Showing 21001 words to 24000 words out of 44283 words

Chapter 8 - Hadin kai Part 1 Complete Hausa Novels by Asma Baffa .pdf

16 Mar 2025

3305

daya,Dirty people begas, Dariya
Emmanuella tayi tace nawawo Aboki hmm ahhh fear them wooo,Zaki gansu so silent kamar
baza su aikata tsiya ba, Baki Amaka ta tabe tana wani shanye hannu tace Almajiri people.

David Dad yace be quite let them be pls Akan ko wacce alumma Ana samun na kirki Dana
banza,Ma sai lokacin tace Ina ruwansu ma suna maganarsu da turanci Ina ji,a tsorace na fito
kusa da Ma na tsaya nace Good morning Dad, da Faraa yace morning, Suma Yan Matan na
gaida su sai lokacin suka kalleni, Amaka ta zabura tace Chineke God Beautiful girl like u as
House made ahhhh.
Emmanuella sai kallona takeyi kamar zata Hadiye Ni,kyau na ya gigita su,yanda suka yi
zaton ganina ba Haka suka gani ba.
Ma dariya tayi musu sannan tace naje Driver zai kaini kasuwa na siyo abinda Babu ta bani
kudi masu yawa tare da jotter inda ta rubuta komai.

Bayan na tafi suka dinga gulmar Wai bana Jin turanci sosai ai Hausawa Basu damu da ilmi
sosai ba Kuma gaskiya suka fada.
Ban Saba zuwa kasuwa ba Amma Haka na zage na siyo komai, sannan muka Shiga store
Nan ma na jido kayan girki muka dawo na shirya komai inda ya Dace sannan na kaiwa Ma
canjinta tace na rike ta bar min na dinga murna naje Driver ya kaini banki na saka dubu Bakwai
dina a accnt.
Yau da dare Amaka ta kirani Wai na hada Mata fresh Juice na Apple nayi Mata yayi Masifar
dadi Ma ce ta fada musu yanda na kware wajen hada juice, ta harde a kujera tana karanta
jarida na zuba Mata a cup na Mika Mata kenan ta kula da agogon Hannuna,mamaki ya kamata
taga agogo na diamond me tsadar gaske da kyau,kirji na ta kalla taga sarkar Dana sa zoben
azurfar Dan bature.

Tace wannan agogon a Ina na sameshi dake su babu boye boye nace na Mijina ne,tace
zoben fa?nace shima Haka,tace Jesus yanzu kamata Haka Ina da aure?nace ae amma Mijin
bama tare,tayi tunanin sakina yayi tace eyya sorry eh? Nace thank u.
Ta fadawa Dad da Mum tare da Emmanuela suka min jaje,tun daga lokacin suke Jin
tausayina, suka ce a schl Ina na tsaya? Na nuna musu takardu na na ssce ,Ma tace zata sani a
University makarantar kudi, na dinga murna na bugawa Attine waya na fada Mata taji dadi,Haka
Yan gidanmu Ya Salman yafi kowa Murna.
Bayan na kwashe wata guda gidan Ma mun Saba dasu sosai,turanci na ya karu na fara
kwarewa,ga albashina farko da aka min transfer naje na cire dake duk sati daya ko biyu Ina
zuwa gidan Attine,Haka na Kai Mata albashina nace na Bata 20k na dauki dubu goma,da kyar
ta karba sai da taga Raina ya baci ta karba.
Safarau ma Ina Kai Mata ziyara itama tazo min gidan Ma sau biyu,Bayan sati daya Ma ta
kawo min Admission da komai anyi min registration a Health education zanyi Degree na
Shekara uku,na fara zuwa schl ba,driver ke kaini ya dakko Ni, Emmanuela da Amaka suka ce
ya kamata na waye na dinga matsewa cikin kana Nan Kaya,nace mu addininmu sai Miji ake
sawa ko a gida,Haka suka suyo min Kaya kana na iri iri Amma bana sawa ganin Haka sai suka
dinka min su atamfa da materials laces,shadda Riga da skert da dogayen riguna tare da
mayafai na sirara masu kyau,takalma da jaka iri iri, idan kun ganni kamar bani ba,tsofaffin Kaya

na Attine na kaiwa ta San yanda zata yi dasu.

