Showing 6001 words to 9000 words out of 44283 words
Chapter 3 - Hadin kai Part 1 Complete Hausa Novels by Asma Baffa .pdf
ba ko kallona baiyi ba,na durkusa nace Ina kwana? Ya ka tashi? Ice ko dai lfy kake? Ya
ruwa jiya Kuma sai kasha dukan ruwa gashi mura ta cafkeka Bature Kai dama ba kwari ba
kamar fiigaggiyar kazar turawa kake.
Kallona yayi kawai ya hade fuska,nace Allah baka hakuri me yayi zafi Ni Fadila,da gani
Amma Kai Masifaffe ne ko irin Hajiyarmu,wlh ka kiyayi kanka mutan gari zasu tsaneka tam ga
Hajiyarmu abinda ya jawo Mata baking jini kenan har mu yaranta aka tsanemi.
Ido kawai ya zuba min Yana kallona nace ae ka kalleni da kyau Kai ba a Isa a Gaya ma
gaskiya ba sai kana fushi Haka ake rayuwar duniya fisabilillah kace baza a fada ma gaskiya ba
to ya kake so ayi maka Kai kaki magana kamar jariri.
Yanzu kaci abinci ko da yunwa ka zauna? Shuru ba magana,Maganar kurame nayi Masa
kaci abinci? Kai ya girgiza min Alamar baici komai ba,nace to na ganoka kurma ne kai Ashe?
Bari na Nemo ma abinci karka biyo Ni ka jirani a Nan.
Zama yayi kuwa Bai bini ba na ajiye farantin goro na a gabansa Ina cewa ga ajiyata Nan ka
jire min Kar ka Bari wani ya dauka, nayi tafiyata abina.
Da sauri naje na damu Mahmood da Ya Salman sai sun bani dari biyar zan siya wani Abu,Ya
Salman yace me Zaki siya? Nace sirri ne idan zaku bani ku bani,Mahmood ne ya zaro dari biyar
ya bani Ina Godiya na fyalla da gudu,na koma gida ba tare da kowa ya ganni ba na dauki cup
me murfi,na Shiga dakin Salman na dauki kayan sawar da ya bani jiya na sawa Bature,da gudu
na arce muka ci karo da Abbu Dan karma ya min magana na Kara karfin gudu na a tamanin
fiiiiit na wuce shi, Ina jinsa yace Zaki dawo ne.
Table din me shayi na na tsaya nace ayi min hadin kauri na dari,Bread na Hamsim,naje na
siyo pure water biyu,na siyo tooth paste da brush sababbi na dawo inda na barshi me zan gani
Yara sun taru a gabansa suna ta kallonsa suna tsokanarsa ga goro na Sunyi kaca kaca dashi a
wajen suna iba suna watsawa kogin, ragowar Kuma suka gatsa su Yanda bazai siyu ba.
Da masifa na koresu,suna tafiya cikin sanyi na nace yanzu kana gani suka lalata min Kaya
Haka? yau duka Hajiyarmu zata min,Bai kulani ba, haka na bude brush na matsa toothpaste ina
Masa Zancen kurame ya taso kusa da rafin, na gwada Masa yanda zaiyi abin mamaki sai ya
make kafada ya ballo abin bishiya yayi Masa kamar aswaki ya fara goge Bakinsa dashi, Haba
shi yasa naga hakoransa neat kullum Ashe aswaki yake yi,a gabana ya goge ko Ina har
halshensa can ciki, fushi nayi yaki karbar nawa yayi brush,kamar ya sani sai ya jefar da
Aswakin ya Miko min hannu na bashi Brush din yayi abinsa kuwa,sannan na bashi pure water
daya ya kuskure bakinsa, brush din na wanke na maida su leda, Ina Murmushi na sake Mika
Masa kayan Ya Salman nayi Masa alamar ya sa harda Boxers, da kyar na rokeshi ya karba ya
zaga Bayan bishiya ya saka kuwa Normal sun Masa kyau da yake yafi Ya Salman Dan kauri sai
ya cika kayan tab yayi Masifar kyau kamar wanka yayi abinka da farar fata.
