Showing 3001 words to 6000 words out of 44283 words
Chapter 2 - Hadin kai Part 1 Complete Hausa Novels by Asma Baffa .pdf
Fadila ta fara haila a gida,ga nonuwa kamar me shayarwa Allah yasa ma ba
maza bane suka jawosu ta karfi sai wukil ta koma daki, Hajiyarmu wacce ke wanke wanke a
bakin rijiya ta mike ta fara surfawa Anty masifa iri iri,Abbu ya zazzageta Wai Bata da hakuri ai
fada Anty tayi min.
Haka Abbu ya fice fuuu,Salman Yana dawowa yaga yanda idona ya kumbura sabo da kukan
Dana ci,me ya sameki Fadila,labari na bashi yaji haushin Abbu Amma sai ya min Nasiha yace
nayi biyayya Allah Yana kallo.
Washe gari Ina kwance a dakina Ina tunani Ina hawayen dan ban San Ina yi ba,ganin kuka
bazai Kare ba kawai nayi Alwala nayi Nafeela tare da Kai kuka na wajen Allah,karshe Nace
Allah ka bani Mijin aure ko wanne iri ne Allah ko Mahaukaci ne zan aureshi haka.
Anan nake Jan hankalin Yan uwa Da yawa Ana samu idan mutum Allah yasa Bai yi aure da
wuri ba ko mace ko Namiji sai dangi da mutane su takura Masa,Ana gulma Ana aibata wasu ko
ace ma fasikanci sukeyi,a garin haka sai mutum yaje ya zabowa kansa wahala ya aura,zaka ji
da yawa hakan na faruwa Mata suna Allah ka bani Miji ko wanne irine aura zanyi Haka sabo da
halin da suke Shiga wajen iyaye,Yan uwa,kawaye da mutan gari.
Ana nunawa mutum shine yaki yi Ana mantawa da Allah.
Bayan wata daya Cikin Yan uwanmu wata ta haihu yau Suna shiryawa nayi naci kwalliya ta
kamar Yar birni dama gani da uban kyau kamar asace Ni,Hajiyarmu ce ta takura min ita baza
taje ba sai Ni na wakilceta Kuma na zaga danginta Dana Abbu, Haka na fito na iske samarin
gidanmu tare dasu Mahmood a majalisarsu suna ta tsokanata nayi kyau daddawar daki yau ta
fito,dariya na danyi na wuce na tafi,Ina sallama a gidan mutane damkam Ana ta cin abinci tun
kafin na Shiga aka fara gulmata Ana kus kus, Abin haushin dangina Yan uwa dasu ake
zagina,tunda na Shiga wasu da gayya suke min habaici,wasu Kuma su fake da Wasa,da kyar
nayi 10mnt na bar gidan, na fara zaga dangin Abbu duk inda na Shiga sai na fito Ina goge
guntun Hawaye,Haka dangin Hajiyarmu ba hadin Kai Sam.
Gidan kakannina na wajen uwa ma suka sani a daki ta inda suke Shiga ba tanan suke fita
ba,kakannina Yafendo da Baffalo sune naje na karshe,Yafendo tana gani na tace oh yau kece a
garin,gashi Nan duk kin tsufa a gida,yanzu Yar Nan baza kiwa kanki fada ba? Wlh Nan da wata
Uku idan Baki fito da miji ba to ko da ubanwa daura Miki za ayi.nan suka Karaci surutunsu na
taso na bar musu gidan Yafendo tace Yar bantan uba me kafa kamar tabarya.
Bayan wata daya Ina wannan Hali da yamma na fita tallan Goro na dawo Ina kan hanyata ta
komawa gida katsam naga mutane damkam a kusa da gidanmu Yara da manya ka rantse
masallacin idi ne Mata da maza har da masu leke ta cikin gida Mata saman katanga, Wani
Almajiri na tambaya me ake kallo me ya ta faru,Almajiri ya washe jajayen hakoransa yace
Bature ne yazo Amma kamar mahaukacine fa an kasa ganewa Yana da hankali ko babu, Baki
ganshi ba Dan gayu Dan birni Baki ganshi ba je ki gani.
