Showing 42001 words to 45000 words out of 52374 words

Chapter 15 - NA TAFKA KUSKURE COMPLET BY JANAFNANCY-1.pdf

wa Nagani DR SAFWAN ne cikin wata rantsatsiyar farar shadda wacce tafito da
zatinsa da kyawunsa lokaci guda tareda murjewa irinta hutu yarinyar naga ya Nufa yana
cewa"Am srry yanmatan..Nayi latti ko..?"ai sake baki nayi kardai ace min wannan matar Dana
Gani tun dazu SaFeena ce ai bangama mamaki ba naji muryanta cikin wayewa tace"bbu
komai..Unku ina yarona"Yace"yanzu zamu biya mudaukosa daga islamiya"mirmishi tamai yana
budemata motar tashiga sai alokacin naga dan cikinta dayafara tasawa Araina na Furta masha
Allah.

Mkrantansu Adil suka biya suka daukosa wanda yadan kara girma da wayo kana suka nufi gida.



Bayan dawowar Safeena daga Asibiti bata sani ba ashe Safwan ya nemata gurbi karatu ajamiar
kadunar sai da ya kammallah komai kawaai yakawomata addimmision letter dinta da time table
dinsu na karatu taga zata karanci Nursing wayyo dadi Safeena sai da tayi kukan Farinciki taje
shashen su momma ta nuna musu tana murna haka takira su Ummi tana fadamusu suma sun
yi murna kwarai.



To daman lokaci yasanya adil wata mkaranta mai Suna command sch dake kaduna yakuma
sanyasa a islamiya shiyasa gari na wayewa dasungama abunda zasuyi sai su shirya yadaukesu
yafara kai Adil mkrnta kana ya biya ya kai Safeena mkranta ranar kuwa da bayanan direba ya

kaisu.


hakika Safeena na jin dadin karatunta sosai shiganta mkranta takara wayewa tasan me yadda
ake taraiyaran mji da kwalliya mai tsari da yabawa hakika Saferna tasamu chanji rayuwa mai
inganci ga dan cikanta wanda ke cikin wata hudu kenan yanzu.

















Commet
and
Share
Vote

*Janafty*
[10/14, 20:02] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..!*

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_�



*DEDICATED TO *My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*



*34*

"Kunya tareda Nauyi sun hana Sakeena zuwa tabawa Safwan hakuri duk da Hajiya kari ta
Matsamata taje tagwada sa'arta azahirin gaskiya dukkansu sunyi nadama kuma suna ta tuba ga
Allah hajiya karima tanemi gafaran yan"uwanta kuma sun yafemata ammh sunce basu da
hurumin dazasu roki Kwamishina yamaidata dakinta sai dai ta cigaba da addu'a Allah yasa
tsakaninsu akwai Sauran Zama



wuni yana shudewa kwana yana shudewa ahaka har watanni suka shude awannan lokaci
Safeena cikinta nada wata takwas aduniya tayi kiba cikin kuma yayi girma sosai kamar dan
wata tara gashi tana karatunta cikin nasara da jin dadi tareda taimakon mijinta kuma gwarzonta
Dr Safwan Sale Safana wanda duk abunda bata gane ba inta koma gida yana kara
koyamata,Shi da kantshi yakemata awo ammh shikanshi girman cikinta na bashi tsoro duk da
yamata scan kuma yaga komai lpy.


Su hajiya mama da momma kuwa rayuwa sabuwa domin yanzu basu dawani mtsala sukam
damar Sakinace damuwarsu kuma yanzu batanan shiyasa yanzu bakajin Hajiya mama na
kwakwazonta na fama sai dai in yan abun sun motsa kunsan mai hali bayasa Halinsa.





KANKIA


awannan watannin in ku ka ga yadda su Sakina suka koma sai kun zubar musu da kwallah
saboda yadda suka rame suka kammajame sakina fuska tayi baki ta kuma cika da kuraje ga
kan nan yayi duku duku kamar na mahaukaciya kumbuna sun yi baki sunyi datti hajiya kari
kuwa kamar tsohuwa takoma saboda wahala.



