Showing 6001 words to 9000 words out of 52374 words
Chapter 3 - NA TAFKA KUSKURE COMPLET BY JANAFNANCY-1.pdf
yakema shegiya da tashiga
taitayinta"momma tayi shuru tana kallon Hajiya dake ta fada tana habaice habaice amsan dan
tayi tana jijjigasa tana fadin"wai shin anbashi nono kuwa,momma tace"ina fa taki
bashi...."kutumar ubancan yau ga yar iska"ba'a bada nono uwarta ta bata"tafada ahasale kan ta
mika mata dan tana ficewa da sauri.
Kai tsaye dakinta takoma ta dauko wayarta kirar Nokia da Safwan ya siyamata to dayake
badamuwa tayi da wayan ba shiyasa bata cika amfani da ita ba,kai tsaye gun Habu mai gadi ta
nufa tana fadin"mai sunan megida dan Allah duba ko zaka ga ansa kabiru,ya amsa yana duba
mata yace"eh Hajiya gashi...Tace yauwa bugamai "tafada tana bubbuga kafa kamar wacce
zatayi dambe
Bugu uku kwamishina ya dauka don yana da Nombar Hajiya maman da sallama yadauka yana
gaisheta ta katsesa cikin masifa"kabiru kazo kaci ma yar iskan yarka da tsohuwar kilakin
matarka mutumci"cikin al'ajabi kwashima ya mike yace cikin rawar murya"wani....Wani abun ne
yafaru Haji....?"kwarai zata kashe min jika kuma ta kashe dan data haifa dan taki bashi
nono"tafada kit wayar ta mutu ba chaji Hajiya mama tayi kayfci tace"kazo ayi ta kare ko ta gyara
ko tabika kutafi tare ina dalili"mallam Habu dake kallonta yace"Hajiya lafiya mai yafaru"?Harara
ta zabgamai kan tace"idon matambayi "Tafada tana wani harararsa afusace ta wuce takoma
part din sakina.
*Shakira...*
Commet
And
Share
[10/14, 20:01] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE...!*
*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_
*DEDICATED TO:My Momma Hajja Hadiza Muhammed Ba"are*
*06*
-----Aikuwa hankalin kwamishina ya tashi dama meeting suke dashi da gwamnah,suna
kammallawa,direba ya wuce dashi,kaduna koda ya isa sashen Hajiya mama yafara isa,aikuwa
ta lissafamai kaf abunda sakina tayi,Hajiya mama takareshe da cewa"kaduba kabiru duk
tsufana bai isa sakina ta ragamin ba,to wlh tsaf take zageni balle Hadiza ai marainiyarta ce.
Hohoho Sakina taga ta kanta don marika biyu kwamishina ya saukemata sai da momma taita
bashi hakuri,yayi mata gargadi da kakkausan murya kan tashiga taitayinta inba haka ba wlh
tallahi sai yasa da kanshi safwan ya sauwakemata tadawo gidan,kuma taci ubanta,yasa ta dole
taba yaron nono agabanshi yakuma ce inta isa ta sauyama yaron suna,Hajiya kari ba yadda
zaiyi da ita illar sata agaba suka wuce katsina,har ya tafi basu hadu da Safwan ba domin kiran
gaggawa yasamesa daga asibiti.
Washegari sai ga,laila tazo daga lagos ai kwamishina yace tayi maza takoma don ya haramta
mata zuwa gidan sakina tunda yagane itace shedan din itada uwarsu,dole laila takoma da tarin
takaichinta,salma ce kawai da ummi suka je sunnan Salisu wanda akama alkunya da Adil,sai
kawayenta da yan uwa da abokan arziki,Sakina tashaka matuka shiyasa tayi alkwarin gasama
Safwan aya Ahannunsa,badai haihuwa ba to ta haifa masa sai ya rena kayansa kuma haihuwa
wlh har abadaí ½í¸³í ½í¸³domin tuni tasa an juyamata mahaifa ita da haihuwa sai sadda tayi
ra"ayi,anya Sakina baki *TAFKA DA KUSKURE BA*?
