Showing 3001 words to 6000 words out of 52374 words

Chapter 2 - NA TAFKA KUSKURE COMPLET BY JANAFNANCY-1.pdf

kansa
daga halaka.


Kullum ta kalli cikin jikinta sai ta zageshi aranta,Haka tacigaba da renon cikin,cikin bakinciki da
danasani saboda mahaifinta yace wlh yaji lbrin wani abu yasamun ciki kashinta ya bushe,ga
bakincikin tadaina fita ko'ina tunda cikin ya tsufa,kullum cikin zuwa Hajiya take tana duba yarta
acewarta,babu mai kula da ita,gashi ta ranma mommah saboda sunganta bamai karamniya
bace.



Ranar da Sakina tafara naguda tun Safe Dr safwan yatafi asibiti,kuma da safe ya bartaa tana
barci,itakuwa Hajiya daman sunyi waya,da ita tafadamata batajin dadin jikinta shiyasa tun
safe,tasa dereba ya daukota suka kamo  Hanya koda ta iso ta iske sakina tafara jigata,shiyasa
da Hanzari tafito da ita zasu wuce asibiti,Itakuma momma tafito tazo taduba sakinar sai taci
karo dasu,cikin azama ta isa tana tambayan lafiya"harara kawai Hajiya kari ke zabgama
mommah takasa bata amsa,da sauri Momma tace Hajiya bari  in dauko mayafi insanar da
hajiya muje"Ko kallonta batayi ba koda ta isa,shashensu ta iske Hajiya mamq cikin daki take
fada mata"Tabe baki hajiya tayi kan tace"Allah raba lfy nikin gama barci nakeji in kinfita
kirufemin kofar"

daga haka tashige ta barta nan mommah takira Dr safwan take fadamai gasunan zuwa da
sakina zata Haihu,yashiga rudu yace su hanzarta,Koda tafito Hajiya na kokarin sanyata cikin
mota tataimakamata suka sanya suka nufi asibitin tanaji Hajiya kari takira yarta laila
tanafadamata abunda ke faruwa tana zagin Mommah din da danta wai sun bar Sakina agida
zata mutu sai da ita tazo Daga katsina,mommah kuwa sai dai kawai tayi mirmishi ta kauda kai.

Shine dalilin kawota asibitin da abunda yafaru.


WANNAN KENAN

Commet
And
Share
Vote.
[10/14, 20:01] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..!*

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty�_


*DEDICATED TO My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*



*04*


-----Tura kofar office din akayi tareda shigowa,Dr tahir ya kariso yana mai karewa Dr safwan
kallo wanda ke kwance ruwa nadiga ajikinsa duk ya jika kujera kwaya dayan datake cikin katob
office din,cikin azama Dr Tahir ya isa garesa yana Fadin"Dr Safana wht wrong with u"?

yafada yana mai dafasa,ajiyar zuciya Dr safwan ya sauke yana mai sauke gwaron numfashi
bayan tsawon lokacin daya dauka yana tuna iya tsawon lokacin daya dauka yana kunsan
bakincikin sakina da uwarta.


Ya dago idanunsa jajir kamar garwashi yana bin Dr Tahir da kallo,kallo daya Dr Tahir yama
safwan yaji mugun tsausayinsa ya tsirgamasa hannu yasanya yana jijjiga kafadarsa yana
fadin"Dr Safwan Dan Allah Dan Annabi kayi.....!"

