Showing 39001 words to 42000 words out of 52374 words

Chapter 14 - NA TAFKA KUSKURE COMPLET BY JANAFNANCY-1.pdf

ne bayanshi"Cikin fusata yace"au sai yanzu kikasan danki ne sai
yanzu kikasan kina da wani dan' kinmanta sanda kika banzarta dashi,kin manta sanda kika
hanasa yaji duminko lokacin dayake bukatarki kika ki shayar dashi kikaki rainansa kika ki basa
kulawa kika banzarta dashi kika wofantar dashi shine kike kiran kanki a matsayin uwa tirr da mai
hallaya irin taki baki dace da akiraki da suna UWA BA"


Hawaye ya gangaroma Sakina ta nuna kanta tana fadin"Nikake ma Tirr Safwan'ko kallonta baiyi
ba yawuce ya bude daki ya dauko adil yaci kuka ya koshi ya mikama Safeena yace " _KO
BAYAN RAINA KECE ZAI CIGABA DA KALLO A MTSAYIN MAHAIFIYARSA....KEKUMA KI
KALLESA A MTSAYIN DA' NA HAR ABADA_ Safeena ta amsheshi tana fadin"Insha Allahu zan
kula dashi kamar yadda duk wata uwa zata kula da danta"mirmishi yayi mata kan yace"Nagode
hanyar dakinsa yayi aikuwa Sakina tayi kukan kura ta isa kusa da Safeena ta bangajeta ta fadi
ita da Adil kan ta daukeshi tana fadin"kunyi kadan na bar miki dana in nabar miki mijina wlh
bazan bar miki dana ba.



Safeena dake dafe da ciki da kurma ihu Ai da gudu Dr Safwan ya isa gareta yana rikota tana
dafe da ciki tana kuka yana duba kasan kafarta saiga jini cikin tashin hankali da karaji yace"
*SAKINA.....!WLH TALLAHI IN KIKAMIN ASARAN KWAN HAIHUWA SAI NA MAKA KI A
KOTU* tsam ta tsaya tana kallonsa kan tace"Shege kafasa Safwan dama dan adam da butulci

akasansa asibitin dakake takama dashi inace ba ubana yataimaka maka ka bude sa ba to indai
har baka sake ni ba BAKA CIKA DAN HADIZA DA SALE BA"cikin wani bakin cikin Safwan ya
saki safeena ya isa kusa da Sakina yana kallonta idanunsa sun kawo ruwa yace"Tabbas da
taimakon mahaifinki nake wannan matsayin ai banzata kina kallona da abun ba....To ammh yau
ya kare ni _*NI DR SAFWAN SALE SAFANA ZAN NUNA MIKI NI DAN HALAS NE....KIJE NA
SAKEKI SAKI DAYA!NA SAKEKI SAKI BIYU!NA S........*_ A'a kada ka karisa kada ka karisa
Safiyanu"



Hajiya mama tafadi haka da karfi ita da momma ce suka shigo tun bayan ihun da Safeena ta
zabga hajiya mama tace"Kabarta haka Safiyanu ko ahaka ka barta kanuna mata kai dan halas
ne"Juyawa kawai yayi ya isa inda safeena ke kwance momma na rike da ita ya ciccibeta yana
fadi cikin raunin murya'momma muje asibiti inaga Safeena bari zatayi" da sauri momma ta mike
tana salati ta rufamasa baya har yakai kofa yace"Hajiya ki karbi Adil don har abada ba danta
bane"Yanagama fadar haka ya fice dauke da Safeena.




Sakina dake tsaye kamar mutum Mutum hajiya mama ta fizge Adil tana cewa"Naso ki gane
kuskurenki tunkan saki ya shiga aurenku ammh kash...Kin kasa ganewa ammh ina fatan
wannan karon ki gane KIN TAFKA KUSKURE

Daga haka ta fice dauke da Adil....Ai Sakina zubewa tayi cikin firgici da tashin hankali tana
fadin"na shiga uku wlh Safwan da wasa nake maka wayace ka sakeni wayyo ni...Sakina na
mutu na lalace"








*Hmmmm....Ai kinyi kuskure ba'a wasa da abunda bana wasa ba Allah ya kyauta*



Commet
Share
Vote
Like

Share

*Anitha...*
[10/14, 20:02] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE.."!*

*Wattpad:Janafnamcy13*
_Mallakar:Janafty_�




*DEDICATED TO:My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*




*32*





"Momma ta shiga motar direct suka wuce S&S SAFANA SPECIALIST HOSPITAL Ma'ana
asibitinsa suna zuwa suka rufi kanta dashi da Dr. Tahir don bai yarda sauran sun tabamai mata
ba Alhamdulillah sun gano ciki dan sati hudu da kwana biyu wata daya kenan,buguwar datayine
jini ya yanke mata anyi saurin xuwa asibiti dat why cikin bai zubeba sun yi nasarar tsaida jinin
suka mata allurai suka kaita dakin hutu.



