Showing 42001 words to 44283 words out of 44283 words

Chapter 15 - Hadin kai Part 1 Complete Hausa Novels by Asma Baffa .pdf

16 Mar 2025

3311

San me yasa ban tuna komai
ba,Amma na fara ji ajiki na nine,Hmm ai nace na gano fa ba Kai bane,takaici ya kamashi yace
to a nemoshi ya sakeki tunda baida mutunci. Nace Nima abinda nake so kenan da Zan ganshi ya sawwake min kawai ko na Samu na auri
wani,idan ya sakeki wa zai aureki nufinki? Nace samari ne Dani fa a schl fa da yawa.
Tsaki yaja kawai yayi Shuru abinsa Yana faman tunani shine ko dai ba shine ba har bacci ya
dauke mu.

Mum Ice Bata San Ina Dan nata ya tafi ba ta Gama bincike ance Yana Abuja,bakin ciki kamar
ya kasheta yanzu ya zatayi ga allurar zata yi expired gobe idan har ba ayi Masa aikinta ya
rushe.ta gigice ga wayoyinsa basa tafiya.
Ni kuwa murna nakeyi Dole sai Bayan 3days zamu dawo lokacin Maganin Allura baida Amfani.

Washe gari da Asuba ya farka ya fita ba tare da na sani ba yaje masallaci tare dasu Abbu sai
ladan yace liman baida lfy sai yau Abbu ya jasu sallah dama watarana shi ke jan sallar idan
Liman bai samu damar zuwa ba,Aliyu yace Bari yaja sallar kawai,yau kowa yaji sabuwar Qiria
na tashi a speaker kamar Shureim na Saudiya, Ni kaina karatun ne ya tasheni na rasa Muryar
waye aka samu Haka kwaro a iya karatun Qurani,su Hajiyarmu ma da mutanen garin Ana ta
tunanin waye wannan Haka sai Wanda suka je masallacin su suka tabbatar wa mutane cewar
Danbature ne Mijin Fadila,lokacin Ina dakin Hajiyarmu ya Salman suka bamu labari Mijin Fadila
ne yaja sallah yau,na dinga mamaki dama Ashe da ilminsa Lallai.
Bayan ya dawo ya samu bana dakin yayi kwanciyarsa yaci gaba da baccinsa Bai tashi ba sai
11am, Brush yayi ya wanke fuskarsa da sabulu a jikin fanfom gidanmu kamar wani mace,shi dai
bazai Shiga toilet ba,muna kallonsa ya Gama,lokacin aka kawo Masa tea,doya da kwai da egg
into egg,baisha tea ba kawai doyar yaci da kwai yasha ruwa faro ya Gama komai, Ni kuwa ban
sake bi takansa ba suna tare dasu Ya Salman abinsu,nayi wankana na shirya tsab komai nayi

naci kwalliya sosai kyau dai nayi matuka,atamfa nasa Light blue Riga da skert ya kamani cif
Ni,lokacin 12pm ya Kira Driver dinsa Wanda suka kawomu jiya sun dawo daukanmu, nace
zamu tafi Amma Zan dawo Ni kadai,Hajiyarmu tace yaushe zamu zo aga gidan naku na
Lagos,gabana ya Fadi na kirkiro karya nace ai iyayensa har yanzu Basu San da auren ba,da
kyar idan zasu yarda sai dai a Taya mu da Addua Amma har yau Ina a matsayin Yar aiki a gidan
daga Ni sai shi muka sani.

