Showing 27001 words to 30000 words out of 44283 words
Chapter 10 - Hadin kai Part 1 Complete Hausa Novels by Asma Baffa .pdf
page dinku mutanena.
Fita nayi na sameta palonta a sama har kasa na Duka nace Nanee gani, tace Haka nake
so Fadila Yar aiki tsab ta Zama kamar kowa ba Wai son Kai yasa kaga Yar aiki kamar an tonota
daga Rami an maidata kamar dabba, akwai Islamiyya ta Yan aiki daban a gidan Nan,sannan
akwai ta yaran masu gida daban,Dan Haka ki dinga zuwa Islamiyyar Yan aiki wacce akeyi da
yamma duk ranar Saturday da Sunday,ta masu gida kuma Kullun kullum suke zuwa,murna nayi
nace Inshallah Nanee na gode,tace tsaya muje ki gaida kowa Kar abin ya zame min bacin Rai a
gidan nan,.
Tana gaba Ina binta a baya misalin 11am muna fita sai ga dalleliyar mota ta alfarma da gudu
guard ya bude mata shiga tayi tace na shigo mamaki ya kamani a gidan Nan part ma za a je sai
an wani Shiga mota,Haka na Shiga muka tafi,Nanee Tasha wanka cikin atamfa Super Holland,
tafiya kadan a mota muka tsaya,na fita da sauri na zaga da gudu na budewa Nanee mota,ba
karamin dadi taji ba Ina mutunta ta Haka, wani part muka Shiga wanda ya gaji da haduwa Yan
aiki sai sintiri suke yasha gyara, Cikin wani katafaren Palo muka Shiga,wata dattijuwa tsohuwa
ce fara yakunanniya Tasha Lace me tsada da Alama itace Babar me gidan,Nanee ta zube a
kasa tare da sallama Nima nayi yanda tayi, Nanee sabo da biyayya kanta kasa ta gaisheta
Nima Haka Amma da kyar ta amsa sau daya, tace Asiya uwar kinibibi komai ki nuna kinfi kowa
ladabi Wai ke kissa ko to baza ki taba birgeni ba.
Mamaki ya kamani tace wannan Kuma kodaddiyar daga Ina?nasan danginku babu farere
kyawawa haka,Asiya Bata damu ba tace Yar aiki nace me min girki tare da Ice, Baki Hajjo ta
tabe tace Dalla gafara can wai me yiwa Ice girki Ice din danki ne? in ba shishigi ba,Kinga je ku
karata can dallah ku barmin part dina ban son ganinku.
Ji nayi na tsani Hajjo tsohuwa haka muka tafi jiki ba kwari Asiya tana share hawaye, nace kiyi
hakuri Nanee komai me wucewa ne nawa take duniyar,dadi taji a ranta tace na gode Fadila kina
da hankali.
Part din gaba muka je Wanda ka rantse gidan wani sarki ne Nanee tace Nan part din mijinmu
ne Bai cika Zama a kasar ba Amma Ni baya bani kwana na yanzu Fadila,na yarda dake shi
yasa na iya fada Miki ban San me nayi Masa ba yace bazai iya kwanciya ko daki daya Dani
ba,yayi niyyar sakina Ice shine Wanda ya Hana hakan,Kinga Dole naso Dana Ice, tace Ina cikin
wulakanta a gidan Nan,kiyi hakuri Nanee inshallah komai zai wuce mu dage da Addua tace na
gode yanzu naji labari Mijin namu ya dawo shekaran jiya muje na gabatar dake.
Mun Shiga cikin part din Palo Palo kafin mu Isa inda yake,kishingide na hango farin Dattijo
me Kamala da haiba,Wata dattijuwa Baturiya wato Amarya Maryam Maman su Ice tana gefensa
tana bashi abinci Yana ci,itace take ciyar da shi kunya ta kamani Amma Naga su ba ruwansu,
ganin Asiya sai ya hade Rai kadan yace lfy ya akayi? Muka zube a kasa tare da gaisheshi da
sakin fuska ya amsa Mana,tace me min girkice Ni da Ice sunanta Fadila na kawo ta gaisheka,
kallona yayi kadan yace na gode Allah ya taimaka kuje kawai, Amarya Maryam ta hade Rai ta
zuba min tsaki tana min mugun kallo da hausarta wacce Bata iya sosai ba tace Ana kwace min
yaro na kamar uban wanine ya aifa Mani shi, wlh Ana ta kashe min yaro sai nayi daure ku gaba
daya.