Sakina tadade tana kuka nadama mai karfi ta shigeta lokaci daya domin tasan duk takamarta
da Safwan take gashii yanzu ya saketa ina zatasa kanta yanzu...yan aikinta ta kira suka hada
mata kayanta kaf bazata iya tuka mota ba saboda halin datake ciki direba tasa yakaita tasha ta
hau mota sukuma su latifa taba kowannesu na mota tace su koma gida tareda albashi.



Sai yammah ta isa katsina dan adaidaita ya sauketa tabashi kudinsa mai gadi ta kwalama kira
yazo ya jidan mata akwatuna yana kaiwa cikin gida Hajiya kari dake zaune afalo tana kallo taga
ana shigowa da akwatuna saurin mikewa tayi tana fadin"Kai daga ina kuma..?

"Bai bata amsa ba Sakina ta sawo kai Falon sororo Hajiya kari tayi tana binta da kallo da gudu

Sakina ta isa ta fada jinkinta tana Fadin"Hajiya ya Sakeni wlh ya sakeni"Cikin karaji hajiya
tace"Yame....."Sakina tace"ya sakeni hajiya safwan ya sakeni"


Ya sakeki kuma shine kika zomin gida"Muryan kwamishina ta katsesu wanda ke kofar falon
yana takowa cikin bacin rai sakina da Hajiya suka kalli juna kafin hajiya tace"Haba Alhaji tanada
inda yafi nan ne"Kai tsaye yace"Wannan ya rage nata ammah na rantse bazanyi kaffara ba duk
randa sakina ta kaso aurenta bawani dalili bazata zaunamin agida ba"Sakina ta sulale akasa
tana Fadin"na shiga uku dady in ka koreni ina zani"Ya juyo ransa abace yace'"inda kika zaba
sakina...Duk hakurin yaron nan sai da kika kuresa ko..?"girgiza kai tayi tace"Abbah hajiya da
Anty lailane sukaje gidana suka na amshi Adil ahannu Safeena wanda Safwan ya bata shi tana
rikonsa"Hajya kari tace"Wata Hajiyar don ubanki"Tafada tana ballamata harara.


Sakina tace"Wlh Daddy susaka sani na aikata abunda har Safwan yasakeni"mirmishin takaichi
yayi yana fadin"Very gud naji dadin haka kinga yanzu sai itama tabi ki....Sai ku nemi inda
zaku"Hajiya kari tace cikin tashin hankali"In bita ina Alhaji...?Ya fara taka step kan ya waigo
yace"Ki bita ku tafi koma ina ne Nima na sakeki Saki daya"Hajiya kari tasa ihu tana fadin"na
shiga uku ni karima Alhaji ka sakeni fa kace"Yace idanunsa cike da kwallah"Eh....Haka nace ba
abunda zance miki sai Allah ya isa tsakani na dake karima aurena dake babu abunda na karu
dashi sai tabarbarewan rayuwa kije duniya takoya miki hankali keda yarki.


Yana gama fadar haka ya haye sama yana share kwallan daya ziraromasa hannu akai Hajiya
kari ta dora akai tana kwarma uhu tana fadin"Shikenan Sakina kinzo nima kin kashemin
aure"Sakina dake gefe tana kuka tace"ni dakuka kashemin nawa fa hajiya"Hambari ta kai mata
tana fadin "Don ubanki waya kashe miki aure kika dai kashema kanki...Ai sai ki tashi mu san
nayi"




akwati daya Hajiya kari ta dauka sai Atm dinta suka rankaya suka fice cike da takaichi megadi
na musu mgana sukayi banza dashi suna fita kwamishina ya kira Anty salma ya labarta mata
komai kuma yace ko sun kira ta zasu zo gidanta tace basunan sunyi tafiya Salma saboda
bakinciki saida tayi kwallah ta amsa to ammh aranta tana so tasanya mizanin wata irin uwa
Allah ya basu.




