Showing 39001 words to 42000 words out of 44283 words

Chapter 14 - Hadin kai Part 1 Complete Hausa Novels by Asma Baffa .pdf

16 Mar 2025

3309

wawiya.

Motoci a Gombe rantsatsun gaske biyu da securities suna binmu a baya,Wai baya Shiga
kauye ba tare da tsaro ba,mutanen kauye suna da matsala aje a dakeshi a banza,sai na tuna
sanda su Ya Musa suka Masa duka Yana Mahaukaci lokacin.
Har kauyenmu Ina nuna musu hanya.

Readers anan za a yita fa.












AsmaBaffa
[8/15, 11:46 AM] +234 813 228 4370: 🏕HADIN KAI🏕






36-40

Official






By
AsmaBaffa








Page dina ne Asmabaffa🤣 Allah ya ji kan Baffa Ameen.









Motocin kawai ake bi da kallo a kauyen Ana tunanin ko wani Senotor ne,ga tint ba a iya
ganin kowa na cikin motar, a hankali ya kalleni yaga Ina ta washe Baki, Baki ya tabe na kalleshi
nace na gode Dan Albarka Murmushi yayi kawai ba shiri,nace zaka ji Ana ce maka Danbature
Dan Allah ka rufa min asiri kace Kaine kawai,ka yarda a Kaine Mijin nawa,idan ba Haka ba Ina
cikin tozarta a kauyen Nan,ko me sukace kace are hane, ko kaji na fada Dan Allah kace hakane
kawai,Bai ce komai ba kawai na dinga rokonsa Amma Bai ce zaiyi ba baice bazaiyi ba,Haka na
hakura jiki na yayi sanyi nasan idan yace ba shine ba dariya za Amin ayi ta gulma.

A kofar gidanmu nace ayi parking,Bayan mun tsaya na hango Ya Salman,Mahmood,da
Musa a majalasarsu da suka Saba zama sunyi kyau da kiba,da sauri na fita a motar,Ya Salman
na Kira tun kafin na Karasa.
Suka juyo gaba daya suka ga wata balarabiya da kyar suka gane nice,Ina karasawa na
Mikawa Ya Salman hannu muka tafa,yace ko waya babu? Nace surprise na muku,Musa yace

kin ganki kuwa haduwa,Mahmood yace da alama an manta da Danbature tunda Baki Kara
Mana zancenba ko a waya ga kiba da kyau,wannan ya nuna tunaninsa ya Kare,nace hmm da
bako muke fa Bari na kirashi,Motar na koma nace ya fito,yau shigar Wani Yard yayi me tsadar
gaske,fadar kyansa Bata Baki ne, kafin kace me Mutane da Yara sun Fara cika wajen ganin
Fadila da motoci harda securities.

DanBature ya zuro kafara daya daga mota Bayan an bude Masa Kofa,takalminsa kawai ya
Isheka kallo,kamshinsa ya feso a garin,fitowa yayi daga motar kowa yace wlh Bature ne daga
kasar waje,wasu suka Fara Fadila tazo tare da Bature,wasu suce ai kasar waje taje watakil
suka taho tare,Amma da suka kalleshi sosai sai sukace mijinta ne Danbature Mahaukaci ya
warke,ta Nemo mijinta.
Gari ya dauka ko Ina, Danbature kallonsu kawai yake yana Jin duk me ake cewa,to Wai shi
yaushe yayi Ciwon hauka ne? Ya Salman gaba dayansu da murna suka tarbi Danbature suna
Alhmdllh ya warke,sannu ya jiki? Fadila ya akayi ya warke? Nace ai tunda ya bar garin Nan ya
warke gidansu ya koma,Ni Kuma a Lagos naje gidansu a Yar aiki me dafa Masa abinci sai muka
hadu muka sake jonewa,yanzu yace muzo yana son yaga dangin Matarsa da garinmu.
Sukace Alhmdllh gaskiya munji Dadi,Danbature Yana gefe yayi galala kawai Yana ji Yana
tunani shi ya za ace yayi aure,kawai Shuru yayi yace in sun gaji sa gane gaskiya.
Cikin gidanmu muka Shiga har Danbature Yana gaba kamar yasan gidan,na matsa kusa
dashi muka jera Dan ace gaskiyane maganata.