Mu dai Shuru mukayi dariya hausar Tata ta bani kawai muka wuce,sai part din Karimatu
uwar gida Nan fa muka Sha matsiyacin kallo ita da yaranta ko kallo bamu ishesu ba muka tafi,
part din Amarya tana wajen mijinta sai kawayenta da Yan uwanta muka gaisa sama sama suna
dauke Kai muka fito sai part din yaran dangin Me gidan Nan fa Naja wacce ake kira da Cilla
tace hmm Yar aiki da kwalliya ayiriri , sadiya misisi tace Ni Misisi Naga ta kaina Wai Nanee daga
kauye take Haka? Ahayye dukkan Yan Matan suka saki shewa, Shehu Niga yace gaskiya Naga
budurwa in da kasan kuluwa tsohuwar budurwata ta kauye, Nanee tace zaku ci ubanku wlh
wannan tafi uwar kuluwa ma,Kuma Kar naji wlh kun sa Mata Sunan banza nasan halinku Yan
iskan kauye da ance anyi sabon bako yanzu zaku kalleshi ku sa masa Sunan banza.
Dariya sukayi gaba daya.
Bayan mun fito Nanee tace yaran Nan Yan iska ne in kika zauna dasu cikinki zaiyi ciwo ranar
Friday gaba daya Family suke Zama ayi Hira aci a Sha zamuje dake kici dariyar su Cilla, ko Ice
da baya dariya watarana Dole suke bashi dariya.
Murmushi nayi nace wato su suke sawa mutum Sunan banza? Nanee tace duk sune suka
radawa kowa suna har Dr Who.zai wahala kema Basu Sa Miki ba.
Murmushi nayi kawai Haka muka Gama zagawa gulmata ko Ina ya dauka a gidan,breakfast
din Dana shirya Naga an cinye komai,nace Nanee waye ya cinye? Tace Ice ne kin San na ebi
nawa na bar Masa nasa,nace to Ni me zanci banci komai ba,Wannan kinfi kowa Shirme kiyi
girki da kanki ki kasa ci,Kitchen na koma na hada cornflakes da Madara Nasha abina a kitchen
din masu wanke wanke da shara goge goge suka fara aikinsu.
Dakina na koma Nasha bacci na har 12:40pm Nanee ta turo me aiki ta tasoni na daura girkin
Rana Ice ya fara Kiran waya,a firgice na mike Ina magagin bacci kaina na daurawa wani Dan
gyale kawai nayi waje Ina tafiya Ido a rufe ji kake Kum munyi karo da wani,kamshi ya cika min
hanci ban bude idona ba na kauce Zan sake hanya naji yace what...Fadila kece a gidanmu Oh
My God,Muryar Dr who naji na bude Ido na kalleshi tar na saki Murmushi gani nayi kamarsu
daya da Dan Bature na bangale Dan bakina na saki Ido Ina kallonsa nace Nanee yanzu nakewa
aikin abinci na dawo Nan,oh dazu kece me kamshin girkin da muke ji? Munci abincin nida Ice
wlh bamu taba cin girki me dadin naki ba bakiji yanda Ice ya dinga Santi ba.
Murmushi nayi Nanee tace ya kika tsaya kin sanshi? Kai na daga Mata tayi Murmushi sabo
da kowa yasan idan Dr who yayi iskanci da mace to ita ta amince bayawa mutum Dole, yace
Nanee ta window din gidan Ijeoma ta sanni wannan ta gari ce karki ji komai,dariya Nanee tayi
tace see u na sani Malam, kan uba wani azababben kamshi muka ji na fitar hankali wajen dadin
Shaka,ban San sanda na lumshe ido ba, wani ne kamar aljani sabo da haduwa sai da na kusa
sumewa sabo da Jarabar haduwarsa, can Naga Yana sakkowa daga sama yasha kyau cikin
wata shadda me tsananin kyau dinkin da kadan ya wuce gwiwa,wandon pencil na shaddar kun
san dai maza yanzu Suma fitted ake damesu, hannun links ya Hadu ya Hadu,sumarsa me yawa
baka me santsi tana sheki yaci uwar wani askin Wanda ya take na Dr who haduwa.