Sai da suka fita suka fara tunanin inda zasu yanke hukunci kiran Laila sukayi Sakina ta kirata
take fadamata Abunda yafaru cikin razana laila tace"mun shiga uku Daddy yasaki Hajiya"Sakina

tace"eh...Nima fa ai saki na Safwan yayi har Saki biyu"Anty laila tace"garin yaya sakina"Sakina
tace cikin fusata"garin bin shawarar dakuka bani....Yanzu Daddy yace bazamu zauna mai agida
ba to gamunan zuwa"Zuwa ina......Ta fada cikin firgici cikin mamaki Sakina tace"gidanki
mana"Da sauri Laila tace"Kut...Wlh badani ba nima kuzo ku kashemin nawa aure tab...Ku tafi
kankia gidansu hajiya zuwa goben ina tafe"daga haka ta kashe wayar sororo Sakina tayi da
waya ahannunta tana kallon Hajiya kari dayake wayar a handfree ne taji komai.


laila ta rike baki tace"kutumar uba in barku kuzomin gida yadda mujaheed yake kume dani ai sai
yace mu rankaya dukkanmu....Tab....Su karata chan nima ina lallaba rayuwatane


Sakina ta fashe da kuka tace"wlh bazan iya zama a kankia ba hajiya"Cikin bacin rai Hajiya kari
tace"to don ubanki sai dai ki nemi gun zuwa domim banda nan bbu inda zamu a
amshemu"Sakina batayi mgana ba ta kira Anty salma sai da tabata 2miss cll kana ta dauka
cikin kuka take fada mata abunda ke Faruwa mirmishi mai kama da kuka salma tayi kan
tace"Ayy bamu kasar mun tafi kasar turkey baban shahid yaje wani aiki ne"daga haka ta yanke
wayar.




Basu da zabi illar zuwa tasha suka hau motar kankia sakina kuka taketa yi tana fadi su suka
kashe mata aure...Itakuma hajiya tana fadin ita ta kashe mata aure abu har yazaman musu fada
amota sai kallonsu ake ana tirr dasu.




Sai bayan issha"i suka isa kanki koda suka isa gidansu Hajiya kari wanda daman iyayanta sun
rasu yayyintane agidan wanda ta gujesu sai tayi shekara bata leko ba sunyi mamakin ganinta
matuka anan take fada musu karya da gaskiya basu yarda ba adaren sukama kwamishina
waya yafada musu komai game da hallayar Karima suna ko jin haka suka ce babu ruwansu da
ita sai da ta shiga wani yanayi ne zata nemesu to sukan babu ruwansu da ita gidane tazo ta
zauna ga dakin mamansu chan data rasu su share kafa su zauna tunda zaman suka zaba.




Haka suka ja jiki asanyaye suka wuce koda suka shiga dakin sai da suka kusa kuka saboda
yadda dakin ya lalace ga ruma tako'ina rufin dakin na azarane duk ya kusa ruftowa ga simintin
duk ya banbare beraye na Safara ga gefe daya wasu buhuhunan kaikayi ne bbu ko katifa
sakina kan akwatin ta ta haye tana kuka ita kuwa hajiya gyalenta ta shimfida ta zauna ga yunwa

na addabansu rabonsu da Abinci tun na safe.




haka suka kwana Sakina kuka ta kwana yi hajiya ko da takaichi ya cika ta dunga durama
sakinar zagi tana cewa"ki rufema mutane baki duk wayaja bake ba inda kinyi hakuri agidanki
har yaushe za'a sako ki balle har kizo nima kashemin aure"Sakina tace cikin kuka"duk baku
kuka kashemin auren ba wlh hajiya keda Anty laila ba abunda zence muku sai Allah ya isa"

Hajiya kari tace"Nima Allah ya isa tsakani da ke inda daya sakeki kin nufi wani wurin har yaushe
Alhaji zai sakeni...Duk iya abunda nakemai baitama furta sake agareni sai akanki ni yakamata
na miki Allah ya isa sakina"


_Hmmmm haka Rayuwa ta gada daman_


Haka suka kwana wanda Sakina dakyar taga Safe saboda cinnaku da beraye sun hanata
sak,ita hajiya haka abun yake agurinta matan gidan kuwa ba wacce ta kallesu saboda daman
tuni suka tsaneta domin ko gidanta kaje tadinga kyamatarka kenan.