Hajiyarmu da Abbu sukace Allah ya kyauta,Anty kuwa sai cewa tayi Allah kiyaye Kar su sa ya
sakoki cab kice aikin banza ne Ashe kina ruwa.
Shuru na Mata ya fito yace muje,nace Zamu tafi har Mota suka rakamu Bayan Danbature ya
musu bulala da kudade.
Da gudu matakan tsaro daya ya bude min kofa na Shiga daya Kuma ya bude wa Danbature
ta daya side din ya Shiga muka musu sallama Ina daga musu hannu muka bar garin,sai da
Naga mun bar kauye naja ajiyar zuciya Ina godewa Allah da Danbature da ya taimakeni ya rufa
min asiri na tsira da mutuncina. Tunda muke a mota yake ta faman kallona nayi kyau da yawa,Abubuwa da yawa yake tunani
a kaina,Ina kallonsa ta gefen Ido na.

yau kwanakin allurar Anty Maryam hudu lokacin yinta ya wuce tuni,tana ta faman Jin haushi
ta gama Tara masifarta sai Danta ya dawo Aliyu zata ci ubansa zaiyi tafiya ya kasa sanar Mata
tana uwarsa wacce ta haifeshi sai wajen Asiya zata ji labarin Yana Abuja,Bata San Abujan ma
karyace daga Ni sai shi muka San inda muke.
Bacci ne ya kwashe Ni a motar Dankwalina ya sabule ya zame ta bayana gashina Baki sidik
Wanda yasha gyara wani ya kwanto a goshina gashi har Dan saje ne Dani me santsi.
Yaune kadai ya tsaya yake ta faman Kare min kallo,mayafina ya zame kirjina luwai luwai ya
bayyana,har gefen Boobs dina Ana hangowa,wani waje ya Danna a motar sai ga wani labile ya
sakko ya raba tsakaninmu da Driver, sai da ya gaji da kallona ya tuna Ina da aure fa ko dai ba
shine Mijin nawa ba.
Tuban muzuru yayi Yana ta istigifari Yana Kuma ci gaba da kallona,ganin Haka yaja tsaki
yasa yatsunsa ya danne idanunsa na mintuna ya bude kayansa tar,ganin ya kasa dainawa sai
kawai ya dakko dankwalina ya rufamin a kaina ya dakko gyalena ya yafa min a kirjina.

Ina bacci ban sani ba na Fado saman kafadarsa na kwantar da kaina baiyi wanka ba Amma
ba Wanda zaice baiyi wanka ba,ga kamshinsa Yana tashi wani shock yaji a jikinsa Wanda Bai
taba ji ba a duniya,na farka tuni naji Ni a kafadarsa wani farin ciki ya kamani ga kamshinsa me
sani nishadi,wani shock nake ji Wanda bazan iya tashi a kafadar ba,sai kawai naci gaba da
baccin karyata.

Shi Kuma ya kasa motsi sabo da abinda yake ji a jininsa,ga wani slow music dake tashi a
motar me shegen dadi, kwanciyata na gyara tare da yin Mika a jikinsa, kamar zai Kama da wuta
Haka yake ji a jikinsa tsabar feeling.

Ya kasa ko motsi gashi Yana so ya janyeni a jikinsa gudun shedan tunda yasan Ina da
aure,Amma Kuma ya kasa katabus,Kara mika nayi na mirgina kirjina na fada Kirjinsa na lafe,
wani Uban Hands-,up yayi Yana ta Mar mar da idonsa kamar Wanda kwaro ya fadawa a
Ido,Wai Dan kar ma shedan yasa ya Kai hannunsa jikina shine ya dageshi sama, ji yake kawai
kamar zai mutu, ganin Zan dauki hakkin bawan Allah na Kara zamewa na koma da kaina
saman cinyarsa ban San anan balain yake ba,na dunguri abar Ashe tunaninsa duk a bacci
nake yi ya wani ja ajiyar zuciya yace ya Allah Zan mutu.

