Showing 24001 words to 27000 words out of 52374 words

Chapter 9 - NA TAFKA KUSKURE COMPLET BY JANAFNANCY-1.pdf


ta jira domin jin kanta bazai barta ta fito ta bude ba, aikwai Habu yasha tsinuwa kamar itace
uwarsa harda cewa zata sallameshi tunda yagaji da aikin tana cikin mai tijaran sai ga Haj.Mama
ta fito dama tunda taji hon din namarasa hankali tasan jakarce,aikuwa tana zuwa sakina tayi
shuru haj.Mama tana kallonta sama da kasa kafin kafin tace"Ikon Allah ke inbanda rashin kunya
da fitsara kitsaya gaban sa'an ubanki kina zagesa harda cewa zai bar gidan ko"..?Takareshe
fada ta tana rike da kugu Sakina tace"plz hajiya niban saki cikin shirgina ba plz stay
out"Haj.Mama tace"kinci ubanki nikike cema pulaz🤣hala nayi kama da sakaryan uwarki ce to
wlh bari kiji ke kanki inbakiyi hankali dani ba to sai kin bar gidanan don banga uwar dakike
tsinana mana ba"Sakina tayi tsaki mtseswwww tashige motar ta ta kirar vibe tana fadin"Inkin isa
in yadawo kisa ya rubutamin saki uku,sai na tabbatar da kin isa uselless kawai"Tafada tana
kokarin zuge glass din motar Haji.Mama takarisa jikin motar tana fadin"Ahayyye....Tayaro kyau
take bata karfo ai ni maryamu bazan taba yarda Safiyanu ya sakeki ba yanzu so nake ki kirbi
abunda kika shuka da hannunki kuma Alhamdulillah abun da namiki tanadi yakusa isowa gareki
wlh sai kin raina kanki tunda ke ballagazar macece wacce batasan darajan kanta ba"Tana gama

fadar haka tawuce tana fadin kai megida wuce kakama harkan gabanka tunda ba ita ta daukeka
aikin ba aikuwa da gudu ya wuce itama Hajiya ta shigewarta sashensu tana wake wakenta.



Sakina tayi turus acikin mota bakincikin kalaman Hajiya dana Safwan suka taru suka sata fitar
da kwallah kamar ita Sakina mai aji da daraja ake cema ballagaza dama jiya Dr yace mata
shashasha,tashare hawayenta tace afili wlh both of dem they will pay 4it kafin ta kwarara hon
habu yazo da sauri ya budemata saura kadan ta takeshi sai da ya kauce ya rike baki yayi
yace"Kai wannan mata baki kyale kowa ba shikanshi yallabai baki kyaleshi ba balle uwarsa da
kakarsa balle mu yan aiki,tab...Ubangiji yamana maganinki"yafada da karfinsa kan ya rufe get
ya koma kan bencensa.




Katsina ta dikko dakin kara ta nufa saidai haj.Kari taganta kwatsam tana mata kuka dakyar
tasamu tafadamata duk abunda ke faruwa Haj.Kari ta mike ta lailayo ashar tace"babban bura
ubanchan har ni za'a kawoma iskanci....Shi Safwan din harwani tsiyane balle uwarsa da
wannan yamutsatsan tsohuwar har ta isa ta saki kuka, ita din banza to wlh bari Abbanku yazo
Sakina nagaji dawannan auren yazo yasan yadda zai yi dashi"tafada tana huci kamar
mayunwacin zaki _chau chau Haj.Kari Allah dai ya biya_ Sakeena tayi saurin cewa"a"a Hajiya
wannan ba mafita bane kema kinsan wlh in Abbah yaji zai iya tsinemin kema kinsani"haj.Kari
tayi shuru kan tace"eh...Kuma hakane shima sun asirceshi ji yake in aka taba yaron nan kamar
antaba ubansa"Tafada harda yamutsa fuska Sakeena ta jingina da kujera tace'kyalesu hajiya so
suke suga na ijiye kasuwancina indawo ina kula dashi da uwarsa inzamarmusu jaka"Haj.Kari
tace"Ina har abada wannan bazai taba faruwa ba domin ni ban haifi malalatan ya"ya ba kudine
zan hada na hannuna laila ma zan mata waya takawo abunda take dashi ki wuce kikama
hanyar ki tafi ki saro kayanki kizo ki dasa daga inda kika tsaya kibarmin komai ahannuna
ninasan matakin da zan dauka"Sakeena ta saki dariya tana fadin"Dat iz my hajiya shiyasa nake
sonki"haj.kari tace'karki damu in ban tallafa muku ba wazai muku tunda irin uban da Allah ya
baku kenan solobiyo"Sakina tasaki dariya tace"Hajiya Abbane solobiyo kuma ..?tace"kona yi
karya"Sakina tace"A"a Hajiya da gaskiyarki"Atare suka sheke da dariya harda tafawa