Tafiya yake cikin wata Izza takama da gadara fuska ba Rahma,waya yake dannawa wata iri
Ni ban taba sani da irinta a duniya ba, komai Fari har takalmi, Dr who naji yace Aljani na Nanee
kaga Ice sabo da sanyin zuciya wannan uban kyau Ina zaka je Haka kamar yau za daura ma
aure? Kansa Yana kasa Yana latsa waya na kafeshi da Ido,dariya Nanee tayi tace Dana kenan
tamkar da dubu ga kyau ga iya wanka,gadanga kusan yaki,kainuwa dashen Allah duk Wanda
yace bashi ba,Dr who Yana dariya ya Karasa min nace mishi shima ba shi ba Nanee.
Dago da kansa yayi ya kalli Nanee yayi Murmushi kadan yace da shagwaba Nanee pls
Mana,ba shiri na kwala ihu nace Yeee wlh Allah Danbature nane,na rantse da Allah shine
Mijina,na dira tsalle na dirga a gabansa na tareshi na tallafi kumatunsa da tafin Hannuna na
saita fuska ta a tasa na tsura Masa Ido na sakeshi naja baya farin ciki ya mamayeni,nace
Nanee wlh na San wannan Mijina ne Aliyu sunansa tun Yana mahaukacinsa,sanda yayi Ciwon
hauka aka daura Mana aure a kauyenmu mun kwashe wata 9 muna tare Allah shine.
Nanee tace ke...ta daka min tsawa Ashe Baki da hankali?yaushe wannan ya taba Ciwon
hauka wlh na rantse Miki Bai taba barin gida ba ta sanadiyyar hauka ba face kasar waje da
yake Dan zuwa,tabbas sunansa Aliyu Hydar Amma bamu sanshi da Ciwon hauka ba,sai wani
kika sani,wannan Bai taba aure ba.
Dr who yace na Dade Ina zargin ke mara hankali ce a cikin masu hankali wlh tun sanda kike
min magana ta window yau na tabbatar Baki da hankali wannan Zaki ce ya aureki Dan son Abin
duniya,ihun danayi yasa Yan Mata da samarin gidan dake kusa shigowa inda muke sai ji nayi
hhhhh sun kece min da dariya sunce anga kyau da kudi za ace mijinki ne ta Ina? Lallai Yar Nan
Makira ce,oh wato anga banza ko? Naja Cilla tace mun San mutan kauye da wayo muma daga
can muke,dariya ake ta yi min shi Kuma Wanda nace Danbature ya daskare a tsaye Rai bace ji
yake kamar ya kashe Ni sabo da haushin na taba Masa fuska ya tsani mace ta rabe shi.
Idonsa yayi jajir Nan take ,Murmushin takaici yayi dimple dinsa ya lotsa nace Yeee...gashi
..gashi...billahillazi la ila ha Illa huwa Danbature nane,ka tuna ta kauyen Dingawa can Gombe
wacce ka Mara lokacin hankalinka ya dawo jikinka kayi tafiyarka bayan ka min duka? Galala ya
tsaya Yana kallona,na washe Baki nace pls ka tuna time din wani me machine ya kaika birnin
Gombe motoci da sojoji suka daukeka?
Mamaki ya kamashi ya harde hannayensa a kirji Yana kallona shifa Bai San komai ba,nace
akwai ma zobe da agogonka suna wajena Amma na barshi gidan Attine watarana Zan dakko na
nuna ma wlh Allah kaine,Kuma wlh Ni matarka ce da igiyarka a kaina uku.
Kowa abin ya daure Masa kai.