Jin ance bature ne nace Nima baza a barni a baya ba,Haka na kutsa cikin mutanen har na
Shiga inda baturen yake, sai da na kusa Suma sabo da cikar zatinsa da haibarsa ban taba
ganin me kyau Haka ba,ai sai na ganni na dawo baka a kansa,kyau kuwa kamar shi yayiwa
kansa sai ka lalace wajen kallon wannan bawan Allah sai wani kamshi yakeyi,Shadda ce fara
Kar a jikinsa me tsadar gaske tana sheki,sai dai ta danyi dirty kadan,Kuma gefenta ya Dan yage
kamar ma kusa ce ta yaga wajen bana mutuwa bane.
Gashinsa yawansa ya baci gashi me santsi ga wani sajensa Wanda ya taru da Dan yawa sai
bakin Nan Pink abin shaaawa.mutane suna ta kallonsa shi kuma Yana jikin bishiya a zaune ya
turo lips dinsa gaba kamar wani shagwababbe,a gabansa na tsaya,Ina ta kallonsa Ina washe
Baki,ganin kallon Bai isheni ba a gabansa na tsuguna tare da Kara tura Masa fuskata saitin
tasa,kamar zan Shiga cikin fuskarsa.
Abin mamaki ko kallona baiyi ba kamar Bai San da mutum ba,rigarsa na Dan ja ai kuwa ya
kalleni kadan ya Kara turo Dan lips dinsa ya tsuke shi tare da make kafadar Shagwaba,a fili
nace ah..ah...tofa sai na tintsire da dariya mutanen ma dake kallo suka fara dariya kamar
mahaukata,wani yaro cikin Yan kallo yace Fadila Dan tabo Mana gashinsa muji,a hankali na Kai
hannu zan taba gashin a tsorace,ai ko ya make min hannu ba tare da ya kalleni ba,ban hakura
ba na Kara Kai hannu ya bige Hannuna ya mike tsaye a fusace idonsa har ya canja kala daga
fari zuwa red,Alawata na Ciro a Jakar da nake Tara kudin tallana na Mika Masa ita,kallo na yayi
kadan kamar bazai karba ba sai ko ya karba,abin da ya bamu mamaki ba tare da ya bare ledar
ba ya cinye har ledar a Nan muka ce yana da tabin kai,mutane kuwa Kara yanyame wajen suke
an samu a tsakiya.
Kallon mutanen yayi sai ya fara toshe hanci Yana ja da baya,sai ya fara buya a bayana, idan
na matsa sai ya matsa ya boye a bayana Yana leken mutane ta bayana,tsoro ya shigeni na fito
daga mutanen nayi hanyar gida a guje, Abin mamaki Mutumin ya biyo Ni Amma cikin takunsa
na Isa da gadara.
Gudun na daina na tsaya kawai sai ya biyoni mutane na binmu Yana buya a bayana,ban
Shiga gida ba kawai na dauki hanyar wani shago cikin kudin tallan na siya Masa pure water
Yana tsaye kusa Dani kamshin sa ya cika ko Ina,na Mika Masa ruwan ya karba kawai sai ya
jefar a kasa da yatsa ya nuna min ruwan jarka da ake siyarwa,Baki na hangame nace Kai
almubazzari Dan asarar kudi sai na roba ko Ni ban Sha ba sai kai,to wlh baka Isa ba, kudin
Hannunna ya nuna da yatsansa sannan ya nuna min ruwan roba,a Shagwabe nace Kai baka
San Ba kudina bane! Na Hajiyarmu ne dukana zatayi daga wannan Ni dai bazan siya ma
ba,Dole na mika kudi aka bani na roba na bashi,sai na ga ya kasa budewa Yana ta
gwagwagwa,na karba Ina masifa Kato da Kai Amma baka iya abin duniya ba ungo na sa Masa
bakin robar ai kuwa ya shanye ruwan tas,Allah sarki kishi yake ji, biscuits ya nuna min Nan na
gane yunwa yake ji na siya Masa biyu, Dana bude na bashi Bai iya ci da kansa ba Haka na
bashi da kaina ya cinye, nace to ka tafi yawonka Ni gida zanje duk ka cinye min kudi na Ina ta
masifa Amma yayi mursisi ko a jikinsa, Dana tafi Nan ma Bina yayi a Haka har kofar
gidanmu,nace ka biyo Ni su Salman zasu koreka ne yaro ba ruwana Ni.
