Showing 36001 words to 39000 words out of 44283 words
Chapter 13 - Hadin kai Part 1 Complete Hausa Novels by Asma Baffa .pdf
komai son danake Masa.
Anty sama ta hau fiya fiya, Linda da Sahr suna tangadi sukayi waje ba kowa sai Ni kadai, a
hankali na lallaba nabi bayan Anty zuwa sama.
Maganarta na jiyo sama sama tana waya, tace A.k wannan sirrinmu ne ba Wanda ya sani a
gidan Nan,daga Ni sai Kai,naso ace kana Jin English ko wani yarenmu Wanda za muna
magana babu me ganewa Amma Kai sai Hausa,hausarta marar fita sosai tace yarona nayi
Masa tsafin..Amma tsafi baya Jin Sa,baya so na,shi ma Dr who nayi na gaji sun rike wasu
banzan iyayensu na tsanesu nayi nayi yaki yi,ita kanta Asiya da kyar na maidata baya a gidan
Nan,miji baya ko kallonta, Karimatu ce kadai na kyaleta itama Dan Ina Amfani da ita ne
watarana, so yanzu abun ya Kara lalacewa,Maganar Dana fada maka din Nan wacce har ka
bani Shawara ga allurar da za ayi Masa kasan nayi,to wlh sakinsa yayi fa ya dawo tuntuni, Ak
yace tabbas sai dai in yaronki Aure yayi Baki sani ba sannan ya sadu da Matarsa,Amma in ba
Haka ba wannan Allurar ta tsafi Bai karyewa Dole sai in aure yayi Kuma yayi sex da Matarsa ta
sunna, ihu ta kwala Wanda ya firgitani, Amma ai na Baki wata in ya dawo hayyacinsa ki Masa
wannan dayar wacce zai Kuma canjawa,da sauri tace yes tunda ya kirani a waya a jirgi na hada
Baki da wani Likita da yaje gani a turai yayi Masa Allurar Amma ba abinda ya canja,bana so
Naga yaro na Yana Ciwon hauka Ina sonsa,wancan ma fa ban San Ina yaje ba,kawai a gidan
Nan ance ya tafi turai na boye Zancen.
Ok Ak kasan Maganar Nan wlh bana so ta tashi Naga kamar yaron zai iya dawo da ita, ka
kawo Idea pls,dariyar mugunta ak yayi yace akwai sabon shiri dana hada Miki Nan da 2wk Zan
Aiko yarona Yana kawowa ki aikata abinda nace na sharadi na,sannan ki samu doctor da zai
Masa wannan a Karin ruwa za a sa Masa a hospital. Kuka kawai nakeyi,tausayin Danbature ya kamani wannan wacce maganace ake Masa
wannan rashin Imani a kanta kuwa,Amma ban San Zancen ba,Jin kamar zata fito ta Gama
wayar na sauka da sauri kasa na bar part din Baki daya,a Dan lungu na labe na share wayena
na daidaita kaina,nayi part din Karimatu azzaluma.
Daga ita sai Kaninta Shehu Niga Yan Matan nata duk basa gida sun fita gantali, Zan Shiga
Palon kenan naji Muryar Karimatu tace ai Ina Nan Ina target Shehu sai na Kori Maryam daga
gidan Nan indai tsafi ne muma sai mu fara gwadawa ai mun San malamai muma tunda na hada
muguntata taki ci Naga yanzu tsafi ke tashe Mata ko wacce tasan gidan Malam,kalli munafukar
Nan Asiya wlh badan Allah ta mallake Ice ba,sai yanda ta juyashi Dan kawai taga shima me
dukiya ne Bayan na Babansa,sannan yarinyar Nan ban yarda da ita ba, Danbature da Alama
Asiya akwai target da take hadawa,in ba Haka ba ka taba Jin zukekiya Haka yarinya kamar ita
tayi kanta ga iya kwalliya ta waye Yar University tace Wai itace Yar girkinta da Ice,yarinya Ido a
soye,ka duba Dr who shima fa kusan yanzu can wajen Asiya yake, Meenal ce kawai a wajen
mamanta,to Nima Naga Ana Bari na a baya,baza ta Sabu ba Dole na mike tsaye.
