Showing 48001 words to 51000 words out of 66129 words

Chapter 17 - Wayasan Asalina Complete Book by Zainab Idris Novels .pdf

15 Jul 2025

3114

da Teddy's .



Yauda matsanancin ciwon ciki pinky ta tashi sannan sai wani ruwa dake fitowa ta
kasanta ammi ce tashugo dakin taga halin da pinky take dasauri tajuya taje tagaya ma
abba shima arude yabiyo bayanta hade da daukan makullin motarshi .
Su biyu suka kamata har wajen mota sannan suka bar gidan asibiti mafi kusa zakuje
ansan gaggawa aka mata sabida tafara fita hayacinta ana shigar da ita dakin haihuwan
bada jimawa ba Dr din yafito yana share zufa dasauri su abba suka karasa gunshi
ammi tace tasauka lafia ko Dr yace lafia lau tasauka saidai baby girl din data samu
takoma yanzu zaa kaita dakin hutu yana gama fadan haka yabar wajen .

Abba wayarshi yacuro yakira sadiq yagaya mai hade Dace mai yakira alamin yafada
mashi dan susan halin da ake ciki .



dakin da aka kai pinky su ammi suka karasa kwance suka tadda ita saidai idonta
biyu dasauri ammi takarasa wajenta tazauna hade dakamo hannunta tace sannu little
daga kai pinky tayi hade dacewa ammi ina abunda na haifa badai har captain ya anshi
abun shiba girgiza kai ammi tayi tace saidai kuyi hakuri Allah ya amshi abunshi hawaye
kawai pinky taji yana zubo mata da batasan dalili ba. Sadiq suna gama waya da abba
yakira AJ bugu daya yadauka dan sai wani zumudi yakeyi yana dauka sadiq yagaya mai
abunda ke faruwa hade dagaya mai asibitin dasuke zaman dirshan AJ yayi akan kujera
hade da dafe kanshi zuly ce tafito daga kitchen rike da trey takarasa inda yake tace
baby dagowa yayi yakalleta duk sai yaji tausayinta yakamashi hannunshi yakai yajanyota
jikinshi ya rumgume hade da buga mata baya yace wifey kiyi hakuri zuly da bata
fahimci komai ba tace baby meke faruwa ne kara matseta yayi ajikinshi sannan cikin
sanyin murya yace wifey babyn da muka dadai muna ma tanadi Allah ya amshi abunshi
zuly da tagama rikicewa bakinta narawa tace captain bangane abunda kake nufi ba
matseta yakara yi sosai yace kiyi hakuri kuka tafashe dashi hade da rike rigan shi sosai
tausayin zuly yakama shi dakyar ya lallasheta yace tashirya yakaita gidan su mami shi
daga nan sai yawuce asibitin .
[10/15, 22:49] saudah: 📚 WAYASAN ASALINA 📚 SAUDAT IDRIS NOVEL 📕
PAGE 54
tun amota take hawaye har suka karasa gidan su mami .
Dan bakaramin sa rai tayi da babyn ba balantana ma idan ta tuno da maganar Dr
sai taji zuciyar ta takuma mata ba dadi ahaka suka karasa villa yana kuma tausanta
yana ajiyeta yace tashiga shi zayje yadawo .
girgiza mai kai tayi tace kabari inga ko fuskan tane pls captain bakasan halin da nake
ciki ba ayanzu tausayin tane yakara kamashi OK kawai ya iya cewa sannan yaja motar
suka bar gidan kai tsaye asibitin da sadiq yafada mishi suka Nufa .

dakin da babyn take aka kai zuly tana ganinta tafashe dakuka tafada jikin AJ lallashinta
yashiga yi sannan sukabar dakin suka wuce dakin da pinky take pinky tana ganin zuly
sai hawaye yafara ambalia akan fuskarta Dan tausayin zuly ne yakamata ammi ce ta
tashi ta taro zuly hade daja mata kujera tazauna gaisawa AJ sukayi da ammi sannan
suka fita daga dakin Shida sadiq dan zuwa tsitirce jaririyan.

