Showing 12001 words to 15000 words out of 66129 words
Chapter 5 - Wayasan Asalina Complete Book by Zainab Idris Novels .pdf
a dakin .
Daren ranan ko hirar dasu keyi basuyiba sbd zuciyoyinsu ba dadi !
sai zuwa bayan isha sannan baki suka tafi hakan yabawa su AJ daman zuwa bangaren
Mami achen ma suka tadda Mr President waje suka samu suka zauna suka gaidasu AJ yace
Abba munyi magana da zulaiha yanayi yana Sosa keya Mr President yace dazu munyi waya da
shi me martaba Mami tace gwanda ma kayi auren ka tattara ka koma cen gidanka kabar
kannanka su tsake ache shi kullin mutum bakin rai Mr President yace so kike yayita wage baki
kannan nashi su raina shi
Daga Kai AJ yayi yace yauwa abba gaya mata wurga mai jarbin hannunta Mami tayi dasauri
yatashi yace da alama dai Abba ne kadai keyi dani good night yana gama fadan haka yafice
yana murmushi .
[10/8, 18:10] Mrs Zaki: í ½í³š WAYASAN ASALINA í ½í³š
SAUDAT IDRIS NOVEL í ½í³•
PAGE 19
washe gari karfe goma jafar ya isa bangaren AJ saida yayi knocking wajen so biyar sannan AJ
ya yaye katon blanket din daya rufa dashi yakarasa yabude kofan sannan yajuya Yakoma kan
gado jafar Sara mai yayi daga kai kawai AJ yayi sannan jafar yace sir ansamo information akan
yarinyan
Daga Kai AJ yayi alaman yana jinshi sannan jafar yaci gaba yace pinky ba boyayyiya bace
Dan duk inda kaje sai kaji Ana hiranta tana maitama guest house din minister danya mallaka
mata gidan a dai yanda naji zaman kanta takeyi sannan tana karatu anan gwagwalada wani
murmushi AJ yasaki danni kaina bansan maanar murmushin ba kallonshi yayi Weldon zakaji alert ynxu sbd naji dadin aikin ka godia jafar yayi sannan yakara
Sara mai yabar dakin .
Yanzu tunanin irin muguntan dazay mata yafarayi tashi yayi yashiga bathroom danko baccin
bazay iya komawa ba
Yana fitowa yashirya cikin blue din suit bakaramin kyau yayi ba Dan akwai taron da aka
gayyace shi a gwagwalaada bakaramin kyau yayi ba Dan side box dinnan nashi sosai yake
kara mai kyau saida yagama shiryawa yawuce dining yayi breakfast sannan yawuce part dinsu
Mami A dining ya taddasu suna breakfast Jan kujera yayi yazauna sannan yagaida iyayen nashi
sannan su Mimi suma suka gaidashi duk da yau sunga sai faraa yakeyi
Mami ce takalleshi tace alamin kayi breakfast kuwa
Rike ciki yayi yace Mami nayi breakfast Dan cikina ji nake kaman zay fashe Sumy tace Kai ya
sai kace mace harara ya zabga mata yace an gaya maku ni irin kune me uban cin abinci Mami
tace kai kenan fada Abba yace dole yayi fada tunda su bakinsu bai shuru mikewa AJ yayi yace
wlhi kushirya on Friday Ku koma skool Mami tace Ko baka ceba Dan before Friday ma zasu
koma
OK yace sannan yace abba natafi taron da aka gayyaceni saina dawo gabaki dayansu suka
mai adawo lafia sannan yafita .
Mota daya yashiga shi kadai sai driver sannan sai motoci biyu agaba biyu abaya.
Kai tsaye uniabj suka nufa
pinky tace yau bakida test ne leema dake kwance a parlor tace yeap pinky tace OK saina
dawo mama sannan tafita yau dayar motar ta tadauka BMW shima black color kuma yasha
bakin tic
wangale mata gate din me gadi yayi tabar haraban cikin gidan
Wakar Beyonce tasaka tadan kure volume tana driving tana bin wakan har takarasa cikin
skull .
daidai inda taga manyan motocin nan daidai wajen tayi parking sannan tafito daga cikin
motan tayi hanyan department dinsu
Allah yasa yau test dayama gareta
taro akayi akan cigaban makarantan dadai sauransu atake a wajen yamusu transfer din
7.5million godia suka fara mai sosai
Sha biyu suka baro dakin taron kuma a wannan lokacin pinky takaraso wajen da tayi parking
tana kada key car din hannunta .