Sakina gari na waye tafice mota ta hau tatafi banki tayi ciro kudi dubu dari tatafi kasuwa tayo
musu siyayyah don tace baza ta iya rayuwa ahaka ba, komai ta siyo su kayan tea indomie
macrooni complex kai katifa da fridge saboda bazata iya shan ruwa bbu sanyi ba ta siyo fanka
komai da komai mota ta sauketa har kofar gida tasa aka shiga dashi matasan gidan tasa suka
kwashe tarkachan daki suka gyara musu kana suka shiga mata da kayan ta biyasu,sai dai
Hajiya kari ta ganta da kaya kawai aranta taji dadi domin daman ko ita da'aka haifa anan bazata
iya irin rayuwarsu ba.

Commet
And
Share
Vote

*Shakira..*
[10/14, 20:02] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..*!

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_�


*DEDICATED TO:My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*



*33*


"Babu wanda yace musu kala kowa yayi banza dasu to da fari dai sunfara gudanar da
rayuwar tasu cikin aminci da jin dadi kadan duk da atakure suke ko wanka sakina zatayi batayi
sai dare yayi tayi awaje kan wai bazata iya shiga bayi ba gani take kamar kasa zai rufta da ita
hajiya kari kuwa haka dai take lallabawa.
*****



Safeena kuwa sai da ta kwana uku a asibiti kafin a sallamota ta dawo gida wanda momma da
Hajiya mama da shikanshi Safwan suka maida hankali gurin bata kulawa Ummi tazo dubata
kwananta biyu takoma tareda sha tara na arziki daga sirikinta masha Allah.


Kwamishina da kanshi ya kira Dr yana bashi hakuri inda yake fadamai hukunci daya yanke
hakika Dr Safwan ya tsausayama Dady domin shi shekara uku yayi da bakin cikin Sakina
shikuwa Daddy shekaru tun ana kurciya bbu jin dadi da kwanciyar hankali hakika shi yafi
kamata atsausayamawa.

Koda Safwan ya fadama su momma sun Nuna alhininsu matuka Hajiya mama tayi ajiyar zuciya
tace"Hakika kabiru yayi hakuri matuka da karima walh da wanine da bazata kawo warhaka
ba....Har ga Allah ba niyyata bakenan karabu da sakina ba A'a kawai so nake tagane
kuskurenta to ammh ko yanzu Sakina ta gyara halinta wlh bani da ja zaka dawo da ita"gyada
kai momma tayi tace"Tabdijam sakina ce zata iya zaman kauye"Safwan yace"Ai momma
awannan lokacin ne zata gane TA TAFKA KUSKURE.

Hajiya kari tace"Kwarai ma kuwa fatan Allah yasa wannan yazama sanadiyar shiryuwansu suka
Amsa da Amin.



Allah Sarki Safeena dataji sakin da Safwan yama Sakina sai da tayi kuka taita rokonsa kan
yadawo da ita zata bata danta domin tafi ta gaskiya dantane data haifesa da cikinta.Dr yaso ya
tsorata ta sai ya sha mur yace"ok kema bazaki rikesa ba kenan gud...Zan kawo wacce zata
rikesa aie"To yana fadar haka tayi saurin basa hakura daganan bata karamai mganar ba ammh
abun na damunta matuka.




******


KANKIA😂



Tabbas abunda hausawa kan ce komai yayi farko zai yi karshe to hakane tafaru dasu Sakina
domin yau da gobe bata bar komai kwanchi tashi sai da suka karar da komai nasu kaf kudaden
dake account dinsu suka gama dasu na kokarin su na inganta rayuwarsu shagunan Sakina tuni
masu shi suka amshe domin bbu kaya kasuwanci tuni ya rushe,hatta da su Fridge din da suka
siya sun saida kayan sawansu da daidai da daidai suke zara wai duk dai karsu bar rayuwar jin
dadi.