"Nagaji Nagaji Tahir wlh Nagaji"ya katsesa cikin kunar rai da kosawa"koda yaushe kaida
momma kalmarku daya inyi hakuri shin bakuda wani abunda zaku iya gayamin sai kalmar
Hakuri eye"?

yafada yanawani zaremai ido idanunsa sun tara kwallah,cikin sanyin jiki Tahir ya karisa kusa
dashi yana riko hannunsa,yana fadin"Babu...Babu safwan babu wata kalma data dace dakai
bayan Hakuri,nasanka kacigabada da hakurin daka saba Allah nasane dakai"shuru Dr safwan
yamai yana kallonsa kamar yana karantan wani abu atareda shi,kara damke hannunsa yayi
yana jijjigawa alamar lallashi cikin kasala ya zare hannunsa ya isa ga wata durowa dake cikin

office din akafe ya bude sai ga wasu jeren kayan sun bayyana kai tsaye ya ciro su yakama
Hanyan toilet Dr Tahir yayi zuru yana kallonsa sai dayaga yana shirin shiga toilet don kana yace

"ta sauka lafiya an sami DR SALE SAFWAN SAFANA Da sauri ya juyo yana kallonsa kan
mirmishi ya subuce masa zaiyi mgana kenan Dr Tahir ya rigasa dacewa"Both momma and bby
are in good Health yanzu ma zan basu sallama su koma gida" gyada kai yayi kafin yace"thanks
so much Dr....."!
"Zan maidasu gida"Abunda tahir ya katsesa dacewa kenan kafin yafice mirmishi kawai Dr
safwan yayi kafin ya girgiza kai yafada toilet.

***

Dr Tahir ya tura kai Dakin da"a ka kawo sakina bayan angyarata,ita da bbyn nata,Momma ta
amsa sallaman tana Fadin"Attahiru sannu da kokari "

"Yauwa mommanmu Barkanmu fa"Yafada shima yana mirmishi karisawa yayi yana mai kara
kallon babyn wanda kamar Dr yayi kaki,momma tadago tana Fadin"kaga danku ko,kungirma
yanZu inashi baban nawa yazo yaga dansa mana"Tahir yace zaizo yanzu momma bari
nadubata in babu matsala inmai daku gida"
Momma tace"Alhamdulillah..."Gurin sakina ya karisa wacce ka zaune kan gado tana shan
ruwan shayi yayinda Hajiya kari ke gefenta tana faman buge bugen waya"cikin mirmishi
yace"Sannu madam munfa gode"Kallon raini ta watsama Tahir kan tace"Dole kace kungode kun
hadani da aiki kun gudu"Yasan da wanda take shiyasa yace mata"is ur duty ai madam kema
kinsani Haihuwa na matane ba maza ba kuma meye ribar auren soyayyah,A Haifi ya'yan
soyayyah"yakareshe Fada yana dariya kasa kasa tunda yafara mgana Hajiya kari dake waya
take zafgmai Harara yana kallonta ta kasan ido aransa yace'oho dai bazan dakuba dai" kasa
bashi amsa sakina tayi saboda tasan waye Tahir gurin maida magana kamar dan Hausa
bakwai.



..Ya rubuta mata maganin karin jini kafin yabata sallama saboda ta haihu lafy ko kari ba'a mata
tana haihuwa kaji kwakwazo tsit tamike ras kamar ba ita ba yana tsokananta yasan ya kunnota
shiyasa yaketa dariya,ita kuwa Hajiya kari jitake kamar ta shakeshi yacika iyayi ga tsinannan
tadi kamar wani aku,momma tana ta zunduma ma Tahir Albarka har suka fito,har mota yarakasu
momma dai ita ke rike da jikanta,har sunshiga mota Hajiya kari ta lego tace"Shi wanchan fa
koda dan shege aka Haifa mai ai yazo yaganshi balle dan Sunnah ne kuma shi
yadigasa"Tafada kanta tsaye Dr Tahir yagyara tsayuwa sanin matan bata da kunya ko kadan
yasa kai tsaye yace mata"Wlh aikine yarikesa ammh kema kinsa bakasha wahalar diga abu da
kanka ba,kuma ka banzarta dashi ba"Yafada yana kallonta ido cikin ido kasa bashi amsa tayi
har dereba yajasu suka bar asibitin yana kallon motan yana killer smile kafin yace'kunyan mara

kunya asara.


