Showing 18001 words to 21000 words out of 44283 words

Chapter 7 - Hadin kai Part 1 Complete Hausa Novels by Asma Baffa .pdf

16 Mar 2025

3313

office din wasu tana Dan aiki suna biya da tsada
musamman idan mutum ya iya aikin ga Tsafta.

Baki na tabe nace me zanyi a kudu Ina da aurena,Hajiyarmu tace to da surutun da mutanen
garin Nan sukeyi ai gwara ki koma can ko banza ma huta da munafunci, Hajiyarmu ta shawarci
Abbu,shi Kuma yace a dawo lfy Ni da zagin da take jawo min ai gwara ta tafi can tazo Mana da
yawo,Anty ma tace da mun huta wlh. Ya Salman na kaiwa Kara Amma Nasiha ya min gwara na tafi Amma na rike mutuncina da
igiyar da take kaina,ya dinga min Nasiha Kar na bijirewa Hajiyarmu again kaucewa Umarnin
iyaye Yana kawo matsala,ba a son Raina ba ranar da Attine zata tafi tare da yarta Safarau na
shirya da akwatita katuwa na bisu munyi sallama da iyaye Yan uwa da abokan azirki,Ya Salman
ba,Musa,Mahmood har Tasha suka rakamu tare da bani dubu ashirin cash,ba tare da na San
wannan state zamuje a Nigeria ba.
Gani nake kamar Watarana Dan Bature zaizo nemana kauye har sallahu na Bari idan ya
dawo Zan siyi waya acan Zan na Kiran gida mu gaisa idan ya dawo a sanar min.

Ban San birni ba sai da yawo a Shiga a fita bare kudu,Haka muka je Tasha naji tace Lagos
Baki na hangame nace Lagos kuma Hawaye ya zubo min shike Nan Dan Bature bazai ganni ba
har abada Ina zai ganni Ina gari kamar Lagos,Attine kuwa haushi nake bata sai masifa take min
muka Shiga mota katuwa doguwa, ita ta biya kudin da komai muna tsakiyar arna karfe 4 na
yamma motar mu ta hau titi.

Tafiya muke ba ji ba gani Safarau sai dariya take min yanda nake ta sheka bacci,ita Kuma
wayarta tecno take dannawa tana chart,tasa earpiece a kunnenta kujerarmu kusa muke a jere
Attine Kuma tana gabanmu tana sheka bacci,Safarau tace Fadila ungo sa kunne daya na sa

daya muyi kallon Nigerian film a wayata,kafada na make nace A'a ke nifa da nayi komai
arayuwata Wanda ba addini ba gwara nayi tunanin Mijina yafiye min komai nishadi.

Attine ce ta zuba min rankwashi shashasha kina wahalar da kanki akan mutumin da ya
rigada ya manta dake Bai sanki ba marar zuciya, Jin tace Danbature ya manta Dani wani kukan
rashinsa ya taso min na fashe da kuka, Baki Safarau ta rike tace ke kuwa Fadila wanne balain
kaddara ce ta afka Miki ta soyayya? Allah ya yaye Miki,kukana nakeyi har bacci ya sake
kwasheni ban farka ba sai da mota ta tsaya za ayi sallah masu fitsari da siyen abinci ma
suyi,sallah mukayi Attine ta siya Mana kaza da yogurt har gurasa,mota taci gaba da tafiya muna
cin abincinmu har muka Gama.

Sai da gari ya waye 11am muka Isa Lagos lokacin Ana shara ruwan sama Amma Haka
mutane ke harkokinsu abin ya bani mamaki sabanin mu Arewa idan Ana ruwa to ba me fitowa,
Attine ba ruwanta ta tare Mana taxi Muka Shiga sai Unguwarsu ta talakawa Wanda Hausawa
Yan ci rani da talakawan Hausawa da Kuma arna talakawa Yan bariki etc Nan muka nufa,wani
gida me bene sama da kasa duk da cewa tsoho ne ya kwararrabe Amma dai Yan haya ne sama
wasu yare ne Yoruba kasan Kuma na Attine ne ta kama haya.amma ciki yasha gyara.

