Showing 27001 words to 30000 words out of 52374 words
Chapter 10 - NA TAFKA KUSKURE COMPLET BY JANAFNANCY-1.pdf
wanka lalle mai hade da
sinadarin turare mai tsayawa aran masoyi cikin kwana biyu Safeena ta chanza jikinta yadawo
yana fitar da wani kamshi mai dadi gashi tayi wani haske da sulbi ita kanta ajikinta tanaji ta
chanza domin kullum cikin zubar da ruwan Ni'ima take ko wayama basuyi inna husai ta kwace
Dr yanaji yana gani Dole ya hakura har komai ya kare.
Ana saura kwana uku tarewar uwargida Sakina ta diro gidan bayan shafe sati uku batanan daga
katsina kano taje daga chan ta wuce dubai kwananta goma ta dawo sai da tsaya tagama
clearing din kayanta suka iso hannunta tukun ta dawo tayi mamakin ganin chanji agidan bata
gama mamaki ba sai da tashi ga sashensu taga ikon Allah batawani damu ba ita duk azatonta
Dr neman sulhu yake da ita shiyasa tana shiga daki tace"Hmmmm dama nasan zaka nemi ni
wlh zaka gane kuranka indai sakina ce"Tafada tana shekewa da dariya.
_lalle sakina kin cika sauna inbanda sakarci ko ada bai baki hakuri ba sai yanzu stupid
kawai_í ¾í´”
*Shakira..*
Commet
And
Share
Vote
[10/14, 20:01] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..!*
*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_
*DEDICATED TO:My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*
*22*
"Koda Dr yadawo yaga Sakeena bai wani yi mamaki ba cos shiyanzu bata gabansa kokarin
yadda zuwan amarya zai zama ready yake.
Bada wuri yadawo ba shiyasa sai da yayi wanka yayi sallah kana yadauki check din daya
rubatama sakina kudi yanufi dakinta da sallama abakinsa ya shiga illai kuwa Yar mulkin na
kwance kan gado tana zuba selfie tana daukan yanayin dakin dariya takusa kubcemai,saboda
ganin yadda take wani ji dakai ita adole miji ya biyota dauke kai tayi kamar bata ganshi ba
tacigaba abunda tajeyi mirmishi yayi kan ya isa ya zauna gefen gado yana fadin"Ashe
andawo....Andawo lpy..?
"kamar baza tayi mgana ba sai chan tace"Lafiya kalau aka dawo duk da akwai wanda baiso
mutafi ba"Tafada tana wani girgiza jiki dariya yayi har hakoransa suka fito yace"Ai wani baice
kar mutum yaje ba iyaka yace mutum yaje da kudinsa ne hakan da yayi laifi ne..?"Yafada yana
kallonta basarwa tayi domin tagane yagasa mata mganane mikamata check din yayi takalleshi
a wulankance tace'Na miye kuma mallam..?Yace"Ki karba nakine"amsa tayi awulakance tana
dubawa check din 2000hud thousand ne arubuce dagowa tayi ta mika mai tana fadin"Ka
makara ai ka rike tsiyarka domin ni yanzu nafi karfin taimakonka ko dama tsautsayi ya kaini
Tambayanka"bude baki yayi kan yace"Ke...abunda kike tunani kenan..?"Yafada hannunsa a
haba Sakina tace"Bangane ba"Yace"Kudin nan hakkinkine fa aure zan kara shine nafita
hakkinki na baki kudin saboda kisai Abunda kikeso..."yafada yana kallonta kallonsa takeyi kan
tasheke da dariya harda faduwa kasa kallonta yakeyi aranshi yana auna dabbancin sakina.
Mikewa yayi ya ijiyemata check din yanufi hanyar kofa yana cewa'Ki bar dariyarnan ina jiyemiki
ranar da zaya koma miki kuka"Saurin mikewa tayi tasha gabansa tana cewa cikin
shakiyanci"Tab...Wai aure zakayi kai bakaji kunya ba,ni zaka razana to ai bari kaji ni Sakina
matar kaddarace mutuwace kadai zaisa kayi aure kai ko mutuwar nayi sai na ga dama balle da
raina'Tafada tana nuna kanta kan takara shekewa dadariya,kallonta yayi kan ya girgiza kai
yace"Kin Tafka kuskure sakina shiyasa har yanzu yake dawainiya dake kinyi kuskuren sawa
aranki zan dauwama dake ke daya....watch and see"Yafada yana kada mata hannu kafin ya
fice.
