Showing 18001 words to 21000 words out of 52374 words
Chapter 7 - NA TAFKA KUSKURE COMPLET BY JANAFNANCY-1.pdf
Dr Safwan kawai yaji yasamu kansa da cewa"An dawo lafiya...?Allah yasa albarka"cikin husky
vioce dinsa ya furta haka tadago tana kallonsa aranta tana fadin"So sweet.."Tace"Alhamdulillah
nagode..Daganan shuru ya biyo baya Ammh lokaci bayan lokaci suna satan kallon juna,sai suyi
mirmishi atare.
Shikuwa D Tahir yana chan yatasa Ummi da hira ita kuwa haka takeso mutum mara bakunta
tana bashi lbrin amintar Haj.Mama da iyami shikuwa yanata jinjina girman Amintansu.
Abun Mamaki saiga Dr Safwan yana abunda bai sababa wato mgana sai gashi wai Safeena Ta
chanzashi da surutu yana tambayanta kan matakin karatunta tundaga na boko har na arabi yayi
mamaki na yadda karamar yarinya kamar Safeena take da ilimin sanin littafan addini haka
gaskiya ya jinjinama iyayanta matuka,tadan Sake dashi sama sama ammh ita aranta mamaki
take wai yau itace ta mallaki miji iri Dr Safwan miji na Nuna sa'a wanda ko wacce mace take
fata ta mallaka amtsayin miji duk ko takamarta da nasabarta da ikonta kallon daya zatamai taji
ta raina kanta da duk abunda ta mallaka kuwa.
salla kawai ke tadasu.
Tabbas su Tahir basu Nuna bakunta ba suka zage suka ci tuwonsu Dr Safwan yaji dadin cimar
saboda abincinsa duk miyar da akayita da ganye masoyiyarsa ce ga lafiyayyah zobonsu wanda
tas suka shanye suna hamdala da wannan gidan irin albarka,saboda dadin Hira basu ankara ba
sai da Tahir yaga shida Saura yaleka su Safeena yana cewa"plz amarya ama na hakuri
hakanan kada muyi dare a hanya"Safeena tayi yar dariya tace"To ni na rikesa"Dr Tahir
yace"kece mana to inbake ba To waye"..?Yafada yana kallonta hannu tasa ta rufe fuskarta Dr
Safwan ya tsuramata ido yanajin wani shauki na dibansa domin wannan sa hannun datake tana
rufe fuska shike burgesa yakesamasa shauki wanda yarasa ko na menene.
Minti biyar minti goma shuru Dr Safwan yaki fitowa yana chan kawai ya zurama Safeena ido
yana kallonta so yake ya fahimci wani yanayi yake tsintar kansa in yana kallonta ammh yagaza
fahimta sam,dakyar ya yakice abunda yakeji ya mike yana kallonta yace"to madam mukam
munyi harama"Da wutsiyar ido ta kallesa kan tace"daman ba kwana zakuyi ba..?"tafada da wani
salo wanda ita batama san ta iya ba,mirmishi yayi kawai yana kallonta kasa mikewa tayi saboda
idon daya zuramata yana kallonta yana wani shafa sajensa yana cizan lebensa na kasa
yunkurawa tayi tamike tayi gaba tana Fadin"Allah yammh tayi kukoma kaduna yanzu"tafada
tana isa kofar dakin da sauri ya isa ya cimmata tana kokarin fita ya bangaji kafardarta atare
sukaji wani shock kamar wuta yaja su dagowa tayi tana kallonsa kawai sai yasamu kansa da
dagamata gira daya yanajin wani farinciki na shigarsa,sunkuyar dakai tayi ta fice da
sauri,Akasalance ya fito yana ma Ummi sallama.