***


Hajiya mama dake zaune a farfajiyar flat dinsu tana tsinkan zogalanta datazo dashi daga safana
radio tane agefenta takure kara tana jin gidan radion freedom ansa wakar sangaya ta daddage,
tana bin abinta Mallam Ilaya mai bawa fulawa ruwane agidan,shine aikinsa shike zaune kusa da
Hajiya tana zubamai labarin zamanta a safana sukaji hon din motan Mallan Habu mai gadi yayi
gaggawan zuwa ya wangale get motar tasu tasawo kai zuwa parking space Momma ce tafara
fitowa rike da baby a hannunta kafin Hajiya da sakina wacce tafito tana wani hura hanci kamar
wata sakarya,Hajiya mama tai galala tana kallonsu Tunda Hajiya kari tafito taga Hajiya mama
tawani hade rai,momma cikin farinciki ta nufi Hajiya mama tana fadin"Hajiya kiyi barka kinyi
sabon maigida"Tsuramata ido Hajiya tayi tana kallonta sama da kasa kafin tace"Au....Wai
tasauka ne na"aza bazata iya Haihuwa da kanta ba?

tafada tana bin sakinar dawani kallon raini jikin Momma yayi sanyi kafin tayi mgana Hajiya
mama taci gaba da cewa" 'au ke kika koma mai renon kuma saboda sunmaidake wata sha
katafi ko"?

tafada ranta abace Momma tadago zatayi magana taga mallam iliyasu ya tsuramusu ido da
sauri tace"Mallam ilaya kunyi d'a fa "yana washe baki yazo ya amasheshi yana sa masa albarka
shima mallam Habu yakariso yana sa albarka.



Hajiya mama tamike tawuce tana fadin"bari naje naji ubanwa zai mata renon dan.."tana fada
tawuce fuu sashen sakina wacce tun fitowarsu suka shige ciki,koda ta isa basu afalo cikin
bedroom ta samesu sakina kwance share share Akan gado Hajiya kari nagefen suna mgana
Hajiya mama tafado dakin,sororo suke binta da kallon Hajiya kari tayi karfin halin cewa"Haba
hajiya da girmanki kina shigowa guri babu sallama"tafada tawani cin mgani Hajiya mama ta
kallesu a wulakance kan tace"Ana sallama inda akasan darajan sallamane ba inda ba'asan
darajarta ba"Cikin kunan rai sakina tace"gaskiya hajiya wlh kija girmanki,kan mene gaskia kija
girmanki tunkan na tunkudesa"takareshe fada da rashin kunya Hajiya mama tace"Kin ma uwarki
bani ba wlh da ita kikeyi don banace kinma ubanki ba don Kabiru yaron arziki ne, nikam nafi
karfinki fitsararriya kawai,kuma wlh kinemi mai miki reno hadizar baiwar uwarkice dazaki
barmata rikon jika tareni d'a kuma ta reni jika bazai yuyuba tunda kika iya bin miji kikai ciki to kin
ko san yadda ake reno"Tana gama fadar haka ta buga musu tsaki tafice.

Hajiya kari takalli sakinar tana fadin"wai wannan tsohuwar anya kanta daya"Sakina
tace"lafiyarta kalau Hajiya tsabar iskanci ne wlh,kuma shi safwan din ke dauremata gindi"Cikin
takaichi Hajiya kari tace"shegiyar tsohuwa mai shisshigin bala'i"Sakina ta karbe da cewa"ta
karshe wlh Hajiya tshohuwarnan tana shigan hanci wlh"Tafada tana bayyana takaichinta.



Hajiya tace"barta mugama da jikanta tukunnah ita karamar alhakice.


Koda Hajiya takoma ta iske momma na tsaye tana jiranta kallonta tayi tana rumgume da baby
kan tace"sai ki wuce ki kaimusu dan'su saura kizauna kina musu bauta tunda nasan ki zuciyarki
kamar ruwan sanyi take"tana fadar haka ta tattara shimfidanta ta shige ciki,koda momma takai
shi itace tamasa wanka tasama sakina nata,ko wankanma saboda lalacewa dakanta tashiga
hajiya na kallonta ko ajikinta momma taga abun mamaki ammh sanin halinsu yasa taja bakinta
ta tsuke.