Key car dinne yasubuce yafada kan motar su AJ shikuma lokacin idonshi yasauka akan
fuskan pinky
dasauri security suka karasa ganin tayi banna amma ko a jikinta saima karasawa da tayi
tadauki key car tayi wajen motar ta
AJ kam yagama kuluwa lallai yanzu zay gyara mata zama cikin Isa da takama yakarasa inda
take yace hello a hankali tajuyo takalleshi bataako Ankara ba saijin yatsun shi tayi akan
fuskanta harso biyu sannan yanunata da yatsa yace r you illiterate kobakiga abunda kikayi bane
harararshi tayi sannan a fusace tace banganiba ko angaya maka Dan kawai nayi kuskuren
goge akwalar motar naka zaka Kai kazamin yatsun ka kan fatar fuskata toh wlhi bashi kaci sai
kaga abunda zanmaka AJ da zuciyar shi ke kuna yace good kafin kedau mataaki ni yanzun
nan zandau mataki baijira cewar taba yakalli securitys din yace kubani karfe babba kuma
nakeso dasauri suka dauko suka mika mai pinky na tsaye tana jiran taga abunda zay aikata
aiko bata Ankara ba sai gani tayi yatarwasa mata glass din bayan mota idanuwa taware tana
kallonshi saida yafasa dika glass din bayan motan sannan yayi wurgi da karfen yakalleta yace
ina jiran sammaci
[10/8, 18:10] Mrs Zaki: í ½í³š WAYASAN ASALINA í ½í³š
SAUDAT IDRIS NOVEL í ½í³•
PAGE 20
baima jira jin meza tace ba security suka bude mai bayan mota yashiga yazauna suka maida
kofan suka rufe sannan driver yaja motar sukabar cikin makarantan .
Ko kallon mutanan wajen batayi ba tashige cikin motan ta a fusace ta tada motan tabar
haraban makarantan dagudu saida tayi nisa da skool din sannan tayi parking abakin hanya
takifa kanta akan sitiyarin tafashe dakuka tace I hate you illiterate i hate you sannan takuma
fashewa dawani kukan saida tayi me isan ta sannan ta tada motan tabar wajen . Saidai har takai gida tana tunowa da marinta da AJ yayi mata agaban jamaa sannan ya
wulakanta ta hawaye kawai taji yana zubo mata ahaka takarasa gida tana parking tafito danko
handbag din ta takasa dauka a parlor ta taddasu mama da leema batare data musu magana ba
tawuce upstairs mama tace maza tashi kibita Dan naga idonta ya kumbura kinsan kuma ban iya
hawa sama dasauri leema tabi bayan pinky .
Tana shiga tafada kan gado tafashe dawani sabon kuka leema takarasa dasauri kan gadon
tace pinky meya sameki meya faru
Shuru pinky tayi taci gaba da kukanta Dan a halin da take a yanzu bazata iya magana ba
ganin hakane yasa leema ta kyaleta harta gama kukanta sannan tace pinky kigaya mun abunda
yafaru dakyar pinky ta iya dago idanuwanta takà lletà a tace leema kinji na rantse miki ko wà llahi
tallahi bashi yadaukar wa kansa Dole saina rama abunda yamun tunda tafara magana tasan da
wanda pinky takeyi amma sai tace wai waye cikin muryan kuka pinky tace wanene kuwa banda
yawuce wancen mahaukacin AJ din leema ta rafka salati tace meya maki Marin daya mata
tanuna mata sannan tace yakuma fasa mun glass din mota yawulakantani abainin jamaa wlhi
baici bulus ba .