Yau tunsafe Sakina taje layin bowol ammh sai wurin takwas tasamu zuba ruwanta tadauko daya
akanta daya yana hannunta tana tafiya zata gida taji ana mata hon abaya kaucewa tayi domim
bata zata da ita ake ba sai da motar tazo daf da ita kana ta tsaya cikin mamaki take bin jeep din
da kallo kafin taga anbude murfin mota anfito wazata gani...Daddy ta furta cikin mamaki ya
amsa da "Na'am sakina kece kika koma haka "yafada idaninsa sunkawo ruwa zatayi mgana
kenan wata farar mata ta bude mota ta fito sanye cikin leshi da mayafinta bawata babba bace
bata wuce sa'ar Anty salma ba.

Ta nufe sakina cikin tsausayawa tana fadin"Innalillahi...Sweety badai dota Sakina bace
wannan..?"Kwamishina yagyda mata ta yi saurin saukemata ruwan ta rumgumeta tana
fadin"Baka kyauta ba Sweet hrt kowa yana kuskure ko Allah muna masa laifi yayafemana
ko"baicemata komai ba sai ma cema direba yayi su karisa.

Sakina sai kallan matan take datake rike da hannunta har cikin gida ai sakina sai ta shiga
kwalama Hajiya kari kira tana fitowa Daidai kwamishina yana shigowa ai sai tayi cak tana
kallonsa shima ita yake kallo yana nuna ta da mamaki hawaye ya zuraroma Hajiya kari sai ta
koma daki da gudu tana kuka...dakin matan tabita tana rike da sakina.

Hajiya kari dake durkushe tana kuka tadafa tadago tana kallonta murmishi ta sakarmata kafin
tace"Don Allah kibar kukan nan hakanan ko Allah muna masa laifi yayafema na balle mu
mutane"Hajiya kari tace cikin kuka wacece ke!...MATATA CE....dana aura bayan
Rabuwarmu...atare sakina da hajiya kari suka kara kallonta itakuma tana musu mirmishi.Dady
Yafadi haka bayan ya sawo kanshi dakin yakarasa shigowa yana fadin"Bayan na koreku kwana
biyu kawai na kara nabar kasar sai da nayi wata uku baninan karkuyi mamaki duk halin dakuke
ciki inada lbr...Dagacham saudayi na wuce achan na hadu da Mariyatul kibdiyya wacce asalinta
yar gombe ce tayi aure mijinta ya rasu ammh bata taba haihuwa ba mahaifinta shine wazirin
masarautar gombe munyi aure wata hudu da suka wuce daman nafadamata yayana hudu shine
da bata ganki ba ta tambayeni nikuma na fadamata komai wlh tallahi tunda na fadamata ta kasa
sukuni akan lalle Saina yafemuku kuma saina zo mun dauko ku.....mu koma gida.




Sakina tafada cikin rawan murya"mu Dady...Kayafemana mu koma gida harda Hajiya"Dady
yace"kwarai ma Sakina tare zamu koma domin tun jiya da asuba na sanya aka maida
aurenmu....Da mahaifiyarku nasan ko ahaka na barku kun fahimci rayuwar danike
gayamuku"Sakina ta guce da kuka kan zube gaban daddy tana kara basa hakuri dagota yayi ya
sharemata hawaye yace"ba'a san raina na muku haka ba wlh sai dan ku gyaru kuma ku gane
yadda Rayuwa tasa gaba,sakina tace"Ba komai daddy hakika kaci ka uba nagari...Wlh ko
ahaka nagane daddy nagane mutum ba komai bane.


gurin Mariya taje ta durkusa tana fadin"mungode Anty hakika bamu da bakin gode miki Allah ya
saka miki Aljannah"kamota tayi ta rumgumeta tana fadin",babu komai yata...Karki damu inaji
kamar nina haifeki Sakina.Mirmishi sukama juna lokaci daya kan taja hannunta suka fice.