Karatu da aikina nakeyi lfy lfy ya rage min tunani da yawa sosai na Kara girma,kiba skin Dina
tayi fresh sai sheki nakeyi kullum kamar wata Amarya haka nake, ga Saloon Ina yawan zuwa
Ana wanke min gashi na,lokacin dasu Amaka suka ga gashina haukacewa sukayi, Ma ta dinga
mamaki kamar gashin Baturiya. Yanzu tuni na dawo saman Benen Ma a Nan ta bani daki kusa Dana yaranta komai akwai
kayan kwalliya iri iri,gashi Hawa biyu ne,Ma da mijinta a saman karshe yaranta a hawan farko.
Mun Gama girki munci mun Sha nayi Shirin kwanciya Bayan na Gama karatuna na mike jikin
window na dake kallon gidajen waje kullum sai na leka na kalli unguwar da tsaruwarta.
Yau ma labile na zuge Ina tsaye da tea cup a Hannuna Ina kurba wani gida nake ta kallo
nesa da mu sosai kaf unguwar Babu kamarsa a kyau duk da kyan na Ma ba komai bane Akan
wancen gidan,wani daki na gani an kunna Kwan lantarki taram ya gauraye da haske,wata Yar
aiki ce Naga ta wuce da plate, ta sake dawowa ta wuce tare da wata mace dattijuwa fara kamar
Baturiya ban fiye gani tar tar ba Tunda da Nisa,Yar aikin ta sake ficewa Matar na gani ta saka
jajayen kaya wani yadi kamar dodon tsafi Haka ta dawo Fuskarta ta rufe tana motsa bakinta da
Alama magana takeyi,sai Naga ta Zama kamar horro ta Bace bat,tsoro ya kamani Bayan 30mnt
sai na ganta wukil ta dawo inda take da wata tukunyar shirka a hannunta,ta ajiye tare da cire
Kaya ta canja nata na farko ta kashe wuta duf sannan ta bar dakin,steal Ina tsaye bul Naga a
dakin an Kara kunna light wannan namijine fari tar shima kamar Bature Amma Banga fuskarsa
ba ya juya baya rigarsa ya cire gabana ya Fadi exertly jikin Danbaturena sai dai wannan yafi fari
da mirjewar skin kamar ka tabashi jini ya fito,ko Dan Danbature a kauye muke ne ga Ciwon
hauka shi yasa,ga wani uban gashi a kansa Wanda yasha askin irin shegun turawan Nan
mawaka ko Yan film kyau iya kyau,gashin Nan Baki,shi ba gajere ba, ba Kuma dogo can ba,ba
rammame ba ba siriri ba, so nake kawai ya juyo Naga fuskarsa, na bude kofata ta baya dama
akwai corido Dan nafi kallonsa sosai na tsaya a Nan,barin wajen yayi ba tare da ya juyo
fuskarsa ba ko yasan da wata tana kallonsa ba, ya Dade Nima Mayyar naki tafiya,sai gashi ya
dawo sanye da rigar wanka fara Kal da Alama wanka yayi,jikin window dinsa ya tsaya shima
dake facing nawa Amma Sam kasa yake kallo Bai kallo saitin gidanmu ba,
Gani nayi kamar Danbature ne ke min gizo nace Kai wannan idan ma ban samu Danbature
ya dawo ba to Naga Mijin aure,Dole ne ma ya aureni tunda suna Kama, Dole na San yanda
zanyi na Kulla alaka dashi, Kuma sai Naga Danbature na kamar yafi wannan kyau da
komai,sannan ya fishi kira da cikar zati har ma kwarjini da komaima.
Da karfi na kwalla tare da Mika Hannuna Ina tsalle nace Danbature......Baturena
.....kaiiiiii.....Dan fari ....juyo.....Nan...gani .....kalleni......Kai......Malam.....nice Fadila......dolene ka
aureni......gaba daya dake dare ne duk kusan layin wasu da dama sunji Ni, amma ba wasu
Hausawa Basu san me nake cewa ba,shi kanshi Wanda nakeyi dominsa Bai ji ba gani nayi ma
an kawo Masa lemo Yana kurba Yana shafa sumarsa, dagowa yayi kadan sai da na firgita da
kyansa, wannan ai Danbature yafi shi, Amma suna mugun Kama, wata budurwa na gani itama
zukekiyar gaske fara tas tazo ta rungumeshi ta baya.