Ummi tace"A"a Tahir dare bai yi ba yanzu fa za'a kira magarib..?'Dr Safwan yace"Babu komai
Ummi muna da Aiyuka gobe asibitine infact ma bamuyi shirin kwana ba"Safeena dake gefe
tsaye jikinta duk yayi sanyi yanzu shikenan mr handsome zai tafi ya barta _topha safeena har
Dr Safwan din yazama mr handsome_í ½í¸›
Ana haka saiga Abba yayo sallama yashigo hannunsa rike da manu da usman ummi
tace"Shikenan ma ga Abbanta nan yadawo, Ummi tanamai Sannu da zuwa tana fadin"Allah
yasa zaku hadu mijin Safeena ne sukazo shine wai yanzu zasu tafi"Abbah ya kariso yana
fadin"Masha Allah...Sannunku da zuwa' zubewa sukayi suna kwaasan gaisuwa ya amsa yana
tambayansu yasuka barosu suka ce suna gaishesu.
Abbah yace"to masha Allahu...Ammh dai zaku fasa tafiyarnan dan magariba ma ake kira'Dr
safwan zaiyi mgana Dr Tahir yayi saurin cewa"Toh Abbah matsalar bamuyi buking din gurin
kwana na bane"Abbah yace'Haba dan wannan babu matsala akaba na wajema balle ku nagida
kuyi sallah Safeena tarakaku nan gidan su baffanta isuhu sai ku kwana"Ummi tace Shikenan
kuwa"Abbah yace akawo musu ruwa abuta Safeena tazuba musu ta mikama kowanne tana
Zuwan kan Dr Safwan sai da ta duka kana ta mikamasa zuru yamata domin a iya tsawon
rayuwarsa Sakina bata taba bashi ruwan alwala ba balle har ta rankwafa karba yayi yana
fadin"weldon..yanmatana"yafada ahankali da sauri ta wuce tana rufe fuska,tare sukayi alwala
da Abbah dasu usman suka rankaya massallaci abun ya matukar burge su Safwan yadda
Abbah yasake jiki dasu yana ta tambayansu aiyukansu abunda Safwan ya fahimta su Safeena
talakawane ammh masu wadatar zuciya kaf da kanta har iyayenta lokaci daya yaji sun
kwantamai arai,sai sukayi issha'i kana suka dawo koda suka dawo Safeena ta musu jallof din
shinkafa da kifi sai kunun aya ta fesa wanka cikin riga da sikat tasauya hijabi humra ta shafa
ajikinta tana fitar dawani sirrin kamshi Su Ummi dakin Abbah suka yada zango suka bar Su
Safeena dakin Ummi.
Itama shinkafan sunci badayawa ba kunun ayan dai suka sha bil haqqi da gaskiyansuí ½í¸‚tahir
gurinsu Abbah yakoma ya bar mata da miji su kebe,to banda kallon juna suna aikin aikama juna
mirmishi babu abunda sukeyi kowanne zuciyarsa tab farinciki.anan ne yake Nuna mata hoton
dansa hakika kallo daya Safeena tama Adil ahoto taji yashiga aranta duk da lokacin da Ummi
tafada mata yanada mata ko ajikinta ammh haduwarta da Dr sai taji dama ita kadai ta mallaki
wannan hot guy diní ¾í´”í ¾í´”
sai after ten Safeena ta rakasu gidan Baba isuhu wanda wa yake ga Abbah gidansu na gaba
kadan danasu yafi Abbah abun duniya kuma yanada manya ya"ya maza shiyasa gidansa keda
dakunan kofar gida to daman dayake Abbah yamai bayani dasuka hadu a massallaci har suka
gaisa da su Safwan din nan suka bar motarsu kofar gidansu safeena koda sukaje anygra musu
daya daga cikin dakunan mazan gidan mai dauke da katifa wacce ke kasa sai sai kafet dake
dakin sai toilet dakin tsaf dashi gwanin shawa'a Safeena bata wani tsayawa ba ta musu sai da
Safe ammh sam Dr Safwan yaki barinta tatafi ita kadai sai da yarakata har kofar gida shima din
tsayawa yayi yana kallon fuskarta cikin hasken farin watan daya haske garin..shigewa tayi gida
tana masa dariya.
