Showing 24001 words to 27000 words out of 44283 words

Chapter 9 - Hadin kai Part 1 Complete Hausa Novels by Asma Baffa .pdf

16 Mar 2025

3304

tace inshallah zata Nemo min gidan musulmai.

Hankalina kwance nake zuwa makarantata sannan muna zaman mu lfy da Attine, na Kara
wani wayewa ga kyau na ya ninka nada,na Kara girma da tsayi shape dina ya fito sosai Duk
Wanda ya ganni sai ya Kara son sake ganina.ina da kawayena na schl Amina da Rahina yaran
mutunci.
Safarau ma ta samu hutu yau tazo zata yi weekend a gida,tace mutuniyar wannan kyau Haka
da Alama an daina tunanin Dan Bature,dariya nayi nace Anty Attine kinji ta ko?ai Yana Raina
har abada yarinya, hmm kin fara chart? Cewar Safarau nace Allah kiyaye, wayata ta karba ta
tura min Hausa novels iri iri ta koya min yanda Zan bude na fara karatu,ai kuwa tunda naji dadi
love iya love ga koyon abubuwan rayuwa yanda zaka kula da Mai gida,na tuna idan Danbature
ya dawo haka Zan dinga nuna Masa love kawai sai na dage da karatu ba dare ba
Rana,watarana Har masifa Attine ke min.
Na waye sosai na Karu ta hanyar karatun Novels Ina yin na schl abina ras.

Bayan sati hudu lokacin mun Gama second semester Ma tayi min registration da komai na
level two muna hutu bamu koma ba,Attine ta rafka sallama ta dawo daga unguwa, sannu da
Zuwa Anty ya hanya, Alhmdllh tace sannan tace kafin na zauna Bari na Miki albishir na samo
Miki gidan aiki gidan musulmai hamshakan masu kudi Ne duk fadin kasar Nan an San da
zamansu,aiki ma idan kika samu a gidan to fa kakarki ta yanke saka, Hajiya Asiya daya daya
cikin matam mutumin ce take neman yarinya nutsatsiya da zata dinga Mata girki wacce ta iya
girki da tsafa girki ne kawai aikinki.

Alhmdllh na huta zaman banza, Attine tace gobe a kaiki sai ki shirya naki ya naki,Family
house ne sai kinyi taka Tsantsan kin nutsu,Bari na Baki tarihinsu kadan yanda naji kafin idan
kinje gidan ki gani da idonki.

Alhaji Sulaiman Araba Lagos shine cikakken Sunan me gidan idan kina Jin radio ko News
Zaki jishi sabo da kudinsa, Dukiyarsa tun ta gado ce shi kadai iyayensa suka Haifa, Babansa da
sauran kannena mahaifansa ko yayye duk basa Raye sai yaransu,Kanwarsa ce daya da
yaranta mijinta ya rasu tana gidan da yaranta part dinsu daban,yaran yayye da kannensa duk
shi yake rikesu suna gidan ko wannensu da part dinsu,Dattijone na kwarai me kirki da son dangi

ga kyauta,bashi da ilmin boko sai business na alatsine uwar me karya kasa kasa bashi da
lokacin kansa.

Babansa ya rasu sai babarsa tsohuwa da ta rage tsohuwa ce wacce take tarwatsa kan
dangi,Bata kaunar zaman lfy,kullum a gulma take tana hada dangi fada ba hadin Kai ko kadan,
Haka kawai zata hada gaba da fitina tsakanin jikokinta da Matan danta.
Hajiya Khadija suna kiranta da Nana tsohuwar banza ce magulmaciya,shi yasa jikokinta ba
wani mutuncinta suke gani ba.

Alhj Sulaiman Araba Lagos Dan Asalin katsina state ne,bafillace ne usul Kyakyawa fari
dashi.Araba Lagos matansa uku Matarsa ta farko sunanta Karimatu Yar garin Adamawa ce,
Karimatu akwai rashin Imani,son Kudi ga Hassada,Dole Mijinta ya Mata Abu ko baya so sabo
da Yana tsoron masifarta. Tana da Yara biyar Habib shine Babba da Matarsa Farida Yana Zama a Abuja,sai Saudat tayi
aure a lagos,sai saddiq Wanda shekararsa 26 ya kusa Gama degree a UK,Ammar 19yrs yanzu
Yana Ukraine,khairat auta 16yrs tana Ss1.