A fili nace na Shiga uku kaga tsinanniya Karuwa,Anya wannan ko dai Matarsa ce wash na

dafe kirjina, kishinta naji na Kara kwallawa da karfi Ina nunata da yatsa kee....Mayya....matsa
daga jikinsa....Mijina..nane....Arniya.....Arniya....Allah ya tsine Miki na Kara tsalle kamar
zararriya na Dane karfen jikin corridor din nace Mayya....ke...uwarki Ina Mata dakuwa kuwa
Allah yasa karaf ta hango,ban hakura ba nace karbi Nan ungo na Kara Mata zagi da tafin
Hannuna Ambola dakuwa.
Kirjinta ta dafe kamar taga Aljana tayiwa Namijin nuni da ya kalli Aljanna a sama can gidan,ai
kuwa ya kallo wajena gabana yayi mugun bugawa daram kamar Danbature,Amma Ina wannan
ya take Danbaturena kyan fata sabo da hutu ya ratsashi,na tabbatar da Danbature ne ya samu
hutu Haka to ya ninka wannan komai,to me ma zai kawo shi Lagos. Haka na dake na nuna shi da yatsa sannan na sarke yatsuna kana Nan biyu maanar aure, Ido
ya zaro,kiss nayi Masa ta iska sannan na hura Masa ta iska, dariya ta kamashi sai yayi Alama
shima ya cafke ya lika a zuciyarsa dariya na kyalkyale da ita na tafa Masa sannan na daga
Masa Babban yatsa irin Good. Tunawa nayi Ina da aure fa sai na fara istigifari.
Budurwarce ta dinga kwasa dariya tana ganin haukata gani Yar yarinya tace kawai irin Yan
iskan yaran Nan ne kawai yayan masu kudi fasikai,shima Haka yayi tunani sai Naga sun koma
ciki matar ta fice shi Kuma ya gyara labilensa tare da kashe light alamar ya kwanta.

Ban taba samun jindadi irin wannan ba Tunda nake a duniya sai lokacin da muke tare da
Danbature na,fes nayi bacci na tashi,inayin sallah da azkhar na Kara lekawa ta kofar dake
dakina ta baya ko zanga me kama da Danbature Amma ban ganshi ba gani nayi ma an rufe
window din ruf,jiki ba laka na wuce kitchen inda na iske Ma ta fara aikin,na gaisheta muka ci
gaba da aikinmu Ina ta faman tunanin Danbature da mutumin jiya me kama dashi.
Bayan na Gama komai nayi Shirin schl na wuce,su Ma da yaranta duk sun wuce Office Suma
ba zama.karatuna nakeyi sosai.
Yau ma dai dai lokacin jiya da dare Naga me kama da Mijina ya sake fitowa Yana Shan iska
direct window na yake ta faman kallo,katsam na sake Nima fitowa, hannu na daga Masa shima
ya dago min Yana Murmushi,Alama ya min wai na sakko na zagayo gidansu,kafada na makale
nace sai dai shi yazo, katuwar paper ta Zane ya dakko ya min rubutu da Babban Baki Ur Name
pls? Nima na rubuta na nuna Masa ya karanta Fadila.
Hausa girl ko? Ya sake nuna min,Nima nace ae Ashe kana Jin Hausa? Yace ae Babanmu
bahaushe ne mun zauna a Kano,Adamawa, jigawa duk gidanmu kowa najin Hausa nace to yayi
kyau.
A Haka muka dinga Hira sosai cike da nishadi Ina magana da me kama da Mijina.

