciyarta wanda furucin Zarah ya harfar mata da hakan. Batasan kuma
meyasa bah
Tayi yaqe Tace hmm tunda naganshi nahangoku anatsayin ma'Aurata
Zarah takalli wani merake da suke shirin wucceshi tace kamar zaki siyama sumayya rakeko
Tace kash kinga naso mantawa. Tafa'da tamaice mishi aban rake Yace nanawa. Na ishirin
Yabata

Bayan sunxu gida Zarah Tace yau agun mamah zan kwana
Labibah Tace dama katifata tayi rashinki nakwana biyu

Todama abin haka yake Zarah tana kwana agidansu Aisha-Labibah idan taso itada sumayya
Haka kazalika itama Labibah tana kwana agidansu Fatima-zarah idan taso
Dan haka bayan sun shiga gidansu Zarah
Sukaba sumayya rakenta
Inna Tace ina kuka baro Usman Labibah Tace yanacan gun soyayya. Tayi Murmushi Tace yau
Allah tayi Zarah Tace aikowa dai
Sumayya Tace Allah ya ha'dani dashi gobe nayimai tsiya
Labibah Tace dama kunsaba
Zarah ta 'dauki littafin Halima k Mashi Wanda take karan tawa Tace saida safe inna
Tace Allah ya tashemu.
Harxasu fita Tace Au namanta kucema maman taku matar jibirilu ta aihu
Sukace toh da fida

Mamah Tace namata murna sosai dan Cikin nata na bata wahala Zarah Tace yanxu gobe
duk xaku fitta Tace toya xamuyi

🌹duk iya tunanin Labibah tagano soyayyar KAMAL CE tamata mugun kamu
Yanxu haka kusan 'dayane na dare Sam takasa runtsawa dan taxaran tarufe ido bawanda
take gani sai hotan fuskar KAMAL
Yarikita mata ganinta tarasa yanda xatayi me kenan
Tafaru taqare
Dallacan kindameni da motsi tun 'daxo kin hanani bacci sai kijuyanan kijuyacan saikace
me tattare da damuwa...
Zarah CE maima Labibah wannan furucin
Tace yi hakuri nakasa baccinne
Tace toh kitashi kiyi sallah man Ni bacci bakeji
Sam Labibah bataqi ta Zarah ba Tatashi tayi dayo Alwala tafara nafula......

Washe gari ta'dan jita garau
Zarah taxubah mata ido Tace lafiyanki ko naganki haka

Labibah takalli kanta amirro taga idanta ya'dan fa'da Tace mekika gani
Tace jikinki yayi sanyi da yawa
Tace nima haka kawai najini yau
da nayi tunanin baxan iya komaiba Amma naga harna'iya aikin gida
Tace damuwata dai ina lafiyanki lau. Labibah tayi Murmushi ha'de da riqe hannun Zarah
Tace lpy nake 'Yar uwata Tace toh madallah



Kyakkyawan saurayine ajin farko fari tas. Kallo xakamai kasan ya ha'du tawajan ku'di ilimi
nutsuwa hankali wayayye kuma karufe kallan naka daga gareshi da miskili ne me sanyin hali.
KAMAL kenan

Misalin qarfe 5 da mintuna dareban daya 'dauko KAMAL daga airport ya saka hancin motarsa
agidansu KAMAL 'din
Cikin nutsuwa ya fitoh yana qarema gidan kallo kamar yau yafara ganin gidan.
Yalla6ai shikenan ba wani abu ko. Direba ya fa'di hakanga KAMAL Cikin girnamawa
Yace no ba Komai yayi Cikin falon
Yayinda direba yayi gunyin parking dan ajiye motar

Hajjiya Anisa wacce suke kira da Momy mahaiyarsu tana zaune kan kujera tana danna waye.
Mace kyakkawa taqarshe 'Yar duma duma
Da sauri KAMAL yaje Yakama hannunta ya sunbata Yace i miss u Momy
Cikin farin ciki Tace nima nayi missing 'dinka KAMAL. Ya kabaro min kakah
Tana lafiya tacema agaisheki. Toh ina amsawa
Yace yanaji gidan shuru bakowa
Momy tayi Murmushi Tace sunajinka suka shige aiki
Yace da kina famah dasuko
Eh wallahi bakaga yanda nadinga cewa sutashi suyiba Amma sukamin kunnan Uwar shegu
Yace hmm Salim fah. Tace Yana gun dadynku office 'dinsu wai suna lissafi akan fudda zakka
Yace oho hakane fah danni kannaje kano nafitar da tawa
Tace madallah Allah ya qara bu'di. Kaje kayi wanka ga abincinka nan anjera maka Komai
Yatashi yana cewa AmEEn da shigewa shashinsa.