Kayan daya cire harda singlet da boxers nasa designers na kwashe na linkesu na zuba a
Leda,agogon dake daure a hannunsa nake kallo na Diamond me kyau da tsadar gaske da wata
azurfa zobe me kyau.
Tea din na bude nasan ba iya Sha zaiyi da kansa ba Haka na zage da kaina na dinga bashi
da bread ya shanye tas,ya fisge ruwan dake Hannuna pure water saida ya ji min ciwo kadan a
fatar Hannuna ya karce ni, shanye abinsa yayi sannan na mike na tafi gida, shi Kuma a Nan
gindin bishiyar yayi kwanciyarsa bacci me karfi ya kwashe shi.
Munafukai yaran Kawu Salisu Dana Usman har sun ganni duk abinda nakeyi suna sa min
Ido,tuni suka dinga yada Ni a gari har Zancen ya koma kunnen Abbu da Yan gidanmu,Bulala
Abbu ya tanada Yana jira na dawo,mutanen gari Ana ta surutu Ina iskanci da Mahaukaci Dan na
ganshi Kyakyawa iskanci na harda mahaukata nakeyi.
Babu Wanda ya nuna min a fuska har na Shiga gida,Ina tunanin me Hajiyarmu zata yi min ba
goro Babu kudin goro,ina rabe rabe na Shiga gida,Hajiyarmu tace au Ashe ma kin siyar har
nace Zaki gane kurenki nawa kika siyar kawo a irga kudin Lallai kina so nayi Miki kayan kitchen
me kyau idan auren yazo inye watarana kirkinki yawa ne dashi.
Ina Ina na fara nace Uhm...wlh ba laifina bane Dan Bature na bawa jira ya bar Yara suka
kwashe,Dan meeeeee kikace? Hajiyarmu ta tambaya tana turo min kunnenta daya tare da
karkace wuyanta, Bature na Bata amsa kafin na rufe Baki ta gasa min mari, ta hada kaina da
bango ta gwara min guf tuni na kwalla ihu ina neman agaji,Abbu ne ya shigo da Bulala ya kulle
dakin ya Shiga tafkata Yana dama taraki nakeyi abin kunyar da kike jawo min ya isheni gwara
na hallaka ki da Hannuna, bulalansa sai da suka karairaye a jikina yayi min jina jina,fuskata da
jikina sun kumbura Sunyi shatin bulala, Hajiyarmu tana Kara Mata Malam.
Anty ta sheke da dariya tace yarinya anga me kyau Oh duniya yanzu ba a soyayya Dan
Allah.
Haka mazan gidan harda Mahmood suka ce Suma sun daina kulani tunda bana Jin magana
Ina Bata musu Sunan family bana jin magana,Ya Salman yace kin San Halin Abbu da
Hajiyarmu idan kinwa kanki gata to ki daina kula wannan Mahaukacin wlh matukar Baki daina
ba Babu mu ba Ke,a hankali nace ai kuwa wlh sai dai a kasheni Kuma kowa ma ya daina kula
Ni din Amma bazan fasa taimakonsa ba.
Haka kika ce? Cewar Ya Salman nace ae sai dai kuyi hakuri,Baki bude yace to muma ba
ruwanmu dake,nace ae kowa yayi harkarsa, Hajiyarmu ce ta Kara kwarfeni da Mari ta harbo Ni
tsakar gida Ina kuka .
Sai Dana kwashe kwana uku Ina jinya ko fita banayi,Amma duk da Haka tunanin Bature nake
ko Yana Raina so nake kawai na warke na Nemo shi.
Abbu Kuma sunyi meeting da Yan uwansa za ayi min aure Nan da sati Uku da Wani dan
uwanmu Dattijo ne ma Talle, Talle yace Yana so na a bashi ai kuwa Abbu yace an Gama ayi
shiri Amma Kar a Bari na sani sai dai naji kawai an daura,Akan Haka Ya Salman yace gaskiya
baza ayi min Haka ba,Amma Abbu ya zazzageshi Dole ya kyalesu.