Hajiya kari takasa dagowa ta kalli kwamishina saboda kunya shine yayi gyaran murya
yace"Basai kin ce komai ba karima Allah yayafemana gabadaya.."Tadago idanunta jawur
tace"Ban chanchanci yafiyarka ba kabiru wlh ban chanchanci yafiyarka ba sam"takareshe fada
da kuka takawa yayi ya isa gareta yadagota yana sharemata hawaye yace"ko alama karima duk
nasan kin min abubuwa masu yawa ammh tunda kingane kuranki wlh har ga raina na yafemiki
kuma nasa anmaida auranmu..da zuciya daya sai dai bansani ba ko zaki iya zama da
kishiya"da sauri Hajiya kari tace"wane ni daja da abunda Allah ya halarta...Ai samun abokiyar
zama irin mariya sai an tona...Ngd sosai Allah yakara girma.Mirmishi ya sakarmata yana kara
gogemata hawaye.



nan suka wuni har su yayyen hajiyan suka dawo sukayi mgana da kwamishina yasaukemusu
kayan abincin dayazo dashi sukuwa su sakina yace kada su dau komai aikuwa murna gurinsu
ba'a mgana dazasu tafi suka roki gafarar kowa suma mutan gidan suna neman tasu ankara
musu fada kan sundai ga rayuwa inzasu natsu yarage nasu,gidansu kwamishina suka biya
suma chan din albarka sukaita sanyawa musu har suka tafi.


Amota mariya babu ruwanta sai jan Hajiya take da hira ita da Sakina su kuwa sunkasa sakin
jikinsu da ita itakuwa ko ajinkinta sai jansu take ajiki.



Suna komawa takai Sakina har daki ta hadamata ruwan wanka tadauko mata wata doguwar
riga ta ijiyemata hakama tama Hajiya kari wacce kunya ya hanata mgana bayan shiganta
wankane hawaye ya zuraromata wai yau itada take iko da gidanta sai gashi yau watace ke iko
dashi...Ba shakkah duk wanda bai godema Allah da Ni'imar sa ba zai godema wuyarsa.

Ita tai ta dawainiya dasu suna godemata kayanta ta daukoma hajiya kari kafin gobe aje asiyama
su nasu kayan.


Allahu akbar Sakina da Hajiya dasuka sa hakarkarunsiu akan katifa suka furta domin ko
amafarki basu taba tsammanin zasu dawo rayuwarsu ta baya ba..Koda gari ya waye hakanne
yafaru a dining suka ci abinci tun basu sakin jikinsu har dai suka fara sakewa da ita.



Kwanan su biyu dawowa komai yafara zama normal tuni an musi sabbi dinkuna abunsu hajiya
kari tazama wata so cool da ita kamar ba itaba itakuwa Sakina Anty na iya bakin kokarinta na
ganin ta saki jinkinta,washegari sai ga Laila tazo gidan tana ba su Sakina hakuri na rashin

zuwanta kankia Sakina ta mata dariya kawai tace"Anty laila kenam bbu komai Rayuwar
kenan...Sai kuma naji ance ya mujaheed yayi aure"tace"eh...Wlh wata biyu dasuka
wuce"Sakina tace"to meyasa kika yarda"tazaro ido tace"so kike in tada hankali nima ya sake ni
ko"Sakina ta kalleta hawaye ya ciko idanunta tace"oh..Ammh ni kikace in tada hankalina ashe
kinsan Safwan zai iya sakina in namai abunda kikace kenan ko"Shuru Laila ta mata mikewa
Sakina tayi tace"basai kinyi mgana ba nagane komai domin ni yanzu ashafin rayuwa ba abunda
bangani ba"da sauri Laila tasha gabanta tana fadin"kiyi hakuri yar'uwata nima nasan sam ban
kyautaba amtsayina na yayarki....Ki yafemin don Allah"Kallonta sakina tayi kan tace'shikenan
bbu komai...Harda haihuwar dakikasa na dakatar duk na yafemiki duk da ke kinata haihuwa
kamar naga ga wani karuwar nan mun samu"tana gama fadar haka ta fice tana sharan
kwallah,hajiya kari dake gefe tace'Mumaka sa sakina ta tafka kuskure mune sila wlh"Anty laila
tace"Allah ya yafemana....Ammh tadade tana saka mganar sakina tasan mgana ta saka mata.