Naja Cilla wacce shugowar ta kenan tace Umma mu dai ba ruwanmu wlh Yan uwanki ne mu
Amma baza mu je wajen Malam ba,wannan fagen babu mu,da kin tsaya iya muguntarki da yafi
cewar Shehu Niga sarkin tsoro me Maganar Dan daudu yace oh Yaya Wlh mu Kam bada mu
ba,yo me yayi zafi Dan Allah Dan Annabi malaman Nan fa idan ba waazi yake ba kalallahu kala
rasulu to kusan bokayene ki fada wuta,ki siyi jahannama da kudinki,to Allah ya shiryeki,duk
zaluncin da kike Bai Isa ba kinga Ni nayi Nan,Shehu Niga ya fito na buya yanda bazai ganni
ba,Umma tace lusari dandaudu ai Kai kayi asara da Kai gwara Babu dama barinka akayi yafi
sauki.
Cilla tace gaskiya fa ya fada haka rannan Ma fa nasan me kika hadawa Daddy kika saci kudi
masu yawa,haba sister ace Daddy yanda yake rikeki da yaranki,gamu muma gaba daya dangi
mun tare a gidan Yana biya Mana schl masu tsada,ci,Sha, sutura,komai munfi masu gidan ma
mulki Amma sai kina satar Masa kudi me zakiyi dasu harfa kudin Ice dollars kike satowa Kuma
masu yawan gaske Haba.
Ashar Karimatu ta dura Mata Wanda yasa Cilla ta haura sama da gudu tasan Yar uwar Tata
yanzu tayi Mata duka ko tasa Soja ya zaneta.
Zaki fito ne cewar Karimatu.
Da sallama na Shiga Palon,tana ganina ta harareni, da faraa ta na gaisheta,tace to atsugwi
anzo gulma ko,Dole ai Asiya ta koya Miki kinibibi, Haba Umma gaisheki nazo yi Naga na Dade
ban shigo ba, tsaki taja tace to an gode idan Dan Allah ne.
Sama ta hau ta barni Ni daya na gaji na fito kawai na koma part dinmu, gobe in Allah ya
kaimu zanje sauran part din.
Ina Shiga part dinmu Nanee tace ke kuwa Ina kika shiga ko yau baza muci Dinner bane?
Murmushi nayi a nutse nace Umma da Anty na gaisar, ok muje na tayaki Nima na motsa jikina,
muna kitchen da Nanee Ya Aliyu ya shigo kitchen din ya mikawa Nanee wasu files yace Nanee
ajiye min wannan takardun wasu gidaje nane ki hada su a wancan, Ok Cewar Nanee ,Ni Kam
dadin muryarsa nake ji ban so Kuma na kalleshi sabo da warning da Nanee ta min Bai son
kallo,nasan hakan lokacin yana kauye a Mahaukaci.
Takardun Nanee ta karba ta fita daga kitchen din,fuskata ya leka yace Yau ba kallo ne,matar
wani tana kallon Namiji Wanda ba sadakinta a kansa,dariya ta na danne ba tare Dana kalleshi
ba nace Namiji baligi Yana kula matar aure matar wani wacce ba muharramarsa ba Yana
neman Jin muryarta sabo da yaji dadi subhanallah Allah shirya.
Ke me Zan kalla a Nan murya kamar ta zakara matar da Zan aura ai sai anzo kallon ta from
different countries,kishi naji ya taso min na Bata Rai, Bai ce komai ba ya fita waje Yana ki shirya
Nan da 2wks muje na taimaka Miki a Nemo mijinki kin takura Mana a gida.
Farin ciki da murna ya mamayeni burina kawai muje kauyenmu Naga dangina,sannan yasan
Lallai shine aka daura min Aure dashi,tuna maganganun Anty Maryam Mum dinsa yasa
lissafina ya rushe Baki daya, Amma Zan Kara dagewa nasan mene makarin next Allurar tsafin
da zasuyi Masa. Ita kanta Mum dinsu ta fara bincike ko da gaske danta Aliyu yayi aure to yaushe? A Ina?