AsmaBaffa
[8/15, 11:42 AM] +234 813 228 4370: í ¼í¿•HADIN KAIí ¼í¿•
2
Official
By
AsmaBaffa
Bai ce kala ba Haka muka je har kofar gidanmu babu kowa duk suna Masallaci sallar
Magrib, Haka na shige gidanmu bayan na dauki kudina Dana kashewa Dan Bature na biya
Hajiyarmu da kudina da nake Tarawa,muna zaune a tsakar gida Ana cin abincin da dare kawai
sai ga Dan Bature ba ko sallama ya shigo kamar gidansu,Anty da yaranta tare da Hajiyarmu
tuni suka fada daki da gudu tunaninsu Bature ne Dan wani fari ne tas ga uban kyau kamar shi
yayi kansa,harsu Salman sunji tsoronsa kasa motsi sukayi,Abbu dake gefe saman carpet jikin
dakinsa shine yayi ta maza ya daka Masa tsawa Kai lfy gidan ubanwa zaka je Haka? Shuru
Babu amsa sai ma toshe kunnansa da Bature yayi sannan ya hade Rai tare da turo lips irin an
takura Masa baya son hayaniya, dube dube ya fara can ya Hangoni saman katuwar Shimfidar
tabarma Ina cin tuwo,a hankali cikin takunsa na birgewa ga uwar gadara gefena ya zauna kusa
Dani a saman tabarmar,Su Anty da yaran gida sai lekenmu sukeyi,mamaki ya kamasu ganin
banji tsoro ba,Baki Bude Abbu yake kallon mu, Su Salman ma Haka,Kwanan tuwona na tura
Masa gabansa,ya zubawa kwanon Ido tunawa nayi baya iya cin Abu da kansa,Hannu nasa na
yanke tuwon sannan na Kai Bakinsa ai kuwa ya bude bakin na saka Masa ya fara taunawa
kamar baya so da gani Bai Saba ci ba kawai Dan Yana Jin yunwa ne yake karba Yana ci.
Muryar Abbu ce ta bamu tsoro yanda ya daka Mana tsawa,Iskancin naki ya Kai Haka dama?
Shi yasa nake murna da Allah Bai bani Yara Mata ba sai maza ke kadai mace Amma sai jawo
min magana kikeyi to Zaki ci ubanki aure zan Miki na Dole Kuma wlh kika sake da mahaukacin
Nan zan hada ki. Kayi Hakuri Abbu taimako fa nakeyi wlh yunwa yake ji,Dan Allah ku daina ce Masa
Mahaukaci duk Wanda ka ciyar Allah zai baka Lada ko dabba ce,Jar uba lallai zan karyaki a
gidan Nan Fadila cewar Abbu, Hajiyarmu ce ta fito daga daki a tsorace ta kalli Dan Bature tace
Kai tashi ka fitar Mana a gida,kallonta yayi sai ya koma ta bayana ya buya Yana leko da kansa
ta kafadata, yau nake ganin Dan iska wannan ko a fili tantiri ne sai shegen Jan kunne,ga uwar
Suma kamar dakin bukkar fulani.
Salman ne yazo ya fara kokarin Jan Bature zai kaishi waje Amma ya kasa Kuma yaki fita sai
ma like min da yake faman yi a bayana, rada Salman yayi min a kunne cewar tashi ku tafi waje
ki jashi ki San yanda zakiyi ku rabu mu rufe gidanmu kafin ran Abbu ya baci wlh duka Zaki ci kin
sani ko ya Miki auren Dole kuma Kinga mu baza muji dadi ba.