_oh ni jami Duniya harta kaimu ga haka_🤔


****


bayan la'asar Dr yadawo agajiye yake dat why yafara isa shashensu sai da yayi wanka ya huta
kana ya fito baiji duriyar Sakeena ba bai damu ba dama kuma ba motsinta yakeji ba har zai fita
sai yasamu kansa da tambayan daya daga cikin yan aikinta ina take kai tsaye tacemai tun safe

ta fice bai damu ba illa zakuda kafada yayi yafice zuwa massallaci sallar mangariba kana
yadawo ya wuce shashen su momma chan ya tarar da haj.Mama da momma suna hira,hajiya
dai batai fushi ba saida ta tsaitsayeshi yafada musu yadda sukayi da mahaifin Safeena ya
kareshe da cewa"Yanzu na yanke shawarar Safeena zata zauna gidana dake anguwan sarki
tunda a nan din babu inda zata zauna.



Haj.Mama tamike tace"kul...Karma ka fara Acikin gidan nan Safeena zata zauna anyi ba'ayi ba
kenan ai inhar Safeena tabar gidan nan ban Nunama ballagazan matarka na amsa sunana
maryamu ba"Dr Safwan yace"To hajiya ina gun da zaki sata..?Kai tsaye hajiya mama
tace"dakuna uku ke shashenka ko?tafada tana kallonsa da kai ya amsa tace"To ka gayamata ta
kwashe kayanta adaya ka saka Safeena aciki tunda duk kaine mijinsu in lokacin da Safeena
zata koma chan yayi nida kaina zan fada maka"Tana gama fadar haka tatashi tawuce har takai
kofar bedroom din tajuyo tace"Umarnine ba shawara ba kafara shiri cikin sati biyu nakeso
Safeena tatare,tana fadar haka tashige daki Dr Safwan yayi ajiyar zuciya aransa yace"Hajiya
daru....Ita kuma momma tana ta jinjina kai kafin tace"kaji abunda hajiya tace ko"Ya gyada kai
tace"to kabi umarninta kazauna lafiya"itama daga haka tashige kichen zata kawomai abinci
shikuwa Dr Safwan yayi shuru yana so yagane dalilin hajiya na zartar da wannan hukunci
ammh ya kasa.



_hoho hajiya mama kinayi muna jin dadi Jamuje Allah ja da mulikinki haj tamu_✋✋✋










*commet, share Vote domin kwarin gwiwata...*


*Shakira..*
[10/14, 20:01] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..*!

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty�_

*DEDICATED TO:My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*


*Wannan Shafin na yau Gabadayanshi na Masoyan HAJIYA MAMA neâ¤ï¸tace na gaya muku
Tana godiya da Sakonnin Jinjinawarku gareta Allah ya bar kauna Tace na sanar daku
Gabadaya Masoyanta na Wattpad da Whatsap SON SO FISABILILLAH*



*21*


" Koda kwamishina yadawo ya tarar da Sakina agida fada yahau yi yace meya kawota sai ta
shirgamasa karya da cewa da izinin Dr Safwan tataho aikuwa baiyi kasa agwiwa ba yakirashi
yake tambayansa abun mamaki Dr ya amsa masa da hakane cos bayaso ta dalilin sa Sakina
tarasa albarkar mahaifinta.


****


Babu yarda Safwan ya iya da mganar haj.Mama domin ko momma bata tsallake umarninta
daya fadama Tahir shima yayi na'am da batun na hajiya domin yace abunda babba ya hango
yaro ko yahau rimi bazai hangoshiba.



kullum sai sunkusa raba dare suna waya da Safina sun maida abu kamar ibada shakuwarsu na
kara ninkuwa atare da juna koda Dr Safwan bai budi baki yayi mgana ba shikansa yasani
Safeena tana kokarin jan ragamar rayuwarsa agida ko office cikin waya suke kamar wasu
tantabaru😛acikin satin yace tasa ido yana tafe saboda shirye shiryen Tarewarta.