Wace matar tasa,ihu ta kurma tace karya ne,is a lieeeeeeeeee wlh ko wace sai na kasheta.
Waya ta latsa tare da Kiran Ak tace Ak ko wace Matarsa ayi min duba a gano ta,sannan pls
a daure Mata mahaifa karta haihu har abada.
Ak yace aiki da tsada,tace Zan biya,yace ai tun Allurar da akayi Masa idan ya dawo
hayyacinsa to Matarsa baza ta haihu ba, good Anty ta furta Amma gano min matar.
Da dare Ak ya kirata yace yarinyar tana kusa daku sosai Amma anyi anyi Dodo ya kasa nuna
ta ko sunanta babu wani alamarta da za a gane, Anty ta fashe da kuka tace asirana zai tonu Ak
pls helf me, gobe Zan turo yarona da kayan aikin.
Godiya ta Masa ta zauna hankalinta ya kasa kwanciya .
Washe gari da yamma naci kwalliyata sannan na fito zuwa part din Hajjo, tana zaune Ana
matsa Mata kafafu kamar Babar sarki, Shekara tana zaune ta kawo Mata tsegumi Banda gulma
ba abinda sukeyi, Hajjo tace Wai Alhaji Nasiru shi zaiyi gogaggaya da Dana Sulaiman, Shekara
tace Wai Alhj Nasiru makwafcin mu? Hajjo tace shifa nawa ya Tara Dan ubansa,abinda
motocinsa basa wuce na million biyar duk irinsu yaransa ke Hawa,shi Kuma ta million
takwas,waye shi a kasar Nan sai ciki kamar an kifa kwarya cewar Shekara, Dariya Hajjo tayi
tare da furta ai gani yake yafi kowa arziki musamman Yar Nan tasa Layula matsiyaciya,Ina
zaune Ina jinsu suna ta zagin mutanen gida da makwafta, Shekara ta mike ta bar Palon tana
waya,sai ga Yar Misisi ta zo ta zauna Nan ma ita da Hajjo suka Fara gulmar Shekara ai ta Zama
Karuwa Shekara talatin da biyar taki aure waye waye,yi suke Naga abin bana karewa bane
nace Hajjo na tafi to Algunguma saura naji kinyi gulmarmu ba tsoro nake ji ba ki fadawa Asiya
nayi zancenta,dama itace ta aikoki na sani,ban ce komai ba nayi waje Misisi tana cewa Ni na
tsani Yar Nan wlh Sam hankalina Bai kwanta da ita ba.
Hmm yarinyar data Fadi halin uwarta Wai Masifaffiya ce ai daga ji ba mutanen arziki bane ko
daga Ina suke oho sai wani iyayi take a gidan Nan Wai ita me kyau cewar Hajjo.
Part din dangin Daddy naje duk basa Nan maza da Mata Wai sun tafi biki wasu suna
cenema, part dinmu Zan koma motocin Ya Aliyu guda biyu rada radan gaske sun hadu masu
Masifar tsada suka shararo suka wuceni har kofar part dinsa Naga an tsaya sai da ya Gama
Izza sannan ya fito cikin Shadda light blue yasha kyau kamar ka sace shi,ko wacce Shiga
hawansa take ya iya wanka, labewa nayi Bayan flowers na dinga kallonsa Ina samun nishadi da
farin ciki,har ya kule ciki sannan na tafi Ina Jin wani farin ciki.
Tunani na kusa kwana yau inayi akan ya zanyi Kar na Bari 2wks tayi suyiwa Danbature wata
Allurar daban Kuma,ban San ya Zan bullo ba gashi lokaci na ja,Dole na rage zuwa schl,Ina
Gama aikina Zan tafi part din Anty Maryam duk da basa kulani shaye shaye kullum shine
aikinsu,wani mutum ne kazamin Arne yayi Sallama da bakar Leda a hannunsa,lokacin Ina
zaune kusa da Anty daga Ni sai ita su Linda gaba daya basa Nan,sama suka hau suna wani
nuku nuku,suna Shiga bedroom tasa key tace ya Haka? Ak yace tun last WK zai Aiko Kaya
Shuru,da sauri na labe a jikin kofar, Maryam Anty tace yaushe za a yi Masa Allurar? Saurayin
yace Nan da 3days karki Bari ya wuce 3days ba ayi ba,sannan sharadi Zaki bamu sperm naki
Wanda ba na sex ba,Ok tace ya za ayi a baka Taya sperm ba sex, ya Ciro wani dogon roba ja
yace da wannan zakiyi Amfani da kanki har kiyi realising ki bani na tafi dashi yanzu,ba kunya
tace Shiga toilet,ya Shiga tasa key yanda bazai ganta ba,ita kuma ta bargaje a saman gado tayi
amfani da kanta ta samu abinda take nema sannan ta budeshi ta sallameshi,tuni na bar part din
cike da alajabi.