Mikewa nayi da sauri Ina Sosa wuyana Ina bude Ido da kyar irin Nasha bacci,nace auzu
billah kasan ba Kaine Mijina ba kana gani na kwanta jikinka cikin magagin bacci Amma baza
kaji tsoron Allah ka tasheni ba,Bai iya magana ba kawai ya rufe Ido Wanda ya Gama komawa
red. Har Munje airport zamu Shiga jirgin Lagos yace an fasa bin flight muje a mota,mamaki ya
kamani Ashe kawai ji yake baya so ma muyi sauri a koma gida mu rabu,nace in hakane ai
bamu duba me kama da Kai ba a Gombe,mu koma aje lungu da sako,Nan take ya daure fuska
yace babu me kama Dani a duniya kawai nine na yarda,kukan karya na saka nace Allah ba
Kaine ba,to muje Lagos a jirgi zanje kawai na fadawa saurayina Dana ke so ba a ga Mijina ba
kawai aje kotu ta kashe auren a daura Mana aure dashi, tsaki yaja ji yake kamar zuciyarsa zata
fashe sabo da Jin haushin kalamai na,Alama na gani nasan ran maza ya baci nayi Shuru kawai.
Kuma yace mu tafi a mota nace hanyarfa ba kyau,Harara ya zabga min kawai yace muje
Amma sai da ya tsaya a Hotel zaiyi wanka.
Shi kadai ya Kama room a hotel muna jiransa a mota yaje ya dinga darje jikinsa,brush ma
kamar zai Ciro makoshinsa,ya Gama ya shirya cikin wasu shegun kananan Kaya 3qtr da Riga
t-shirt harda wata pcap ta Yan gayu,ba karamin kyau yayi ba kamar a sashe shi kayan daya cire
a hotel din ya bar musu,ya fito hannunsa daya a aljihu daya Yana Danna waya,kallonsa nake
tayi kamar na lasheshi Haka nakeji,sai naji dama yanzu na kwanta a jikinsa ba Dazu ba,kafin ya
shigo nayi sauri na dauke kaina ko kallonsa banyi ba irin Bai dameni ba.

Driver ya shigo tare da Miko Mana wata Leda yace Sir gashi abinda kace a kawo.
Karba nayi na Mika Masa ya karba Naga Guava,Apples, yogourt lafiyayyu,juice,Chewgum
orbit,ya ajiye muka tafi Bai fasa ba yace a tafi a mota,na dinga murna ko banza zanga hanyar
Lagos gani ga masoyina Yana kusa Dani Ina Jin dadina.
Securities din Yan Gombe ne ganin zai Basu wahala ya sallamesu da makudan kudade yace
su koma aikinsu zai tafi a mota daya ta Isa shi da Driver.

Tafiya muke ba tsayawa tun Ina kalle kalle har na gaji,nayi bacci na gaji,munje tsakiyar Wani
daji wasu Yan Fashi Ashe sun datse hanya Ana ta fashi muma harda mu,Na tsorata Ina Jin
labarin Yan fashin Lagos kisa sukeyi,karfin Halin Aliyu ko firgita baiyi ba a nutse ya fita Ni kuwa
gaba daya jikina rawa yake Ina adduoi,Driver ma ya kusa tsuga fitsari,Mata da maza ansa kowa
yayi flat a kasa muma Haka mukayi sai da suka Tara mota da yawa suna karbar kudi suna
sallamar mutane,Wanda baida su a harbeshi.
Aka zo kanmu,suka tashe mu,suka ce kudi, Aliyu yace nawa za a baku? Ogan yace au
tambaya ma kake ku fada ko nawa ne Zan rubu ta muku check,Dariya sukayi Hhhh Lallai me

kudi ne,daya a ciki yace na ganeshi ana nuna shi News yafi karfin kudi wannan ko nawa ne
oga,Oga ya kalleni yace Matarka Ce wannan?yace aa Kanwata ce,sai Oga ya Kira wani
matashi a wata motar yace Kai yace Yi Amfani da wannan,kayi Mana kaca kaca da ita
gabansa,kuka na fashe dashi Ina rokonsu wlh Ina da aure Kar ayi raping dina,Wani ciki ya kawo
Hanu zai kwada min Mari,Aliyu ya rike hannunsa,su kansu kwarjini Aliyu ya musu sosai sai zasu
yi Masa Abu sai su kasa,Oga yace wannan yaron akwai raini,ko Yan mafiya ne wlh dodo bazai
Sha jininsa ba.
Matashin suka dakawa tsawa ka aikata abinda mukace,matashin ya taho kaina gadan gadan a
firgice Yana sabule wando.