Mikewa nayi na dauki wani kwanon na zubo Masa tuwo da Miya na rufe da murfi,Hajiyarmu
tace a kwano na me kyau Zaki zubawa Mahaukaci abinci?ubanki ne ya siya min,to kudina nasa
na siya Dan gwal ne da sai a kwano me kyau zaici?, Mayar ki zubo Masa a wannan tsohuwar
langar wacce ta kwankwatse idan ta Bace ma taje,amma kwano na me kyau sabo a bawa
Mahaukaci abinci a ciki ai kinyi karya Yar Nan,Anty ta leko tace Wai ita iyayi ga Yar me kudi
komai nata sai anyi karya Yar karya kawai shine harda daukan sabuwar silver.
Bance komai ba na canja kwanon lokacin Bature ya biyo Ni har kitchen Yana buya,Hajiyarmu
ta rike haba tana Salati tace wannan yaron mashahurin Dan iska ne,Dan ubanki wlh ki
kiyayeshi,Anty ta karbe da Allah ya kiyaye Kar ya dirka Miki ciki kafin ta rufe Baki Abbu yace da
kuwa na kasheta da Hannuna.
Bance musu komai ba nayi hanyar waje ai kuwa da sauri ya biyo Ni mun wuce Abbu kenan ya
Sa Muficin da yake fifita dashi ya kwalawa Bature a kafafu Amma kamar dutse ya daka,Abbu ya
sake rade Masa kafafu sosai da zafin gaske,Bai ko kalli Abbu ba yabi bayana muka bar gidan.
Can nesa da gidanmu saman wani dakali na zauna shima ya zauna a gefena,tuwon naci
gaba da bashi ya ci da yawa kuwa nasan Yana bukatar ruwa haka na tafi shago Yana Bina a
baya kamar jela na siyo pure water biyu na bashi daya da kaina wannan time din Bai nuna
ruwan roba ba.
Saman dakali muka zauna na dinga Masa magana Amma Bai ce kala ba,nace Dan Allah ya
sunanka? Yayi Shuru ba magana,ko Kai kurma ne? Nan ma Shuru, maganata naci gaba da
fada Dan Allah ka daina zuwa gidanmu wajena Abbu na zai Duke Ni,Amma ban San Ina zaka
kwana ba,ga hadari a gari tabbas ruwa zai zaneka wayyo ya zanyi na taimake ka ni. Haka dai
na karaci surutuna na mike zan tafi gida ganin dare yayi da yawa,na gargadeshi Kar ya biyo Ni.
Nayi Nisa da tafiya kawai na hango shi Yana Bina a baya Nan na kwashe da gudu na fada
gidanmu sannan na kulle kofar har Hawaye nayi na tausayin bawan Allah yau nasan idan anyi
ruwa ba shakka zai zaneshi.
Shi kuwa Yana karatowa yaji gidan Gam a kulle sai ya zauna a bakin kofar gidan namu ya
fara gyangyadi bacci ya kwasheshi.
Misalin Sha biyun dare na kasa bacci tunanin Dan Bature nakeyi gashi tuni an fara ruwa
nasan ruwa Yana dukansa yanzu hawayen tausayi ya zubo min,a hankali na tashi na fito a
dakina na lallaba naje na bude kofar gidanmu a hankali, Aiko na ganshi a zaune Ana tsinka
ruwan sama kamar da bakin kwarya shi kuma Yana zaune ya dunkule waje daya ruwa na
labtarsa Yana ta karkarwa.
Salman ne ya fito yaji kamar an bude gida tunaninsa barayi ne sai ya ganni Ina leke,yace
Sister lfy?, Nace leko ka gani,ya leka yaga Bature shi kanshi ba karamin tausayinsa yaji
ba,yace taimaka Masa ya kwana ko a zaure ne Amma Da Asuba ki zo ki fitar dashi kafin Abbu
ya tarfa ki.