sai da ya koma yasamu sukunin kiran momma yake Fadamata halin da'ake ciki tayi musu fatan
dawowa lafiya Haj.Mama na gefe take fadamata abunda Safwan din yacemata haj.Mama tayi
tafi tace"Allahu akbar oh ni Maryamu Allah na gode maka kingani ko Hadiza yaushene safiyanu
zashi wani guri har ya kwana"tafada harda rike haba kan ta cigaba dacewa"lalle Nasan yayaba
da zabina kenan..Allah na godemaka.Itama momma murna take tana kara rumgume adil tanaji
aranta komai yakusa zuwa karshe.
Dr Tahir yanata tsokanan Dr Safwan kin tankasa musa yayi wanka yayi yabaje a katifa daga shi
sai boxer ya rumgume filo yana wani lumshe ido kamar wani tsohon maye sororo Dr Tahir ke
kallonsa kan yadauki filo ya wurga akasa yana Fadin"Bari na barmaka katifan saboda tsaf cikin
dare zaka iya turmusheni kazata Safeenar ce,Tunda na lura jaraba ce fal aranka..."Tsaki Dr
Safwan yayi kan yace"gwanda dani nasan dadin abun kai kuwa har yanzu kana kasa
ne...Banza dan sa ido kawai,Dariya kawai yayi ya juyamasa baya.
Itama Safeena anata bangaren kasa barci tayi tana juye juye data juya ta rufe ido sai taga Dr
yana mata wannan tsadaddan mirmishin nashi mai kashemata jiki,dataga barcin yaki zuwa tashi
tayi ta dauro alwala tafara Nafila tana godema Allah daya mallakamata Dr safwan amtsayin miji
aurenta.Tadade tana addu'a kafin takoma ta kwanta tana mirmishi ita kadai.
*Domin samun Damar Zamay Daya Daga cikin wacce zata Karanta Kayattacen Labarinmu na
Silar Hallaci zata iya Tumtubata ta wannan Layin 09069067488 akan Naira 300 kachal*
*Anitha..*
Commet
And
Share
Vote
[10/14, 20:01] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..*
*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_
*DEDICATED TO:My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*
*18*
----- Dukkansu barcinsu rabi da rabine domin kowani dakika zuciyoyinsu suna bugawa da sunan
juna,amassallaci kusa da gidan su Safeena suka yi sallah sun gaisa da Abbah sundade tare
suna mgana har Dr Safwan yafadama Abba,da zarar ya koma ammh insha Allahu yana
komawa zai tanadarma Safeena inda zata zauna sai susa lokacin da za'a ayi bikin Abbah
yafadamasa kar ya takura kansa Safeena kanwa take agurinsa.
suna dawowa sukayi wanka domin yau monday tushen aiki suna da aiyuka a hospital,shiyasa
Allah yasa shi Dr yana ijiye kaya amota kamar yasani dinkinsa daya amso wajen kala uku su ya
dauko ya sanya daya yabama Tahir daya kafin karfe bakwai sun zama ready.
itakuwa Safeena tana idar da sallar asuba bata komaba,fita tayi ta share gida tagyara dakunan
tazo ta musu abun karyawa kunun tsamiya tamusu da kosai daman tana tashi waken tafara
wankewa,sai ruwan zafi wanda yaji citta da na'ana'a tashirya cikin riga da sikat na leshi milk and
green kayan fiteed ne sun amsheta sun mata das da ita green din hijabinta ta tasaka,dogo har
kasa ta dauki kayan akwando tama Ummi Sallama hakika Ummi taji dadin ganin yadda yarta
bata Nuna wani damuwa ba duk da dai tasani aurene kawai ammh Dr Safwan ba ajin yarta
bane _Abun Allah kenan_
Koda ta isa da kaya niki niki ta iske daga cikin gidan ankawomusu soyayyen arish da kwai
harda kayan tea ta iskesu sun shirya ta duka har kasa tana gaishesu Tahir ne ya amsa yana
dariya kan yace"Tashi mana amarya mun amsa gaisuwar aie"Shikuwa Dr Safwan tunda
Safeena ta shigo kamshim humran data sa yashakeshi yarasa Natsuwarshi kallonta yake cikin
wani yanayi wanda ya kasa gane kanshi Dr Tahir daya Fahimci haka ya fice ya basu wuri.