Yau mun kwashe kusan sati Uku kullum sai munyi Hira da wannan mutumin Wanda yace min
sunansa Doctor who ake ce Masa,kowa na tambaya Dr Who za a nuna min shi da gidansu.
Sosai muka Saba da juna, Amma dare daya ya nuna min manufarsa Yana so yayi xxx Dani
shi manemin matane tun daga lokacin naji bana sonsa na tsaneshi, ba wani boye boye yazo
wajena har gidan Ijeoma ya fada min halayensa da niyyarsa a kaina,zuwansa wajena biyar
tunda Naga ba mutumin kirki bane na daina saurararsa Amma Kuma sai suna matukar Kama
da Danbature.

Ijeoma tayi mamakin alakata da yaron masu kudi Haka Wanda Babu kamarsu a Lagos, ji
akeyi dasu kowa yasan da zamansu.
Yau Sunday kowa Yana gida yau Amaka zata kawo Mana saurayinta Dan Rivers Wanda tare
sukayi karatu a turai Kuma shi zata aura,sosai aka shirya Masa liyafa,matashin Igbo me kudi
gurjeje dashi katon Arne, yazo Ni nayi serving Nasa abinci Wanda sai kallo na yakeyi kamar
maye,Silvester sunansa Ma tabar Palon,Emmanuella Bata nan,Amaka ta mike tace Bari ta
dakko wayarta zata Kira Emmanuella tazo taga mijinta,Yana ganin Haka ya matso kusa Dani
Yana fada min wai yanzu Ni yake so nafi matar da zai Aura Amaka kyau,Amaka karaf a
kunnenta da ihu ta karaso tare da rufe Ni da duka Evil hausa girl, Silvester da sauri ya bar
gidanta, Amaka tace zamu hadu da Kai I will kill u.

Ma ta fito taji labari Haka ta dinga zagina tana Harara ta da kyar na Basu hakuri suka hakura
Wai laifi nane.
Bayan sati biyu Emmanuella ta kawo nata Richard Wanda zata aura a gaban kowa ya dinga
min signa,ranar kaca kaca suka Bata da saurayinta,Nima Ma tace you again ta fara min gorin
abubuwan da suka min wai naci Amana suka kamani suka yi min dukan kawo wuka naji jiki duk
sun kumbura min jiki, ranar Ma ta bani ragowar kudin aikina ta sallameni,duk abinda suka siya
min na kayan sawa da kayan kwalliya sai da suke cika min akwati biyu da komai Basu kwace
ba suka sani a taxi sukace na tafi gidan ubana bazan zauna musu a gida ba,schl Kuma Ina
level 1second semester suka ce naje naci gaba da zuwa har na Gama level 1 na biyawa kaina
sauran shekarun ko na tsaya iya nan na karbi transcript.












AsmaBaffa
[8/15, 11:45 AM] +234 813 228 4370: 🏕HADIN KAI🏕

16-20








Official








By
AsmaBaffa









Ina sonku fans a zubo min Sharhi naji dadi typing kunayi Ina Jin dadií ½í²‹í ½í¸í ½í¸


MAMAN ABBA,HABIBA,AICHA,AUNTY SUMEE,ZAINAB ATIKU SALAMA,MAMAN
MEENAT, OUM page naku ne Yan gayu na.








Katsam Attine ta ganni da Kaya Niki Niki cike da bacin rai kamar zanyi kuka,Attine tace karki

yi kuka fada min me ne ya faru nasan Baki da laifi Fadila,abinda ya faru na kwashe na sanar
Mata,tace to kyalesu idan sun gane gaskiya zasu nemiki na tabbatar Babu Wanda zai zauna
dake Baki Shiga ransa ba Fadila.