Good night sai kunjini zuwa gobe insha Allah
[10/8, 18:10] Mrs Zaki: í ½í³š WAYASAN ASALINA í ½í³š
SAUDAT IDRIS NOVEL í ½í³•
PAGE 22
AJ yace babu wahalan dazan bata matan ne sai a hankali daria Faisal yayi yace itama zuly
dandai karsu Mami su dame kane amma ba kalar macen da kakeso bane tunda kadadai kana
fada mun kafi son ka aura mace me kyau wacce tafika kyau ko kuma kuzo daidai amma Zuly ko
kafanka bata kawoba wajen kyau . Tsaki AJ yasaki yace kaji ka dawani magana nibari intashi inyi gaba
Dan na biye maka saika bata mun mood dina girgiza kai Faisal yayi yana murmushi sannan
suka mike suka fice AJ yace kai kadai kaman maye sai yaushe su mummy zasu dawone Faisal
yace ina tunanin cikin week dinnan sudawo AJ yace gwanda ma kadage Kayi aure Dan naga
zaman kadaicin zay dameka Faisal yace sai kafara aure zanyi duk da kaidin jarumi ne da alama
saika auri mace fiye da daya bata rai AJ yayi yace Allah ya kyauta ai zuly ta isheni .
Bayan mota aka bude mai yashiga yazauna faisal yace kagaida su Mami inaga inshigo zuwa
gobe OK AJ yace sannan aka wangale musu gate din suka bar haraban cikin gidan.
Cikin yan kwanakin nan gaba daya pinky da leema basa zama sabida bikin wata kawarsu
daza ayi .
Daidai gate din gidan faiza tafaka motan sannan tadauki wayarta takira bugu daya aka
dauka tace pinky fito ki amshi kayan Dan sauri nakeyi mum najira na agida
Pinky daga cen tace ganinan fitowa
Tashi tayi daga kan kujeran da take kwance tace ma mama magajia tana zuwa daga ita sai
yar gown tafita takarasa inda motar faiza take tace amarya murmushi faiza tasaki tace daga
wajen tailor nake hannunta Tamika baya tadauko wata katuwar Leda Tamika ma pinky tace Dan
Allah Frnd kizo gobe kikuma zo dashiri Dan kinsan gobe za a Fara event Pinky tace naji sai minyi waya kigaida mum .
Sannan tajuya takoma cikin gida.
a Daren ranan taje saloon aka gyara mata Kai aka mata design ba ita takoma gidaba sai sha
daya .
Washe gari hudu na yamma faiza ta dameta dakira doguwar riga na material tasaka sannan
tayafara Dan karamin veil akanta sai karamar akwatin da tasa kayanta sannan handbag dinta
tare suka tafi da leema .
Kai tsaye asokoro suka nufa tun daga bakin gate din gidan mutum zaysan gidan babban
attajiri ne har cikin gidan suka shiga da mota suka yi parking sannan suka fito hanyan shiga
parlour suka nufa har daki suka Shiga suka gaida mum din faiza sannan suka wuce part din
faizan . suna shiga faiza tace wlhi fushi nake dake tun dazu yakamata kizo gashi har frnds din nasir
sunzo sun tafi kuma kinsan kece gaba gaba akomai
Hade hannayenta pinky tayi waje daya tace afuwan amaryar nasir bagani nazo ba.
. hararar wasa faiza tawasa mata tace 7:00 zasu dawo daukan mu no African time Dan nasan
Hali tabe baki pinky tayi tace kema kinsan nikaina nasani African time .
Wardrobe faiza tabude tacuro wainsu hadaddun materials Tamika ma pinky tace naki daya na
leema daya nakine me pink flower
Daidai lokacin ferry meyin makeup tashugo tace bride are you ready murmushi faiza tayi tace
yeah m ready.
[10/8, 18:10] Mrs Zaki: í ½í³š WAYASAN ASALINA í ½í³š
SAUDAT IDRIS NOVEL í ½í³•
PAGE 21
Leema tace rabuwa dashi shi zay fiye maki zama alkhairi sabida duk wani hukunci dazaki
dauka akan AJ wlhi abanza Dan zay maki mafiyin shine kiyi hakuri kawai ki kyaleshi .
Wata uwar harara pinky tama leema sannan tace tashi kitafi kawai ina bukatan zama nikadai
tana gama fadan haka takuma kifa kanta akan gadon taci gaba da hawaye.
Leema kam tashi tayi tafita Dan tasan dakyar pinky tadau shawarar ta koda tasauka
downstairs gayama mama magajia komi tayi hade dacewa mama kifa mata magana inba
hakaba babu abunda AJ bazay iya mata ba.
A bangaren AJ kam kai tsaye gidan aminin shi yanufa shima anan maitama yake .
Har cikin gida suka shiga sannan yasauko daga mota yayi sashin Faisal
Handle din kofan yarike yabude kofan sannan yashiga Faisal yana ganinshi yamike yace irin
wannan zuwan bazata haka captain murmushi AJ yayi hade dafadawa kan lallausar kujerar .
