Showing 24001 words to 27000 words out of 66129 words

Chapter 9 - Wayasan Asalina Complete Book by Zainab Idris Novels .pdf

15 Jul 2025

2327

yana shiga dakin wani kamshiy yabigi hancinshi murmushi yasaki ganin zuly zaune a
tsakiyan katon royal bed din a hankali yataka yakarasa har inda take yazauna hade dakai
hannunshi yaye gyalen dukar da kanta tayi alamar jin kunya cikin rikitacciyar muryarshi
me rikita ma mata lissafi yace wifey kunya ta kuma kikeji murmushi tasaki daukarta yayi
yakaita har bakin bathroom Sannan yadireta yace kishiga kiyi alwala ina zuwa .
Bayan shigan ta bathroom ne yafita daga dakin yawuce wani part yarage kayan dake
jikinshi sannan yashiga bathroom yawatsa ruwa hade dayin alwala sannan yazira wata
milk color din jallabia sannan yabar part din yadawo nata part din yashiga kitchen
yadauko gasasshiyar Kazan da aka gasa musu tako sha kayan kamshi dansai kamshi
takeyi me dadi sannan yadauki fresh milk da cups yawuce bedroom zaune yatadda ita .
Saida ya ajiye tray din yace wifey taso miyi sallah tashi tayi hade dabude wardrobe

tadauko hijab sannan suka tada sallan suna idarwa yamata tabbayoyi akan addini kuma
daidai gwargado tasani takuma bashi amsa.
Daga nan kuma yaciyar da ita dakanshi harta koshi sannan shima yaci yana gamawa
yakai tray din kitchen yawanke hannunshi sannan yadawo!
a Daren ranan dai bakaramar soyayya yanuna ma zuly ba Dan yasameta a cikakkiyar
budurwa .
[10/10, 11:03] saudah: 📚 WAYASAN ASALINA 📚 SAUDAT IDRIS NOVEL 📕
PAGE 36
washe gari bayan AJ yadawo daga sallan asuba dakanshi yadauki zuly yakaita
bathroom yagasa mata jiki sannan yafito yakyaleta tayi wankan tsarki.
bayan tafito ne tasanya wata doguwar riga da AJ yafito mata fashion ta tada sallah !
tana idarwa ta dukar da kanta kasa tace baby ina kwana antashi lafia
AJ dake zaune kan kujera sankowa yayi har inda take yazukunna hade dakai
hannunshi yadagota yana tsakar mata murmushi yace lafia qalau wifey
Hope kema kintashi lfy murmushi tasaki kawai hannu yakai yacire mata hijabin sannan
yadauketa cak kaman wata baby yakaita har kan gado yakwantary da ita sannan shima
yakwanta suka koma bacci.

dakyar ta iya tashi daga kan gado tana bin agogon Dakinta dakallo wani dogon tsaki
tasaki Dan tasan har tayi missing lectures guda !
Tashi tayi tashiga bathroom tawatsa ruwa dasauri tafito tana cikin shiri leema tashugo
dakin harara pinky tawatsa mata hade dacewa kinfa san Inada lectures yau karfe tara
amma koki tasheni murmushi leema tasaki hade dacewa afwan kokin manta bagida
nakwana ba dawowana kenan pinky tace ina zan sani tunda ina bacci kika fita . leema tace hakane fah da alama dai yanzu kinhuta da takura captain tunda yayi
sabuwar amarya pinky batasan sanda tasaki tsaki ba tace matsalar shice danni harna
manta dawani AJ .
Murmushi leema sannan tafita
Yau doguwar riga na atamfa pinky tasaka kuma bawata kwalliya tayi sosai ba amma
tayi kyau sosai kam Dan karamin gyale tayafa kalar kayan sannan saita tsaka flat shoe
hade da daukan handbag dinta tasauko downstairs dakin mama magajia tashiga
tagaisheta sannan tawuce parking space tama motar key tashiga sannan tabar gidan!
Sati daya sukayi suna shan amarci
Dan hutun shi saura kwana biyu yakare kuma tare da zuly zasu tafi!

Da dare suka shirya zasu gidan su zuly ta damu AJ subiya shoprite zata tsiya abu
babu yanda ya iya haka Suka biya yana parking motar pinky ma tana shugowa kusan
waje daya sukayi parking saidai Sun riga pinky shiga ciki !
Duk da itama abu dayane kawai yakaita zuly wajen saida perfumes tanufa AJ yace
saline gayamun perfumes kikeso dasai insa akawo maki .
juyawa fuskanshi yayi gefe dan matan wurin Sun cikashi da kallo yana juyawa
yahango pinky daga ita sai yar yellow din gown daya Tsaya mata iya gwuwa sai dan

karamin gyale baisan sanda yasaki tsaki ba yayi wajen da take dasauri yana karasawa
yakai hannunshi yajanyota gefe inda ba mutane kallon juna suka farayi pinky tayi saurin
kwace hannunta tace meye haka hannunta yakara rikowa yace wane irin rigane kikasa
haka kiko san wannan shigan arna ne sbd duk ilahirin jikinki abayyane yake idan har
bakison zaman garin nan ya gagareki dole kiringa sa kayan mutunci bata fuska pinky tayi
tace irin kayan danake dasu kenan kuma ni nasha gaya maka bana son sa ido !
Dayan hannunshi yakai yaja mata baki dakarfi sannan yace rashin kunya na dawainiya
dake nadai gaya maki keba kyauba saison sa kayan masu kyau yana gama fadan haka
yasaketa yabar wajen yakarasa inda zuly take ya amsa basket din pinky tana kallonsu
har suka je suka bada ATM aka cire amount din kudin nandanan taji ranta yabaci. dan taga sai nan danan yakeyi da zuly tsaki taja tace Dan rainin hankali kawai matar
taka aiba kyau tafini ba !.