Asatin Anty salma tazo ita da Ummi daman tana hannunta tuni tayi murna matuka kuma ta kara
musu fada sosai lalle ta yarda duniya tahora hajiya koda yarda tayi sanyi Anty mariya tana ta
fadin"Yaya kaza,yaya kaza...Hajiya na amsawa da kulawa...Zamansu gwanin sha'awa kamar ba
kishiyoyi ba,Anty kwananta biyu takoma ammh kafin takoma sai da tace ta shirya taje har gida
ta ba Dr hakuri ko ya maidata dakinta tabbas tayi na'am da shawararta shiyasa washegari nayi
ta shirya cikin dogon hijabinta har kasa Anty mariya ta aramata motarta tamusu sallama ta fice
suna mata fatan sa'a.




Cikin sanyi jiki ta dumfari gidansu Safwan lokacin da Habu mai gadi ya budemata get bai
ganeta ba sai da ta paka motar ta fito tana gaisheshi take tambayansa ko Safwan yana gida,ya
amsa mata da "eh...Yana nan hajiya mirmishi ta mai kawai tace"Sakina sunana ba hajiya ba"Ai
sake baki yayi yana kallonta kan yace"Au...Sak...Oh hajiya barka da zuwa"wucewa kawai tayi ta
barsa sake da baki har yana kara lekata.



Shashen su momma ta nufa ta shiga da sallamarta wanda Hajiya mama ke zaune afalon ta
amsa tana fadin"Maraba shigo......

Commet
And
Share.
Vote




*Shakira..*
[10/14, 20:02] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE...!*

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty�_

*Dedicated to my momma Hajja khadija muhammd Ba'are*




*35*



"Karisawa tayi cikin falo tasamu gefen hajiya ta zauna kallonta hajiya mama keyi ranta na bata
kamar sakina ammh kuma tana karyatawa Sakina tadago ta kalli hajiya kan tace"Hajiya baki
ganeni bako..?


.Hajiya mama tace"eh...Kiyi hakuri ban sheda ki ba yan"nan"Mirmishin takaichi Sakina tayi kan
tace idanunta na tara kwallah"Sakina ce fa Hajiya"Ai da Hanzari tamike tana salati da karfi ta
furta"Sakina...Nashiga uku ni Maryamu Sakina ciwo kikayi naga kin lalace haka"Fashewa da
kuka tayi tana Fadin"wlh hajiya nagani kuma nagane koda kika samin tsama sona kike...Don
girman Allah Hajiya ki yafemin'Hajiya ta karisa kusa da sakina tadagota tana fadin"Mekika min
Sakina wlh bakimin komai ba duk abunda kikaga ina miki don ki gyaru ne...Allah yayafemana
gabadaya"Rumgumeta Sakina tayi tana godiya cikin kuka momma dake tsaye tundazu ta kariso

tana cewa"Tabbas baki mana komai Sakina har yanzu kallon ya'muke miki"Sakin Hajiya tayi kan
ta isa gaban momma ta durkusa tana fadin"Momma...Ban chanchanta kiyi afuwa agareni ba
ammh gani durkushe agabanki kiyi duba ga Allah ki gafartamin wlh na tuba nabi Allah baran
kara ba nagane kune masoyana na gaskiya"Momma tadagota tana sharemata hawaye tace"Har
Abada ban chanzaki ba sakina ki na nan amatsayin yata ta har abada...Karki damu daman baki
man komai Allah yayafemana gabadayanmu"Rumgume momma tayi tana Fadin"Nagode
momma Allah yakara girma.