*Anitha..*

.Commet
And
Share
Vote
[10/14, 20:01] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..!*

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty�_


*DEDICATED TO: My Mommah Hajja Hadiza Muhammed Ba"are*



*05*



-----Karfe goma da wani abu Safwan yabaro asibitin sa dake anguwan rimi kaduna daura da
iyali hospital kai tsaye anguwan sarki yana nufa cikin motarsa kirar benz baka,cikin slow yake

tafe har ya kariso get din gidan nasa hon ya Zuba da hanzari mallam habu ya wangalemasa get
yana masa barka da dawowa tareda masa barkan karuwan da'aka samu.



Kai tsaye part din momma yadosa cikin takun isa sanye cikin suit masu ruwan toka rigar
likitancinsa sabe a kafadarsa wayarsa ke rike ahannunsa daya kuma yana sanye cikin aljihu,da
sallama yashiga falon momma kadaice,afalon zaune kan darduma alamar sallah tagama tana
lazimi cikin fara'a ta amsa sallanma tana cigaba da laziminta takalminsa sawu ciki na fatar
damusa ya cire kafin ya kariso gabanta ya zauna yana fadin"Momma......"Tadago tana kallonsa
cikin Annuri da farinciki,kansa yadora kan cinyanta data tankwashe yagyara
kwanciyarsa,itakuma tasanya hannu tana shafa kansa lumshe ido yahau yi yanajin wani
farinciki na ratsashi cikin kasala da gajiya yace"momma...Yunwa nakeji"mirmishi tayi kan
tashafa addu"an shima yashafa yana fadin "Allah ya karba mommanmu"Allah ya maka albarka
babana yajagoranci lamarinka yasama zuru"arka albarka"Atare suka Amsa gabadayansu da
Amin harda hajiya mama data fito daga daki tana kallonsu.


Kichen tashiga tadaukomasa dambun zogalan datayimai saboda tasani masoyinshine,ruwa ta
hadomai dashi sai furan data damamai don shinema basa rabo da furar'gabansa ta ijeyi tana
fadin"kin cikasa da tadi....Maza ci abinci sufiyanu nasan kana jin yunwa"Mikewa yayi yana
fadin"kai i so much luvs u Hajiyata kinaji dani"yafada yanajan kulan gabansa fara'arsa takarune
dayaci karo da abunda ke ciki yadago cikin Annuri yana kallon momma da Hajiya dasuke
kallonsa cike da so da kauna yana fadin"thanks so much hajiyata Allah biyaki da
Aljannah"Amin...SufiyanuAllah yayi maka albarka"bata rai yayi yace"kinga hajiya wlh zamu bata
basunana sufiyanu ba am Safwan sale safana by name"


Hajiya tace"kai kasan wani Safawa, nibansanshi ba sufiyanu nasani Ato"Tafada harda da
jaddawa kara bata rai yayi yamata banza yayi bismillah yafara cin abincinsa,har ya kammala bai
sake mgana ba sai daya wanke hannunwansa kana yamike zai kwashe kwanukan momma tayi
saurin amsa tana fadin"A'a barshi babana,kaje kahuta kuma kaga masu jego da safe ma
hadu"Tafada tana amsa farantin ajiyar zuciyar ya sauke yana juyawa yace"Sai Allah ya kaimu
momma"ta amsa da"Allah ya tashemu lafy"Hajiya tamike tayi hanyar dakinta tana fadin"muda
ba'a son mukwana lafiyan sai mun tashi da izinin Allah ehe"tafada harda buga kafa dariya
takusa subucema momma da Safwan sukayi saurin shanyewa saboda sunsan Halin Hajiya
yanzunan takara harzuka.




