Showing 63001 words to 66000 words out of 66129 words
Chapter 22 - Wayasan Asalina Complete Book by Zainab Idris Novels .pdf
tabi dan
gabaki daya tagama rikicewa yana shiga dakin yaja yatsaya dan ganinta kwance akan
gado tana ta birgima tana rike da cikin ta a rude dagashi har pinky suka karasa inda
take saidai Sam bata masan suwaye akan taba hankali tashe AJ yadauketa yace ma
pinky tadauko mukullin mota dagudunta takarasa bangarenta ta dauko key car din tabude
gidan baya yasa zuly pinky kuma tashiga mazaunin driver taja suka bar cikin haraban
gidan kai tsaye asibiti mafi kusa suka nufa suna isa Dr yana zuwa nandanan yasa aka
kaita emergency room!
]10/19, 15:16[ ﺓﺩﻮﺳ :ﺲﻳïºïº©ïº‡ í ½í³š WAYASAN ASALINA í ½í³š SAUDAT IDRIS NOVEL í ½í³•
PAGE 67
safa da marwa kawai pinky da AJ sukeyi da suka gaji da tsayuwan ne suka samu
kujera suka zauna zuciyoyinsu ba dadi saida suka kusan hour daya da wani abu a zaune
sannan doctor din yafito yana share zufa suna ganinshi suka tashi dasauri suka karasa
wajen shi pinky ce tayi saurin cewa meke damunta hope taji sauki duk lokaci daya tama
Dr din wainnan tabbyoyin kara share zufan dake fuskan shi Dr din yayi sannan yace
saidai kuyi hakuri Allah yamata rasuwa AJ da hankalinshi gabaki daya yagama tashi shake
dr din yayi yace karya kakeyi taya zakace ta mutu bayan ciwon bai yi tsananin da zaace
tamutu ba Allah sarki AJ kamanta da cewa da ciwo ko ba ciwo idan lokacin mutum yayi sai
yatafi kuka pinky tafashe dashi dakyar Dr din yakwace kanshi awajen AJ yanda kuka san
karamin yaro haka yafara kuka dakin da zuly take suka shiga dakyar kwance yaganta
kamar me rai sabida fuskan ta daya kara haske da kyau baisan sanda yakarasa
yarikeeta sosai ba yafashe dakuka pinky dakyar ta iya daidai kanta tasamu aron waya
sabida basu taho da wayoyin suba sabida hankali ba akwance ba takira sadiq tagaya mai
shima hankali tashe yakira su ammi yagaya masu sannan abba dakanshi Yakira Mr
president yagaya mai salati Mr president yaringa yi sannan Yakira mami tazo bangaren
shi yafada mata hankalin ta ba karamin tashi yayi ba nandanan mutuwar zuly ya watsu
dan suma tuni Mr president yakira me martaba yagaya mai nandanan suka shirya suka
biyo private jet hankali tashe su sadiq dasu abba dashi kanshi Mr president suka isa
asibitin halin da suka samu AJ aciki bakaramin kara tada musu da hankali yayi ba Dan
mutuwar ta matukar girgiza shi pinky tana kuka takarasa motar sadiq tashiga tazauna
AJ kuma kamashi sadiq yayi yakaishi motar su Mr president sannan aka dauki gawar
suka dunguma gabaki daya Zuwa gidan su Dan kafin suje har mutane suncika gidan
Dan kowa kagani mutuwar zuly bakaramin tabashi yayi ba sabida kyaun halinta bayan
Zuwan me martaba ne aka mata wanka aka tsitirceta hajiyarta tamata addua tana kuka
sannan aka dauketa zuwa kaita gidanta na gaskiya AJ kaman ba namiji ba saidai aga
hawaye yana zubowa a idonshi !