Addua kawai nakeyi na rasa ma ya zanyi karfa kwana uku su cika,Ina ta faman tunani na
shirya Dining naji kamshin Ya Aliyu Yana baza wajen,Bai ko tsaya ba yace gobe tafiya get
ready, da sauri na sha gabansa nace dan Allah Kar kace tare zamuje unguwa,kace Abuja zaka
je meeting,Ni Kuma Zan sanarwa Nanee zanje ganin gida sai mu hadu a airport mu wuce ba
tare da kowa ya sani ba bare azo Ana Mana wasu tunani daban.
Ashe da ragowar hankalin naki no wahala ya fice abinsa,Nanee na sanarwa gobe zanje
kauyenmu Yayana baida lfy jiki yayi zafi,tausaya min tayi tace Allah ya kaimu Idan na shirya na
sanar Mata,amma kar na dade,.
Abin murna da dare Ice ya sanarwa Nanee zai je meeting Abuja tace Fadila zata tafi kaima
Haka da wa zanyi Hira,dariya kawai yayi yace ai bazai dade ba.
Inda Allah ya taimakemu Ice iya Nanee kawai ya sanarwa zai je Abuja.
Babu wanda ya sani,nayi Shirin sosai kayana kala biyar da tarkacen abin bukata,Shima
gogan da nasa ya hada Driver ya kaishi airport ya sallami Driver Dan kar ya ganni,Nanee kudi
da atamfa shadda ta bani na Kai gida tsaraba,naji dadi,taxi na Shiga zuwa airport, zaune na
hangoshi yana Shan ruwa Eva yaci uwar wanka.
Yaga yanda Nasha kyau ya zuba min Ido kamar ya sanni,tunawa yayi matar aure ce sai ya
dauke Kai gefe, Arabian gown nasa black and sky blue nayi kyau karshe kamar zanje Dubai ko
wata kasa Haka na cakare,kana Nan Kaya yasa white crazy Jean da shirt sea green yasha
kyau babu Wanda zai ce Dan kasar Nan ne ko girman Nan. Yau Fadila za a Shiga jirgi, Bai ce komai ba yace muje Ina binsa a baya aka Gama screening
muka Shiga jirgi,Ina kujerar baya Yana ta gaba Wai sabo da ina da aure bazai zauna kusa Dani
ba.
Ni kuwa Dadi kamar ya kashe Ni gani ga Danbature sabo da rashin zuciya irin tawa,sai dai
bana nunawa kawai mazewa nayi Ina Danna waya,Abu kadan zai juyo ya kalleni,idan Allah
yasa mun hada Ido sai yace daina kallona, kan waye ya juyo Yana kallon matar wani? Banza
yamin,Inda muke a jirginma daban ne wajen masu kudi babu Wanda zai ganka ko kaga wani,
,an fara bamu lemo,ruwa,ko tea,da abinci kafin nayi Maganar me nake so sai yace ruwa take
Sha a Bata ruwa.
Takaici ya kamani shi Kuma harda kaza da fried rice da wani juice yace a bashi, yawu na
hadiya Ina ta cika Ina batsewa ko kallo ban isheshi ba Yana ta ciye ciyensa Ni kuwa yace Kar a
bani komai sai ruwa,ko Sha banyi ba.
Sai na tuna sanda Ni nake Nemo Masa abinci ko ta halin Kaka sai yaci,na bashi ma a Baki.