Sai ta biyu Asiya Mai hakuri,nutsuwa saliha ga hankali ba ruwanta.Araba Lagos Bai damu da
ita ba Bora ce a gidan,kowa taka ta yake, yaranta shida,khausar tayi aure itama a Abuja, Yousuf
26yrs shima a Paris ya Gama degree ya dawo gida,saif 23yrs Yana level 2 a China,Khadija
20yrs tana level 1 a India, Kabir 17yrs Yana ss2, Ahmad auta 11 yrs Yana jss1 Nan Nigeria. Yara ne masu tarbiya ba ruwansu.Asiya Yar zamfara State ce.

Sai mowa Amarya wacce tafi kowa fada Babu wacce ta Isa ta kama kafarta wajen me gida,
sai abinda tace Aunty Amarya Maryam kenan Kyakyawar baturiyace ta gaske dattijuwa me
kyau gata itama iyayayenta Yan Paris ne masu kudin gaske ne,Bata auri Araba Lagos ba sai da
ta tabbatar yafi su kudi,kudi ta gani ta aureshi,musulman kasar France ne Amma lalatacciya ce
ta gaske Bata bin addinin nata,iyayen Sunyi Mata fada har sun gaji, itace Shan giya,Shan
wiwi,Bata son talakawa,Bata da mutunci ko kadan,tunda tazo Nigeria take Hulda da Yan kudu ta
koyi tsafe tsafe iri iri wajen arna.

Gata tana neman mazan waje Yara matasa tana Basu kudi,shi yasa taki yarda ta haihu da
yawa Yara uku kacal ta Haifa, mazanta biyu mace daya, Namiji na farko 30yrs yake suna Ce
Masa Ice ance wannan sai kinyi taka Tsantsan baya ragawa Wanda ya Shiga gonarsa,Bai son
kazanta,baya Shiga harkar kowa gashi da zuciya,cikkaken Masifaffe ne,kaf gidan tsoronsa
akeji,sannan Bai son kallo sabo da Yana da kyau ance kamar aljan sabo da kyau ki kiyaye wlh.
Nace to Attine shi ba musulmi bane naji ance wani Ice, hmm yafi kowa addini a gidan musulmi
ne,gidan suna da nickname kowa dashi ake kiransa, Basu da aure ne?sabo da masifarsa suke
Ce Masa Ice, baya ko dariya.

Ae duk Namijin da kika gani a wannan gidan to baida aure,na biyun Kuma Who nickname
nasa shi ance yafi kowa saukin kai,sai dai Yana Shan giya watarana Kuma Yana neman Mata
Amma ance duk yafi kowa kirki,shima kyakyawane.

Sai Autarsu Meenal suna son kanwarsu akanta sai su koreki a aiki,ki kula tana da kala sharri
iri iri mate dinki ce 18yrs.

Maryam Amarya
Ta Gama tsafe Alhji sai abinda tace,farko a jigawa suke zaune tace ya Mata kauye Kano take
so sun kwashe shekaru ashirin a Kano tace Abuja ya maidasu can tace Rivers State Bayan
Sunyi 3yrs tace a dawo Lagos yanzu shekarunsu takwas a Lagos tare da danginsa da Dangin
matansa gidane na Alfarma na fada a jarida.
Sabo da Yana son zumunci yaki raba musu gida yafi so yaransa su shaku da juna su hada
kansu,Kuma abin mamaki yaran Amaryar suna da nutsuwa ance Basu gaji halinta ba Amma
Babban ya Dan dauko wulakanci da izza kadan Kuma baya ragawa duk Wanda ya Shiga
gonarsa. Matan dangi ma duk sun dawo Yan Mata da samarin cikin danginsu ko wacce an Basu part
na Yan uwanta a Nan suke karatu da komai Mijin na daukan nauyinsa.
Yaran da ake rikewa kiyi hankali dasu sunfi Yan gida iya shege Kuma duk farko daga kauye
aka kawosu suka yi clean.