Hajiyarmu ce taji kamshi ya bude gida,tana daga daki take kwallawa da karfi tare da masifa
Kai Musa turaren da Hajiya Yabi ta kawo min tsarabar Makkah ka sace min ko,sai da na
gargadeka to ka dawo dashi ko naci mut.....Sallama Danbature yayi cikin kasa da murya, kunya
duk ta kamamu har su Ya Salman Sabo da yanda Hajiyarmu ke faman zazzago masifa daga
dakinta, Sallamarma da fada ta amsa,Dan Palon da Abbu ke karbar Baki muka bude yasha
gyara kuwa Yana kamshin turaren wuta gashi carpet ne me kyau kawai a ciki,sai wata
makekiyar katifa sabuwa ga tudu ga Fadi Tasha bedsheet,Dan Bature ya zauna gefen katifar, ya
Salman ya Kira Hajiyarmu,Anty kuwa tana dakin Abbu suna tare,Ya Musa ya kirawosu.
tuni nayi waje zanga Hajiyarmu,tana ganina tace Fadila kece kika dawo Haka? tana murna
sosai muka gaisa sannan nace tazo da bako nazo,Abbu da Anty sun fito suka ganni,da kyar
suka gane ni,Abbu Fadila ce fa da bako muke,Nan na tsuguna na gaidasu, Anty ta rasa ma Ina
kanta yake ko me zata ce ma ba Baki.
Suna Shiga Abbu,Anty,da Hajiyarmu numfashinsu daukewa yayi na wucin gadi da suka gane
Danbature Haka,Abbu a fili yace Lallai yanzu kake Danbature ba da ba,ikon Allah cewar
Anty,Hajiyarmu tace Kai Dan Nan yaushe ka warke Haka? Abbu yace Sannu da jiki kasha jiki,
Anty kuwa ganin Danbature me kudi haka tace oh ai mun Sha fama da Kai,har na tuna sanda
muke tallafa maka da abinci, oh sai da jarin Zobo na da kunun Zaki ya karye a kanka,Haka
Fadila take zuwa ta kwashi na dari uku taje ta tarairayeka kamar jariri ta baka ka zuke.
Allah sarki ai ansha fama ka godewa Allah ka rugurguza jarin bayin Allah da dama, Yaron Nan
Talle me Lemo kankanarsa kullum ba yankewa, Abbu ya kafe Danbature da Ido yace to yaro
Wai ya akayi ne Fadila yi Mana bayani Yata Ina kika tsinto abinki? Yanda na bawa su Ya

Salman labarin karya Haka na sake bada labari.

Abbu yace Allah me iko Yar Nan a kansa kika kaini Kara wajen Yan Hisba oh...yiiii Abbu ya
fashe da kuka yaga kudi Wai Dan a tallafa masa,Shi dai Danbature kansa ya kulle Haka kawai a
dinga kala Masa cutar Hauka,Ba yanda zaice su yarda kawai sai ya karbi taimakona ya sauka
kasa sosai ya gaishe da Abbu dasu Hajiyarmu kamar gaske,Dadi ya kamani, yace Alhmdllh na
gode kwarai da kulawarku a kaina na warke yanzu Kuma Allah ya hadani da wife dina nazo
dama na ganku ne na kawo gaisuwa.

