Showing 1 words to 3000 words out of 44283 words

Chapter 1 - Hadin kai Part 1 Complete Hausa Novels by Asma Baffa .pdf

16 Mar 2025

2736

[8/15, 11:42 AM] +234 813 228 4370: HADIN KAI









1







Official







By
AsmaBaffa












BISMILLAH

Alhmdllh fans Allah ya kawo mu sabon Novel,Allah yasa mu fara lfy mu Gama lfy,Kuma
Allah ya bada ikon amfani da fadakarwarsa.

Pls Sharhi nake so da Haka zanfi Jin dadi typing,Kuma zanyi kokarin yiwa kowacce reply
inshallah.



Son Kai zanyi wannan page Na ASMABAFFA FANS CLUB ne, ku zan fara
bawa..












Gombe state Kauyen Dingawa Babban kauye ne kusan ma kamar Local Government ne
Amma ba a bashi LGA ba, garine na fulanin asali kana Shiga ba sai an fada maka ba.
Fadila Tahir shine cikakken Suna na,Tahir Adam tukur shine Sunan mahaifina,Tahir Adam
tukur Asalin fulani ne mu Amma yanzu ba shanu sun Kare,Tahir Su uku ne duk maza iyayensu
suka Haifa Wanda har yanzu Suna Raye kakanni na na wajen uwa Dana uba duk ba Wanda ya
rasu suna da ransu, Babana shine Babba wajen iyayensa daga shi sai kaninsa kawu Salisu da
kawu Usman, gaba daya Allah ya wadatasu Alhmdllh a kauyen Nan Babu masu kudinsu,harkar
noma da siyar da kayan masarufi ne sanaarsu,Babana Tahir har mota kurkura da Golf yake
dasu duk Ana jigilar Kai Kaya kasuwanni daban daban,Kawu salisu ma Yana da kurkura,Haka
Iyayensu Baffa da Yafendo suna Jin dadi ba yunwa ba rashin sutura,sai abinda suke so, daga
kakannina har iyayenmu duk sun je aikin Hajji,mune kawai yaran bamu je ba.

Suna da matukar biyayya sai abinda kakanninmu suka tsara shi sukeyi,Tahir da kannensa
duk auren zumunci akayi musu,Salisu da Usman matarsu daya Basu Kara aure ba,Salisu Yana

da Yara Biyar manya samari guda biyu Mahmoud 28yrs da Umar 26yrs samarine kyawawa
farare kasancewar Family dinmu kaf Babu Baki kowa fari ne tas sai dai wasu sunfi wasu fari.
Bayan Umar akwai mace wacce mate Dina ce Saratu18yrs,sai Zainab,da Kuma Abida Yar
auta.

Kawu Usman kuwa yaransa biyu Rak Matarsa Bata haihuwa sosai Duk Mata ne Aisha da
me Sunan Yafendo Fatima Ana ce Mata Mama.
Babana Wanda shine Babba Tahir Matansa biyu Babata itace ta farko da akayi Masu hadin
zumunci Hajiya Hadiza muna kiranta da Hajiyarmu,Bayan Sunyi aure Ta haifi Salman shine
28yrs saurayi saan Mahmood ne Kuma abokai ne,sai kaninsa Musa saan Umar 26yrs, sai Ni
Fadila Yar auta a wurin Hajiyarmu Wanda Kuma Ni kadai ce mace a gidanmu,Sai kishiyar Babar
mu Haj Balki Amarya tana da Yara hudu Amma duk maza ne Kuma yarana ne kanana Babban
15yrs Abdullahi,Ramadan 12yrs ,Shahid 9yrs sai Ahmad autanta a yanzu 5yrs.