check din ta dauka kan tace"raba mugu da makami....Ibadane'tafada tareda fadawa kan gadon
tana fadin"ji shi wai aure kamar auren banzane"Daga haka tajawo wayarta tacigaba daga inda
ta tsaya
*Chai chai wlh kedai sakina anyi dabba wlh kin tabajin inda akayi wasan kishiya mtsssss mai
kwakwalwar kifi kawai*í ½í¸¡
ko washegari tun safe Abuja tatafi saboda isar kayanta kotakan mganar Dr bata bi ba gani
takeyi bazai taba iya kara aure ba sai da ta fito zata tafi yaganta shima zashi aiki yake
cemata"Madam business sai ina kuma..?"Tayi mamaki ammh saita danganta haka da neman
shiri yake a yatsine tacemai Abuja Mirmshi yayi mai kayatarwa yace"Allah ya kiyaye hanya
madam business"Daga haka ya fice shashen momma ya barta nan itama daga nan tahaye
motarta tayi gaba.
Ashashen momma daru suka sha da haj.Mama don yace tabari abincin sha'anin bikin yayimusu
odar Daga Restaurant haj.Mama tace"Ina bazai yuyu ba tuka tuwon ne akafi su iyawa kokuwa
miyar ne za'a nuna musu kukowa dafa shinkafanne za'a nuna musu to maza karya ya sake
wannan ai barnan kudi ne yan'uwanta zasu zo Daga Safana suzasu komai yi kada inji ka
gayyatomana wasu kedararru suna bamu abinci"Dole ya hakura ammh yana jinjinama karfin
halin hajiya mama na fadar abunda bamai sauki bane a gareta.
Tun aranar bakin Safana suka fara zuwa matar kawu bala uwani da abokiyar zamanta sai
makotansu hakika haj.Mama tayi farincikin ganin baki sun fara hallata mussamman Haj.Mama
tasa aka gayyatomata masu kidan kwarya daga zaria dushi _wayyo za'a tuka tuwon babban
gida_ momma kuwa farinciki yagama cikata duk inda ka ganta bakin nan har kunni goye da
bawan Allah Adil.
Washegari kuwa sai ga mota tahau sauke musu drinks kala kala da ruwa abun sai wanda
yagani baki kuwa suncika gida harda yan garinsu momma Allah sarki aikin haj.Mama ce tace
kowa yazo ataru anuna farinciki domin yanzu safiyanu yayi aure,koda Sakina tadawo daga
Abuja taji hayaniya ashashen su momma ammh bata leka ba tunaninta yan kauyen nanne suka
zo sucika ma mutane gida da hayaniya ko kallon shashen batayi ba tayi shigewarta shashenta
agajiye take shiyasa wanka kawai tayi tafada gado sai barci yan aikinta naso suyi mata tsegumi
domin gunsu habu maigadi sukaji yallabai zaiyi aure ammh ganin ba fuska yasa suka ja bakinsu
sukayi shuru.
****
Zurmi...
Sai ana gobe tarewar Safeena tadawo duk wanda ya ganta sai yakara kallonta saboda wani
sheki data keyi kamar daren goma sha biyar Koda tadawo tayi gyaran kanta da lallenta
kawayensu na mkranta sunyi mamakin jin tarewar safeena kuma wai andaura tuni harta Mallam
yahuza takaima katin Tarewar ya amsa yana sama mata albarka da aurenta gabadaya _Allah
sarki loser_ batada wasu kawaye shiyasa daga ita sai Aisha suke gudanar da komai gashi
daman Dr yace"Su zama cikin shiri karfe biyu za'a zo atafi dasu saboda kada suyi dare ahanya.
mganar kaya kuma hajiya ita tayi mgana Da Abbah tace kadama ya wahalar da kansa domin ko
sunkawo zatasa amaidamai saboda safeena da safwan duk dayane agurinta ba bambamci to
bbu yadda ya iya domin hajiya nada wata kima a idanunsa bbu abunda zaice sai godiya domin
iyalan justice habule safana sun gamamai komai.
*YININ BIKIN TAREWA*
_*Both kaduna and zurmi*_
Tabbas inda ake dashi nan akeyi domin tuni takowani bangare shagali yakachame bari mu leka
kaduna.
Haj.Mama tun asuba tasa aka dora tunkunya lamba talatiní ¾í´£í ¾í´£na tuwo da na miya aka shiga
sha'ani atsakar gidan masu yanka alaiyahu nayi masu yanka albasa nayi wuri yahade sai hira
ake ana shewa.