Yasami komai tsaf kamar yanda taxata. Nan yayi wanka ya canja kaya yana niyar fita saiga
qannansa biyu Safna da Sagna
Suka durkusa suna gaidashi da mai sannu da xuwa
Cikin kulawa Yace Yauwa nasameku lafiya
Sukace qalau yayah ya kakah
Tana gaidaku
Muna amsawa
Suka fitoh atare.
Direct kan dining yayi.
Momy taxubamai abincin yafaci yana cewa yau nasamo miki sirika momy......

Saura ka'dan tasake cup 'din dake hannunta Tace KAMAL mekace
Yace dagaske Momy nasamo miki sirika Fatima-zarah
Zama tayi Cikin farin ciki da annushuwa ta'daga hannu sama tana kwarara addu yau tasamu
labarin da takesanji
Tace a ina take kuma 'yar waye
Yace ba 'yar kowa bace dan iyayanta talakawane lis.
Tananan unguwarsu Auwal
Tace toh Allah ya tabbatar da alkairi Yace AmEEn Momyna.....
Dadyn shine yashigo shida Salim
Yace my soon kadawo Yace nadawo dady dafatan nasameku lafiya Yace qalau my soon dama
inasan magana dakai inkagama kasaman Yace angama dadyna
Murmushi yayi yayi Cikin 'dakinsa ko ince shashinsa
Salim Yace sannu brother kadawo lafiya Yace lau lau ina maryam
Yasosa qeya Yace aitafi qarfina yayah shiyasa kawai narabu da ita. Yace ko
Yace da gaske
Momy tayi Murmushi Tace hmmm yaudai yayanka yaxomin da xance me da'di yayomin sirika
Da sauri Salim yakalleshi Yace kako kyauta yayah Allah yasa ayi damu
Yace AmEEn

Shin suwaye Bayin Allan nan


Alhaji Sale da Alhaji Nasir uwarsu 'daya ubansu 'daya Mahaifinsu yarasu tunsuna yara
Tun tasowarsu sun bu'di ido da ku'di dan haka su'din tun asulinsu masu dashine mahaifiyarsu
hajiya Saude nanan da ranta
Itace suke kira da Hajjiya
Baqaramin so suke mataba. Itama tana sansu

Alhaji Sale da Alhaji Nasir suna San junansu
Sana'ar iri 'dayace watoh Su 'yan canjin ku'dine
Sannan basu tsaya ananba suna ta6a kasuwanci sosai
Shiyasa sukeda ku'di bana wasaba

Sunada mataye 'dad'dai
Alhaji Sale yana zama garin Abuja shida matarsa Hajjiya Anisa balarabiyace 'yar usuli dan acan
Saudi Alhaji Sale ya Aurota
Mace mekyan hali dasan mutane Sam abin hannunta bai rufe mata ido bah. Dan kan tasamu
sheda tagari
Sunada yara 4
KAMAL
Yusuf
Safna & Sagna
KAMAL shine Babba sai Yusuf Wanda ayanxu yake qasar Saudi da xama shida Matarsa
'yarcan dan iyayanta sunqi yarjemai yaxo musu da ita Nigeria Kasan cewarta ita ka'dai garesu

Toh dama shi Yusuf 'danba ruwansa ne. Dan yasaba da Saudi shiyasa baiwani damuba saboda
yana ganin 'yan uwan momynshi
Dan haka aka musu Aure da Matarsa Mufeedat. Sunada 'yayansu biyu Sadeeq da Aliyu
Yusuf dai sana'ar saida gwala gawalai yake anan Saudiyan

Sai KAMAL wanda yake cikakken doctor nasalin ciwuka daban daban
KAMAL yasan kan aikinsa
Duk wani matashin doctor dayakejin kansa agarin abuja saidai yakoma Bayan KAMAL
Dan manyan qasarnan nasansa saboda kwarewarsa akan aikinsa
Suna girmamashi
KAMAL yataka matsayi babba danshi'din na musammanne

Doctor KAMAL waraka shine sunan da manyan doctors 'din kasarnan suke kiransa dashi
A England yayi karatunsa cibiyar bokan duniya