Mirmishi kwance afuskar sa ya isa part dinsu koda ya shiga falon yadau shuru ga wata katuwar
plasma tana yi ita kadai,kashewa Yayi kafin ya nufa bedroom din daya zama mallakinsa kan

doruwar gadon ya ijeye wayoyinsa guda biyu kirar i phone8+ da lapcoat dinsa ya fada toile
wanka yayi kafin ya dauro alwala,daure da tawul ya fito a kugunsa daya kuma yana goge jikinsa
kan dressing mirror dake shake da kyan kwalliya kamar za'a bude shago ya isa kan yahau goga
jikinsa da man detol,turaren avon yahau fesawa jikinsa sai da ya feshe ko'ina kana ya zura
jallabiya ash colour yashimfida sallaya yadata sallah raka'a hudu yayi kafin yayi sallama yadade
yana kwararo kirari ga sarki Allah daya bashi wannan kyauta haihuwa tareda addu'an Allah
yakarasa masa juriya da hakurin akan sakina.



Kai tsaye bedroom din sakina ya isa ya tura da yar siririyar sallamarsa sakina na kishingide
akan gado wayace ahannunta tana latsawa yasani baiwuce chart takeyi da kawayenta ba
Hajiya kari na gefe ta baje sai kwasan barci take harda munshari dariya takusa kubcemai ya
waske,kai tsaye ya isa ga jaririn dake kan dan gadonsa yaduka yasa hannu yadaukesa yana
mai kare masa kallon cikin kauna,tsantsan kamar da yaron yake dashi yake kallo,hatta da
yatsunsu iri dayace,sonsa da kaunarsa mai zurfi,yakamashi lokaci daya,rumgumesa yayi cikin
shauki,da soyayyah ta har abada


Sakina dake kwance ta tsuramai ido tana kallon kyakyawan mijinta dogon dan safana tasani har
abada bazata daina,son mijinta ba, tana sonshi har gobe kuma tana kishinsa batasan sanda
tatashi ta isa kusa dashi inda yake tsaye tadafa kafadarsa ahankali ya waiwayo kwallah tataru a
idanunwansa da azama yahada ta da yaron ya rumgume yana fadin"Thank u Sakina....thanks
so much sakina"yafada yanajin kamar kwalla zata zubo mai.



Jikin sakina yadan yi sanyi shiyasa tayi huging dinsa back,na tsawon lokaci suna rumgume da
juna kafin su saki juna suna bin juna da kallo cikin ido itace tayi saurin sadda kanta kasa
saboda kar ya sata cikin wani yanayi.



Hannunta kawai yaja kiii.....Tana biye dashi har bedroom dinshi kana ya saketa ya haura gadon
ya ijiye yaron yana kallon sakina cikin ido kan yace"Kinga kyautar da Allah yamana ko"?


kallonsa kawai tayi batace komai ba,yacigada da cewa"Sai wanda Allah yaso da rabon yake
basa ammh kinaso kimana wasa da damar da Allah ya bamu"yakareshe fada yana sa idonsa
anata,Hamma tayi kan tahaye gadon blanket taja tarufe jikinta tana fadin"Kabarni na huta Dr
haihuwa fa nayi ko barci bansamu ba"tafada tana runtse ido alaman bata son damu.

Girgiza kai kawai yayi yacigada da kallon dansa har barci ya daukesa yana kan kirjinsa,koda
yatashi daddare yana tsala kuka yatashi sakina tabashi nono tsaki ta buga tana fadin"Don Allah
kabarni nayi barci mana"tana gama fadar haka takara jan bargo dama tunda yazo duniya bata
bashi nono ba,sai ruwa da aka bashi,shi yayi ta girgizasa asaman kafada har yayi barci saman
kujerar dake bedroom din yakwanta yadorasa bisa cikinsa hannunsa zagaye dashi har gari ya
waye.