Bayan naji sauki na kwaso shardarsa tare da Singlet da boxers Dana kwaso na bashi na Ya
Salman ya Sa,Sabulun wanki da Omo na dauka a tsakar gidan na zage na fara wankewa,gashi
yamma tayi kowa Yana gida Musa da Salman tare da su Hajiyarmu mamaki ya kamasu, yanda
na zage nake dirzar kayan Mahaukaci,Su Salman da Anty suka Shiga sheka min Dariya irin
Nima na haukace,Abbu ne ya shigo yaga na wanke farar shadda fari tas Malam tana daukan
Ido, faraarsa ta fadada yace ah Lallai yau Ashe Ladan mahaifi ake nema harda yi min wankin
Kaya,Ya Musa suka kwashe da dariya tare da cewa Abbu kayan saurayinta ne Mahaukaci take
wankewa ta bashi kayan Ya Salman ya canja take wanke nasa,kalli Singlet din da Boxers
kalarsu daban,Amma duk inda wannan guy din ya fito masu hannu da shuni ne.
Nan take Abbu ya Bata fuska yace Allah wadaran naka ya lalace ya mace daya tal ta buwayi
mutane,Sha shashar banza, na kusa maganinki ya shige daki Yana fada ba ji ba gani,Ni kuwa
naci gaba da wankina har Waka nake rerawa.
Bayan kayan sun bushe daf da Magrib na goge su tas,Kuma kamshin turarensa suna jiki Bai
fita ba duk sun bulle gidanmu da kamshi, da dare na saci jiki na Kai rigar shagon tela inda
kamar kusa ta yaga na bada hamsin aka dinke Dan wurin sannan na gyara ninkin na saka
kayan a akwatuna.
Washe gari wajen Ya Musa naje nace ya ranta min dari biyar, da kyar ya bani,na fita na siyi
sabulun wanka Giv da soson wanka sabo na saci jiki da kayansa a Leda har brush da komai,Ina
fita waje ikon Allah na hangoshi a kofar gidan mu nesa kadan ya zauna a jikin bishiya abin
tausayi sai kallonsa akeyi kamar watan Ramadan, Yana ganina ya saki wani Murmushi Wanda
bani kadai ba har mazan ya sumar dasu dimple dinsa ya loba kyawawan hakoransa suka
bayyana,cike da takunsa na gadara ya nufo inda nake Nima Murmushi na Shiga yi ba tare da
na sani ba,kamar me hankali ya karbi ledar Hannuna ya bude ya duba sai Naga ya hade Rai
tare da turo Dan lips dinsa, Yunwa kake ji? Na tambaya Kai ya daga min Alamar yaji me
nace,Hannuna zai rike na boye hannun nace ba kyau zo mu tafi na Masa da Maganar
kurame,Muka jera gwanin birgewa sai labari nake Masa Amma kamar da dutse nakeyi.
Ban tsaya ko Ina ba sai bakin titi shagon aski muka je dashi,da kyar na lallaba ya Shiga
Haka Zama a kujerar ma Nasha fama dashi,nace me aski na Yan gayu Zaka Masa Dan kadan
zaka rage Masa sumar ka Masa gyaran fuska sosai haka kuwa akayi sai gashi ya Kara wani
mugun kyau, nace nawa? Me aski yace kyauta nayi Masa sabo da taimako ne tunda bashi da
hankali kuje kawai.
Cike da masifa nace Kai kiyayi kanka Kar ka Kara cewa bashi da hankali wannan da kake
gani ya fika hankali da baiwa,yanzu idan da Kaine a matsayinsa ai dukan mutane zakayi Dan
kayi Masa aski kyauta shine zaka zage shi ga hamsin Dinka Nan bama son kyautar.