Kwamishina da kanshi ya dauko mai zama da Sakina goggo Ramatu daga kankia tazo tana
kula da Sakina da Adil hakika goggo Ramatu taga duniya agidan sakina rashin arziki kiri kiri
yimata takeyi da rashin kunya duk dan tana kokarin gyarata shiyasa datagama abunda zatayi
take komawa shashin Hajiya mama su barke da Hira dama zamuce ta tarar da mujemu.
Su sakina nayin arba'in goggo Ramatu,takoma tareda shatara na arzikin da Dr Safwan ya
hadamata hakika tayi kewar mutanen kirki hajiya mama da momma tatabbatar da Sakina tana
kokarin Tafka kuskure matukar tabari suka sallamata.
kamar jira take tayi arba'in tacigaba daga inda ta tsaya washegarin ranar tatafi kano wai anyo
mata odar kaya,haka take kullum cikin yawo,kuma Adil agida take barinshi sai dai kaganshi
bayan Hajiya mama ko bayan Momma suna aikin jijjiga in dare yayi Safwan ya amshesu wlh har
kwallah sukemai aboye saboda tsausayin Dr safwan bai huta asibiti ba kuma agida ba
Hutu,shidai kawai yabarma Allah komai ya yarda cewa wannan itace KADDARARSA.
**************************
*Zamfara*
Zurmi...
 Tafe suke su biyu sanye da dogayen hijabai marun colour har kasa da nikabi kafafunsu sanye
cikin safa baka ganin komai sai tafin hannunsu,littafaine a hannunsu sun rumgume alamar daga
mkrantan islamia suke.
Aisha ce takauda shirun dacewa'Nikuwa *SAFEENA* ina so in tambayeki"?
wacce aka kira da Safina tajuyo tana kallonta ta cikin nikabin ta tace cikin siririyar
muryanta"Nasani daman zaki tambayeni....Nasan mganan bata wuce ta mallam yahuza ko"?
Aisha tace"oh ashe ma kinsani....Ni wai meke tsakaninku anya ba sonki yake yi ba"?
Dariya Safeena tayi mai ban sha'awa kan tace"Nima ban sani ba Aisha....Kawai dai inajin wani
iri in ina tare dashi"
Duka Aisha tadakamata kan tace"Yar iska ashe dama kina sonsa"
mirmishi kawai tayi batayi mgana ba har suka iso kofar gidan su Safina,Safinar ce taja ta tsaya
tana kara rumgume littafanta tace"To sai gobe Aisha ki gaida mama"
"ALLAH yakaimu nima kigaidamin da Ummi yammah tayi shiyasa bazan shigo ba.."
Mikewa Aisha tayi,ita kuma Safina tashiga wani dan madaidaichin gidan bulo,da sallama
tashiga,Ummi dake kichen ta fito tana amsawa,
Safina tace "Sannu da aiki Ummi" amsawa tayi cikin farinciki yauwa"Safinatu baiwar Allah
andawo" tace"eh Ummi ina Abbah,tace"Yanzu ya fita zuwa massallachi shida Usman.
Shiga daki tayi ta kware hijabin jikinta da Safa da nikabin,sanye take da riga sikat na atamfa
sunmata das da ita fitowa tayi tazari buta tashiga ta kama ruwa kan tafito tayi al"wala tashiga ta
gabatar da sallar mangariba tadade tana azkar kafin ta mike ta fice ta iske Ummi na kwashe
tuwo ta taimakamata suka kwashe suna Hira.