Ammi lallashin pinky take tayi Dan kukanta yaki tsayawa balantana data tuno irin
zaman da sukayi da zuly sai takuma fashewa da kuka a haka aka dawo daga kaita nansu
AJ suka zauna a haraban cikin gidan suna amsan gaisuwa saidai ko ammai gaisuwa dakyar
yake iya amsawa . Toh saidai ince Allah yajikan zuly yasa aljanna tazama makomarta mukuma Allah
yamana kyakkyawan karshe Aameen
]10/19, 15:47[ ﺓﺩﻮﺳ :ﺲﻳïºïº©ïº‡ í ½í³š WAYASAN ASALINA í ½í³š SAUDAT IDRIS NOVEL í ½í³•
PAGE 68
su hajiyar zuly saida akayi sadakan uku sannan suka koma kano cikin kwanaki ukun
nan gabaki daya AJ baya cikin hayacinshi danko abincin kirki bayaci sai pinky tazaunar
dashi tukunna dakanta tabashi a haka akayi sadakan bakwai shine ma yadan fara tsakin
jikinshi yafara dawo wa kamar da bangarenta sam yadaina shiga dan yasama ankwashe
kayan gabaki daya hotunan su kuma pinky takwashe ta ajiye .
daman rayuwar batada tabbas kana naka Allah na nashi gashi yanzu wata biyu kenan
da rasuwar zuly komi yafara chanzawa .
AJ dake zaune akan kujera cikin pinky yake shafawa yace nifa ban yarda da wannan
katon cikin ba daria tayi tace meka gani kashe mata ido daya yayi yace kamar nayi
ajiya acikin nan daria tafashe dashi Dan ita kanta tana jin wani iri kwanakin nan
AJ yace yaushe rabonki da ganin period dinki nazari tafara yi sannan tace kaman so uku
ken...
Tun kafin takarasa AJ yace maza tashi kishirya muje asibiti kallonshi tayi tace habibi
menene na zuwa asibiti AJ yace gwada munke zaayi make kafada tayi tace menene sai
munje asibiti tunda ga abu yafito fili AJ yace ban yarda ba saifa kin tashi munje shagwabe
fuska tayi sannan ta tashi zaune tace toh Saidai ka goyani ka kaini har bedroom in sauya
kaya Daria yayi yace abun me sauki zukunnawa yayi yace oya hau daria tayi sannan
tahau tace habibi bayanka akwai dadi AJ yace anjima nima sai kinmun abunda yafi goyo
bedroom yakaita dakanshi yacuro mata kayan da zata sa saida ta shirya sannan suka
sauko downstairs pinky tace amma ni zanyi driving kallonta AJ yayi yace bafa ki isa ba
kinsan nakashe wannan tuntuni sannan yarike mata hannu suka karasa parking space
family hospital dinsu suka nufa gwajin farko Dr yace tana dauke da ciki har na tsawon
wata biyu da kwana hudu AJ rumgume pinky yayi yana kissing dinta sannan yace Dr
kana da babban tukwuici zaka ji alert godia dr yamai sannan suka bar asibitin kai tsaye Villa
suka wuce a Palo suka tadda mami dasu mimi suna cikata da surutu bayan Sun gaisane
mami tace yau hala abishir din me aka maka kaketa washe hakora kanshi yashafa pinky
kam tuni ta tashi tawuce bangaren su mimi dan tasan AJ zay aika yagaya wa mami ita kam
bada ita ba wannan rashin na ido kara shafa kanshi yayi sannan yace daga asibiti muke
mami nakusa zama baba murmushi mami tayi tace kaidai kunyanka ragagge ne alamin
]10/19, 16:15[ ﺓﺩﻮﺳ :ﺲﻳïºïº©ïº‡ í ½í³š WAYASAN ASALINA í ½í³š SAUDAT IDRIS NOVEL í ½í³•
PAGE 69
acikin watan da muke ciki acikin sa pinky da leema da kuma AJ da Faisal da su ammi
suka shirya Dan Zuwa ganin yan uwan leema dake kaduna tudun wada duk da bawani
karban arziki aka musu ba amma hakan bai dame suba sabida Sudai burinsu leema
tadawo gaban yan uwanta kafin aurenta da Faisal a hakan ne kawai zasu iya shiryawa da
yan uwan nata yayan baban tane yashugo gidan ya tadda su ammi yakuma ga leema
sunanta yakira yace halima kece Ashe zaki dawo hawaye yafarayi sannan yasamu waje
yazauna yace in bamu nemi yafiyar kiba halima sai wutar Allah tacimu sabida Munci amanar
da Dan uwan mu yabar mana Dan Allah ki yafe mana itama kukan takeyi tace babu komai
baba Allah ya yafe mana gaba daya saida suka shirya da yan uwan ta sannan su ammi
suka tafi akan ranan daurin aure sai ta taho abuja gaba daya .