Anty tace ba komai wlh sannu da kokari ai kasha jiki,Hajiyarmu tace jarin goro da yarinyar
Nan ta karya min a kanka ya baci,Dan kudina ta bankada pillow ta dauke ta siyo maka kayan
dadi,kunya ta Kara kamamu yanda iyayenmu ke zubar da mutuncinsu gaban suriki, Ya Salman
tuni Sunyi waje sai gasu da lemo kala uku harda Maltina,Ruwan roba. Hajiyarmu tace gashi tuwon shinkafa mukayi miyar kubewa danya ban sani ba ko baya
ci,Murmushi nayi nace ai wannan da kike gani saukin Kai gareshi zai ci.
Haka na kawo Masa tuwo Nima na ebo nawa,baya son ci Amma sabo da Kar suji Haushi na
dinga Masa signa da Ido da kyar ya daure yaci kadan, yace to in kin Gama mu wuce ko? Abbu
yace Haba Haba kawai ku kwana gobe sai ku tafi Amma kuzo yau ku koma yau bazai yiwu ba
sai Gobe,kamar yayi kuka Haka yaji.
Abbu mamaki ya hana zuciyarsa sukuni tunda ya fita waje yaga motoci da Sojoji, Anty da
Hajiyarmu suka leko suka Sha kallo, Allahu Akbar kaga kudi inda suke ,kudi na inda suke cewar
Hajiyarmu yaro kamar shi yayi kansa,nayi dacen suruki,Anty bakin ciki tuni ya cika Mata zuciya
Yar kishiyarta ta samu me kudi,Hajiyarmu ta kalla shekeke tace ke mene bakiwa mahaukacin
ba? Kin manta Sanda kike cewa karta zuba Masa abinci a kwanonki me kyau sai dai ta dauki
tsohuwar langa wacce ta farfashe tayi kwatsa kwatsa shine yanzu anga kudi ko? Hajiyarmu
sarkin fada Nan suka fara musayar yawu sai da Ya Salman yazo ya musu fada,Ina dakin da
Danbature yake muna Jin fadansu rangadadau kunya duk ta rufe ni,Abbu ma Yana ji muna tare
ya mike ya fita Yana kaci abinci Aliyu kaji,tunda Danbature ya shugo baiyi ko digon Murmushi
ba sai sau daya da zai gaishe da iyayena.

Su Ya Salman ma ganin ba wata magana yake ba sai Izzar tsiya sukayi waje abinsu,Ya
Mahmood yace cuta ma fa tana tarar da Hali,ko sanda yake da tabin kai karku manta haka
yake,baya magana sosai sannan baya wata dariya sai in Fadila ya gani itama ba sosai yake
Mata ba.
Shuru yayi Yana ta faman tunani shi yaga ta kansa har yaushe yayi Ciwon hauka aka Masa
aure karya ne bashi bane da sauri ya kautar da tunaninsa cewar karya ne kawai dai zai taimaka
a bar kauyen a Haka.
Abincin fa?nace Masa kadan ya kalleni yace kin san Ni bana cin tuwo ko dazu ma karfin Hali
nayi naci, a gida Kuma Haka nake bawai ko wani abu ba, ledoji bakake na ebo a jaka ta na
shirya su tuwon da aka kawo Masa na kwashe rabi a leda,miyar ma Haka na daure nayi Leda
cikin Leda yanda baza bule ba na bude Yar jakata ta kayan sawa na saka a ciki na zuge idan

min fita sai na jefar.
Na zauna gefe naci nawa,na kwashe kwaninkan na maida musu kaf,sai Murna Hajiyarmu take
ta bude kwanonsa tace yaci Ashe Kai gaskiya baida kyankyami,waya yayiwa securities kawai
su koma cikin garin Gombe gobe sai su dawo,shi ya zaiyi ance sai ya kwana, shi ya jawowa
kansa daya biyo Ni yazo kauyen.
Da yamma Abbu yace sai mu fito mu zaga dangin iyaye,ba yanda ya iya Bayan munyi Sallar
laasar muka fito, sai da muka Isa can Bayan gari daga Ni sai shi da ruwan roba a hannunsa
yace jira Kuma ki juya bayanki fitsari zanyi,nace da ka Shiga toilet tun a gida yace bazan iya ba
ko wanka bazan yi ba har mu tafi gobe, Shuru nayi kawai na juya bayana yayi fitsarinsa da
tsarki yace muje.

Muna tafiya Ina Masa labarin irin yanda mukayi rayuwa da Danbature na Yana
mahaukacinsa Ina nuna Masa wuraren da yake Zama da yanda yake komai,nayi hakane Dan
ya tuna Amma saima dariya da yake kwasa watarana kuma yaji tausayina,Gidan da me gari ya
bamu mukayi rayuwar aure na kaishi Ya Salman na Kira a waya nace ya karbo min aron key
wajen Mai gari zamu dauki wasu Kaya, Aiko cikin sa'a ya bayar na bude gidan duk yayi kura
komai namu Yana Nan inda yake nace ga gidanmu da muka zauna dashi kalli komai Yana
Nan,muka Shiga na nuna Masa ko Ina,Yana mamakin rayuwa da Mahaukaci.
Shuru Aliyu Bai ko San munyi rayuwa a gidan ba,yace na jinjina Miki da kika iya kula dashi
Haka,Allah ya dawo Miki dashi Kuma Allah yasa ya soki shima kamar yanda kike sonsa,Allah
yasa ya Miki son da yafi Wanda kike Masa.