Me aski ya taso da masifa kamar zai mareni Yana kamar ba Ke ba Fadila,kin canja ke da
kike me hakuri da kunya ga kawaici Amma akan Mahaukaci kin lalata rayuwarki,idan Baki sani
ba ki sani kaf garin Nan ba a kallonki da mutunci zaginki akeyi, tsakiya Bature ya Shiga ya
kareni wani kallo ya watsawa me aski sai gashi yayi mukus. Gidan wasu samari na tsaya nace Dan Asabe Dan Allah ku bashi aron bayinku zaiyi wanka
Baki bude suke kallona,Rabiu yace Fadila ko dai kema kin zare ne Taya Mahaukaci zaiyi
wanka?,a wajen nace idan zaku bashi ku bashi, daya cikinsu yace wlh kika sake sai na fadawa
Abbunki kin San dai halinsa,Nan tsoro ya kamani na tuna dukan Dana ci nace Allah baku hakuri
naja Bature muka tafi Rafi da ruwa ke zuwa garai garai.
Da kaina na gwada Masa yanda ake wanka Amma yaki yarda sai na bashi sabulun da soso
nayi kamar na tafi na labe a Bayan bishiya,ya Dade Yana tunani sai Naga ya cire kayansa kaf
daga shi sai Boxers ya Dan Shiga gefen kogin abin mamaki yayi wankansa tas yanda kowa keyi
har ta cikin boxers din Bayan ya Gama ya fito kawai sai na rufe idona Allah yasa wajen ba
mutane ya buya Bayan bishiya ya Sa boxers dinsa Dana wanke da singlet,sannan yasa
shardarsa Tasha wanki da guga.
Ina kallo yayi aswakinsa tas,sai da ya Gama na dawo, na kwashe kayan daya cire na zuba a
ledar.sai Hamma yake da alama yunwa yakeji.
Haka na siyo Masa soyayyar doya da kwai da ruwa na dawo na kawo Masa,hayam hayam ya
cinye ya shanye ruwan da gani ya Dade rabonsa da abinci tausayinsa ya kamani,na koma na
Kara siyo Masa shinkafa da Miya da wake Nan ma ya cinye tas ya watsar da sauran ya Sha
ruwa, sannan nace taso muje yawo kaga gona alama na Masa da hannu ya biyo Ni. Yana Bina muna tafiya Ina ta Masa labari iri Wanda Bai ko kulani ba.
AsmaBaffa
[8/15, 11:43 AM] +234 813 228 4370: í ¼í¿•HADIN KAIí ¼í¿•
4
Official
AsmaBaffa
Gajiya nayi da Shuru din nace Wai ya Sunan babarka ne? your Mum, Mama,
Ummanka,kallona yake ta faman yi da kyar yace uhm? Nace Mamanka Wacce ta
Haifeka,tunani Naga ya tafi me zurfi ya dafe kansa maana Yana tuna abu, da karfi yace
Mum...What? Mum alamar ya tuna,zumbur ya mike Yana Kiran Mum, Palon ya Shiga bi da kallo
daya Bayan daya Yana lekawa tare da Kiran Mum,kansa ya sake dafewa sai Hawaye zarr suke
keto Masa Wanda ya bani matukar tausayi ban San sanda Nima na fara nawa kukan ba,Jin
sheshekar kukana ya dawo da hankalinsa wajena ya zauna da sauri kusa Dani
Yanda yaga Ina goge hawayena Haka ya Shiga goge min da kansa,ji nayi Ina wani Masifar
kaunarsa kamar Dan uwana, Shuru nayi naci gaba da bashi abincin Amma kadan yake karba
yanzu tunani kawai yakeyi.
Bayan mun Gama muka sake yin brush Wanda dama shi ya iya Brush baya gudunsa, nazo
zan canja Masa kayan bacci Wanda Mahmood ne ya siyo Masa har kala biyu ganin ango ne.