Duk da a kauye muke muna zuwa makarantar Gomnati da Islamiyya,Haka Salman da Musa
tare da yaran su Kawu Salisu duk sun Gama HND a garin Gombe Sunyi service Kuma yanzu
aiki ake nema musu sannan sai suyi aure Amma har yanzu aiki Bai samu ba sai da hanya
Babba.
Ni Kuma na kusa candy muna Ss3 jarabawa zamu zana ta fita,sauran kannena suna
secondary wasu primary,muna da kokari gaba daya danginmu Babu dakiki,Sabo da Kawu
Usman Yana dauko mana Yan bautar kasa iri iri suna koya Mana turanci karatu da rubutu shi
yasa muka iya turanci duk da cewar ba kamar masu yin makarantar kudi ba,ko mutanen
birni,iyayenmu suna son juna suna da hadin Kai Amma duk da Haka mu yaransu ba a fiye
Zama lfy ba,sabo da munafunce munafunce irin na dangi musamman iyaye Mata su ke
haddasa fitina iri iri.

Hajiyarmu Allah yayota Masifaffiya ce number 1 a kaf kauyen Nan an San da zamanta sabo
da masifarta,har mu yaranta Bata raga Mana,ita Bata fiye tsokana ba Amma idan aka tabo ta ba
mutunci,shima Babanmu Tahir Abbu balainsa yayi yawa Babu Wanda ya kyale Amma Kuma
Yana da Dan saukin Kai,ga addini,Kuma Yana da nutsuwa kamar Hajiyarmu matsalarsu rashin
Kara da kau da Kai komai masifa.

Kishiyar Babarmu wacce muke Kira da Anty ita Kuma tana da hakuri gata Shuru Shuru sai
kisan mummuke,a boye take shuka tsiyarta ga tsokana,shi yasa kullum fadansu baya karewa
dare da Rana Amma kowa mutan gari laifin Hajiyarmu ake gani Ana tunanin ita take zalintar
Anty sabo da ita Bata kyalewa idan anyi mata. Babanmu kuwa shima yafi ganin laifin Hajiyarmu,shi yasa ya tsaneta ya tsanemu mu
yaranta,Yaran Anty da Anty yake kauna.

Matan su Kawu Salisu kuwa magulmata ne su ke haddasa rashin zaman lfy a dangi,Kuma
Kakanninmu sunfi kaunar Matan Kawu Salisu da Usman sai Anty da yaransu,basa kaunar
Babarmu ko kadan,muma yaranta abin ya shafemu basa kaunarmu,Hajiyarmu Har danginta ba

wani sonta suke ba sabo da halinta na Saurin fada da masifa,Bata da kawaici iyayenta kadai ke
Dan sonta,muma kakannimu na wajen uwa basa wani sonmu Wai bamu da kunya Yan iska ne
mu sabo da kawai muna karatun boko mun Dan waye muna Yar kwalliya mun banbanta da
mutanen kauyen shine kawai suka ce mu Yan iska ne Haka mutanen gari ma Ware mu
akeyi,kawayena kullum zagina da gulmata sukeyi akan nace zanyi University bazan yi aure ba
sai naci da biro, Hajiyarmu tana daura min tallan Dafaffiyar gyada Ina kaiwa makarantar boko
da ta yamma,sannan Ina sai da goro da Sassafe kafin na tafi schl sai nayi tallan goro,Sabo da
Abbu baya son Hajiyarmu Bai Hana a daura min tallan ba,Amma yaran Anty hanawa yayi a
Dora musu talla.
Takaitattun matsalar mu kenan Nan gaba za kuji Wanda baku San dasu bama.

Allah yayi min baiwar hakuri ban gaji iyayena wajen masifa ba,sanyin Hali gareni,ga
tsoro,sannan Ina da matukar addini,sannan kaf danginmu Babu me kyauna da kokarina,nafi
kowa kyau da fata me kyau kamar jinin balarabiya wasu sun Dan fini haske da kadan duk da
cewa Nima farace Amma hancina Bai cika tsini ba Kuma ba gajere ba,sannan Dan bakina
karami jajir,gashina Baki sidik ga tsayi ko kitso baya yi,har gadon baya,idona farare tas Dara
Dara,tun daga gaban goshina zaka ga gashina yalala ya kwanto, Ni ba rammiya ba ba Kuma
me kiba ba,ga shape dirina abin kallo ne duk Wanda yayi tozali Dani sai ya kara, sabo da
tsananin kyau na, idan baka sanni ba zaka rantse balarabiya ce ni, Amma duk kyan Nan nawa
bani da saurayi bani da mashinshini sabo da halin Hajiyarmu Babu Wanda ke son hada zuria da
Tata an Gama yadawa da sharri iri iri ake yi Mana kowa yazo wajena sau daya bazai dawo ba,a
cikin dangi za a samu wasu munafukai suje su fada cewar Yar iska ce Ni har cikin shege na
taba yi an zubar,sannan suce idan ya aureni zan mallakeshi,ga Masifar uwata,duk kawayena
anyi musu aure tuni, sai Ni kadai Wanda a rashin miji ne yasa nake Karasa secondary Amma
da ace na Samu miji ko jss1 bazan je ba za ayi min aure,yaran su Kawu Mata du Sunyi aure
suna da Yara biyu Kuma mate Dina ne.