Ta idar da isha'i kenan taji sallaman Abbanta da shi da Usman kaninta,da sauri ta fito sanye da
hijabi tana fadin"Sannu dadawowa ABBAH"
Yadago cikin annuri yace"Yauwa HAFIZA SAFINA brkan ki da gida"
Mirmishi tayi kan ta sunkuyar da kanta tana dariya saboda haka Abbanta ke kiranta saboda
zamowarta Hafiza abangaren Alqur'ani mai girma.
da sauri takoma daki ta dauko tabarma ta shimfidamai tare da kawomai abincinsa da roban
wanke hannu lokaci Daya tana zauna a gefen tana fadin"Abbah yau aka fada mana amkranta
zamu jigawa gasan alqur"ani kuma dani aciki"
"Masha Allahu....Allah Yasa albarka Allah ya albarkaci Rayuwarki" ta amsa da Amin ta na mai
jin farinciki bismillah yayi kafin yafaraci shida usman ya kalleta yace"Sako hannunki Safina muci
tare ko masamu albarkan ci cikin taro"cike da zumudi ta wanke Hannu ta tsoma suna ci suna
Hira sama sama.
Ummi Data sallame sallah ta fito tazo tazauna tana fadin"Au abun na ya"ya ne kenan "kai tsaye
yace mata"eh na ya"yane iyaye sai su koma baya"
..Safina tace"La Ummi kema fa kinsan tare muke ci da Abbah kema kinso kiyi mgana ne"
"Allah miki albarka,tasani jan magana ne kawai"
Ummi tayi mirmishi tace tana zama"Ni ne maijan mgana..? yace"to waye,?rigimarki nada yawa
Zainabu ko safina bazatayi abunda kikeyi ba"
Kai tsaye tace'Me nakeyi..? tafada tana kallonsa shima kallonta yakeyi kafin yace"Kinfini
sani"saurin sunkuyar dakai tayi tana dariya Safina tayi dariya Ummi ta dungureta mata kai tana
fadin"Baki da kunya ko"
Yace"kyalemin yata itama tasan gaskiya.Haka suka kammallah cin tuwonsu cikin farinciki da
annushuwa.
*Shakira..*
Commet
And
Share
Vote
[10/14, 20:01] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..!*
*Wattpad:Janafnancy*
_Mallakar:Janafty_
*DEDICATED TO:My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba"are*
*07*
WACECE SAFINA
*SAFINA ALIYU ZURMI* shine cikakken sunanta,mahaifinta mallam Aliyu zurmi dan asalin garin
zurmi ce dake jahar zamfara malami ne wanda ya shahara abangaren ilimin addinin
islama,yana da matar aura guda daya wacce ta kasance diyar malaminsane dayayi karatu
awurinsa agarin jalingo bafullatanan chan ce,to dayake yakasance na hannu daman mallam
alokacin shiyasa ya dauki yarsa zainabu abu ya aura masa batareda yayi duba da shidin
marayane wanda baida komai,da kowa ba,hakika zainab tacika ya tama mahaifinta biyayyah,su
biyu iyayansu suka haifa ita da yayarta iyami,tare akayi bikinsu da iyamin wacce ta auri wani
dan kasuwa a safana ita kuma Aliyu yadaukota suka dawo zurmi da zama.sana'ar saida hatsi
yake a kasuwa Allah yasama abun albarka sunada rufin asirinsu.
Aurensu da wata biyu suka samu,lbrin rasuwar mahaifansu,sakamakon gobara takamasu cikin
dare hakika anyi matukar rashi,rashi ma mai girma daga baya suka fauwalama Allah komai
suka rumgume mazajensu.
sai da Zainab ta shekara,uku kana ta haifi yarta mace wacce aka samata Safina hakika safina
tazo dawani al"amari domin soyayyata tuni tayi katutu azuciyar iyayanta,tun tasowarta
yarinyace mai hankali da Natsuwa,ga hazaka mahaifinta yazage gurin koyamata ilimin addini
tana shekara,goma sha biyu aduniya ta sauke alqur"ani,tana bitan sauran littafai.alokacin ne
kuma ta sake haihuwan Usman daganan haihuwa ta tsayamata.
Tana da shekara sha biyar da aduniya ta kammallah sakandiri sch dinta sakamakon yarinyace
da duk,garin zurmi ansan da ,da baiwanr da Allah ya bata,tana aji biyu a sakandiri akamata
jumping taje ss1,Safina tahaddace sahihul bukhari da muwadda malik tana da sanin kan hadisi
sosai gasan alqur"ani kuwa na gari gari ba inda bata zuwa kuma tayi na daya,hatta mkrantansu
suna alfahari da ita tuni ta kammallah aji shida yanzu suna ajin manyane.