Yana zuwa ya finkoni da karfi ban San sanda na mareshi ba sabo da takaici da aurena wani
banza zai rikeni,Bindiga ogan yasa ya saitani Dam ya saketa Aliyu kafin bullet yazo ya tare
bullet ya sameshi ya zube Nan cikin jini.
Innalillahi wa Inna ilaihirrajiun na furta tare da Ihu na saki na fada kansa Ina kuka Ina Ihu da
tumami,Driver ma yayo kansa,Sai mukaji jiniyar Yan Sanda,Nan Yan Fashi suka watsu a Daji da
gudun tsiya.
Idonsa Ice ya bude da kyar ya Mika min Atm dinsa tare da fada min code number yace a
jakana da International passport Ina da visa Usa kaini can,duba wayata zakiga suna Ayman ki
kirashi ki fada Masa,close frnd na ne.. Nan ya lumshe Ido kamar ya mutu Ina kuka.mukayi sauri
da Driver muka sashi a mota.
Wani private hospital muka kaishi can wani garin arna,kuka kawai nake Ina Addua Allah ya
taimakemu Harbin a hannu ya sameshi aka cire bullet ya farfado,sai lokacin na Samu damar
Kiran Ayman na sanar Masa,cikin kankanin lokaci sai gashi. Har yau dai Aliyu bacci yake Bai
San me akeyi ba har mukayi kwana daya da yini. Lokacin Ayman ya karbi komai a hannuna tare da tafiya Dani kawai yasa aka yi min passport
da visa,nace nifa bazan je ba,yace ban San wace ke a wajensa ba Amma bani da time da zanyi
jinyarsa a can ki taimakemu Zan biyaki kudin jinya pls, tunani nayi wata dama ce a guna nace
na yarda Amma nawa za a biyani? Yace 1million karki Bari wani Dan gidansu ya sani kinji?nace
to an Gama.

Aliyu yaki dawowa hayyacinsa numfashi kawai yakeyi Amma Bai ma San me ake ba,Haka
hankalina a tashe muka tafi a jirgi har Ayman, wani katafaren Hospital muka tsaya a Usa bana
kwanciyar hankali shi yasa ko kallon gari banyi ba bana ganewa kawai dai gani a turai dare
daya,sai da yayi settling komai ya tafi tare da bani ATM yace Kar na taba kudin Aliyu ga ATM da
kudi ko me ake so ko nakeso nayi Amfani dashi,sannan ga waya da number dinsa ko me ya
faru na sanar Masa zai Kuma dinga Kira shima.
Wasu turawa biyu ya hadani dasu mace da Namiji masu taimaka min.
Ya hau jirgi ban San wacce kasar yayi ba Kuma.

Can gida Kuma Anty Maryam ta koma wajen tsafi an sake yo Mata Hadi Wanda za ayi,sannan
ta koma gidan boka anyi mugun aiki an gano sunana Fadila Yar aikin Asiya.
Sosai Anty ta gano nice matar Aliyu,an Hado balai iri iri Ana jira na dawo Aliyu ya dawo a

Gama damu.ga aikin Dole sai muna Nan gidan za ayi shi, ita Kuma Karimatu ta shiryo nata kan
Aliyu ya koma part dinta ya bar Asiya, ita zata mallakeshi, hhh Allah ya San gaibu mu Kuma
kaddara ta Fado mun Cale turai Allah kenan me yanda yaso yasan kaza zai faru da Kai a
wancan waje sai ya canja ma waje ta hanyar wata Kaddarar wacce Kai kana gani anyi ma ba
daidai ba kana bakin ciki da kuka,Ashe baka San Allah yafi sonka ba.








🤣🤣🤣




AsmaBaffa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login