Bayan barin su dakin zuly ta tashi takarasa inda pinky take tazauna hade dakamo
hannunta tace nagode sabida da taimakonki naga jinina a dunia nagode sosai farida Dan
bansan dawane baki zan iya gode maki ba murmushi pinky tasaki me hade da hawaye .
zuly tace ki taimaka ki yarda da hukuncin dasu abba suka yanke kada kiyi tunanin

wai ko captain mijina ne Dan Allah badan niba ki yarda da auren AJ.


Ammi dake jin maganan da zuly takeyi tuni taji yarinyan tashiga ranta tashi tayi tafita
daga dakin tabasu waje .

Hawaye pinky takeyi sabida bata Taba ganin me kyaun hali irin zuly ba lallai dole ayaba
mata .
zuly tace kinyi shuru pinky murmushi tasaki tace nayarda amma badan ina son hada
kishi dake ba saidan kin rokeni sosai zuly tayi farin ciki tace nagode !
Allan yabamu hakurin zama da juna Aameen pinky ta amsa dashi .


a haka akayi sadakan bakwai duk da yanzu zuly takwantar da hankalinta saidai tasa
tunani sosai a ranta
pinky kam kullin sai ammi tamata wankan jego har nakwana arbain.

dan tadawo yanda take da Dan yanzu har wani kyau takara da haske.
Mr president kam ya dage akan sati me zuwa zaa daura auren AJ da pinky tuni AJ
yatada hankalin shi dan shikam harga Allah bai shirya ma auren acikin kwanakin nanba
danma zuly tana kara karfafa mai gwuwa akan auren.

Kuka pinky ta tasa su ammi tana musu sadiq dake gefe azaune yace little kiwa Allah
kiyi hakuri kiyi shuru ba gwanda andaura auren yanzu ba kihuta wani kukan takuma
fashewa dashi abba yace ikon Allah nidai banga aibun alamin ba da kika tasamu agaba
kina mana kuka ammi tace aikam alamin baida aibu tunda kowa yabonsa yakeyi kallonsu
pinky tayi tace Allah wallahi ammi bakusan muguntan captain bane Daria ma tabasu .
Abba yace toh naji tunda baki sonshi wa kike so tsit tayi tarasa bakin magana dan dai
ita ko ada bata Taba son kowa ba .
Abba yace yi magana ina jinki dakyar ta iya bude bakinta tace abba duk wanda
kazaban mun ina so amma banda AJ abba yace toh shikenan shidai alamin dinne bakiso
daga kai tayi alamar eh abba yace toh shikenan zankira Mr president muyi magana.
Murmushi tasaki hade da mikewa tsaye tace nagode abbana nagode ammi tace yar
nema sadiq yace wallahi kada kidawo kina mana kukan wayyo captain kikee so shagwabe
fuska tayi kamar me shirin yin kuka tace abba kagan shiko ammi tace yi hakuri kai kuma
tashi katafi dare yanayi saida safe.


Daria pinky tayi hade dacewa yaya saida safe kagaida mun da yarona da auntie haja
gobe insha allahu zanzo .
Sadiq yace kada insake inga kafarki agidana daria tayi tace nida gidan yayana hararar
wasa ya watsa mata sannan yamike yace ammi abba saida safe.

jikinshi sosai tashige tafara mai magana a hankali tace baby ko yar hirar fa baka zuwa
tsaki AJ yasaki yace kinsan ko kema ba kasafai nake zuwa zance wajen kiba zuly tace
nasani amma ni ai muna da nisa ita kuma farida gari daya kuke yakamata Dan Allah gobe
kaje tunda dai kaga su abba sunfara shirye shiryen biki OK yace hade dacewa kedai
bansan wace irin mata bace yar aljanna daria tayi tace harka shigar dani kenan daga
mata kai yayi hade da hade bakinta da nashi
[10/16, 06:43] saudah: 📚 WAYASAN ASALINA 📚 SAUDAT IDRIS NOVEL 📕
PAGE 55

washe gari da yamma pinky tashirya cikin riga da sket na Atamfa Dan yanzu ammi
tasaka an dindinka mata kaya English wears dinta saidai tasasu agida.