Itakuwa momma tana ciki ita da bakinta mommy na tare da ita ga dan Amanar ta Adil shima
yaci gayunsa yau takefa ranar itama momma taci gayunta cikin swice less dinta tadau dauri
momma ta fito ras da ita ita kuwa hajiya mama doguwar rigar shadda taci taji aiki abunta harda
daurin gwagwaroí ¾í´£,kan kice kwabo am kammallah tuwo an kwashe aleda an zuba a kuloli
miyama tuni ta sauka wacce taji naman rago zubu zubu aciki ga jallop din shinkafa itama an
kammallah ansa a kuloli ga alalen leda shima an kammallah abun gwanin sha'awa tuni aka
tsabtace wurin kamar ba'ayi komai ba.
Itakuwa sakina sai wajen 12 tatashi tayi wanka tafito falo koda ta fito taji hayaniya ta leka har
sungama komai sun shige ciki sai hayaniyarsu kawai takeji tabe baki tayi takoma tasanya
tashar bollowood tana kallo ko ajikinta shidaman Dr tun Safe yayi wanka yafice suna chan suna
tsara yadda za'a tafi dauko amarsu ta ango.
Azurmi ma shima abunda ya gudana kenan domin ana hada hadan saukewa da dorawa ita
kuma Amarya Safeena tana gidansu Aisha ita da kawayenta suna sitting cirewa kawai take tana
zurawa chan bayan sallar azahar iyami tazo tatafi da ita gidan baffanta usuhu aka kaita yamata
nasiha wanda tuni Safeena tafara kuka sun kawo kofar gidansu kenan sai ga motocin daukan
amarya guda goma sha biyu hadaddu domin ba motar banza tahir da taufiq da jabir da
Gidado,da sauran abokansu dai sukazo Tahir ne shugabansu.
Cikin gida akayi da Safeena domin kaita gun Abbanta yamata Nasihan zuwa gidan miji.
*Anitha..*
Commet
And
share
Vote
[10/14, 20:01] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..!*
*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_
*DEDICATED TO:My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*
*A hearty and Birthday to the most Adorable, and sweetest person i have know...Happy Birthday
KHADIJA CANDY#Maamaâ¤ï¸Wish u Allah khairs and Noor*
*23*
'"Kai tsaye dakin Abbanta aka kaita wanda yake ciki domin anfadamai za'a tafi da safeena ita
kadai aka bari dashi tana durkushe agabanshi sanye cikin dogon farin hijabinta tana kuka.
Abbah yayi gyaran murya Yace"Safeena kibar kukan nan hakan ki saurari nasiha mafi daraja da
tsada daga mahaifinki wanda rashin sauraran zai sa kirasa abubuwa dadama
arayuwarki"Yadakata cak kuwa kukan safeena yadauke Abbah yacigaba da cewa"Rana bata
karya sai dai uwar diya taji kunya hakika yau ranar da amanarki zai fita ahannunmu yakoma
ahannun mijinki ne to nasihata agareki yake yata shine na farko kiyi biyayyah zuwa ga mijinki ki
kasance baiwa agaresa shikuma yazammiki ubangida kibisa sau da kafa domin aljannarki tana
karkashin kafansa ne yake yata kada kizama mai bijirema bukatar mijinki akoda yaushe kisance
mai goyamasa baya aduk abunda yasa gaba kada ki kasance mai gardama agaresa kuma kar
ki kasance mai saurin fushi agaresa ki koyi mu"amala da kowa ki kyautatama yan'uwansa sai
kema ya kyautata naki ki girmama abokiyar zamanki sai itama ta girmamaki domin keki ka
auran mata miji kina kasa da ita sannan abu na karshe ki girmama mahaifiyarsa da kakarsa
kamar yadda zaki giramamu Safeena ki kaunaci Safwan da duk abunda yadanganceshi to
inkikayi haka kin rabauta duniya wa lahira yata'.."
yafada muryansa tayi rauni safeena ta fashe da kuka tace"insha Allahu Abbah namaka alkwarin
baza kasameni mai saba umarninka ba'.."Abbah yace"Nasani Safeena bazaki bani kunya ba
tashi tashi asada ki da dakin aureki na har abada"Yafada yana mikar da ita tana mikewa ta
rumgumesa kam tana kuka hannunta yakama ya sanya mata karamin al'qur'ani izu sitti kafin ya
kira iyami yace suzo su fita da ita shikanshi hawayene ya gangaromai na rabuwa da yarsa mafi
soyuwa agaresu su iyami suka banbareta jikin Abbah da kyar sunkusa fita da ita Daga Dakin
yadaga murya cikin rauni yace"abunda na baki ki rikesa da kyau duk halin kuncin dazaki shiga
to karki manta dashi domin shi din haske da warakane ga duk wanda ya rikesa ku tafi ubangiji
ya kaiku lpy yakuma sanya Albarka arayuwar Aurenki..