Dangi an Kara tsanata Wai ni nake korar samari sai talla da iskanci a garin Ina kwalliya Ina
iyayi,Hajiyarmu ma da Abbu laifina suke gani shi yasa suke Kara Jin haushi na,dangi ko biki ko
suna bana iya zuwa kullum daga schl sai gida sabo da irin ci min mutunci da akeyi Akan Wai
naki aure Nasa yaudara a gaba,dangin uwata ma Haka ga mutan gari,Haka nake Addua Ina
kuka kusan kullum Allah ya bani Mijin aure ko wanne irine aura zanyi na huta da bakin cikin da
nake kunsa.

Yaya Salman ne kadai da Mahmood suke lallashina sannan suna matukar ji Dani,Mahmood
ya taba furtawa zai aureni babarsa Matar Kawu Salisu tace zata tsine Masa shine yasa ma ya
hakura Dani.
Takaitaccen tarihina kenan.

Ci gaban labari.

Rataye nake da Yar Jakar makaranta ta wacce Ya Salman ne ya siyo min a garin Kaduna
lokacin da suka je service, Uniform dina fes dasu Allah yayoni da Tsafta sosai kullum fes nake

ko Ina kungu da sako na jikina,ga Mahmood Yana yawan bani kyautar turaruka masu kamshin
gaske dake su Yan gayu ne sun Gama wayewa sabo da karatunsu a birni sukayi.
Ina hanya na mike titi zan dawo gida sai ga motar Abbu Yana tukawa Golf ya rarako wuta
kamar zai tashi sama Yana kallona Ina kallonsa Ina daga Masa hannu ko rage min hanya yayi
sabo da makarantar Tamu da Nisa sosai ga Rana Amma ta window ya leko sabo da rashin
tausayi Yana min Dariya ya wani daga min hannu irin sai na taho,gaba kadan kuma kannena ne
su biyu yaran Anty Suma sun taso a gabana ya tsaya ya dauke su a motar suka tafiyarsu tare
da bula min kura.

Bansan sanda Hawaye ya tsiyayo min ba,kawai na bawa zuciyata hakuri har na Karasa
gida,Ina sallama gida Kuma ko kayana ban cire ba Hajiyarmu ta fara fada uban me kika tsaya yi
a hanya banza shashasha kina girma kina hauka,na bude Baki kenan zanyi magana ta dungure
min Kai Dalla rufe min Baki sai ki dauki abinci kici kiyi Shirin Islamiyya ga gyada ta tana jiranki ki
tabbatar kin siyar, sabo da takaici ban iya cin komai ba wanka kawai nayi tare da Shirin
Islamiyya, Ya Salman ne ya shugo tare da kallona yayi Murmushi yace Sister kinci abinci kuwa?
Ganin Hajiyarmu zata min fada kawai nayi Murmushin Dole nace sai na dawo bana Jin yunwa,
da masifa Hajiyarmu tace me bakin Hali munafuka Wai fushi tayi Akan an Mata fada baza taci
ba, Anty uwar tsokana tace kanki kika yiwa cikinki yarinya,gandareriya dake kice baza ayi Miki
fada ba,idan Haka kike so ubanwa ya hanaki aure ki tafi dakin mijinki sai kiyi abinda kike so..