Kayan bakaramin zauna mata sukayi ajiki ba gakuma wani uban dauri da tasha sosai
tayi kyau Dan Rambo color tahada key car dinta tadauka tafito daga dakin ammi ta
tadda aparlor Itada wainsu baki gaidasu tayi sannan tace ammi na zanje gidan yaya ammi
dagowa tayi takalleta tace adawo lafia kigaida mun da hajara kuma karki kai dare . Insha Allah pinky tace sannan tafice daga parlourn kai tsaye parking space tanufa tama
motar ta key har zata tada motan taga bakuwar mota tashugo gidan hakan yasata
tsayawa .

Har wajen da ake parkin yakarasa yayi parkin sannan yabude murfin motan yafito
manyan kayane ajikin shi maroon color yayi kyau sosai suna hada ido duk zuciyoyinsu
saida suka buga .
Kokarin tada motar takeyi AJ yakarasa dasauri yasanya hannunshi yacire key car din.

Hararar shi tayi tace meye haka shima hararan nata yayi hade dacewa ina zakije uwar son
yawo kallonshi tayi sannan tace inda ka aike ni nikawai kabani mukullin motata .

AJ yace naki na karfine murguda mai baki tayi hade dacewa nifa shishigine bana so
kuma tunda yauba nasha gaya maka AJ yace kwana nan nan zanyi maganin bakin rashin
kunyan nan .
Dan haka idan har kina son fita dole saikin gayamun inda zakije juyar da kanta tayi
sannan tace gidan yaya zani oya bani key car na murmushi yasaki sannan yace bari
ingaida ammi infito sai in kaiki har yafara tafia pinky tace ammi natare da baki juyowa
yayi yace ok fito mutafi badan tasoba haka nan tafito daga motar ta tawuce tashiga motar
shi shima yashiga yatada motar sukabar haraban cikin gidan saida sukayi tafia me nisa
sannan AJ yadan Kalli pinky tagefen ido yace dakin daina yawan sa turaren nan Dan baida
amfani Mace tawani feshe jikinta da turare in zata fita .
Banza pinky tamai wayar ta dake cikin handbag dintane yayi ruri hannunta takai
tazage zip din jakan sannan tadauki wayar Dan har saida gabanta yafadi da taga me
kiran nata Dan harga Allah batason yin magana ko haduwa da duk wani abokin harkanta
ada barin wayan tayi yaci gaba da ringing .

AJ yace wannan karar wayar taki ta dameni In baza kiyi picking ba toh gwanda kisashi a
silent. Yana rufe bakinshi aka Kuma kiran wayar kuma duk mutum dayane tsaki taja hade
da daura wayar akan cinyarta yaci gaba da ringing shi Kadai .


AJ hannunshi yakai kan cinyarta yadauki wayar sunan minister yagani akan screen din
baisan sanda yasaki tsaki ba hade da kashe wayan gaba daya pinky tace meye
nadaukar mun waya banza yamata sannan yafaka motar abakin hanyan yabude wayar
yacuro SIM din yakarya hade da watsi dashi awaje kallonshi takeyi cike da mamaki tace
kasan Allah bazay yuyuba saika biyani SIM dina Kaiba mijina ba kuma kaiba aurenka zanyi
ba amma kawani karya mun SIM dogon tsaki captain yasaki yace wayar ma bazan baki
ba Dan na fahimci haryau bakiyi hankaliba yana gama fadan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login