Zamanmu Shar nida Attine muyi hirarmu.
Kwana uku tsakani Ma da yaranta su Amaka suka ga amfanina a gidan,suka gane gaskiya
bani da laifi mazan ne masu laifi maciya Amana.
Wayar Attine ce tayi kara Ma ce da kanta ta nemeta tana dagawa ta Bata hakuri tace sun
gane gaskiya da Allah a sani a taxi da kayana na koma,murna da farinci ya kamani sabo da naji
dadin Zama dasu ga kyautata min da sukeyi inyi abinda nake so kamar Gidana,wanda
musulmammu baza su zauna da Yar Haka ba bare har a wani sani a University, Kuma bana so
na daina ganin Dr who me kama da Dan bature.

Inda yake birgeni yanda zaka San wayayye ne idan ya nemi kuyi fasikanci kika Ce no to bazai
Miki Dole ba,Kuma bazai Kara miki Zancen xxx ba sannan bazai fasa muamula ta mutunci da
ke ba,ta Nan zaka San Dr Who ya Gama wayewa baya Dole,sannan kyauta da mutuntawa zai
Miki,sabanin wasu mazan Wanda idan ba wani Abu zasu samu wajen mace ba to fa ba
ruwansu dake.

A ranar Attine ta kaini again gidan Ma da kayana,suka tarairayeni tare da bani hakuri Akan
abinda ya faru,nace ba matsala,Attine Tasha kyautar Atamfa me tsada turmi guda da kudi masu
kauri.
Dr who Bai San Ni Yar aiki bace Amma Yana mamakin musulma a gidan arna,sai daga baya
yaji labari ba karamin mamaki yayi ba Jin Wai Ni me kyau Haka a matsayin yar aiki,Bayan masu
kyau da dama gasu Nan Akan son Kudi sai karuwanci sukeyi suna Zama hamshakan masu
kudi sai kaga mace tana Hawa dalleliyar mota Wanda gidansu Gawayin girki ake
siyarwa,Makkah duk Shekara Ana daukan pics Ana sawa Dan kawai q burge mutane anje
Makkah da kudin Haram anyi shawagi an dawo.Allah ya shirya.

Bayan na dawo da sati biyu Emmanuella da Amaka suka koma London abinsu,daga ni sai
Ma muke rayuwa kowa Yana addininsa, ga schl dina Ina zuwa ina karatu na.
Daga makaranta na dawo a gajiye,Ma tana wajen aiki Bata dawo ba wanka nayi tare dasa
gown marar nauyi iya gwiwa Zama da arna har na fara koya Nima kwanciya nayi na huta.

Wani Cikin Securities ne yazo yace Wai nazo inji Dr who,a wata arniyar mota yazo sanye
cikin kayan likitoci nasa hijab naje, Bai fito daga mota ba ya sauke glass muka gaisa yace masu
Hijab gashi ya Miko min wata Leda cike take da snacks sai Ice cream,Godiya nayi na karba Bai
jira nace komai ba ya ja motarsa ya tafi na koma cikin gida Ina daukan abinda nake so Ina ci.
Satina Uku da dawowa Mijin Ijeoma ya fara shaawata a gidan yanda yaga Ina kwalliya da
gyara kaina,kullum muka hadu sai ya faki idon Matarsa ya dinga min maganganun batsa, na
Masa magana yaki ji ba yanda zanyi dashi,idan yaga Ijeoma Bata Nan sai ya dawo gida daga
Office ya takurawa rayuwata,har schl Bina yakeyi,Ni Kuma Ina tsoro na kasa sanarwa Ma yace

idan na fada zai batar Dani.

Gajiya nayi sabo da ina kitchen ya shigo ya fara shafa min Mazaune Ina guduwa tuni na fara
hawaye Ina fada Masa Ina da aure Amma yaki ji kicif sai ga Ma ta Fado kitchen Ina kuka nake
fada Mata ba laifi na bane wlh gwara ma ta sallameni tunda matsala nake zamar Mata a
gida,karshe Nace na tsani gidan Baki daya sabo da cin mutuncin aure na da yayi bazan yafe
Masa ba.

Ma tasan bani da laifi kawai Haka ta sallameni again salin alin tayi min kyauta me
yawa,sannan tace naci gaba da karatuna zata dinga biya min nayi ta Godiya na tafi gidan Attine
na sanar Mata komai taji dadi sannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login