Daga nan gidansu mami suka wuce
[10/10, 21:03] saudah: 📚 WAYASAN ASALINA 📚 SAUDAT IDRIS NOVEL 📕
PAGE 37
a parking space yafaka motar Sannan yasanya hannunshi yabude murfin motan zuly
ma haka perfumes din data tsiya tadauka kallonta AJ yayi yace tsarabar su mami ne
kenan daga mai kai tayi alamar eh sannan suka jera sukaayi part dinsu mami!
da sallama suka shiga cikin parlorn dagudu Mimi da sury suka tashi suka taro zuly
hade da amsan shopping bag din hannunta gaishe da mami tayi cikin ladabi sannan
tasamu gu tazauna !
AJ ma waje yasamu yazauna hade dagaida mami !
Atare su mimi suka ce ya ina wuni lafia qalau yace sannan yace Waiku bazaku koma
skool bane marairaice fuska sukayi sukace ya AJ this week zamu koma tunda muna final
year ne .
Mami tace daga zuwanka zaka fara takura ma yara sosa kanshi yayi hade dacewa
Abba yana office ne mami tace yana office amma yana tare da baki !

tana Gama tsiyan abunda yakaita tabar wajen tana driving amma gabaki daya tunanin
AJ takeyi sbd yanda taga yama gama raina mata wayo tayaya ma Zayce mata
mummuna bayan tafi matarshi kyau Allah yakuma hadata dashi tabbas saita gaya mai
magana daidai bakin gate tatsaya tayi horn gate man yabude mata gate tashiga haraban
cikin gidan !

Tana parking tafito hade da daukan handbag dinta dakuma shopping bag din tayi cikin
gida mama magajia kawai tasamu Dan yauma leema ba gida zata kwana ba '

zama tayi a parlorn suka dan taba hira da mama magajia sannan ta tashi tawuce
upstairs tana shiga dakinta tarage kayan jikinta tashiga bathroom tawatsa ruwa Sannan
tafito Dan karamin rigar bacci tasaka red color hade da feshe jikinta da turare dan
pinky akwai son kamshi fadawa kan gado tayi tajayo bargo sannan takara gudun AC .

hira sosai akeyi saidai sam hankalinshi baya tare dashi tunanin yarinyan yadame shi
ko yanzu takoma gida oho ji kawai yayi bazay iya zama ba saiya je yaga kota koma
gida !. Dagowa yayi yakalli zuly yace wifey Bari inje indawo mami tace alamin ina kuma
zaka bayan goma takusa ai gida yakamata kutafi yanzu ! shafa kanshi yayi dandai baisan karyar dazay ma mami ba hakanan babu yanda ya
iya Mami tacewa zuly ta tashi su tafi har wajen motarsu suka rakasu saida sukabar
haraban gidan sannan suka koma cikin gida!
shi kam har ga Allah yaso yaje yaduba ko takoma gida toma meyasa ban amshi
phone no dinta ba duk acikin zuciyarshi yake wannan maganar baisan sanda yasaki tsaki
ba a fili zuly tayi saurin juyawa takalleshi tace baby lafia batare daya kalle Taba yace
lafia ! Koda suka koma gida part dinshi yawuce zuly ma tawuce nata bangaren dan ita ba
irin me kula da mijin nan bane sam Amma akwai ladabi !
Saida yayi wanka sannan yadauki wayarshi yakira zuly yace takawo mai coffee .
Dasauri tawuce kitchen tahada mai hade da daurawa akan Tray da cups guda biyu
sannan tawuce sashin shi zaune ta taddashi akan kujera ya lumshe ido aje Tray din
tayi hade da cewa baby ga coffee din Dan wallahi bacci nakeji kasan kwana biyu bana
samun bacci sosai bude idonshi yayi hade dacewa baki samun coffee dinba kuma zaki
tafi karasawa tayi tasa Mai sannan ta ajiye tace inka gama kasameni bacci ne a idona
kallonta Kawai yakeyi Dan sam sai yanzu yasan bai auri kalar macen daya keso ba
shiyafi son wacce zata ringa bashi Kulawa amma ita komi sai ansata harta juya zata fita
saikuma tajuyo tana murmushi tace baby dazu nagama waya da daddy yace yashirya
mana honeymoon zuwa Paris zuwa nanda jibi yakamata mutafi dagowa yayi yakalleta
sannan yace babu Paris din daza aje shagwabe fuska tayi tace haba baby umarnin
daddy nefa kuma kasan burina kenan miyi honeymoon dinmu a Paris tsaki yasaki yace
inbiki mutafi nikuma inbar aikina kenan toh bazay yuyuba saidai idan ke kadai zaki tafi
hawaye tafara yi ganin hakane yasashi cewa tafi dakinki idan kuka zaki mun dan ko
kukan me zakiyi babu inda zaaje tunda ni nake iko dake ba daddy dinki ba dasauri
tabar dakin tana shashshekan kuka !
Tana fita yaja wani dogon tsaki daman yasani dole yasamu irin wannan matsalan nan
dan dabiun yan gidan sune duk abunda me martaba yakeso shi ake yi dogon tsaki
yakara tsaki akaro nabiyu yace badani zaayi haka ba ni na banbanta dasauran dan babu
wanda ya isa ya juyani . [10/10, 21:38] saudah:

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login