Hajiyarmu Bata so wani yayiwa yaranta fada sai ita ko Abbu Nan take ta hayayyakowa Anty
da fada yarki ko tawa?,Ina ruwanki,kije kiji da yaranki uwar iya Yar shishigi, Musa ne ya taka
musu birki Wai Dan Allah Hajiyarmu me yasa kuke Haka ne why? Kun girma Amma bakwa
gani,Ubanka kayiwa turanci ba Ni ba,sabo da kaga bama Jin turanci zaka zagemu da yaren
nasara cewar Anty,Hajiyarmu Kuma tace Wai shi Dan boko to Munga Nasara ma marar tarbiya
fitsararre.

Salman dai Hannuna yaja Ni Kuma na daura faranti gyada ta a kaina na bishi muka fita tare,
har bakin titi ya rakani muna hirarmu ya tsaya wajen masu soya doya da kwai tare da egg in to
egg ya siya min na dari biyu harda lemon kwalba mirinda da ruwa pure water guda biyu ya bani
a Leda sai ga Mahmood Dan Kawu Salisu suka rakani har schl sannan suka tafi zasuyi Shirin
zuwa filin ball dake kauyen.

Naje schl Ina tunanin rayuwata ko karatun yanzu na daina fahimta burina na siyar da gyadar
dana zo da ita schl Kar na koma gida Naci duka wajen Hajiyarmu.
Haka na dinga zaga class dake makarantun kauye ne na Gomnati ba damuwa akayi da ilmin
ba Babu ruwansu.

Ajin Yara na Shiga lokacin anyi break Ina so su siye min gyada ta,na fara musu wayo
kasancewarsu Yan primary, wani bench na Yara na Samu duk sun fito da kudinsu zasu fita
break na zauna saman desk na washe musu Baki nace Yan Yara Yara gyada me sihiri Ina tafi
dama sun San wakar sai ko suka fara Baki daya ajin Ana tafi Ina bawa Yara guda biyu,suna ci
nace duk Wanda ya siyi gyadar Nan zan bashi alawa me dadi,Nan Yara suka dinga turuwar

siyan gyada da alawata a jaka Ina Basu daya daya,suna siya,kafin kace me sai ga wasu yaran
ma na wani ajin muna rera waka,watarana ma idan na faki idon yaro kawai sai na kwace
kudinsa na bashi gyada ta kudinsa Dole ya hakura yaci,Dan da Nan na siyar da gyada tas.

Wurin Magrib muka tashi daga schl sai gida,Ina dawowa ranar Girkin Hajiyar mu ne Haka
tace yawwa maza je ki karasa min girkin can,Haka ba hutu na Karasa na Gama tuwon shinkafa
miyar Danyar kubewa da kifinta dake gidanmu ba laifi muna cin me kyau,Kuma gidan mu ba na
kasa bane na bulon siminti ne ko Ina a shafe sumul yasha fenti.
Ina gamawa zanyi wanka kenan na huta Anty ta Miko min katon botiki tace tuzuruwa ebo
min ruwa a tuka tuka na waje,tsakanin uwa da danta sai Allah Hajiyarmu karaf a kunnenta
fuuuuu sai gata ta fito ta kwace bokitin a Hannuna tayi ball dashi Nan take ya fashe,sai ga Abbu
ya shigo daga masallaci,ganin Anty Amarya aka yiwa laifi ya fara masifa kamar zai cire bakinsa
sannan ya kalleni tare da cewa zo ki tafi makarantar dare Dan ubanki mene amfaninki,ya kawo
min duka Hajiyarmu ta Kare ya sameta a hannu, Hajiya ta kwalla ihu da uban karfi Wanda ya
dawo da hankalin makwafta gidanmu,hannu aka ta Dora tana an tsaneni an tsani yarana,sai ka
kasheni ka huta,azzalumi tunaninku ban son yarana,Anty tuni Sumi Sumi ta koma dakinta tayi
luf tabar Hajiyarmu da babatu mutane suka cika gidan Ana kallon Hajiyarmu a Masifaffiya marar
ilmi Ana ganin ita ce ke zaluntar Anty sai zaginta akeyi ita kuma tana ta faman hayaki da
masifa.