Karimatu uwargida yaran Yan uwanta
Naja (cilla)
Fatiti
Zahrau Yar dagwas
Zulfau zuly kanwarta ce.
Sai maza
Saad Boy 40yrs ba aure.
Shehu Niga 35yrs

Yan uwan Asiya daga kauye
Sumayya(chakwas)
Kanwarta Rahina da kaninta Usaini Usy 27yrs
Sai na Amarya Yan kasar waje da kawarta
David Dan uwa Arne 30yrs
Michael Dan uwa arne 25yrs
Muhammad 26yrs
Irfan 17yrs.
Kawarta Sahr
Sai Linda itama Kawarta.

Shi Kuma kanshi me gidan Yana da yaran Yan uwa maza da Mata sun Kai su goma Sha ko
wanne akwai part dinsu daban tsakanin part da part Nisa ne sosai kamar estate ba abinda Babu
a gidan,masallaci da Islamiyya duk akwai,mota idan zasu Shiga sai driver ya kawota har kusan
bakin kofa,basa muamula da talaka,mutane komai kudinka Basu damesu ba musamman
turawa na Amarya Maryam rayuwarsu daban a gidan.

Fadila Zaki Sha kallo a gidan,Zaki fafata sai dai ki Zama wise karki sake a takaki Kuma karki
Shiga sabgar kowa Amma fa Zaki Sha kudi ki samu iyayenki da Yan uwa suyi Alfahari dake. So
nake ki Dan Tara da yawa Abbu sai yasha mamaki Ina Miki tanadi.
Ki Zama me juriya kawai,Murmushi nayi nace Inshallah ko Dan Na kularwa da Danbature na
jikinsa ai nayi,dariya Anty tayi tace iyye marar kunya,da gudu na kule cikin bedroom na fada
saman bed tare da lulawa tunanin Mijina abin kaunata.

Washe gari da yamma karfe 5 muna taxi Ni da Anty Attine da akwatunan guda biyu manya
shake da hadaddun kayana Wanda Ma ta siya min da komai na bukata ta kun San yanzu fa na
fara wayewa,unguwar su Ma ta masu kudi Naga mun nufa Attine tace kin San masu kudi Ne fa
Dole kiga unguwar su Ijeoma,abin mamaki sai Naga katafaren gidan su Dr who me kama da
Danbature Ashe gidan yafi ma yanda nake zato.
Attine tace wannan gidan Babu kamarsa kaf unguwar Nan bama layin Nan ba,alatu ma sai
mun Shiga karki tsorata Zaki ga ko Ina sojoji da masu aiki iri iri, tun daga bakin gate na Raina
kaina na ganni wata kucaka Dani, ban Gama mamaki ba saida Attine ta Kira Yaron Asiya a
waya ya sanar Mata ta bada Umarnin bakinta ne a barmu mu Shiga gate aka bude kofa karama
cewar baza mu Shiga da kazamar taxi ba gidan, idan ba Motocin gidan ba Babu Wanda ya Isa
ko parking yayi da motarsa yanzu sojoji zasu saki harbi,rawa jikina ya fara yi Kar karkar, gidan
duk inda kuke zatonsa ya wuce Nan,kafin na Shiga da akwatina na sai da sojoji suka duba ciki
suka tabbatar ba abin cutarwa sannan suka Bari muka Shiga ciki tare da Driver na Asiya Yana
Mana jagora,Attine ta kalleni yanda taga na hada uban Gumi jikina na rawa, Murmushi tayi tace
ki kwantar da hankali kamar Kinga wani malaika Fadila,jikina Yana rawa kamar tsohuwar
Shekara dari nace to..to Anty.

Gidane ko Ina tiles da tiles ga flowers swimming pool iri iri har kala nawa,motoci kuwa a
parking space kamar wajen saida su,masu tsada Babu ta kasa da million goma, Ni ban San
yanda Zan kwatanta maku gidan ba,duk wani Abu da ake yayi a kasar Nan Babu shi a gidan
nasu kalar latest ne sai sun Gama yayin Abu da shekaru sannan ake Fara kawo abin kasar nan.
Komai nasu baza ka ganshi a wajen mutane ba tsada ma baza ta Bari a iya siya ba.