Palo ne sai daki biyu da toilet sai kitchen ba laifi akwai rufin asiri na talaka, gidan muka
gyara fes sannan Attine ta dafa Mana jallof din taliya da kifi muka koshi sannan muka kwanta
baccin gajiya.

Sai yamma lis muka tashi wanka mukayi da sallah sannan muka daura abincin dare Ni da
Safarau tuwon shinkafa miyar alaiyahu mukayi me dadin gaske ko Attine ta jinjina mana, Attine
tana da kirki ba laifi ga son Dan uwa Bata so taga Dan uwanta cikin damuwa, Haka take koya
min aiki da kayan Yan gayu sabo da Kar naje aiki gidan masu kudi na kasa komai,har girke
girke na Yan gayu take koya min,waya tecno Yar dubu ashirin da biyar ta siya min Nan Safarau
ta dage wurin koya min yanda ake Amfani da har browsing yanda ko girki Zan iya koyar
Abubuwa ta YouTube etc, tace Bari na bude Miki Facebook da WhatsApp Kya dinga rage
tunanin da kike na masifa,Baki na tabe nace tunda dai kin koya min Google da YouTube ya Isa
bana fatan muamula da kowa idan ba Mijina Zan gani ba,Dariya Safarau tayi tace to Allah ya
shiryeki nace Ameen.

Satina uku a Lagos nayi kyau da kiba hasken fatata ya dawo har nafi sanda nake kauye
haduwa lokacin da Dan Bature Yana Nan,Attine sai Jin dadi takeyi tana fadawa Hajiyarmu
kasancewar kusan kullum Attine sai ta Sa min katin waya nayi waya da Yan gidanmu.
Ni kaina Ina Jin dadin zama.watana daya Safarau ta koma can Company inda take aiki a
wani reception Ana biyanta.
Attine kuwa Yar kasuwa ce tana Saro irin su Maggi,Omo,katin waya etc tana siyarwa sannan
itama tana aikin kula da wata dattijuwa Igbo wacce danta Hamshakin me kudi Ne,kullum Ni
kadai ce a gida,yan kudu ba Zama Mata da maza neman kudi,Ni nake aikin gida sannan na
dafa abinda nake so,Lallai cimar mu danan da kudu ba daya ba,su Dole sai anci dadi iya
talaucin mutum sai yaci Mai kyau Lallai Dole sufi mu girma da komai.

Attine ce ta dawo nayi Mata sannu da zuwa,da Murmushi ta amsa min tace kina Nan ke daya
ko sai tunani,a hankali nace ai na rage Auntynmu,da dai yafi sauki ki taimakawa kanki,me kika
dafa Mana? Pounded yam with egusi soup,to Bari naci na huta sai mu fita yawon zaga gari
kema kina ganin duniya,dake Attine kyakyawace itama Yar gayu ta waye sosai,dama na fada
duk danginmu kyawawane masu hasken fata.

Hmm da kin bar fitar Nan Antynmu komai baya gaba na Ni dama Danbature na Zan gani,fada
Attine ta fara min ke Baki da hankali Naga Alama so kike ki kashe kanki akan wani banza
Wanda Bai sanki bama yanzu, Idan Attine tace Danbature ya manta Ni Bai sanni ba shine ke
matukar daga min hankali kamar Ana zuba min garwashi a zuciyata,kukan tausayin kaina na
shigayi sosai har sai da ta tausaya min ta lallasheni,tace Fadila kiyi hakuri kamar yanda kike da
addini ga sallah da yawan adduoi ina so ki fawwalawa Allah lamarin kici gaba da Addua sai kiga
Allah ya kawo Miki canjinsa ko ya hada ki dashi again ba abinda yafi karfin Allah.
Sai kikaga ya dawo ya daukeki,inye ya kaga Fadila ga Dan baturenta ku santalo yaranku
kyawawa,ban sanda na fashe da dariya ba tare da share hawayena na Kara gyara zama, nace
Auntynmu sai fa kiga ya dawo ko watarana? Attine a ranta tana mamakina tace kwarai ma
kuwa,nace Alhmdllh Antynmu ya kamata ki Nemo min wurin aiki na fara zuwa sabo da nayi
sauri na Tara kudin da Zan gyara kaina sannan da yanda Zan kashewa kaina kudi kafin
Danbature na ya dawo Kar ya dawo ya iske banci gaba ba banyi kyau ba,Dariya Attine tayi tana
ganin shirmena zalla.