Gashi qaramin yaro Amma sai aiki
Dan Allah yabashi

Shekarun KAMAL ishirin da tara cif 29 Amma sai baiwar ilimi da sanin aikinshi

Wasu doctors suna mamakin aikinsa idan suka duba shekarunsa


KAMAL yayi ku'di bana wasaba
Saidai yanada zuciyar sadaka da kyauta shiyasa yakeda tarin Masoya

KAMAL yanada wani hali shidai bayasan hayaniya shiyasa baicika magana bah
Amma yanayi da wa'yanda yasani

SAIDAI FAH 😳 'DAN LUV NE 👈🏻

Yanasan soyayya Amma baisamu wacce tadace dashiba sai Fatima-zarah

Tunda Yusuf yayi Aure Momy da Dady suka sakashi agaba wai sai shima yayi

Shiyasa daya kawo musu xancan Fatima-zarah zuciyoyinsu suka cika da farin ciki

Tunda KAMAL yadawo daga karatu yakasance a Kano naniqe da Hajjiya kakah. Tsowuwar da
take sanshi kamar ranta. bataso KAMAL yayi nisa da ita koka'dan
Shiyasa daya fara aikinsa Abuja yake xuwa duk qarshen. Wata yana dubata
Yakanyi kwana biyu haka. saiya komah
Bashakka Hajjiya kakana najin da'di

Yanxu ko jin da'dinta xaifi nada tunda yaxo mata da xancan Fatima-zarah

Ta'udurce aranta xata saka KAMAL yaqarasa gininsa nanan kusa da inda take yasaka
Fatima-zarah aciki

Safna da Sagna ko sune 'yan autar Momyn KAMAL
'Yan biyune.
Masu bambancin ra'ayi
Itadai Safna yarinyace mehankali da nutsuwa Sam magana bata dameta bah
Shiyasa KAMAL yake shiri da ita


Yayinda Sagna takasance maraji da San shige shigen yawo da surutu
Ga 'dan rashin kunya dasan raini idan kasake mata
Amma tasan wa'yanda takema rashin kunyar tata.
Dan aduniya bawanda take jin tsoro kamar KAMAL dan baya mata da wasa Sam
Shine yake gyara mata xama

Ayanxu dai ita da Safna suna aji shidda na secondary Bayan dama sun kusa sauke alqur'ani da
sanin wasu takaddun addini

Alhaji Nasir ko yanada Kano da xama inda Hajjiya kakah Mahaifiyarsu Tace baxasu watse Su
barta ba.
Ba Alhaji Sale bashi baxai yuhuba
Dan haka yaxauna a Kano shida Matarsa Hajjiya Zainab
Yanada yara goma cif
Kuma "dayane dansa namiji watoh Salim
Ya aurar da mata hu'du4 saura biyar5 wayanda suke karatu uku kansu 'daya dasu Safna biyu
kuma qannansu ne
Salim Yana harkar kasuwancinsa da Dadyn KAMAL.

Wannan sune asalinsu KAMAL
〰〰〰〰〰〰〰

Hira sosai KAMAL yakeyi da Momy Yana bata labarin Su Fatima-zarah
Yace kinsan wani abu.
Tace aa Yace dana ha'da ido da 'yar uwarta Aisha-Labibah sainaji gabana yafa'di
Momy tagyara xama Tace toh ita FATEEMA bakaji fa'duwar gaban agareta bah
Yayi Murmushi Yace banji komai ba illa sanda da qaunarta dayama xuciyata shigar baxata
tanada kyau sosai ina Santa
Tace ita AISHA ba kyakkyawa bace
Yawaro ido Yace wow tanada kyau Momy sosai gatada da'din murya
Wallahi Momy inasan jin muryarta dan gaskiya tafi FATEEMA da'din murya
Murmushi kawai Momy tayi.