Kunya tasa gaba dayanmu muka bar gidan sai dare wurin 10pm muka fara dawowa mu
kullum gidanmu ba zaman lfy.
Da Sassafe Abbu yace na fito ya aikeni na siyo Masa petrol,Salman yace tana mace Abbu ka
bani Ni na siyo ko Musa duk ga Yara sai Fadila zaka aika,Abbu wata Harara ya watsawa
salman Wanda yasa Salman yin shuru ba shiri, ita nayi niyyar aike idan ta gaji ta fito da miji tayi
aure., Kudin kawai na karba da jarka na tafi naje na dawo sannan nayi Shirin schl.
Abin takaici an fara registration na waec da Neco Amma da na sanarwa Abbu sai yace
karatun ya mace bashi da Amfani a duniya Fadila nasan baza ki taba ci gaba a rayuwa ba,baza
ki wuce kauyen Nan ba ko aure zakiyi to mene amfanin biya Miki makudan kudi haka,Dana
biyawa mace taci gaba da karatu gwara na zubar da kudin,mene amfanin karatun boko wajen
ya mace, Hawaye na fara ,sanyi,iska etc Dana Sha a banza bazan karbi certificate ba,ko bazan
ci gaba ba ai na karbi Certificate a Hannuna.
Da kuka na fito daga dakin Abbu,Hajiyarmu tasan me ya faru Baki ta tabe duk ke kika jawa
kanki da kinyi aure ai da kin huta, Ina Hawaye tare da rakubewa a jikin bangon dakina kamar
almajira nace Hajiyarmu Wai komai ba Allah ne yake tsarawa Dan Adam ba Amma kamar baku
San hakan ba,ai aure lokaci ne komai dadewa idan da Rai zanyi, rufe mana Baki ai Baki niyya
ba komai sai da niyya yake tabbata kiyi niyya ki gani idan bakiyi ba ehe cewar Anty
tsokana,Mahmood ne ya shigo gidan wurin Mahmood ya Iskeni Ina kuka,Kanwata me akayi
miki? Nace Abbu ne yace bazai biya min Waec ba,Kuma naje wajen kawun Salisu da Kawu
Usman sunce baza suyi asarar kudi ba Wai aure ne kadai idan zanyi zasu kashe min kudi
Amma boko ai zunubi zasu kwasa ma, dariya Mahmood yayi Dan an biya boko mace tayi shine

za a kwashi zunubi, lallashina yayi sannan yace Zamu biya Miki Ni da Salman dasu Musa ki
daina kuka,Nan take farin ciki ya mamayeni.

Washe gari kuwa da safe Salman da Mahmood suka je suka biya min Waec da Neco, zo
kuga murna Ina ta gode musu, Salman Yana dariya yace ki Bari yarinya Allah yasa muyi kudi
Zaki ji dadi,nace Allah yayana?yace sosai ma,to Allah ya hore suka ce Ameen sannan suka tafi
daga schl din.
Koda Abbu yaji cewar an biya min kudin jarabawa sai ya dinga fada,da sauri ya shugo yace
Ina Fadila,nasan halinsa da gudu na fito nasan halinsa yanzu na Sha Mari,yace naji kinje kin Sa
an biya Miki jarabawa ko? Wato Ni ban Isa ba,kin shahara to wlh sai dai ayi asarar kudin Amma
Baki Isa kin zana jarabawa ba,ni Zaki tozarta,to zanga me iko dake tsakanin Salman Dani,daga
yau na soke zuwa makarantar taki har Islamiyya, Wai ke sai kin ci da biro ko? Ai naji me kike
cewa a garin sai kinci da biro,Rokon Abbu na fara Ina kuka,Abbu yace Abu daya zakiyi na
kyaleki ki zana jarabawa,da sauri nace me zanyi Abbu? Aure ya bani amsa na gaji da gorin da
ake min gari,da maganganu da ake Akan zuriyata,wlh kika sake sunana ya baci wlh kinji na
rantse sai na koreki daga Gidana,Anty zaraf ta leko tace wlh kuwa yo yarinya ta Gama balaga a
gida,ace kamar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login