Da kyar ya yarda na sa Masa, bed din na nuna Masa ya kwanta fafur yaki,yin duniya yakiya
sai ma kasan ledar tsakar daki ya kwanta,Ganin da sanyi gashi sabon gini ne sai na dauko
bedsheet na shimfida Masa nasa Masa pillow nace ya koma ya kwanta kai Amma yaki sam.
shi kasa zai kwana Dole na kyaleshi na haye bed dina na kwanta bacci ya kwashe Ni,tsakar
dare misalin 2am ya farka naji Yana ta kici kicin bude kofa,Ina kallonsa ya fita na bi bayansa a
hankali ba tare da ya ganni ba,sai Naga ya nufi kofar waje zai bude ya fita, da sauri nayi gyaran
murya tare da kamo hannunsa,Ganin haka sai ya saki Murmushin Jin dadi ya ganni don ya
manta ma tare muke 1room baida tunanin da zai gane,sai ko ya biyo Ni da sauri ya rikeni kamar
za a kwace Masa Ni,muka koma Bedroom,ganin idan har na koma bed nayi bacci zai fita sai na
dawo kasa Nima kusa dashi na kwanta, Hannuna na sarke da nasa bacci ya kwashe Ni sannan
shima yayi bacci again nasan shi mayen bacci ne.
Bamu farka ba sai da asuba na tashi nayi Alwala da sallah shi bacci yake Amma na tasheshi
nayi nayi yayi sallah yaki yi sai hakura nayi dashi, baccinsa yake har 10am lokacin na Gama
gyara gida neat ko Ina Yana kamshin turaren wuta, wanka nayi nasa sabuwar atamfa ta Yar
dubu uku Tasha dinkin Yan burni Riga da skert sunmin daf daf sabo da aikin su ya Salman ne
Yan gayu sune suka kaimin dinkin cikin birnin Gombe.
Ban iya dauri ba kawai nayi irin ture kaga tsiya powder kawai na shafa sai maroon jambaki,
da kwalli abinka da fara sai nayi kyau sosai,gidan naji an kwankwasa na bude tare da lekawa
sai Naga Ya Salman da kansa dauke da food flask kala biyu da na ruwan zafi, farin ciki ya
kamani nace Ya Ina kwana, dariya ya Salman yayi ganin Ina tare da Mahaukaci Amma har wani
cakarewa nakeyi haka Ina nishadi na ko a jikina,Lallai mace indai tace tana son Abu a kyaleta
kawai.
Shugo Mana Yaya Hajiyarmu ce ta Aiko ka? Kin San Abbu yace baza a Baki ko ruwan tea ba
a gidanmu Ni na siyo muku a bakin titi ga tea Nan wannan kuma doya da kwai ne, Zan na
kawo Miki har na kwana uku, Kai Amma na gode ubangiji Allah ya Kara budi gaskiya bani da
kamarka Kana ji Dani fa,Har Palo ya shugo ya zauna muna hira,yace Ina angon naki Wai? Nace
sa Ido kazo kawai? muna dariya nace bacci yakeyi,Kai ya jinjina sannan yace an gaisheki
masoyiya yanzu Wai Allah kika iya kwana dashi Fadila?
Dariya nayi nace kune fa kuke tsoronsa Amma wlh ba wani Mahaukaci bane,Hmm Haka dai
kikace Amma mutumin da ya kusa halakamu kiyi dai a hankali,muna Haka sai ga Dan Bature ya
fito ya tashi daga bacci kenan, Baki bude Ya Salman ke kallonsa yanda yayi uban kyau
haskensa ya Kara fitowa, cike da mamaki yace Wai duk jiya kika canja shi Haka? Lallai Sister
Kya so abinki Dole kema ki haukace wannan ko dai balarabene ko Bature a farar fata ma
samun irinsa sai an tona.
Wani farin ciki ya kamani an yabi Dan Bature,ji yanda kike murna,sunansa Aliyu ko yace? Da
sauri nace ae Mana Ina wani fari da Ido ,dariya Ya Salman yayi sannan yace Allah ya shiryeki
wlh Baki da kunya yanzu Fadila a gabana.
Nace uhm Bari