Washe gari KAMAL ya tashi ya kintsa kansa da shiga irin tasu ta likitoci doctor sai Qamshin
turaransa yake
Yafitoh kenan daga part 'dinsa kamar ance yakalli window. Aiko yaga Sagna ta falle Ado meba
fulayoyi ruwa da mari
KAMAL ya bu'de window da mamaki yaji tana xaxxagama Ado masifah wai dan tsabar iskanci
Yana galinta xata wucce yawani watsa mata ruwan da yakeba fulayoyi
Yace Wlhi saginiyatu banganki bah
Ran Sagna yaqara 6aci dan tatsani yacemata saginiyatu dan haka taqara falleshi da mari Tace
wai waye saginiyatu. Kullun saika kirani da sunannan wai Sagna ne baxaka iya fa'daba dan
qauyanci
Ado yayi shuru yana ganin rashin mutunci irinnan Sagna. Sam bata ganin girman manya
aqallah ya bata Kusan shekara shidda Amma hakan baisa ta raga mishi bah
Yace toh kiyi hakuri.......
Takaici ne yasa KAMAL wuccewa xuwa dining yana kuma mamakin Sagna Ashe rashin kunyar
tata tawucce inda yake tsammani

Dady da Momy da Salim Safna suka kalleshi da mamakin 6acin randa yake fuskarsa Safna da
Salim suka gaisheshi ya amsa. Sannan yagaida Su Momy
Dady Yace yanaga kamar ranka a6ace lafiyadai ko
Yace no is ok
Yafara break 'dinsa kenan Sagna tashigo falan fuskarta a 'daure.........

Ganin mugun kallan da KAMAL yawatsama yasa jikinta yafara rawa
Momy takalleta tata6e baki dan tasan babanxaba KAMAL yabita da mugun kallannan
Aiko Yace watoh kega 'Yar iska mara kunya ko
Shi Adon qanin ubankine daxaki falleshi da mari da haka

Tuni Sagna tarikice Tace dan Allah yayah kayi hakuri
Yace ko.
Tayi shuru.
Tashi yayi yabata mugayan marika biyu wa'yanda suka gigitata Sannan yayi boll da ita Yace duk
ranar danaqara ganin kin 'daga hannu kin mari Wanda ya girmeki Wlhi ranar saina miki dukan
mutuwa

Cikin kuka Tace Wlhi baxan qaraba
Cikin tsawa Yace jekibashi hakuri yanxu
Da sauri tatashi xataje yabi da qafah
Aiko takwasa a guje tana kuka

Yajah tsaki da 'daukar jakar laptop da wayoyinsa
Yace Momy Dady natafi
Xasuka mishi fatan alkairi yafito yashige motarsa sai hospital....

Cikin kukako Sagna takebama Ado hakuri

Baiyi mamakiba dan yaga futan KAMAL yana jifanta da harara
Yace karki damu saginiya.......
Baiqarasa ba tagallamai harara Yace yi hakuri Sagna
Kwafah tayi tayi falo

Momy mah harararta tayi Tace mutuniyar banxa aigwara yadinga gyara miki zama kokya kintsu
Dady Yace shashasha ba. kedai bakiyi hali mekyau ba dan albasa batayi halin ruwa Yana fa'din
haka yafita shida Salim
Momy mah tashi tayi tabar falan
Aiko Sagna taqara fashewa da kuka gani take kowa ya tsaneta bamai Santa sai yayanta Yusuf
dake Saudi
Tausayinta Yakama Safna Tace kidena kuka kinji
Kikuma tashi mutafi lokaci natafiya
Tsaki tajah tasa6i yakar skull 'dinta tafita batare da tacema Safna komai bah
Itama Safna nan 'daukar jakarta tayi tabi bayanta
Direban Su yajasu xuwa skull



KAMAL ko yana xuwa asibitin nasu yadinga kar6ar gaisuwa agun doctors da ma'aikatan gun
Dan dai KAMAL shina mutanene
Sakina 'daya daga Cikin ma'akatan itada Nafisat wa'yanda suke bala'in San KAMAL kuma
qawaye ne Amma kowacce taqi yarda da manufar 'yar uwarta haka suke tafiya acewarsu
kowacce tata tafish sheta
Suka gaida KAMAL Cikin girmamawa ha'de mai kwarkwasa
Yaxuba musu ido dan yada'de da harbu jirginsu. Nan take yatuno da Fatima-zarah yayi
Murmushi yashige office 'din

Murna tacika su atunanin kowacce acikinsu ko yafara santa ne


KAMAL kam yau aiki kawai yake yana tumanin FATEEMA
Yayinda yake hasashen acikin satinnan xai koma Kano

〰〰〰〰〰〰

Suna tafiya Cikin nutsuwa dan xuwa gidan matan Bashir yayan Fatima-zarah dan kaimata
'dinkinta datasa FATEEMA takar6arnata
LABEEBAH Tace nidai naqagu mutumin nan yaqara dawowa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login