Ni kuwa na dage nace gashi gashi komai na gane kaine,kune baku Sani ba Amma wlh yayi
Ciwon hauka lokacin da ba Wanda zai iya rabarsa Ni na sanshi na soshi na aureshi na zauna
dashi,Nasha wahala wajen iyayena akansa Amma na jure sabo da sonsa da nake wlh badan
kudi na soshi ba,lokacin da na soshi ko mahaifiyarsa nasan baza ta rabeshi ba a lokacin Ni
kuwa na yarda na soshi....Gau......naji an zuba min mari Ni kike cewa Mahaukaci? Yaushe nayi
Ciwon hauka Dan ubanki kika Kuma fada sai na yankaki,kinji na rantse Miki ba Ni bane yar iska
ki nemi mijinki mahaukaci, banyi Shuru ba Ina kuka nace wlh kaine,Kuma da kasan ko Ni wace
a wajenka wlh baza ka soma daga min ko yatsa ba bare ka mareni,Kuma Kaine Nan Mahaukaci
da Aliyu Hydar Sulaiman da Kai aka daura min Aure,mamaki ya kashe su tunaninsu hada
sunan kawai nayi sabo da naji sunansu yanzu Zan cucesu.
Dariya suka dinga sheka min Ana ganina mahaukaciya har Nanee,kitchen Danbature Wanda
suke cewa Ice Naga ya Shiga ya dauko kwandon tace taliya yace ki tsaya yanzu zamu gane
tana da hankali ko a'a?
Kwandon ya Mika min yace ungo na karba yace ebo min ruwa a ciki na gani Wai ta haka zai
gane haukata Babba ce ko karama Murmushi sosai na kalleshi sonsa ya Kara ninka na baya
nace lokacin da muke soyewa muna Shan love da Kai kana Mahaukaci ai Ni ban ma Haka
ba,marina yayi sosai me zanci dake zakice munsha uban love Dan uwarki.
Murmushi nayi nace ku sani Yan gidan Nan wlh Ina da auren Aliyu Hydar Sulaiman Kuma har
kwanciyar aure munyi sau daya Banda romancing din juna da muke tun Yana kazaminsa
mahaukaci lokacin Bai iya komai na duniya ba.
Dariya aka Kara dauka harda ihu Ice duk tsanar Mata da yayi baya kula kowa yau gashi ance
har kwanciyar aure yayi Wai da ita Yar aiki, idonsa jajur yace Ni Virgin ne Dan kan ubanki, nace
wlh karya ne ba virgin bane Kai an taba yi ye wullu..plate din tangaran ya dauko zai kwada min,
na sheka da gudu Bayan Nanee nace daga fadan gaskiya ta Bayan Nanee ya damko ni na bige
plate din ya Fadi ya fashe Ina ihu nabi ta saman kujera ya biyo ni,sabo da tsokana nace Ina
gudu da Haki,sau nawa Ina maka wanka tas, kullum sai na maka wanka kana cewa My love
Nan Bai fita ba a wanke can,ihun dariya Yan dakin suka Sa,naja Cilla harda tsalle Dan
dariya,Nanee tace tunda bakya ji ke dashi ta haura sama tana Naga abin naki tsokana ce.
Har ya kamo rigata na koma bayan Dr who Wanda ke dariya ganin ba Babba a Palon Ina
haki nace kasan lokacin gajeren wando ma Ni nake sa maka,Mika daya ya damko Ni ba Wasa
sai da na Sha Mari yafi biyar fuskata ta kumbura,ya sameni da wayar charger jikinsa na rawa
babu Wanda ya ceceni ya Zane fes sai da ya farfasa min jiki, Ina ta kuka a hakan ma saida da
Dr who ya karbeni da kyar.
Yace wlh in kina Wasa ki daina kaf gidan Nan tsoronsa akeyi baya Wasa da kowa zuciyace
dashi zai iya halakaki ba ruwansa,yanzu da kike gani ba hucewa yayi ba ki kiyayi haduwarki
dashi anjima ko gobe.