Kamar wanchan zuwan wannan ma tare da Tahir suka tafi Ranar Asabar wanda tun adaren da
Dr Safwan yafada mata suna tafe takasa zaune ta kasa Tsaye,gari na wayewa taje akamata
kitso dama tun adaren tasanyama kafarta sajen yayi ja sosai tana dawowa dama ta aikama
Aisha suka zage suka musu alalan hanta da lemon kankana wanda Safeena tahada shi da
hannunta,suna kammalawa suka share gidan suka gyara dakunan Safeena tashiga wanka
itakuma Aisha takoma gida ta shiryo.

Karfe 12 tamusu kofar gidansu Safeena wanda suna isowa yadaga waya Yakirata lokacin
tagama shiryawa cikin wata doguwar shadda light green taji aiki da Sallah Abbanta ya
dinkamata turaren ta Wanda Humrace kanwar Abbah inna husai ta aikomata dashi ta shafa tuni
tadau kamshi ba make up tayi ba hoda kadai ta shafa,sai liptick data sanya ammh ta fito ras da
ita fitowa tayi tana sanya hijabi tace"Ummi sun iso"Ummi dake dakin Abbah tace"To
Alhamdulillah...Ki shigo dasu".


Cikin takunta na natsuwa ta isa kofar gidan dukkansu suna jingine jikin motar Idanunta suka
fara sauka kan Haskenta Yau kam sanye yake cikin wani farin yadi mai stantsi da yarari yana da
ligo ligon zane a jikinshi ammh shara sharane domin hatta farar vest dinsa ana gani kafarsa
sanye cikin bakin buddaden takalmin na fatar damisa hannunsa sanye da agogo na kamfanin
rado,hularsa kansa kubece bakace idanunsa boye cikin gilashin dake karamasa kyau,cikin
mutuwar jiki yake kallonta itama shi take kallo kasa kasa tana jifanshi da mirmIshi Dr Tahir ne
yayi gyaran murya Yace"To mr and mrs love kunbarni atsaye fa"Da sauri Safeena tace"La...ya
Tahir yi hakuri barkanku da zuwa ku shigo"Tana fadar haka tajuyawa suka take mata baya da
sallama suka shiga cikin gidan Ummi ta fito tana amsawa zubewa sukayi suna kwasan gaisuwa
ta amsa cikin farin ciki tana tambayansu mutanen gida sukace suna gaishesu.



Daki suka shiga suka iske Safeena ta turare dakin da turaran wuta mai kamshin dadi ta
shimfida musu darduma a inda zasu zauna suka zauna Dr Tahir na fadin"Gamu akaro na biyu
amarya kuma insha Allahu na karshe"Da sauri ta dago tace"Na karshe kuma..?

Tafada da tashin hankali yar dariya yayi kan yace"Eh man daga wannan zuwa sai dai na zuwa
daukanki zuwa kaduna ko..?"Yafada yana kallonta da sauri ta rufe fuska tayi waje tana mirmishi
shukuwa Dr ba baka sai kunni domin duk inda Safeena tayi yana binta da ido ne yakasa mgana
saboda jiyake kamar yana wayo a gajimare saboda farinciki.



Daya bayan daya tajera musu komai agabansu Dr Tahir na mata tsiyan ta shirya likitan nata ci
ne dashi ta shirya mirmishi kawai tayi batace komai tabasu wuri su ci abinci kafin takoma tayi
mamaki taga yadda suka ci alalan lemon ma sun kusa shanyewa🤣



Dukawa tayi kana tafara gaishesu Tahir ya amsa yana ta mata tsiya itadai batacewa komai sai
mirmishi ana haka saiga Aisha ta shigo itama ta shirya cikin kayanta mai kyau Safeena ta

gabatar da ita a matsayin kawarta suka Gaisa da Dr kana Tahir har yana cewa"Shine taki zuwa
sai yau"Dariya tayi tace"Yau din aka gayyaceni"Harara safeena tazabgamata karaf a idanun Dr
Safwan wanda ya mata kuri da ido yana cizan lebe ai su tahir sai suka fahimci sukadaine ke
hirar Dr Safwan da Safeena hirarsu ta aikama juna sakonni ne ta idanunsu Dr Tahir ya mike
yana fadin"Kinga kawarmu zo mu fita tunkafin mara kunyar nan yabamu kunya"Aisha ta mike
tana fadin"Kwarai kuwa don itama ba kunyar ta isheta ba"mirmishi suka musu kafin su fice suna
fita Safwan ya maida hankalinsa kachokan kan Safeena itama tanaji tasan kallonta yakeyi
shiyasa taki dagowa ajiyar zaciya ya sauke tareda Numfashi da sauri tadago ta kalleshi yayi
saurin langwabar da kai yace"Shine ko dan sannu da zuwa ko..?"Yafada idanunsa kyar akanta
cikin sauri tace"la...Bana muku ba"Shima da saurin yace"NO...ke agarinku haka ake ma miji
oyoyo...?