Faisal yace da alama dai yau kana cikin farin ciki meye sirrin AJ yace nothing kawai ina cikin
farin cikin ne yau Faisal shidai bai yanda ba Dan iya saninshi da AJ ba kasafai yake murmushi
ba sai yayi mugunta .
Amma saiya share kawai yakalleshi yace sai Hutu kakesha abunka Shafa kanshi AJ yayi
yace kuma wlhi hutunma ya isheni sbd ko yanzu din bana hutawa sbd yawanci Abba idan
angayyace shi wani taro ni yake turawa
Murmushi Faisal yayi yace ina gadai nan gaba siyasa zaka koma mawa dasauri AJ yace Kai
ina ai bana shaawan yin siyasa yanzu dai dazu nasir yaturo mun da invitation card na bikinshi
hope kaima zaka Dan kasan bana son zuwa biiki bikin nan Dan kawai nasir ma Nada mutunci a
ido nane shiyasa zanje Faisal yace gaskiya dole kaje blue shadda ne zaasa ranan dinner da red hula
AJ yace OK nafara ma tunanin kiran zuly tazo tarakani sbd tsaro
Daria Faisal yayi yace wahala dai kawai kakeson bata
[10/8, 18:10] Mrs Zaki: í ½í³š WAYASAN ASALINA í ½í³š
SAUDAT IDRIS NOVEL í ½í³•
PAGE 23
Zama pinky tayi akan stool ferry tabude katon makeup kik dinta tafara sansarawa amarya
kwalliya tun Ana Mata pinky tafara daukanta pictures ana gama Mata faiza tace saura ke pinky
Zuwa tayi tazauna ferry tafara mata kwalliyan tun Ana mata su leema suka Fara zuzuta
kyaun da tayi sai Takara kyau ga purple gown din da tasa Ana gama mata aka Nada mata
head duk da an nade gashin kanta sai daya tabo wuyanta faiza tace wow gaskiya ferry pinky
tafini kyau daria sukayi cikin hadin baki sukace waya gaya maki anafin amarya kyau . Leema ma anmata makeup din zama sukayi ferry tadaukesu hoto .
7:00pm daidai frnds din groom suka fara zuwa saida aka kwashe mutane dika sannan bride
and groom saisu pinky sai wainsu frnds din groom su kadai suka rage motar couples dinne
asakiya haka suka karasa har cikin
Ralmeton hotel wow abunda nace kenan da naga saruwan wajen
Komi purple and white ne amaryan ma shigan purple tayi shikuma ango white shadda sai
hula me rantsi rantsin purple ajiki frnds din ango kuma ash shadda sai hula me ratsi ratsin
purple .
Tun daga bakin gate zaka fara jin tashin kida a tsakiya sukasa couples din har suka karasa
cikin katafaran hall din wajen zaman bride n groom suka karasa suka zauna sannan kowa
yasamu gu yazauna
Faisal ne yabude taron da addua sannan yakoma wajen zamanshi yadauki wayarshi yakafa a
kunne yace AJ kana inane dagacen AJ yace ynxu zanshugo .
MC ne yafara gabatar da taron sannan yabukaci babban aminin ango yafito yafada tarihin
ango .
Takardan dake hannunshi Mc yakalla sannan yace captain Alamin junaid tuni wajen yadauki
tafi shikuma daidai lokacin yashugo da irin shigar da sauran frnds sukayi
Zan iya cewa kayan sunfi yima AJ kyau tuni matan wajen suka tsare shi da idanuwa Dan
guntun tsaki yaja sannan cikin takama yakarasa ya amshi MA kel phone a hankali yafara
jawabi Yakuma fada yanda masoyan suke son junansu pinky tunda takalle shi so daya tadukar
da kanta taci gaba da latse latsen waya . Bayan yagamane yakoma kusa da Faisal yazauna sannan Mc yace yanzu Zamu kira babbar
kawar amarya tazo tafada mana tarihi akanta
Paper din hannunshi yakara dubawa sannan yace pinkylecious
AJ dake zaune yace pinky
A yagance ta tashi daga kujerar tafara tafia duk Wanda yake wajen saida yakalleta banda
mutum daya da yaketa tsaki shi kadai
Cikin tsiririyar muryarta