Kan kujera suka karisa nan Sakina tabasu lbrinta tun bayan sakin da Safwan ya mata Hajiya
mama tace"Allah sarki kabiru hakika ya jarabtu sai dai mu fatan Allah ya kara shiryar
damu"Suka amsa Da Amin.


Adil ne ya shigo da gudu yadane cinyar hajiya mama yana Fadin"Hajiyata...Turesa tayi tana
fadin"A'a Alhajine...Kai wai bana ce ka kiyayeni ba"Tura baki yayi yatashi ya isa ga momma ya
haye cinyarta yace"Bani chonki...Momma nake cho"Yafada yana rumgumeta Hajiya mama
tace"To sai me...Aikin banza chan da tsiyarka ni nan har akwai soyayyar data kai na marigayi
Habule na nane wallahi bata"Tafada harda jaddadawa.


Sakina dake gefe tana kallonsu ta share hawaye tana kallon Adil dayakara girma da wayo ga
yayi kiba abunshi alamun yana Samun kwanciyar Hankali abun takaichi wao ace danta na
cikinta ma baisanta saboda wani sakarci nata...Hannu tasa ta share hawayen daya zubomata
kada su hajiya su gani ammh ina sun riga sun ganta.

Sallamar Safwan shi ya dakatar da dramar dake tsakanin Hajiya da Adil Tafe yake shida
Safeena dake sanye da doguwar riga baka ta sanya mayafi ya rufema cikin jikinta wanda
yakusa rinjayarta saboda girmasa kanta na gefen kafadarshi shima ya zagayo hannnsa ta
kugunta yana Sanye cikin bakar jallabiya tunda suka shigo Sakina tayi galala tana binsu da
kallo ganin yadda suka chanza cikin lokaci kankani Dr Safwan yayi kiba ya murje yakara haske
itama Safeenar,tunda suka shigo momma da Hajiya suka mike suna ma Safeena Sannu shiya
taimaka mata ta zauna akasa yana mata Sannu Safwan yace"Momma...Wlh zan dawo muku da
Adil damun yanmatana yake d kiriniya wai harda goyasa yakecewa ayi fa"Hajiya mama ta
dunguremasa kai tace"kaga min mugu...Don ubanka da uban cikin da ubanka yamata zataji
kokuwa da goyaka"😂kunya takama Safeena da momma shiko Safwan ko ajikinsa Tabe baki
yayi zai fashe dakuka tace"Kaji gidanku wlh kanamin kuka zaneka zanyi ja'iri kawai"Kuka yasa
yatafi da gudu gun momma yarumgumeta Safeena tace'Amana hakuri Hajiya kin manta yace
zai Siya miki jirgi"Hajiya tace"Bani so Raggo kawai'dagowa yayi hawaye shabe shabe yace"Ba
chan chiyanmiki jigi ba Daddy da mami na jan chiyama wa...Kuma baja ki hau ba"Yafada harda
murguda mata baki dariya sukasa mishi gabadaya.