Ameen nace na Ina goge kwalla ta a boye Kar ya gane,tausayin kaina nakeji Bai gane komai
ba,na rufe gidan muka tafi zamu Fara gaida me gari,Mutanen gari Majalisa majailisa kowa har
Yara Ana ta tayani murnan ganin Danbature ya warke,ko Ina Zaka ji Yara Suna kwalawa Aliyu
Kira Danbature... Danbature sai binmu sukeyi,manyan Kuma hannu kawai suke bashi suna
gaisawa Ana Masa murnar warkewa, shi dai kallonsu yake a mahaukata Yana biye musu da
Faraa kamar ya sansu ana gaisawa,Ni kuwa murna nake ya rufa min asiri banji kunya ba,duk
inda muka je kawai kudi yake rabawa Yara da manya ba ji ba gani,wasu Kuma ya zuba min a
jakata yace ungo kina bawa wasu.

Ta wajen Talle me Lemo muka bi Yana ganinmu ya mike tsaye yace jar uba Ashe da gaske ne
me kudi ne Kuma ya warke,Kaga Danbature wlh da gaske ikon Allah,Dariya Danbature yayi Bai
mikawa Talle hannu ba Talle ya fito daga rumfarsa sai gani mukayi ya cafki Hannun Dan Bature
yayi gaisawar Dole dashi,Yana yashe Baki yaki sakin hannun Yana girgiza hannun Danbature
Yana jero gaisuwa muna lfy,ya gida,ya aiki,ya birni,ya mutan birni,ya aiki,manyan naka
kalau,Kuna lfy kun samemu lfy, Danbature yace lfy ya gaji da amsawa gashi yaki sakin
hannunsa,gashi tafin hannun Talle duk kaushi,da kyar Ice ya janye hannunsa ta karfi,Talle yace
oh hannu kamar adduga haka Kuna Jin dadinku,kudi ya bashi da Dan yawa, Talle sai Godiya
yake harda cewa Lallai Dole ka kasa ni a wajenta. Lemo ya zuba a Leda da yawan gaske yace
za a Aiko muku dashi gida,nace ka barshi baza mu cinye maka jari ba.

Gidan me gari muka je,Me gari ya dinga mamaki da murna,nace shine ya bamu gidan da
muka zauna,Nan Danbature ya dinga zuba Godiya kamar gaske ya bawa me gari Dubu Dari
kyauta.Me gari kamar zai haukace sabo da murna.
Bayan Nan Munje wajen Wanda ya bamu kayan abinci,Wanda yayi min kayan daki sosai ya
musu kyauta ta ban girma,sai Addua da murna suke Mana,Ya Mahamood na nuna Masa nace
shi ya biya Sadaki,shima Dubu dari biyu ya bashi,sannan yace ya bashi takardunsa zai canja
Masa wajen aiki a Gombe,Haka nace Ya Salman farko aure shi ya dinga kawo abinci lokacin da
iyayena suka gujeni,Shima ya bashi nasa,Ya Musa Haka,sannan duk ya karbi takardunsu,
harda wasu kannen ya Mahmood yaran Kawu Usman da kawu Salisu mutum shida ya karbi
takardunsa da suka Gama degree yace aiki a Gombe city inshallah, Kawu Salisu ma sunsha
kyauta,matansu gulma ta koma ciki,Haka Kakanninmu,danginmu kaf sunci arzikin Danbature
harda mutanen gari.
Ni tsoro ma naji irin kudin daya kashe ya wuce tunanin me tunani,ko na hanashi sai yace ba
ruwana.sai dare muka dawo gida.

Ya Salman ya shirya Mana liyafa Gasashiyar kaza,Yan Shila,lemuka,fresh yo,ga chips
hadadde.
Saman katifar ya kwanta Yana huce gajiya Bayan yayi sallar Isha a masallaci tare dasu Ya
Salman har Hira suka danyi ba laifi.