Bamu Dade ba jirginmu ya sauka a Kano state, Jakar kayansa ta Yan gayu ya Mika min wai
ya gaji ansha tafiya me Nisa bazai iya dauka ba,nasan muguntarsa ce kawai, Aiko Haka na
karba ga tawa wata rantsatsiyar mota na gani tayi parking a gabanmu ya Shiga Nima na zauna
kusa dashi driver yaja mun kame a baya,muryarsa naji yace matsa can, Ina fa jikin kofa Ina
kake so na matsa,rashin kunya zaki min Dan ba a Baki abincin jirgi ba sai fushi kikeyi,
Murmushi nayi nace Akan me zanyi fushi,ke kika sani dai.
Tahir guest palace Naga an kaimu Hotel,nace da Rana Haka har zamu tafi masauki ai
kamata yayi mu tafi neman Danbature gidajen mahaukatan idan mun Gama sai muje masauki
ko?
Duk wannan gajiyar da gwajab jagwab din hanyar Zan iya fita wani neman wani Dan iska
can,sai gobe yanzu Ni na gaji Hutawa zanyi,Kai sai kace mace gaka da kirar cikakkun maza
Amma sai lalaci, Harara ta yayi dama nasan kallo na kike Kullum, dama Ina so na Miki Nasiha
na manta,Sanda na kawo Miki mutane nace ki nuna mijinki,a gabansu kika ci musu fuska sabo
da hankalin ki kadan ne,Dan Adam daraja ne dashi,kowa da baiwarsa,Basu sukayi kansu ba
Allah yayi su,ki daina aibata mutum halitar Allah ne,kema da kika ganki haka ba Wai kin fisu
bane,kin ci musu fuska Wanda a Haka sai da na Basu hakuri sannan na Basu kudade masu
yawa,karki sake ganin mutum ko ya yake ki zagi halittarsa.
Nasan Gaskiya ya fada nace to na daina Astagafrllah, Ustaz na gode.bai ce komai ba.
Room biyu ya Kama nawa da nasa Ni tsoron Hotel nakeji Amma Haka na daure,Abinci yayi
Mana order me tsada lafiyayye naci na Sha nayi wanka na kwanta saman lafiyayyen bed,bacci
ya kwashe Ni ban farka ba sai Magrib,nayi sallah cike da nishadi nayi shirina sosai kamar zani
wani party Nasha kyau na fito Zan zaga gari, arba nayi da Danbature ya fito daga mota shi da
Driver alamar wani waje yaje, yasha kyau shima,kishi naji ko wajen wata yaje,haushinsa ya
kamani na fice fuuu ta gabansa shima Bai nuna ya sanni ba.
Ko Ina ban iya zuwa ba kawai Dan tafiya nayii da kafa na dawowata na kwanta,da dare naji
anyi knocking na bude Ashe abinci ya bayar a kawo min.
Washe gari ma 9am sai ga lafiyayyen breakfast, na shirya 11am yace na fito mu tafi,a motar
jiya Driver ya kaimu asibitin masu rangwamin hankali.
Nasan ba Wanda Zan gani,aka bude muka Shiga,da yaga fari zai ce wannan ne ko? Nace
A'a, Muka Gama zaga har Private hospital na mahaukata babu,yace to muje Hotel Ni na gaji
bazan iya zuwa katsina yau ba sai gobe nace to.
Mun sake kwana sannan muka sake Shiga jirgi zuwa katsina, yau ya daure yace mu zaga a
yau mu tafi Gombe sai Murna nake zanje gida.
Mun Gama zagaye babu kowa Nan ma motar da aka kawo daban da Driver.
Muna jirgi zuwa Gombe yace Kai kirki da tausayina Sunyi yawa sai taimakonki nakeyi,kudina
da lafiyata abin a jinjina min ne,Amma ko yabo na bakiyi ba,sabo da ke na fuskanci raini Ne
dake.
Dariya nayi kadan nace sai wani yabon kanka kakeyi Ni me zance tunda kayiwa kanka.
Muna zuwa Gombe na dinga Murna, yace to wannan garin zamu kwana biyu sabo da Dan
iskan a Nan zai labe da Alama ma yaudararki yayi ya ganki