Safwan yadago yana dariya kawai caraf idanunsa suka sauka kan Sakina dake zaune gefe tana
ZUBAR KWALLAH...Aziza idiris gombe...Bana gajiya da Novel dinnan walle....Kuramata ido
yayi cikin mamaki da firgici kamar fa Sakina yake gani ganin inda yake kallo yasa suka bi gun
da kallo Safeena takurama Sakina ido tana kallonta Aranta tana so tace Anty ammh wata
zuciyar tana cewa ba ita bace"Sakina tayi saurin mikewa tana fadin"Momma..Zan tafi dama
nazo gaishekune"Tafada tanayi hanyar waje...SAKINA..Dr Safwan ya furta da mamaki cak ta
tsaya ranta na mata kuna Hajiya mama tace"kwarai...Tun dazu tazo neman gafararmu"Kai
tsaye yace"kuma kuka yafemata"Juyowa tayi cikin kuka tace"Daman nasan ban chanchanci
yafiyarku ba...Safwan"Tafada kuka yaci karfinta baya ya juyamata kawai ransa namasa kuna
rarrafawa tayi ta isa zuwa gabansa tana fadin'Na san ban chanchanta ka kalleni ba Safwan
ammh kadubi darajar Allah kadubeni da idon Rahama kayafemi ko naga daidai Rayuwata"shuru
yamata Safeena ta mike dakyar ta isa kusa da Sakina ta durkusa tarike hannunta dagowa tayi
tana kallonta ita kuma ta mata mirmishi kallonsa tayi tace"UNcle....Saurin jiyowa yayi yana
kallonta kan yayi saurin cewa"Ke kina da hankali kuwa bakiga halin dakike ciki ba...Tashi
tashi.."Kin tashi tayi saima cewa datayi'Kazama mai yafiya unku...Kaima sai Allah yadubeka da
idon Rahama...Anty tayi kuskure kuma tagane kuskurenta Don Allah kabata dama baxata sake
ba"Shuru yayi kan yace"ki tashi nace itama kallon idanunsa tayi tace"Bazan tashiba sai ka furta
ka yafemata"kallonta shima yakeyi kan yayi ajiyar zuciya yace'Taji albarkacinki....na yafemata
Allah ya yafemana gabadaya"Alhamdulillah...Haka cikakken musulmi yake"Hajiya mama ta
furta.


Sakina tasa hannu tadago Safeena ta rike hannunta tana fadin"Bansan mezan cemiki ba
Safeena...Ban sani ba'Tafada idanunta na kawo ruwa"Safeena ta damke hannunta tace"Basai
kin ce komai ba Antyna wlh kin wuce haka agurina ammh alfarma nake nema agunki"Sakina
tace"Ki fadi komiye safeena indai baifi karfina ba zan miki shi Safeena"kai tsaye Tafada tana
kallon Dr Safwan"Ki dawo kizo mu zauna mu reni ya'yanmu tare kuma mu rumgumi
mijinmu...Mu zauna har Abada"Kallon kallon aka hau tsakanin Dr Safwan da Sakina saurin
sadda kai yayi yace"A'a.....Safeena tayi gaskiya ka maidata dakinta ku taru ku rufama juna
asiri...Ku zauna lafiya da juna"Hajiya mama tace"shikenan kuwa...Allah yayi miki albarka
Safeena Allah ya rabaki da cikin jikin ki lpy"gabadayansu suka amsa Da Amin.


Rumgumeta Sakina tayi tana kuka tana mata godiya safeena tadagota tana sharemata hawaye
tace"Kidaina godemin Anty kin wuce komai agurina"Itama sai hawaye sharr Adil ne yaga suna
hawaye duka biyun zuwa yayi ya rike ma Safeena hannu yana Fadin"Mami...wacece
wannan.."yafada yana Nuna Sakina shafa kansa tayi kan tace"UMMINKANE...Itace
mahaifiyarka"Kallonta yayi yace yana kallon Sakina"UMMI.....Yafada still yana kallonta sakina ta
rumgumesa tana hawaye tace"Ni Umminkane ta haihu Ammh Mami mahaifiyarkace ta har
abada"Tafada tana shafa kansa abun mamaki shima rumgumeta yayi yana sharemata hawaye.

_Allah sarki Uwa Uwa ce komai lalacewarta_




Komai ya daidaita cikin lokaci kankani Sakina nan ta wuni tana dawainiya da Safeena da Adil ita
tataya momma Aikin girkin dare sai da suka kammallah kunsan Raba dare sukai suna hira kafin
safeena ta barota cikin dakinta takoma gun Dr Sakina tayi kuka awannan daren na ganinta
kwance kan gadon tabata tsinana komai ba sai lalacewa...Raba dare tayi da ibada da asuban
fari tatashi kokan Su Safena su fito Sakina ta tsaftace gida ta hada musu break kwai ta soya
musiu da ruwan tea suna karyawa DR yayi harama abun mamaki har Adil na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login