To daman komai ubangiji yaso ma bawa sai ya amsheshi gashi ayau sun wayi gari basu da
komai abincin dazasu ci ma garararsu yakeyi sai da Hajiya kari taita rokon yayyinta kan suma
matansu mgana su dinga basu abinci suma din sai da suka ce sai da sudinga fitowa suna

tayasu aiki don wallahi bazasu cida kardawa ba dole tasa suke fitowa domin samun abunda
zasusa abakinsu Yau sai gashi Sakina ta rame tayi baki domin bbu mayukan da"aka saba
shafawa,kayanta duk sun kode sunyi yage saboda wahala haka zaki ga Sakina ta tike tana
buga bowol din ruwa ta cika bokitai takai gida ayi tuwa a yarfa musu akwano wanda ko Sakinar
tacinye bazata koshi ba agari ko lbrinsu ya bazu duk inda suka bi ana tirr dasu Rayuwa tajuya
musu baya domin hajiya kari har gidansu Daddy taje tasamu goggonsa taita rokonta kan tasa
baki ya maidata ammh sai ta kalleta tace"Ada dai munmai dole ya aureki ya zauna dake ammh
yanzu dayasan halayyanki karima bamu da ikon sashi yakara zama da ke sai dai inhar shi yake
Ra'ayi"gwiwa a sacce tadawo da tarin nadama duk ta rame tazama tsohuwar karfi da yaji.Har
satan hanya tayi taje katsina ammh sai megadi yake fadamata Alhaji yafi wata biyu bai nan
yana london yaje hutun karshen shekara tayi tayi yabarta ta shiga ko kaya tadauka ammh yayi
kemene yace"yallabai yace kada ya barta ta shiga"To yazatayi bata da ko sisi tana kuka take
rokion maigadi yataimaka mata da na mota kallonta yake aransa yana Fadin"Kowa yaki sharan
massallachi yayi na kasuwa yau shi Hajiya kema kuka tana rokon shi kudi,dubu daya ya bata ta
amsa tana godiya kamar ta tsugunnah mai saida tatafi ya girgiza kai yace"wlh Hajiya kin tafka
kuskure dakika bari kika rabu da gwarzo mai hakuri da nagarta irin yallabai....Allah yasa kin
tuba harga Allah.


Sai da tadawo take fadama Sakina ga inda taje da abunda yafaru"Sakina dake zaune akasa
bbu ko leda riga dabam zani daban tana ta shoshe soshe tace"Hajiya kinga yadda Allah
yamaidamu ko kowa ya gujemu saboda hallayanmu hatta da Anty laila yanzu bama asamunta
awaya ita kuwa Anty Salma nasani daddy ne yace karta nememu saboda abunda muka aikata
akan son zuciyarmu"Takareshe tana fashewa da kuka hajiya kari tatashi ta isa kusa da ita
tadafata tace cikin karyayyan murya tace"Hakika Sakina duk abunda ya Sameki nine sila domin
amtsayina na mahaifiyarki banta nuna miki abunda kikayi ba daidai bane saima kara miki
gwarin gwiwa danikeyi akan abunda kikeyi tabbas Allah ya nuna mana kuskurenmu tun ba aje
ko'ina ba"


Sakina takara fashewa da kuka suka rumgume juna Hajiya kari tace cikin kuka"mun Tafka
kuskure sakina...Sai dai munada yadda zamuyi mu gyara kuskurenmu kafin lokaci ya
kuremana.


sakina tadago idanunta jawur tace"taya Hajiya taya zamu gyara alhalin bamu da wanda ke
goyan bayanmu'Hajiya kari tace"Safwan....Kije kibawa Safwan hakuri ya hakura ya maidake
Dakinki indai kika koma dakinki ni ko ban komaba nasan Allah zai dubeni ya yafemin abunda
na aikata in cigaba da zaman anan harta Allah ta kasance"rumgumeta Sakina tayi cikin kuka
tace"A'a Hajiya wlh bazan iya kallon Safwan da ahalinsa ince su yafemin ba saboda ban kyauta
musu wlh bantaba kyautata musu ba koda na rana daya ne.."Hajiya ta runtse ido hawaye na
kwaranyomata ranta namata daci Nadama mai tsanani ya baibayeta.

_Allah Sarki ita daman Duniya haka ta gada inkaine yau bakai bakai bane gobe_





*After Three month*





Wata mata nagani chaculate colour Ce sanye cikin wata doguwar rigar abaya tayi rolling din
bakin veil din akanta har zuwa wuyanta kafanta sanye da cover baki hannunta rike da jakar
gucci baka sannan dayan hannunta rike da wasu littafai kallo daya zakamata kazata yar kasar
maroco ne saboda yanayinta.
Tsaye take abakin get din KADUNA STATE UNIVERSITY Wato KASU sai gawata rantsantsiyar
range cover baka tazo tafaka a gabanta aka bude motar akafito wow....Abunda na furta masu
karatu kunsan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login