Iyami wacce suke kira inna bata taba haihuwa ba har Allah ya karbi ran mijinsu to dayake
kishiyarta nada ya'ya tare da ita suke rike dasu har kwanan gobe,Safina tana bala"in son
innanta iyami saboda har hutu take zuwan mata,da kuma Aminyarta Hajiyar safana wacce
wanchan zuwan datayi inna iyami ke fadamata,jikanta yadauketa sun koma kaduna duk da
bataji dadi ba shiyasa safanar tafita aranta.
Samari dadama suna kawoma safina kai ammh bata basu dama ba saboda burin mahaifinta na
zamowarta wacce al"ummah zasuyi alfahari da ita tareda kasarta Nageria,tana son iyayenta
saboda suna da kyakyawan alaqa atare dasu inkagansu suna raHa da ya'yansu kace
kannensune.
Safina yanzu tana da shekara goma sha bakwai ne aduniya yarinyace doguwa,bakace domin
mahaifinta ta dauko sak doguwar fuska gareta tareda dogon hanci tana bakinta dan daidai
matsakaitan idanuwa gareta Safina bawata kyakyawan azo aka gani bane ammh kyanta mai
tattare da baiwane,tana da dogon gashi har baya baki silik wanda saboda yawansa yasa take
kitso biyu ta rabu dashi.
Dirinta mai tsayawa arai ne domin daga kasanta a tsuke take samanta shima atsuke ba kallo
daya zakamata kafahimci ta mallaki baiwa mai tarin yawa ba sai ka zauna da ita,miskilace ta
karshe bamai wayan haniya ba tanada zurfafa bincike kullum agida in bata komai to zaka ganta
cikin Nazari ne shiyasa iyayanta ke alfahari da ita matuka.
Bata jin wani namiji ya burgeta ba saboda kaf masu cewa suna sonta bbu wanda yadace da
tsarinta,tana son Namiji yakasance mai aji ne kuma yakansance yanada fukafukai guda biyu
wato ilimin addini dana zamani yakuma kasance yafi zurfafa ana addini,sosai yakuma zamonto
mai alkunya,kawaichi,da dattako,kuma bamai yawan kwaranniya ba kuma wanda yaba duniya
baya wanda yafi fuskantan lahirarsa yakuma kasance mahaifiyarsa na raye saboda tasamu
makwafin Umminta,Nikuwa nace tab anya Safina zaki samu kuwaí ¾í´”
Mallam yahuza ne yakusa hada wannan abubuwan duk da baigama hadawa duka ba ammh taji
ta natsu dashi duk da bai furta yana sonta ba ammh alamu sun nuna haka,mallam yahuza
malaminsu ne amkrantan dasuke karatu wanda kowa yasan matashine jajirtattace mai ilimi da
hangen nesa,shiyasa dashi kadai zakaga Safina na mgana harda mirmishi.
WANNAN KENAN
*********************
KADUNA
----Yau din ma Sakina kano ta kama Hanya tatafi tabarma shazeey Adil shazeey wata kedarace
mara sallah Sakina ta dauko a mtsayin Nanny wacce zata reni Adil sai da takwana biyu da
zuwa kana Dr safwan ya ganta bakinciki kamar yakasheshi yanzu ace arasa wacce zata renin
mai d'a sai,kafura mara sallah kuma ace har yakoyi wasu abubuwa atareda da'ita,dawannan
bakinciki ya isa shashen momma Adil na sabe akafadarsa wanda yanzu kimanin watansu uku
yayi bulbul dashi sai wutsul wutsul yakeyi ahannunsa.
Momma na zaune cikin dakin Hajiya tana shafamata man zafi akafa saboda tace yau kafan ta
matsamata,chan kasan makoshi yayi sallaman wanda momma ce kawai taji shi,kai tsaye ya
shigo ya zauna kan stool din gadon yana rumgume da Adil momma takallesa tsausayinshi na
tsirgamata.