A fili tace inshallah kin kusa tafiya aiki kema sai dai kizo wajena da yawo Kinga Safarau a
Company nasu har Wurin kwanan aiki ne dasu 24hrs ba hutu Amma akwai samun kudi kema
Nemo Miki inda Zaki samu kudi nakeyi inda baza ki Sha wahala ba.
Murmushi nayi nace Allah yasa.

Bayan sati biyu zazzabi me zafi ya kamani Attine ta kaini asibiti hankali tashe,Bayan gwaje
gwajensu ya nuna Hawan jini ne kadan,jini na ya hau kadan,Doctor yace ya kamata idan akwai
abinda ke damuna na rage na daina damuwa sannan ya rubuta Mana Magunguna Attine ta siyo
min,Bayan na warke Ras,yanda na Kara dagewa da Addua naji sauki a Raina yanzu gani da
damuwa Amma Bata damuna sosai sabo da Qurani Dana rike ya Zama abokina dare da
Rana,Kar nazo Danbature ya dawo ya iske bani da lfy ai abin baiyi ba Sam shi yasa na dage na
rage sabo da Danbature ya sameni lfy lfy muci soyayyarmu.
Tunanina Kullum yanda muke romancing juna,muci abinci tare, wanki tare,unguwa tare,ko
Ina muna tare.

Yau kwana biyar kenan kullum sai Attine ta fita Dani yawon zaga gari gaskiya Lagos ta hadu
domin wani yankin ko a Abuja baza a Sami wuri me kyau Haka ba,sai ko turai shima ba ko Ina
ba.

AsmaBaffa






AsmaBaffa
[8/15, 11:44 AM] +234 813 228 4370: 🏕HADIN KAI🏕









11-15










Official

By
AsmaBaffa








Hajara Atiku sallama (laver),
Zahrau Abubakar Dambuwa
Sadiya Abubakar Dambuwa.
Ina kaunarku wajen Sharhi ga page dinku fans na kwarai.











Na kwashe wata daya da kwanaki a Lagos muna yawan Fita da Anty Attine tana aikena
yanzu na fara sanin gari sosai,kasuwanni super market etc,Yau da Wuri Attine ta dawo tace
maza shirya kije ki siyo kayan kwalliya ke ko kwalliya kin daina sai dai kiyi wanka kawai kisa
Kaya ba kwalliya kamar ba mace ba. Murmushi nayi kawai nace wa Zan yiwa kwalliya? Wanda Zan Masa kwalliyar yayi min Nisa
sai sharrrrr....Hawaye suka tsiyayo min masu dumi,Attine jikinta yayi sanyi tace Dole ki tafi aikin
Nan ko aikin ya Isa ya hanaki tunani, saman kujera na zauna dama hijab ne jikina kaina na rufe
gaba daya Cikin hijab Ina ta kirsar kuka me sa Wanda ya saurara tausayi,Attine tayi
Shuruuuuuu tana ji har na Gama Bata ce komai ba tace zo muje yawo kiga gari,haka muka fita
Ina ajiyar zuciya,wani eatery muka je ta siya mana snacks da Ice cream sai wata burmukekiyar
cinyoyin kaji.