Ina wajen Hajiyarmu muna ta Hira ta uwa da yarta, shi kuwa tuni yaci duk abinda Ya Salman
ya kawo,ya kwanta Yana Hutawa sannan ya fita waje inda Suke taruwa ya zauna cikinsu Ana
Hira jefi jefi yake Sa Baki,Bayan ya gaji 10pm kowa yana gida,ba yanda Ya Musa Basu yi dashi
ba kan ya Shiga toilet dinsu yayi wanka yace bazai yi ba,Wai kunya yake ji gidan surukansa
ne,dariya sukayi sun zata gaske yake yi,Ni kuwa nasan kawai fada yayi.

Da dare nayi Shirin bacci dakin Hajiyarmu tace in Banda haukarki Fadila ai wajen mijinki
zakije ki Taya shi kwana,shi kadai a daki ba kowa ai bazai ji Dadi ba,ga su Ya Salman Suma ba
dashi zasu kwana ba, nace kyaleshi Ni a Nan Zan kwana,Hajiyarmu ta dinga masifa ta koreni
Dole nasa hijab na tafi dakin Anty itama tace can Zan tafi ta koreni da gorinta iri iri. Na Dade a tsakar gida to ya zanyi Ni Kam,Zama nayi a tsakar gidan kawai sai ga Aliyu ya fito
ya gaji shi kadai kamar maye, a waje ya ganni yace an koroki ko? Ke karamar kwakwalwa
gareki kamar Baki sanni ba ai da sai ki zo ki fada min sai ayi wata dabarar, taso mu tafi,Mikewa
nayi nabi bayansa yace muje zamu je yawo sai mu rage dare a waje can wurin 12am mu dawo
sai ki kwana a zaune a kasa,ni Kuma Ina saman katifata tunda ke kika Jaja min masifa Allah ya
gani kina matar wani Zaki sa Allah ya konani.

Haka muka je can waje ga sanyi anayi muna zaune kowa yayi Shuru shi waya kawai yake
latsawa.
Mun Dade nace zaman Nan bashi da amfani kawai mu koma gida,muna komawa gida kowa
ya kulle kofarsa Shuru gidan,hanyar dakin Hajiyarmu na bi yace bakya Jin magana ke ko?na
dawo na bi bayansa Yana zuwa ya fada saman katifa ya kwanta.
Nima na kwanta can karshen dakin a kasa saman carpet.

Tunawa nayi da rayuwarmu ta baya yanda Muke kwana Shimfida daya,da Romancing dinmu
na wani Feeling nake ji,Shaawarsa ta darsu a Raina sai mutsu mutsu nakeyi na kasa bacci na
tsurawa bayansa Ido ji nake kamar na kwanta a bayansa na rungumeshi,a Raina nace Kuma
ace ba Kaya a jikinmu Wai da naji Dadi,tsaki naja kadan na Kara juyawa baya,shi Kuma ya juyo
ya tsurawa bayana ido,Yana tunani yanda ake cewa Ni Matarsa ce,duk da Hijab din dake jikina
Bai Hana shape dina fitowa ba Nan ya Kare min kallo,ji yake kamar ya sanni tin da,Kuma ma
me yasa idan Ana cewa Mijina nane yake Jin wani farin ciki da nishadi, Wani birgeshi yaji
nayi,tunani yayi matar aure ce yayi sauri ya sake juya baya can.

Can dai yaji tunanina yaki barin zuciyarsa sannan ga wani Abu dake Masa yawo a zuciya
abin yayi Masa yawa,can abinsa ya ciyoshi a hankali ba tare da ya juyo ba yace kika Ce Ni
mijinki ne dai ko? Ina jinsa na juyo Ina kallon bayansa nace ae Mana da can ba Amma yanzu
na gano Ni ba matarka bace, ba Kai bane Sam,yanzu na gane Kuna da banbanci,Haushi yaji
sosai yace to me yasa Yan garinku kowa ya sanni,Kuma ma ai ke kika fada da kanki Yar rainin
hankali makaryaciyace Dame ke tuntuni?

Nace ae ai dama Ni watarana nakan tsokani mutum na Shimfida masa karyata,yace to karya
kike to nine Nan tunda kowa ya tabbatar nine kawai dai ban

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login