Dadi naji sosai shi Kuma Salman ya juya ya koma dakinsu,Da gudu na fito na Karasa inda
Bature yake na Dan bugi bayansa da Hannuna ga ruwa ya Kara tsugewa, da sauri ya juyo ai
kuwa ya ganni ba shiri ya mike tsaye duk da duhu Amma ya gane nice,karo na farko da naga
Dan Murmushinsa kadan,ban jira ba kawai na figi hannunsa me Masifar laushi muka Shiga
gidanmu, Salman ne ya kawo min wani kayansa Shadda Riga da wando Tasha guga yace gashi
ki bashi ya canja Kar sanyi ya Masa Illa,sannan ya dakko min wani bargo guda biyu,ungo ki
Masa Shimfidar da daya ki lulluba Masa,na fara Masa Godiya Ina murna yace ke dai kiyi sauri
karfa a Kama mu ya juya dakinsu.
Bature na kalla Ina Murmushi nace cire Kaya n ka canja,kafada ya make alamar yaki, nace
sanyi zai maka illa Ashe kana Jin magana,rigarsa na daga zan cire Masa ya zuba min uban
yakushi saida ya dauke min fata, haushi naji sosai na bude kofar nace to fitar Mana a
gida,kawai sai Naga ya fita kuwa yayi tafiyarsa cikin ruwan Nan ga duhu ya dauki hanya sosai.
Gidan na rufe na maidawa Ya Salman kayansa na koma na kwanta da kyar bacci ya daukeni
Ina tunanin Bature yanzu Yana can ruwa Yana zaneshi. da Asuba na tashi nayi Alwala da sallah
sannan na fara tasbihi da sauran azkhar har Rana ta fito gashi dama Abbu ya hanani zuwa
makaranta talla kawai nake fita sabo da na duba Bature ko ya kwana lfy? Da wuri na Taya
Hajiyarmu girki shayi muke Sha lafiyayye da kosai sai bread,sannan ga Koko da dumamen
tuwo,Bayan na sake yin brush nayi wanka na fes na sa doguwar rigar atamfa ta me kyau nayi
acuci da gashina tare da yafa Dan gyale na,sabo da kallo a waya yanzu mutan kauye ma sun
waye ba a wuce su a iya wanka da kwalliya sabo da kallace kallace a waya, Kuma da yawa Yan
makaranta basu fiye kauyanci da yawa ba, suna wayewa bare gidanmu da muke da Dan rufin
asiri daga mazan har ni daban muke ga kyau.
Hajiyarmu ce ta kalleni ta tabe Baki ga kyau har kyau ba miji,yau Kuma tallan goron da wuri
za a tafi haka? Anya ba akwai wata tsiyar da Zaki shuka ba nasan halinki Fadila, Murmushi nayi
nace nafi so na siyar da wuri kafin mazan su tafi gona kin San tsofaffi da gona, Hmm to ya Naga
kina wani nishadi ke da kullum fuska ba rahma Kuma sai wani zumudi kike Bayan tallan idan
Zaki je kamar Zaki mareni Haka kike tafiya.
Shuru nayi Mata ta Kara tabe Baki tace dauki ki tafi tuku tuku mugun ice a Haka kamar
saliha,Ni dai Shuru nayi na dauki talla na na fita Bayan na Shiga dakin Abbu na gaishe shi Yana
muzurai Ni dai na fice abina,ko wajen tsofaffin banje ba,na fara duba gari ko zanga Bature
Amma ban ganshi ba,hankalina ya tashi sosai na Shiga zagaye kauyen nan, har kusa da wani
Rafi da mutane ke wanki ga bishiyoyi da ciyayi Kore Shar ga sanyin Niima a wajen,na duba ko
Ina Banga kowa ba na juya hankali na tashe na fara tafiya naji an ja min gyalena kadan,a
tsorace na juyo sai nayi tozali da Bature,kasa kallonsa nayi sabo da tsananin baiwarsa da
kwarjini ga wani kyau me tafiya da imanin Dan Adam.
Ajiyar zuciya na sauke a hankali wani farin ciki ya cika ni, nishadi ya kamani gashi lfy
Lau,juyawa yayi ya fara atishawar mura sosai,kayan jikinsa Sunyi dirty,hannunsa naji me
matukar laushi cikin nawa ya rike Ni wani zirrrrr naji jini na ya amsa,Har gindin bishiya ya Jani
sannan ya zauna Nima ya min nuni da na zauna,Zama nayi nace Ina kwana Bature? Bai ce
komai