Tadago tana kallonsa lokaci daya fadi tace cikin shagwaba"To yayane akeyi..?"Mirmishi yayi
yace"Gud girl bari kigani....Ya mike tsam ya isa gabanta yasanya hannu yadagota ya zaremata
hijabin jikinta yana karema kallo cikin sha"awa kafin Safeena tayi wani yunkuri yayi wuf ya
rumgumeta tsam akirjinsa yana fidda Numfashi sama sama hannunsa ya saka yazagaye
kugunta dashi ya matseta sosai hannunsa yadauko yakara azawa bisa hips dinta atare sukaja
Numfahi shiii!!!kamar suna shan yaji tuni Dr yaji wani abu na mai yawo tudun hip din Safeena
yagama rikitasa baisan sadda yake sanya hannu yana shafashi a hankali ba cikin kwarewa
itakuwa Safeena neman shidewa takeyi saboda Dr yazomata da wani al'amari mai girma wanda
kwakwalwarta baza ta iya dauka ba tafara mutsu mutsun kwace kanta dat why ya
sausautamata rikon yadago yana kallonta idanunta arufe ya kurama ma lips dinta ido dayake
wani maiko baisan sadda ya dora lebensa akai ba yafara wasa da harshenshi akan lebentakara
kamkame ido Safeena tayi tanajin wani abu na zirgamata sai da yagama lailaya lebenta kafin
yatura harshenshi cikin bakinta topha anan wasan ya fara wani irin sumbata ne mai tsaya aran
masoyi yake mata tare da shafa ko',ina na jikinta tabbas Dr yafara rasa control dinshi yafara
nishi sama sama ya neman turamata hannu cikin riga gashi tana tsoron ashigo agansu batasan
sadda ta fashe maida kuka ba jin kukanta yasa yayi saurin sakinta yakoma ya jingina da bango
yana sauke Numfashi idanunsa a rufe yace cikin murya kamar ta mara lpy"Shiii!iz ok bazan
kara ba"da sauri tasa hijabinta zuciyarta na bugawa yadade tsaye kafin ya koma ya zauna
abunda ta lura dashi jikinsa gabadaya yayi sanyi yadukar dakai kawai Safeena taji gabadaya
ranta ba dadi tayi sanadiyarta da mijinta yayi fushi da ita shiyasa tatashi a hankali ta isa kusa
dashi ta zauna kanta akasa tace"Don Allah Uncle kayi hakuri baran kara ba"dagowa yayi yana
kallonta idanunsa sunchanza kala mirmishi yamata kafin ya riko hannuta yace"Karki damu yan
matana dama nadade awannan yanayi kawai nidai fatane in kika tare bara ki dungamin rowa ba
ko..?


"Yafada yana kanne mata ido daya"saurin kauda kai tayi tana mirmishi yace"Common tashi kije
kifadama Ummi ina son mgana da ita tunda Abbah bayanan kuma sauri mukeyi yanzu zamu
koma",tayi lau da ido zata yi magana yayi saurin cewa "Yaushe kika fara gardama"da sauri ta
mike ta fice ta iske babu Tahir balle Aisha Ummi ke fadamata wai ta kaishi zaga gari rike baki

kawai tayi nan tafadama Ummi sakon Dr tako sanya hijabi ta shiga bayan sunkara gaisawa Dr
Safwa yace"Ummi dama mganar tarewar Safeena ce hajiya tace nan da sati biyu ina fatan babu
matsala..?"Ummi tace'Sati biyu safwan gaskiya yayi kadan...Ina laifi wata biyu kan lokacin
anfadama wanda yadace"mirmishi yayi yace"Duk don wannan ba mtsala sai a fadamusu yanzu
ko..?"Ummi tayi shuru kafin tace"A'a Safwan abarshi ahakan kawai"Dr yayi shuru kafin yayi
mirmishi yace"Ummi duk nagane meyasa kikace haka Safeena ko ba aure kanwatace nimai
mata komai ne na Aure saboda haka Ummi karku tada hankalinku Safeena kadai na aura ita
kuma zaku kaimun"Ummi tace"Ayi haka Safwan mahaifinta bazai yarda ba"Yace"Haba ummi in
hajiya taji bazata ji dadi ba zata ga kamar kun waretane"Ummi tace to shikenan ubangiji Allah
ya saka da aiheri yakuma bada zaman lpy,ya amsa da Amin.