Wani Palo muka Shiga gari guda kujeru na Alfarma set kala sun Kai biyar a ciki,sanyi da
kamshi ta ko Ina labile ma Dana ganshi tsab zance wani material ne na dinka naje gidan
ratsatsan biki dashi, wasu abun ado kamar Gold a palon, Kai abin yayi yawa jikina na ya Kara
daukan rawa ganin wata zukekiyar Yar budurwa ta gilma ta wuce ko kallon inda muke Bata yi
ba,cikin kana Nan Kaya take hadaddun gaske masu tsada,wani yawu na Hadiye makwat,Driver
yace Hajiya kalle kallen naku yayi haka muje Mana,wani Palon muka wuce Nan yafi na baya
haduwa,muka Shiga na uku yafi ko wanne haduwa,a Nan yace mu zauna zata fito,ita kanta
Attine ta rasa bakin magana.

Mun Dade a zaune har na fara gyangyadi sai mukaji Karar takalmi kwas kwas wata dattijuwa
take sakkowa daga saman bene chocolate color ce sanye cikin shadda dakakkiya dinkin
Senegal,Tasha aiki Purpple color, hannayenta da wuyanta duk Gold ne,kamshi ya bulle
mu,jikina na rawa har yau, ta zauna tare da daura kafa daya kan daya,Attine tace Ina yini ba

laifi ta saki fuska tace lfy Alhmdllh kune bakuwar? wace cikinku me aikin? Attine ta nuna Ni,Nan
murya na rawa na gaisheta ta amsa tare da bin akwatina da kallo,tace Amma bada kauye kike
ba ko? Kai na iya dagawa tace Good, waya ta dauka tare da Danna Kira ta Kara a kunne
chakwas kawo min Handbag dina.
2mt sai ga wata budurwa zata Kai 20yrs ta sakko cikin matsatsun kana Nan Kaya kanta
yasha gyara ba dankwali ba laifi tana da Dan kyau Jakar ta Mika Mata sister gashi,ba laifi tana
da Dan kyau,a wulakance ta kallemu tace sister sabuwar Yar aikince Haka zukekiya da ita hala
bada ga kauye ta dira ba?ta Dan goge a nan,? Ta furta tana Mana kallon raini, Chakwas ban
son iskanci da rashin tarbiya ki gaida su,Kuma na hanaki matsewa maza na sintiri Amma bakya
ji jiba shiganki banza.

Bata gaishe mu ba ta juya tana Danna makekiyar wayarta tayi tafiyarta,Matar tace na gode
Zaki dinga dafa min abinci shine aikinki abinda nace shi Zaki dafa karki sake wani ya saki aiki a
gidan Nan kiyi sai kishiyoyina sai yaro na Dana ke kauna Zaki ji Ana kiransa Ice ba Dan Dana
Haifa bane Amma Ina sonsa yafi Zama a part dina yafi cin abinci a Nan,satinsa biyu da dawowa
daga British.

Ki kiyaye ban son rigima,ya sunanki? Nace Fadila tace nice name sunana Haj Asiya nice ta
biyu a matar me gidan,Ana kirana da Nanee, tunda ke me girki ce bazan kaiki part din Maaikata
ba Zaki zauna a Nan part dina Zan Baki daki can Palon farko,akwai maza da yawa a gidan Nan
Marasa tarbiya ki kiyaye ki Kama kanki ki rike mutuncin ki, masu girkina dama duk fasikanci
yasa na koresu Dan Allah muyi Zama na Amana abinda kike so ki sanar min,da kanta ta nuna
min ko Ina na gidan da part dinta har sama sabo da Kar na bace a gidan, kitchen duk ta nuna
min iri iri.ta kalleni tace kinyi karatu ne? Nace yanzu Ina level to a Niclos University Ina karantar
Health education, wow wa yake biya miki?,, Murmushi nayi nace Wata Ijeoma minister dake
makwaftanku nayi aiki a gidan na girki shine dadin Zama yasa take biya min, Asiya tace me
yasa kika bar aiki wajenta? Mijinta ne fasiki Yana min Maganar batsa sannan ya dinga kokarin
taba Ni,shine nace ta sallameni,tasan bani da laifi yasa taci gaba da biya min schl.