"Yanagama fadar haka yajuya baya hawaye sun gangaro masa haka aka fice da ita tana kuka
gun Ummi aka kaita wanda tun shigowarsu take kuka ana bata hakuri iyami tace'",zainabu
lokaci na tafiya kisama yarki albarka "Ummi tace cikin kuka tana dafa kan Safeena dake
durkurkushe gabanta tace"Duk nasihar da zan miki yan uwana da mahaifinki sun miki nidai abu
daya zan gayamiki kibi mijinki kibi mijinki ki mai biyayyah kana daga karshe ki kasance mai
tsafta da kamshi akoda yaushe sannan ki girmama mahaifiyarsa da kakarsa in kika kuskura
kika saba musu Safeena ban yafe miki"Maman Aisha tace"Ashsha maman Safeena"Ummi
tatashi tadago safeena ta rumgumeta suka kamkame juna Ummi tace"ku tafi yata Allah yabaku
zaman lpy yasa gidan zamanki kenan har mutuwa Allah ya miki albarka na yafemiki duniya da
lahira"Allah sarki rayuwa duk mai tsausayi sai da yayi kwallah dakyar aka rabasu ummi na kuka
safeena na yi haka Usman dakyar aka bambaresa ajikin safeenar aka sanyata cikin motar tahir
wanda iyami da inna husai da maman Aisha suka sata a tsakiya sauran motocin kuma jama'a
sukai ta shiga abun mamaki chan naga zugan Janaf novels 1&2 sunci ankosu na perper less
blue and pick sundaura head pick su mom khadija mom Amira my xee Abi my juree name sake
sahiba gun shiga mota harda faduwa, hakika sun bada kala domin kaf dinsu sun halarta ba
wanda aka bari gadin gida wow.. Chan naga yan Na tafka kuskure fans suma sun kame awata
jeep chan kuma na yan kungiyata Interlligent writers association suma da nasu gayyar suna sun
kame awata bakar corrolla x hadaddiya na rike baki nace"Tab. To yaushe suka zo nibanma san
zuwansu ba nima dai na lallaba na shige motar kawayen Amarya kada atafi bani.
Karfe 4:00 dai dai muka dau hanya sai fatan Allah yakaimu lpy.
******
Kaduna
Karfe 8:39 daidai muka shigo kaduna domin dai ba'ayi wani gudu ba domin Dr ya tsawartar
yace"Kada ajamai asarar da baiyi niyya ba dole aka lallaba dasu ahankali ammh ina kallon yan
janaf fans sai da suka ce atsula gudu dasu domin motarsuce akan gaba nidai nace to Allah
yasa kada haj.Mama tace nayomata zugaí ½í¸›.
Magadi najin hon yabude get motoci suka dunga sulalawa ciki aikuwa kikaji guda na tashi
domin haj.Mama najin hon tayi waje matar kawu bala kuwa ta dinga sakin guda abun sai wanda
yaji haj.Mama ta bude murfin motar amarya iyami ta fito da ita haj.Mama ta waiga tace wai ina
matan ne banji guda na tashi bane ai kan hajiya tace me kuda ya kacame gidan domin yan
janaf ma ba'a barsu abaya mussaman murya mom khadija data Name sake tafikowa murya
sahiba kuwa muryanta kadai akeji gida ya hautsine da murnan isowar amarya hajiya ta rike
Amarya tana fadin"Aminiya kin biyashe ni domin kin kawomin safeena har gida ina kara
godiya"iyami tayi dariya tace"hajiya duk mu godema Allah domin shine abun godiya"Haj.Mama
tace hakane kam bari tashiga shashen hadiza tukun kafin taje barayinta tako amarsu kinzo
gidan karamci gidan mutumci da amana tako da bismillah Amaryan Safiyanu tako da izinin Allah
aifa nan aka dau sowa da guda anayi har shashensu momma itadai Safeena tana dunkule cikin
hijabi tana kukan rabuwa da iyayenta.