Hajiya mama taja tsaki"mtwssss...Kai wai da girmanka kashigo ma mutane daki babu sallama"
banza ya mata bai tankataba takara harzuka tace"Kai tashi kafita tunda ba dakinka bane haba
ina dalili kazo kama mutane zaune kamar kabasu ajiya"
A Harzuke yace"Haba Hajiya kewai baki gane yanayin da mutum ke ciki ne eye"?yafada dadan
karfi galala tayi tana kallonsa kan ta kwace kafarta tagyara zama tace"To Habule gani dakeni
kaji tunda wuyanka ya isa yanka"tsaki yaja kawai ya mike yana gaida momma kan ya mikamata
Adil yana fadin"momma ki rikesa agurinki zan tafi asibiti," tasa hannu ta amsheshi kan
tace"Adawo lafy Allah yabada sa"a" ya amsa da Amin
Hajiya mama tafara salallami tana fadin"yau anyi tsinanna yau din ma ficewa tayi tabar d'an oh
ni maryama naga takaina"tafada harda dora hannu akai,Dr Safwan ya isa bakin kofar yana
fadin"Momma ko anzo karbarsa kar kibada shi.. Wai sakina arniya ta dauko wai ita zata
renanmim d'a,dan Allah momma ki rike adil agurinki nasan bazaki gazaba"Ai da sauri Hajiya ta
sauko daga kan gado tana fadin"Ar....Me lalle sakina yar tasha ce yanxu haka ta raina mutane
to wlh billahil azim sai tabar gidannan bazan zauna da kedara ba agidannan ba wlh"Tana fadar
haka tabi bayan Dr safwan tafice fuu.
Yana kokarin shiga mota yaga ta shige sashensa,kada kai kawai yayi ya shige mota yabata
wuta don ahalin dayake ciki baida lokacin hajiya mama.
Shazeey taga bala"i domin hajiya mama tadunga mata watsii da kaya bayan tagama tasa yan
aikin Sakina sujata sufitar da ita dagan gidan,fadi take"kuja shegiya kafurar banza agidan nan
wlh baki isa kizauna ki koyamana kafurci ba kuja shegiya naceí ¾í´£í ¾í´£í ¾í´£sukuwa suna janta tana
kuka tana rokon hajiya mama tana fadin"Madam plz help me....Srrry ho..."sorin uwarki inkika
kara kirana madam sai kinci ubanki"waje suka watsata sai da kanta yabugu da kasa da sauri
tace"jesus ai da wani gudu Hajiya tabita tana fadin"mun shiga uku zata konamu jejesas din
babankií ½í¸‚ agidannan,Ai da gudu shazeey ta rarimi kayanta megadi yabude mata get tayi
waje,Hajiya tace"tsinanniya kawai da ki tsaya dasaina na fasa katon kanki kamar na
kwakwaí ¾í´£í ¾í´£í ¾í´£í ¾í´£kowa na kunshe dariyarsa sabida in Hajiya taganka wlh sai kasani.
Momma tana gani ammh batayi mgana ba saboda sanin halin hajiya yanzunan ta dawo kanta
Ranar hajiya wuni tayi tsinema sakina da uwarta daga karshe akace"ai ba shegen d'a irin
sufiyanu sai da na hanasa daukoma yarinyannan saboda nasan arina ko ganin uwarta kamar
wata tsohuwar kilaki amma dayake kunnen kashi gareshi ya kwasomana bala'i har gida,daga baya kuma aka hau share hawaye tana
fadin"Allah ya jikanka salisu dakana nan a raye dabai auromana tsinanniyan yar"nan
baí ¾í´£í ¾í´£í ¾í´£í ¾í´£Haka hajiya ta wuni ashar.
*Hoho sakina kinga ta kanki tunda Hajiya mama ta tsaneki*í ½í¸‚í ½í¸‚í ½í¸‚
*Anitha...*
Commet
And
Share
Vote
[10/14, 20:01] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..*!