Sosai na Samu nishadi sai na tafi tunanin inama da Danbature nazo wannan wajen ba da
Attine ba, washe gari da yamma likis Attine tace na shirya yau Zan tafi gidan aiki,Attine tace sai

dai kiyi hakuri ba a samu Company ba sai Gidan wata Igbo Ijeoma girki kawai Zaki dinga tayata
a kitchen,mijinta baya cin abincin Yan aiki so Bata son wahala da yawa girma ya kamata
kuma,wata zata dinga biyanki dubu ashirin ya kamata ki bude accnt sai ki dinga Tara kudin,
farin ciki ya kamani har dubu ashirin nace Antyna ai Ina da accnt a gtbank ya Salman yaje Dani
na bude ina da komai a kaina,good cewar Attine Dan Allah ki tsare mutuncinki da
addininki,Kinga gidan arna Zaki je ki kula ki Zama wise, nace inshallah wacce unguwa ce Anty?
Tace Island unguwar masu kudin gaske ce sai wane da wane, idan kika Shiga Zaki ce a kasar
waje kike aljannar duniya ba hayaniya Shuru,gidaje na alfarma.
Matar tayi senator sau uku sannan tayi Yar majalisar tarayya sau biyu,ta rike ambasador a
kasar India yanzu Kuma Minister ce har sau uku Ana Bata mukamin minister ta Tara kudi,mijinta
Steven Defence permanent secretary ne a Nan Lagos ki kula gidane gari guda dauke da
securities ko Ina ga Yan aiki iri iri, yaransu biyu kacal Emanuella da Amaka dukkansu matane
Yan Shekara 36 da 33yrs a turai suke rayuwarsu Amma tace yanzu sunzo Nigeria kafin su
koma.

Hmm to Anty nifa bana wani Jin turanci da yawa,Haka Zaki ta jagalgalawa har ki kware Nima
ai a Haka na koya,Murmushi nayi sannan na hada komai nawa na bukata muka Shiga taxi sai
unguwar.

Unguwar ma ba a barmu mun Shiga ba saida Attine ta Kira Babban yaron Ijeoma sannan
aka barmu muka Shiga da taxi har kofar gidan,gaba daya na rude sai kalle kalle nakeyi sabo da
tsaruwar unguwar, gidan Ijeoma yafi karfin a kwatanta shi karshen haduwa ne gari guda part
part Babu Bata lokaci Yaron Ijeoma Dennis ya Mana iso ko Ina matakan tsaro ne da Maaikata
suna zirga zirga, ganin Palon da muka Shiga sai na susuce ban San Dame Zan kwatanta muku
ba,ga wani sanyi da kamshi ta ko Ina,mun Dade a zaune Ina ta kalle kalle.
Daga baya muka ji wani kamshi na daban ya gauraye Palon tare da kwas kwas na
takalmi,wata dattijuwace Fara irin na Igbo Sai hancin Nan kamar carpenter yasa guduma ya
dakeshi, ga Baki chokoko lebe shaftarere,sai kiba dum gashinta wani kwaikwaye kamar birbiri
ya yada zango a kanta,sai dai gashin yasha gyara Yana kyalli da sheki,Riga ce ta material me
hannun bra har kasa ta sata ga wata sarka ja me kululai kafta kafta,abin hannunta sai Kara
suke da gani arniya ce ta gaske,anci haram an koshi,Zama tayi da kyar tana yanga yanga,kafin
tayi magana sai da ta dauki dogon lokaci mun gaji da jira sannan, Attine ta gaisheta tace Good
Evening ma,Hope u r fine ma? Da kyar tace im fine thank u, Nima da guntun turancina na
gaisheta ta amsa.

Da harshen turanci tace itace me Taya Ni girki? Attine tace itace,hope she's clean? Yes Ma
so very clean cewar Attine, Ijeoma ta danyi Murmushi kadan sannan ta zaro kudi a Jakarta
dubu ashirin ta mikawa Attine tace na Bata Number accnt dina ita a accnt take biyan maaikanta
salary,Nan take ba kuskure na bata, Attine sallama tayi min zata tafi, hawaye na fara ta dinga
lallashina tace ke da zaka nemi kudi kizo ki gyara kanki kafin Dan Bature ya dawo kwana
Nan,wani sanyi naji sannan nayi Murmushi na nace Haka ne Anty sai nazo weakend munyi
sallama ta tafi,Ijeoma tasa wata Charity ta kaini part din Yan aiki.