Gari na waye momma ta iso part din nasu,ta iske basu tashi ba kichen tashiga tasa ruwa a kittle
tazo tazauna tana jiran tashinsu,Dr Safwan ya fito sabe da yaron yana lallashinsa yatashi sai
yaga momma da sauri takarisa ta amsheshi tana fadin"Yaya kuma,kuka yakeyi ne"?Sakarmata
shi yayi yana fadin"Wlh momma tun jiya yake rigima"momma tace"to yasha mama kuwa"tsuru
yayi mata kan yace"indai ba'a asibiti ta bashi ba ba to bata bashi ba momma"ajiyar zuciya ta
sauke kan tasabaashi tana aikin jijjiga har yayi shuru.





Yana zaune momma tamasa wanka tashiryasa cikin kayan sanyin masu kyau yafito ras dashi
momma tamika ma safwan tana cewa"nono yake bukata ka roketa ta duba wannan yaron karta
dau alhakinsa"cikin mutuwar jiki da kunan zuciya ya amsheshi ya rumgumesa yanajin
tsausayinsu har cikin ransa itama momma shi take kallo cikin tsausaya aranta tana fadin"insha
allahu HASKE yakusa shigowa rayuwarka Safwan".



Huduba yayi mai kan ya mikama momma yana fadin"Sunan dady nasa masa momma"yafada
da raunin murya washe baki tayi tana fadin"kai masha allahu da zuwan sabon megida Allah
yaraya ka SALISU"..



WHAT....""

Sakina ta furta da karfi wacce fitowarta kenan daga bedroom cikin rigar barci kai a hargitse,.

Taci gaba da cewa cikin karaji"me kace sunan dan sali wa"? Tafada da renin wayau galala

momma tayi tana kallonta yayinda mamaki da al'ajabi ya daskarar da Dr safwan,ashe iskancin
Sakina ya wuce inda yake tsammani.




Rike kugu tayi kan ta kariso falon tana cewa"tabdijam da sake an ba mai kaza kai,dan kunga
nayi banza bawai ina nufin banason abunda na haifa bane balle awani roro sunan yan da na
tsoffi a sama y.......SAKINA....!!! Safwan yakatseta da tsawa wanda ya firgitata har momma dake
rike da jinjiri balle shi yaron daya yanka ihu tsawar ita ta data Hajiya kari, wacce take sharar
barci cikin tashin hankali ta fito falo, dai dai lokacin da Safwan yace cikin bacin rai"na rantse har
ga Allah inkika karisa abunda zaki fada sakina sai na baki mamaki inkin musa kuma"yafada
yana kadamata hannu


Tadan tsorata ammh tsabar rashin kunya yasa tace"me zaka iya eye "? tafada tanamasa wani
kalon sama da kasa juyawa yayi zai koma daki tabishi tana fadin" Wlh ba wanda ya isa yasama
d'ana wani rubabban suna wai sal...."jika ke tas!tas! ya wanketa da mari sai da ta kifa yace cikin
bacin rai "wlh tallahi babu wanda ya isa ya sauyama yarona suna nine ubansa kuma nace
sunan dana SALISU inga uban da isa yachanza masa suna shashasha kawai wacce batason
darajan mijinta ba"yana fadar haka ya shige daki harda bango kofa jikake bam!!!!


Kasa Sakina ta zube tana kuka tana fadin"wlh Allah ya isa,kuma zakasan waka mara sai kayi
nadama kuma suna baka isa ba kasama dana wannan sunan ba"tafada tana gunjin
kuka,momma tadake rike da jariri ta isa kusa da Sakina zata rikota "tayi saurin dagowa tana
ballamata Harara kafin ta mike ta shige daki da gudu tana cigaba da kuka,Hajiya kari tabi
bayanta.




...Momma ta koma ta zauna asanyaye Hajiya mama dake bakin kofa tace tana tafa
hannuwa"yayi daidai....abun yayimin dadai wlh dahaka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login