Nanee ce ta gasa min jiki tasa aka kaini asibiti duk inda Naga wani ko wata Yan gidan sai su
kwashe min da dariya,tsoron Dan Bature ya kamani bama naso ko a hanya na ganshi Amma
sabo da sonsa yasa nake labewa na dinga lekensa,abincina ma tunda yasan nice ya daina ci a
part din Asiya Nanee,da kyar ta bashi hakuri ta lallabashi ya dawo Yana Dan karba yaci. Nanee tace karki Kuma zuwa inda yake wlh dukan da zai Miki sai yafi na baya,Haka ban
Kuma Bari mun hadu ba tsoronsa nake ji kamar malaikan daukan Rai.
Har na koma makaranta ban ganshi ba,yau Tuesday Bayan na Gama aikina na shirya cikin
Riga da skert na lace takalmi da jakata iri daya da mayafin duka peach color lace din blue and
peach nayi kyau Amma banyi wata kwalliyar kirki ba,Nanee na sanarwa tace naje driver ya
kaini,ganin Yan gidan Basu da mutunci nace a taxi zanje,ta bani kudi tace kin huta jawo min
magana,karki manta 12pm Dole kizo kiwa Dana abinci,nace ba damuwa na tafi.
Na makara 8am nake da lecture Amma Yanzu har 8 din tayi,da gudu gudu sauri sauri na fito
Haka ta compound na fito, Ice ya fito cikin daukan wanka yayi kyau iya kyau sanye cikin kana
Nan Kaya kyau dai ba a fada Yana kamshi,Ina ganinsa tsoro ya kamani na koma na labe Dan
kar ya ganni Ashe ya ganni ya tsaya jikin wata dalleliyar motarsa yaki tafiya Nima na gaji gashi
Zan makara,na fito Ina lallabawa Zan fice yacewa wani Soja ya dauko Masa Ni,sai ji nayi an
sabani a kafada,kuka kawai na fashe dashi Raina ya baci da aurena Kato ya daukeni,nace wlh
Ina da aure Bazan yafe ba cin zarafin aurena da akayi,a gabansa aka dire Ni na zube a kasa
jikina sai rawa yake nace da aurena wlh kasa za a ci min zarafi,yace oh yanzu ma Zaki ce Ni
mijinki ne? Da sauri tsoro yasa nace A'a karya nake Kai ba Mijina bane,kayi hakuri ka yafe min,
fuska ba Rahma ya kalleni shekeke yace to a gaban kowa Zaki tonawa kanki asiri kamar yanda
kika yi wancen lokacin,kaina a kasa hawayen so Yana zuba nace na yarda Amma don Allah ka
Bari na dawo daga makaranta da yamma,mamaki yayi yasan babu Yar aikin dake zuwa
makaranta sai yanzu yaji yasan Islamiyar Saturday Sunday ta gidan kawai sukeyi.
Kina Yar aiki har wani schl kike zuwa? Nace ae Mana University ma kuwa Yar jamia ce ni
level 2 nake Health education, Minister Ijeoma na taba aiki a gidanta itace take biya min kudin
Niclos University me tsada sabo da kyan halina take biya min,Kai ya jinjina naso na bashi dariya
harda yabon kaina Wai sabo da kyan halinta ya furta a ransa,sai da ya Gama ji yace to ubanwa
ya tambayeki Dalla bace min a gani kafin Raina ya baci na halakaki.
Jikina na rawa na mike da sauri na fice daga gidan Ina godewa Allah Bai min komai ba,da
gudu gudu na nake tafiya ina so na Isa titi na hau mota,rantsatsiyar motarsa na gani tana slow a
titi driver na jansa ya kame a baya Yana Danna waya,Driver dinsa ya ba Umarni yace tafi ka
kwashe min yarinyar can da mota,Driver yayo kaina sosai da mota,na kauce ya bini again na
kwashe da gudu ya biyo Ni zai takeni da mota Naga wata waya an zagaye wani garden da ita
na Kama wayar na daka tsalle na haure na rufta ciki wayar ta yankeni a kafata sosai jini na
fita,ban sani ba a ciki Ashe kusa da miciji Kato na fada ya kafta min Sara a hannuna.
Da gudu na Kara yo tsalle na fito waje ban tsaya ta