*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_
*DEDICATED TO:My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*
_Ina mata yan kwalisa masu Bukatar su Fito su kere Sa"a cikin Sa"anni ko matan abokai ko
cikin kawaye..? Ina Mata wadanda ke Bukatar Gwangwajen ya"yansu cikin kayan alfarma
domin kere sa"a da Fitowa cikin Alfarma cikin Sa"aninsu,Toh duk kusha Kuruminku ina tafe
muku da Wani Karin Albishir ko kuna da Labarin DIJA COLLECTION,wanda ya Hada komai na
kayan kawan Mata da maza domin fitowa Tsab,da Sanya mata suna Dagawa..?Ki hanzarta ko
kuma mu hanzarta wajen samun daman zama mace yar Kwalisa muna saida komai na kayan
adon mata da maza da yara,Irinsu Atamfa,leshi,Material,Takalman mata dana maza na yara
dana manya,akwai dan kunnaye masu kyau da Tsari,kina bukatar mayafai na nuna Tsara..? Toh
duk zaki samesu a Dija Collection ,kina bukatar Abaya.. ?shima karki damu duk zaki samu a
Dija Collection kayanmu suna da Ingancin Domin ingancinmu ne yasa muka Cigaba,Zaku iya
Tuntubarmu ta wannan Nombobin wayar kamar haka 07045112780,ko kuma 09036617473,Sai
kunzo...karku Manta Siyan Nagari mai da Kudi Gida.._
*08*
------Koda Sakina tadawo ta iske hajiya mama ta kora mata shazeey Ranta yabaci tadinga yada
mganganun acikin gida,takira hajiya kari tafadamata,suka taru suka dunga tsinema Hajiya
mama ita kuwa Anty laila cewa tayi"Fine and good sai kibarmusu dansu su rena tunda sun raina
kokarinmu don dai bazaki zauna ki ijeye kasuwancinki kina masa rainan d'a ba"
Sakina ta shaka game da Hajiya mama Shiyasa ta kudiri niyyar yi musu abunda bazasu manta
da ita ba,ammh duk maganganun data keyi,iya shashen ta ne,don tasan wacece hajiya
mama,in Taji ta jita bazata ji da dadi ba.
*Zurmi...*
  Usman ne ya sheko da gudu cikin gida,yana haki Ummi dake bakin rariya tana wanke
wanke,tasaki aikin tana fadin"Usman...Lafiyarka kuwa?"yana haki yace"Ummi yaya Safina ce
nagansu yanzu suka dawo"
Ummi tasaki mirmishi tace"ikon Allah...Allah yadawo dasu kenan"?
"eh...."yabata amsa kan yakara shekawa da gudu,yakara ficewa.
Ummi ta rausayar dakai tace,"oh Usmanu ba dama,ta cigaba da wanke wankenta cikin farin ciki
na dawowar yarta daga jigawa gasar karatun qur"ani ta jaha na Fidda gwani kwanansu biyu.
Ta kammallah kenan taji sallaman yar' tata cikin farunciki tareda rakiyar kawarta Aisha,da gudu
tarumgume Ummi tana Fadin'oyoyo Ummi nayi kewarku wlh"
Ummi tana dariya tace"Oh Safinatu na barka da dawowa "Safina tace"yauwa Ummi nasameku
lafiya"?
Aisha tace"la Ummi shine dan kinga Safina kika manta dani,Ummi tayi mirmishi tana fadin"haba
ai har abada Aisha kema diyatace kamar yadda Safina take diyata"Mirmishi sukayi tare Usman
kuwa yana jidan kyaututtukanta yana shiga daki dashi
Aisha tace"Ummi ku tayamu murna Safina taci lambar yabo ta daya a jahar mu ta
zamfara"guda Ummi tasaki tana nuna Farincikinta.
Abba daya sawo kai cikin gidan yake fadin"Ash....Ash...Zainabu guda kuma"?
ta amsa da cewa "Nuna farinciki ne Abbah diyarmu tasamu nasarar cin gasan zuwa gasan a
kasa gabadaya zata wakilci jahar zamfara.
Yana kawata fuskarsa da fara'a yana fadin"Masha Allah yakamata ki furta zainabu ba