Tana nan durkushen kanta na kasa tana wasa da gefen hijabinta gaban na tsananta faduwa
domim tasan wannan kallon nashi mai kadamata yayan Hanji yake mata ahankali tadago kanta
caraf suka hada ido yana tsaye sanye cikin wani farin yadi milk mai sansti bayi da kauri tunda
har ana hangan farar vest din dake jikinsa hulan kasan zannah bukar ce fuskarsa tayi fayau da
ita yana furta da Annuri Kamar daren goma sha tara duka hannuwansa ya rumgume
akirjinshi,kasa jaye idanunta tayi jitayi kamar kasa baza ta iya daukanta ba saboda wani kasala
ke rufeta tsigar jikinta na tashi yarr!!!
saurin jaye idanunta tayi saboda tana gab da zubewa agurin mirmishi yayi kawai ya jawo
kwandon data shigo dashi ransa yamasa dadi dayaga kunun tsamiya da kosai,masha Allahu
yasha sosai kosan ma yaci sai ruwan na'ana'a shima yasha kadan ammh kowani lokaci tadago
idanunsa na kanta,yana kammalawa yasa tissue yagoge baki ya mike yana
fadin"Alhamdulillah...Yafada yana kallonta kai tsaye ya isa kusa da ita bata ankara ba shima ya
durkusa har gwiwansu na gogan juna da Hanzari taja baya kallonta yayi kan yace'"yan matana
yakamata amin ramgwame naga wannan kwalliyar kan in Tafi"Yafada yana wani lumshe
idanunwanshi tuni jikin Safeena yafara rawa takasa dagowa sai ma kara dunkule data keyi cikin
hijabi wani yanayi keJan Safwan yayi saurin mikewa kada yabi shawaran zuciyarsa na
Rumguman yar mutane.
Wayoyinsa ya Dauka yayi Hanyar ficewa yana fadin"Shikenan tunda kin Hanani ganin Halas
dina"yafada muryansa kamar zai yi kuka,taga da gasken ficewa zaiyi da sauri ta mike cikin
rawan murya"Am.... _*UNCLE*_"cak ya tsaya kafin ya waigo yana kallonta so yake ya tabbatar
da itace takirasa da Unku kai verry interresting.
Cikin kunya matsananci ta yaye hijabinta ta rike hannunta kanta na duke tace"kayi
hakuri…"tafada dajan Numfashi kamewa Dr Safwan yayi yana kallon Safeena tun daga sama
har kasa yake kallonta idanunsa na yawo ko'ina ajikinta Safeena doguwace mai dauke da
doguwar fuskar gashin idanunta sun matukar burgeshi structure din jikinta shi ya tafi dashi uwa
uba Nonuwanta dasuke cike tab atsaye suna masa maraba cikin mutuwar jiki da wata irin
fitinanniyar murya ya Furta'Tsarki ya tabbata ga ubangijin dayayi wannan Halittar...."Yafada still
idanunsa kyam akanta ita kuwa yadda idanunsa ke yawo ajikinta haka takejin wani sanyi na
ratsata kamar wacce zata yi masassara,cikin tafiyar kasaita ya karisa kusa da ita yasa
hannunsa ya tallabo habanta yana fadin"Baki kyautamin ba Sam Safeena daki Ka hanani ganin
wannan kyakyawan suran taki da wuri"Ya fada yana kokarin sa idanunsa anata itakuma taki
saima runtse ido da tayi zuciyarta na bugawa tsuru yamata da ido yanajin wani magnet najansa
wanda baisan sadda yasa Hannunsa duka biyu ya rumgumota ba yamata kyakyawan tarba
afaffadan kirjinsa.