SAKINA Na daki taji dirin motoci zuwa chan kuma sai guda na tashi ta ko'ina taji abun yawuce
misali shiyasa ta fito ta isa ga windon falo ta leka sai ko taga tawaga guda ga haj.Mama rike da
wata lullube cikin hijabi ana ta guda gabanta yafadi ras'ras lokaci na farko tareda rawan jiki a
idonta aka wuce shashen su mommah jikinta asanyaye ta saki labule takoma kan kujera ta fada
yaraf tana auna abubuwa akwanyarta ta tuna kalaman Dr _kudinki ne aure zanyi nabaki ki siyi
ra'ayinki_ tatuna kuma abubuwan da ake tayi daga jiya zuwa yau ana shagalin biki ta tuna
sanda taji wata nacewa"Brka da zuwa amarsu ta ango"zuciyarta ta buga lokaci daya tareda
mikewa tana dafe kirji tace afili"Kardai da gaske auren Safwan yayi..........?
*Antiha..*
commet
Vote
Share
Like
[10/14, 20:01] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..!*
*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_
*DEDICATED TO:My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*
*24*
"Sai kuma takoma ta zauna tana cewa"Haba yama za'ayi safwan yayi aure haba nasan waye
safwan mutum ne mai ra'ayin kanshi mace fiye da daya bata cikin tsarinsa"dariya tayi
tace"Haba ni nasani"Kamar wata mahaukaciya tajawo waya tana dannawa ammh abun mamaki
kowani dakika zuciyarta na bugawa takasa yarda da abunda kunnanta yajimata karfin hali kawai
take.
Sukuwa tawagar Amarya suna shiga kai tsaye gaban momma aka direta haj.Mama
tace"Samata Albarka Hadiza samata albarka da bakinki mai daraja"Momma tayi mirmishi tadafa
kan safeena dake durkushe gabanta cikin hijabi tace"ina miki barka da zuwa ya ke yata ubangiji
yasa albarka arayuwar aurenku da safwan"Tafada idanunta sunkawo kwallah anata amsawa da
Amin cikin tsausayawa haj.Mama tace"Bar kuka hadiza da izinin Allah safeena haskece
agaremu"Iyami ta amsa da "Insha Allahu maryamu sai ance gwara da akayi"Nan fa akayita
addu'an zaman lfy agaresu gaba kidaya sai ga haj.Mama tadauko turare ta hau fesema amarya
ana sakin guda guri ya dau sowa kowa na fadin Allah barna ke Hajiya mama.
Sun dan jima ashashen su momma kafin hajiya ta musu jagora zuwa shashen Amarya suna
tafe ana guda sakina na zaune taji hayaniyar na ta karuwa kuma kamar shashenta ake dosowa
bata gama mamaki ba suka shigo haj.Mama agaba tana kwarara sallama Amarya da tawagarta
suna baya Sakina dake rike da waya batasan sanda wayar ta subuce ba ta fadi kasan tayels din
dake falon ba,Da Sauri ta mike idanunta sun fito jikinta na rawa tana kallon jama'an dake
shigowa da guda bata gama mamaki ba taga hajiya mama ta nufi dayan bedroom din dake
kusa da nata tasa makulli zata bude Sakina bakinta na rawa tace"Am....Am....Nace ba..?
'Tafada murya na rawa hajiya ta dakata ta juyo tana kallonta kan tace"oh...Na manta iyami ku
fara isa da ita gun uwargida ku mika amana yadda ake na al'ada"Tafada harda dariya iyami
tace"hakane tako ja hannu safeena dake rike da kawarta Aisha sai gaban sakina dake tsaye
kamar mutum mutum aka dukar da ita inna husai ce tace"uwargida ga Amanar kanwarki nan ku
hade kai ku zauna lpy da juna shine kwanciyar hankalin mijinku"tafada tana kallon
Sakina,Sakina ta zura ma safeena dake durkushe gabanta ido tana so tababbatar da ba mafarki
take ba Hajiya mama tace"Ta karba Allah ya tayamu rikewa ku karasa da ita ciki kunsan
uwargidan akwai mulki"Tafada harda shewa jikin wasu yayi sanyi domin sudan fahimci cewa
sakina bata cikin hayyacinta,haka suka mike suka rankaya dakin safeena iyami tace"Kishiga da
kafar dama safeena kiyi