Hmm to yanzu Yar aikin girki na University ya za ayi da girkin Rana?ga Dana baya jure
yunwa, 1pm ake Kai Masa abinci Office ko ya dawo gida yaci, ai ba damuwa ko me nakeyi a
schl Zan dawo kafin 1 nayi ko lecture ba damuwa Dan na rasa wata kin San makarantun kudi
Babu wata matsala wasu ma sai su kwashe watanni Basu je schl ba kuma kiga sunci exam
sabo da kudin kawai suke so basa ka da kowa,Murmushi Asiya tayi tace wlh kin waye ba wani
nuku nukun magana Haka nake son rayuwa da mutum, Dan Allah before 12pm ki dawo 1pm
dot ki Gama shirya abinda nace ki dafa ko wanne time,nace Inshallah yanzu ma hutu muke
saura sati biyu mu koma.good sannan tace gobe ki shirya Zan kaiki part part a gidan Nan sabo
da kisan kowa kema a asanki,tare da uwar mijinmu. Nace to.

Attine tace to Ni Zan tafi Kudi ta Bata sun Kai dubu Hamsim ta siyi recharge card,Nima
albashina har dubu Arbain tace zata iya Kara min fin Haka idan har na iya aikina Kuma ban
jawo Mata magana ba.

Bayan Attine ta tafi ta bani dakina hadadden gaske a Palon farko sannan tasa aka kawo min
abinci lafiyayye kala biyu,tace gobe da safe Zan fara aikina, a Raina nace Ina wa zai hada
gidan Nan Dana Ma ko kusa ko Alama.

Da Asuba na shirya tsab bayan nayi sallah da azkhar na Shiga kitchen Bayan naje na
gaisheta da ladabi ta fada min abinda take so da safe tace nayi daga ita sai danta Ice sauran
Yara da Yan uwanta masu Dafa musu abinci daban,naji dadi bazan Sha wahala ba,
Girki ne na Yan gayu iri iri ta sani nayi wani abunma sai da na duba YouTube,gani dama na
iya girki tuni part din ya dau kamshi ko Ina Wanda yayi sanadiyar jawo hankalin mutanen gidan
kowa sai ya nemi a wanne part wannan kamshi ke tashi Haka?
Kafin kace me Sumayya Chakwas ta fasawa gidan labari Nanee ce tayi sabuwar Yar aiki Wai
Fadila wata budurwa kamar balarabiya kyau iya kyau wata Yar gayu.

Mamaki munafuncin yakai kunnen kowa dake kowanne part, yau har kunne Kaka Babar
Araba Lagos Hajjojo labari ya sameta,jira kowa yakeyi yaga wace ce Fadila me kamshin girki.

Bayan na Gama girki iri iri cikin kankanin lokaci na shirya Dining sannan na gyara kitchen na
sanar da Nanee na Gama mamakin saurina ya kamata tace na gode da Alama za a je dake
Murmushi nayi na fita abina,dakina na fada toilet na fesa wanka Naga gidan Nan sai da kwalliya
in ba Haka ba rainaka Matan zasuyi, lotion Dina na shafa me kamshi na sa wata doguwar Riga
ta Arabian dark brown sosai nasan tana min Masifar kyau Kuma Bata dameni ba powder na
shafa da man lebe pink kadan na fesa Yan turarena sama sama,wata Yar aiki ce ta buga min
kofa lokacin Ina gyara dakina tare da shirya komai nawa, Ina budewa ta harareni sabo da na fita
komai tace kije inji Nanee ta juya abinta.









AsmaBaffa
[8/15, 11:45 AM] +234 813 228 4370: 🏕HADIN KAI🏕

21-25









Official








By
AsmaBaffa








Asycool, Fancy Honey, Oum Hanan,zulaihat,Queen kk,Jannat, Maman Abba,Maman
Fahad.
Ga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login