Ijeoma tace idan har taga kyan aikina sannan kuma tana jin dadin Zama Dani to part zata
canja min na dawo part dinta muna ci gaba da yiwa me gidanta abinci tare, ko part din Yan aiki
ya Hadu kamar bana Yan aiki ba,daki kowa Mata biyu Amma Ni tace a bani daki guda sabo da
kwar jini irin na addinin musulunci,Haka Yan aiki duk nayi musu kwar jini sai Nan Nan akeyi
Dani sabo da musulunci da yawan addinina.

Yau da dare misalin 8pm Bayan nayi sallar Isha Ma ta Aiko nazo zamu Shiga kitchen mijinta
ya kusa dawowa,dama nayi wanka na na canja Kaya naje palonta Wanda ya gaji da haduwa
kallo ta Kare min ta ganni fresh neat tsaf Dani Murmushi tayi hankalinta ya kwanta Dani tace
let's go na bita a baya har hadadden kitchen dinta,muka fara aikin dake kalar abincinsu daban
Dana Hausawa sai tace na dinga dauko Mata Abu Wanda ya kama a yanka tasa na yanka
Mata,Wanda za a wanke na wanke,Wanda za a markada nayi ban samu matsala ba ko kadan
tana nuna min Ina kallon yanda suke kalar abincinsu tana yi tana koya min Nima,muna Yar Hira
sama sama tana tambayata kalar namu girkin Ina Bata labari da guntun turancina tana ganewa
Kuma ba wulakanci ba komai muka Gama na shirya Dining na gyara kitchen sannan tace na ebi
nawa naje part dinmu naci, na eba duk abinda Naga Zan iya ci sannan na Mata sallama, wanka
nayi naci abincina na kwanta bacci da wayata wacce nake bincike a ciki.

Washe gari ma Haka muka shirya break lafiyayye tana jin dadin aiki Dani ga Tsafta ta,yaranta
Yan Mata Amaka da Emmanuella Wanda suka dawo daga turai ne suka sakko Amaka Tasha
wando short da Yar Riga taci kwalliya Wai Shirin fita tayi Nan ga wani gashin doki brown tayi
kyau sai dai fuskar Nan kamar an taka Kashi sai farin kawai shima da Karin Mai,Haka
Emmanuella ita Kuma bakin gashi dogo tasa tana sanye cikin wata Yar Gown da kadan ta wuce
duwawunta itama ta cakare da makeken glass a Fuskarta Baki ga takalmi me tsini sunsha da
jaka masu tsada sai uban farce da suka Sa yasha paint zako zako kamar na horro.

Mum dinsu suka rungume suna gaisheta ita Kuma mundukar arniya tana manna musu kiss,
Wani kato,murjeje,wani dunkulelen gardi Dattijo ne ya sakko Baki wuluk dashi ga sandar girma
ta kudi ya rike a hannunsa wuyansa yasha murjani,wani Zanin atamfa ya daura ga wata rigar
yard me Masifar tsada da kyau 3qtr ce, kamshi kawai suke bulbulawa tare da warinsu na arna,
saman Dining gaba daya suka zauna,Ma da kanta tayi serving nasu,duk abinda suke Ina labe
cikin kitchen Ina gani, naji Ma ta kwalla min Kira Fadila kamar ita ta Rada min Sunan, yes Ma
nace daga kitchen,Mijinta David yace who is she? She is my new House made, the name saund
like Hausa, Ma tace Yeah ofcourse she's beautiful Hausa Girl, very Beautiful girl and clean,that
girl she's different Imfact I like the girl so cool,friendly and Nice.
David yace da turanci ai dama a Hausawa akwai mutanen kirki sosai wasu kuwa Sam Basu
da amana sannan gasu da kyawawa.

Baki Amaka ta tabe tace those criminal Hausa people Mum kika dauko Mana Yar aiki sai ta
harbe mu ko ta saka Mana Bum a gida mun Kone gaba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login