Nan yayi sallama da Ummi kan tafito a waje suka hade da Safeena yacemata sauri sukeyi but
komai kenan zasuyi mgana ta waya Dr tahir kuwa sai da ya dinga kiransa kana yadawo safeena
tasha tsaraba kayan makeup dana makulashe ya siyo mata jibge da kudu 20k yabata itakuma
Aisha 5k yabata sun nuna bazasu amsa ba ranshi ya baci dole suka amsa wannan tafiyar ma
sai da Safeena tayi kwallah shima Dr dai sai ahankali karfe 4 suka mika hanya suna daga musu
hannu.



Koda Abbah yadawo yaji abunda Dr yace cewa yayi "bazai yuyu ba zainabu, saboda komai ba
sai saboda darajar yarmu zamuyi mata daidai karfinmu bazan janye lokacin dasuka sa ba
saboda dama kyan aure mace tatare gidan mijinta zan ma yan"uwana bayani akwai kudade
ahannuna kome suka yanke shikenan.
*****
Kaduna


Suna komawa yafara gyaran gida kuma har lokacin Sakina bata dawoba bai damu ba shiya
bashi ikon yin gyaran gidan a tsanake kamfanin MARHABA Suka zo suka chanza tsarin
dakunan bayan an shanza tsarin fentin, da kawatattun kayansu gabadaya sashen su dana su
momma sai da aka chanza komai falon nasu an kawatashine da black and red shima bedroom
dinshi an kawatashine da black and ash ita kuma Safeena pick and white na uwargida kuma
daman kalanta k kenan blue and purple sukuwa su momma an kawata musu ne da kalan black
and red ko'ina hakika gida yadau kyallin amarci kayan kaf habu da iliya yabamawa yace
sukaima iyalansa sunrasa bakin godiya saboda alherin megidansu agaresu mai girma ce.

Kudi ya damkama momy mahaifiyar Dr Tahir itama yar kasuwa ce 2million yace tahadomai
komai na bukatar aure na akwatin mace na Safeena kawai banda Sakeena ita kudi zai bata
saboda sanin halinta ita yar tsarice.



Haj.Mama abu nasu mganin akwabesu tab ta shirya tatafi Safana tagayyaci yan'uwa da abokan
arzuka na suzo su tayasu murnan tarewar matar jikanta sunyi sallama da iyami na sai sun hadu
in sunkawo amarya,hakika Dr ya gwangwaje safeena akwati takwas shake da kyan alfarma
momma da haj.Mama kowacce kala biyar biyar yayi musu bayan kayan abincin biki daya
jibgemusu hatta Adil ma ba'a barshi abaya ba Dr ya gwangwajesa.




Ana saura Sati daya aka shirya kai kaya ai haj.Mama tabuga lamara tace da ita za'a dole kuwa
akaje da ita sai matar kawu bala uwani sai momy sai wasu yan uwansu na Safana suka
dunguma sai Zurmi wanda Tahir ya kaisu hakika mutanen zurmin sunga inda ake abun arziki
domin kayan da'akawoma Safeena yazama abun yawo agari,su maman Aisha ne da matan
baffa isuhu da su iyami da kanwar Abbahsu inna husai data zo daga cikin zamfara sai makota
suka amshi kayan tare da kayan abinci buhu buhu na da kwalaye an amshesu cikin farinciki da
karramawa to daman anzama Daya kawai aka baje ana sa albarka Ummi sai da tayi kwallar
farinciki domin ko a mafarki bata taba zato ba.




Shikuwa Tahir gidansu Aisha ya Samu su Safeena ya basu sakon da yazo dashi kati na shaidar
gayyata guda dari sai kwalayen cimgam da minti guda goma da tsabar kudi dubu Hamsi yace
inji Dr in suna kuma bukatar wani abu samai mgana ta waya ai sunma kasa mgana saboda
mamaki illar kawai godiya,sai wajen bayan la'asar sukayi haramar komawa cike da kyan soye
soye irinsu dubulan cincin da alkaki cikin farin ciki aka rabu.




sunkoma suna bada lbrin karamcin mutanen zurmi wanda suka kasa boyewa ita kuwa Safeena
washegari inna husai ta tara ta suka wuce zamfara ita da Aisha domin ta gyarata sai dai tama
Dr text tafadamai dariya yayi yace"Allah ya kiyaye hanya ai ni za'a gyarawa mawa ko"..?Dariya
kawai tayi ta shareshi.

Tabbbas inna husai tadage da gyara yarta magunguna masu inganci irinsu kumbar da take sha
da nono da wanda akeci hakanan sai kayan fruit data hada mata sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login