Ya salam Safeena ta furta akasan makoshinta saboda wani schock dayajata kamar ta wutar
lantarki tunda take arayuwarta babu Namijin daya taba rike mata hannu balle har ya rumgumeta
sai gashi tafada cikin wani yanayi wanda kwKwalwarta tagaza hasaso mata komeye
shi,shikuwa Dr wani chemistery ne ke aiki ajikinsa wani dumi mai hadi sanyi dadi ke ratsasa
hannunwansa yasa duka yakara matseta gam yana Fidda Numfashi sama sama tuni hijabin
Hannun Safeena ya Sulale ya fadi dankwalin kanta yafadi gashinta data dunkule yawarware
yarufemata fuska"wow..Shine abunda Safwan ya Furta yayin dayayi tozali da gashin Safeena
haka yasanya hannuwansu duka biyu yana lailashi idanunsa arufe yanaji kWakwalwarshi na
wani amsawa zut,zut kamar zai shida.
Sun dade ahaka Dr Safwan yakasa sakin ta Saida karar wayarsa ya fargar dashi cikin kasala ya
sausautamata rikon yazaro wayar a aljihu yana dubawa yaga Tahir ne yana Dauka Tahir yafara
cewa"Kai Dallah mallam kafa shanyani bakasan tafiya ke gabanmu ba"saurin katse wayar yayi
saboda bazai iya mgana ahalin daya ke ciko ba so yake su hada ido Safeena taki yarda sai
wani sunne kai take kan kirjinsa wayyo Dadi Dr Safwan suma kadai baiyi ba shi yaushe Sakina
tatabamai shagwaba juz hug da kiss sai tace duk salon takurane.Mirmishi yayi kawai ya dauko
dankwalinta yadora mata bisa kai yana Fadin"Sarkin kunya...Mu zamu wuce Tahir ne
yakirani,yana fadar haka yana mika mata hijabinta ta amsa ta sanya tana dukar dakai kallonta
yakeyi yanajin wani bakon lamari na ziyartashi kardai ace in yakoma gida wanka yakamasa
_Wanka fa Dr Tab koda yake andade ba'a hadu ba_í ½í¸„
Tare suka fito yana gaba tana binshi baya sai da suka shiga cikin gidan ya musu sallama 20k
yabasu suka amsa suna godiya,haka dasuka shiga yima Ummi sallama 30k yabata tace bazata
amsa ba ya marairaice yace"Ummi...In baki amsa to kin Nuna min Safeena ce kadai yarki"Ummi
tace"Kaima Danane duniya wa lahira Safwan nagode Allah yamuku albarka ya kaiku lapy"Suka
amsa Da Amin Abbah kuwa daya bashi 30k kin amsa yayi sukayi sukayi yace'bazai amsa ba
shidai burinshi ya rikemai Safeena da Amana"Hakika Mahaifan Safeena sun burge Su Dr
Safwan matuka wanda har hakan yayi tasiri aransu.
Abun mamaki sai gashi kawai sun bude boot yara na jidan kayan abinci suna shiga dashi buhun
shimkafa,katan din taliya katan din makaroni dadai sauransu narike baki cos nikaina bansan
yaushe akasa kayan ba,sai dai Ummi su sukaga kaya kawai,Abbah baice komai ba saboda
wannan karon in yace bazai amsa ba to surikin nasa bazai ji dadi ba.