nan aka fara shirye shiryen bikin leema da Faisal duk wani hidima pinky ne takeyi duk
da cikinta yana cikin na wata hudu ne saidai bata laulayi bata komai tun daga dubai
mummy Faisal tayi order din kayan lefe Kuma cikin satin da muke cikine aka kai lefen har
kaduna leema Kam sosai take samun gata wajen yan uwanta .
ranan juma'a aka daura auren Faisal tahir da haleema dahiru kuma a ranan akaje aka
dauko amarya daga kaduna zuwa abuja sabida zaayi dinner da dare wanda gabaki daya AJ
ne yadauki nauyin komai .
Kada kuso kuga yanda leema tayi kyau tafito saf amarya da ita takwas aka fara dinner
aka tashi karfe sha daya daganan direct gidan ta aka wuce da ita ana kaita Kowa ya
watse aka bar ango da amaryar sa.
]10/19, 16:35[ ﺓﺩﻮﺳ :ﺲﻳïºïº©ïº‡ í ½í³š WAYASAN ASALINA í ½í³š SAUDAT IDRIS NOVEL í ½í³•
PAGE 70
leema da Faisal soyayyar su suke sha sosai Dan kome zatayi idan Faisal yana gida
saiya tayata a haka auren yakai wata daya cikin pinky kuma yashiga na wata biyar tuni
AJ yafara order din kayan baby daga dubai .
Ammi dake bangaren abba a zaune taji sallaman megadi lekowa tayi megadi yace wata
matace take son ganin alhaji ammi cewa tayi yashugo da ita sannan takoma tagaya ma
abba suna zaune apalo tayi sallama tashiga su abba suna ganinta suka tashi tsaye sukace
bilki hawaye tafarayi tace nazone in nemi gafarar ku tunkan in mutu komawa su abba sukayi
suka zauna sannan ita tazauna akan carpet tace kuyi hakuri ku yafemun ammi tace me
kika mana share hawayen fuskanta tayi sannan tace niche nayi sanadiyan bacewar farida
kuma dakaina nakaita har kofar gidan karuwa salati su abba suka dingayi ammi tace me
muka miki kika aikata wannan babban laifi bilki tace sabida nasha kaima alhaji hari akan
son dana ke mai amma saidai kaman baisan ina yiba Dan sabida haka nakamu da ciwon
hawan jini nikuma ne alkawarin nima sai nasashi kuka kamar yanda yasani ganin yana
matukar son farida shiyasa nadauketa .
Mamaki ne Yakama su abba ammi tace toh duk munji bayanan ki tashi kitafi Allah ya
yafe mana gaba daya abba yace wallahi babu inda zatace saina daureta sai an hukunta
ta hakuri ammi tafara bashi tace kayi hakuri tunda anga farida ai komi yawuce dakyar ta
rokeshi sannan takalli bilki su tace tashi kitafi bayan fitan tane abba yace amma ta
cucemu bazan taba yafe mata ba saiki kira little kigaya mata girgiza kai ammi tayi tace ba
amfanin gaya mata tunda yanzu tasamu duk abunda tarasa abaya.
ranan lahadi pinky ta sumbulo baby girl dinta me kama da babanta aiko ranan suna taci
sunan marigayiya zulaiha amma ana kiranta amatullah duk wani gata shi ake bawa
amatu.
Bayan shekara biyar AJ yasa mar ma pinky makaranta a city university dake US zata
ci gaba da karatun law dinta shikuma Ankara mai babban mukami .
saidai tun bayan haihuwan amatu bata kuma samun wani cikin ba leema kam yaronta
daya ana kiranshi Khalifa lafia lau suke zama da Faisal Dan kullin sai kara kaunar juna
sukeyi .
Mama magajia Kuma ta auri wani tsohon saurayinta da suka taba harka ada suna dai
zaune a wannan gidan da pinky ta mallaka mata