Tabbas soyayyah gaskiya Safeena da Dr Safwan zukatansu sun aminta da juna domin daga ita
harshi jikinsu yayi sanyi lokaci dasuka shiga mota zasu tafi Safeena na kofar gidansu tana
kallonsu batasan sadda hawaye ya gangaro mata ba har Tahir ya tada mota Dr Safwan ya
dakatar dashi ya bude mota ya fice sai dai ta ganshi agabanta kama hannunta yayi yana
fadin'Kukan mekikeyi yanmatana"..?kallonsa tayi idanunta tab hawaye tace tana turamasa
baki"Yaushe zaka dawo"..?tafada da shagwaba tab wlh badon mutane na wucewa ba abunda
zai hanasa rumgumeta ya sumbaci bakin nan daya kusa zautar dashi ammh duk da haka sai da
yakara matse hannunta yace"Yaushe kike so nadawo'..?kallonsa tayi ido cikin ido kawai sai
tasamu kanta da furta"Ko gobene inaso"Mirmishi ya subucemai baisan sadda yace'Gobe. fa
kikace,..?tagyada mai kai mirmishin yasake yi mata kan yace" Am srry bazai yuyi in dawo gobe
ba,saboda in nadawo wazai kula da patient din..? "yafada yana kallonta kafin ya cigaba da
cewa"kiyi hakuri verry soon zan dawo" yanzu tunda baki da waya ga wannan ki rike kan in dawo
in siyo miki taki ko..?"yafada yana mikamata dayar wayarsa da hannu biyu ta amsa tace"Na
gode Allah ya saka da alkhairi",wow....Shi yaushe Sakina yataba bata abu tagodemai ai gani
take dolema yabata ta amsa tana wani bude hanci kamar ta bashi ajiya,kura mata ido kawai
yayi yana kallonta zuciyarsa yaji tana zafi in ya tuna Tafiya zai yi Tahir ne yaga abun bana
karewa bane yadinga zabgamusu hon,Safeena ce tayi karfin juyawa tana Fadin"ka
tafi....Kagaida hajiya da momma harda Adil Allah ubangiji yakaiku lpy"Tafada wasu hawaye na
gangaro mata dagudu ta ruga gida wani kuka ya kwacemata.
jikinsa sa babu laka yakoma mota yana Shiga Tahir ya kallesa kawai ya girgiza kai ya tada mota
suka dau hanya,sun Fita garin gusau jefi jefi yana kallon shashen Dr Safwan yake wanda
yamaida kansa jikin kujera ya lumshe idanunsa kamar mai barci ammh hakika ba barci yakeyi
ba gabadaya ransa da tunaninsa naga Safeena kwana daya kacal ammh tasamu wani gurbi
mai girma azuciyarsa wanda baisan sanda tasameshi ba,ji yake tamkar yasakota cikin mota
yazo kaduna da ita kallonta kawai da yanayinta kansashi nishadi balle yangarta da salon
kunyarta.
Dr Tahir yakara kallonsa kan yace"Duk wannan Damuwar ta mecece Dr Safana..?"yafada kansa
tsaye shuru yayi masa wanda har ya fitar da rai da zai yi mganasai chan yace cikim sanyim
murya"Bai shafeka ba plz Tahir karabu dani bana son damu"yafada still idanunsa suna rufe
shuru Tahir yayi kan ya jinjina kai yace"I can belive my Dr fall in luv wit Safeena....Any why ta
cancanta saboda kyawawan halayyata congratulation mr man wlh kadace ta ko'ina"Abun
mamaki sai ga Dr Safwa yayi mirmishi yace'Thanks u mr Tahir bello suraj.
_to ya kuka gani kunga yadda soyayyar Allah take ko,sai Allah yabaka wanda ko a mafarki baka
taba tsammani ba,juz imaging Dr Safwan yafada tarkon son Safeena konace sun fadama
Juna,kuna ganin salon Safeena bakwa ganin lokaci kadan za'a Shafe babin Sakina arayuwar
Safwan ba_?