Showing 45001 words to 48000 words out of 52374 words

Chapter 16 - NA TAFKA KUSKURE COMPLET BY JANAFNANCY-1.pdf

zarin shi zai bita
lallabasa sukai suka shiga mota suka kaisa mkranta kana suka biya suka ijiye Safeena asch
tana da test tai musu fatan dawowa lpy,suka kama hanya shida Sakina direba yana binsu abaya
da motar data zo dashi,Shizai kaita saboda mganar Maida aurensu.


Hakika kwamishina yayi murnan dawowar Safwan amtsayin sirikinsa a kashi na biyu...Hajiya
kari saboda godiya harda kuka tarokesa gafara kuma tace ya rokan mata su Momma kan
tazo...Anta dawainiya dashi an fahimci juna sosai cikin mutumci da girmama juna sai la'asar
yayi shirin tafiya rako sa tayi gun motarsa kallonta yakeyi bako kiftawa Kauda ido tayi kan
tace"Wannan...Kallon fa"mirmishi yayi yana Shiga mota yace"Mamaki nake wai Ke Sakina kabir
kankia ce kika zama ustaziya"Dariya tace"Ka adana mamakinka sai Auren ya maidu
tukunnah..."Tafada tana rufemasa murfin mota kallonta yayi yace"Sure....Gyada kanta tayi
kawai dagamasa hannu tayi har yafice daga gidan.














commet
And
Share
Vote.

*Anitha...*
[10/14, 20:02] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE...!*

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_�


*36*

Shirye shirye takowani bangare ya kamkama Tahir dayaci lbrin komai shima kansa yayi
mamaki ammh kuma mamakinsa ya gushe domin tare suka koma kt shida Safwan jin shirye
shiryen da take gudanarwa abun mamaki Sakina tace bata dawani shiri itakanta walima ce
kuma sunyi mgana da Safeena ranar asabar za"a shirya ma'ana bayan ta taren.
Ranar jumma"a Daddy shi yazo kaduna bayan sallar jumma'a amasallachin sultan bello aka
maida aurensu akan sadaki dubu talati,kuma ana gama daura auran Tahir ya wuce yaje ya taho
da',ita domin daddy yace kada wacce taje Anty salma dama bata samu zuwa ba Anty lailace
tazo itama kuma Daddy yace gobe takoma gidanta,Anty mariyace kadai tarakata bayan tarin
masihohin data sha gakuma gyaran da Antyn nata ta zage ta Mata.

itakanta Anty mariyan bata jima ba ta musu sallama Daddy ya zo suka wuce...Suka barta nan
shashen momma ita dasu Safeena da Adil wanda ke yaketa tsalle Sakina tadawo gidansu bbu
wani gyaran da Safwan yayi ma gidan sakamakon yana chan yana kera musu wani gidan a
Malali Gra katon gidane sama da kasa shima din bangare biyu yayi musu ammh shi wannan din
wlh duniyace ko su hajiya basusan da gidan ba Shida Tahir ne kadai suka Sani.

Sakina Da Safeena sai da Dr Safwan yadawo su hajiya suka tarasu suka musu Nasiha kan su
hada kansu su zauna lpy,sai wajen 9 na dare suka Nufi shashensu achan din ma dumguma
sukayi dakin Sakina suna hira Safwan duk sanda ya kalli Safeena ransa kara fari yake domin
komai yake faruwa ayu wlh itace sillar daidaituwan komai...sai da taga Dare yayi kana ta musu
sallama Safwan yadaukan mata Adil dayayi barci yarakata daki wanda Sakina tace ta yafe yaje
gun Safeena ya kwana tunda ita tana da lalura...Kin yarda Safeena tayi shiyasa yana kwantar
da Adil  tashige bayi tana fadin"Unku mu kwana lpy...girgiza kai kawai yayi yawuce saboda
yasan da gangan tashige bayin don karya mata wani mgana ne.

dakinsa ya koma yayi wanka ya sanya jallabiya yafeshe jikinsa da body spry masu kamshi kan
ya nufi dakin Sakina da Sallama ya shiga ta amsa tana ninke darduma kallonta yayi kan
yace"Me kikayi...?Tace"sallar issha'i...Yace'ok...Koma muyi sallah don yau ta dabam ce you
know...Mirmishi tamai kawai yajagorancesu sukayi Ra'ka"a hudu yadade yana musu addu'a
kafin su kammallah yasan Sakina nada rauni a addini dat why yai mata alkwarin koyar da ita
Insha Allahu.

Tabbas Daren na Alkhairi ne domin Safwan da Sakina sun darji juna iya son ransu an famshe
watannin da'aka diba ba'a tare...Tun asuba sakina bata koma ba tahau gyaran gida tana
kammallawa takoma kichen doya ta soya musu da kwai sai ruwan tea domin dai girkin ba wani
iyawa tayi ba wannan ba don komawarta ne take gani gun Anty mariya yasa ma ta iya wasu
Abun.

Hakika zamansu yana gudana cikin kwanciyar hankali da zaman lpy duk da Sakina na iya bakin
kokarinta yanzu ammh duk da hakan tasani kuma tana gani safeena tanada wani mtsayi agidan
wanda daga Safwan har su momma girmamata sukeyi...Tasani ita tabar damanta har wata ta
kwace sai dai kawai tayi yar hawayenta ta share,kwana uku yabar dakinta bisa na al'ada
yakoma suna kwana daya akowani daki.

Bai bafada musu mganar sabon gida ba saida ya bari weekend kana yace kowa ya shirya za'a
fita hardasu momma mota biyu sukayi safwan na tuka su momma da hajiya sai Tahir ya tukasu
Safeena basu gama mamaki ba sai da suka gansu a wani makeken gida upstair kamar kasar
turai ba kai tsayawa bada lbrin wannan gidama kauyancine sai dayagama zagayawa dasu
ko'ina na gidan yaji alatun kayan more rayuwa gida dai wallahi ko akasar turai.

Sai da suka koma gida ya tarasu yafada musu cewa achan zasu koma dukkansu bayan
haihuwar Safeena kwarai da gaske sunyi murna ammh sai Hajiya mama tace"Hakika naji dadi
safiyanu kuma muna maka murna ammh zahirin gaskiya nida Hadiza bazamu biku ba domin
me muke nema arayuwa komai kagama yimashi sai muyi ta maka addu"a da fatan dacewa
muna nan gidan ya ishemu jin dadin rayuwa ko yi komawarku chan kai da matanka Allah in
kunsamu lokaci kwa leko agaisa"Babu yadda sukayi iya domin Hajiya mama da ce wlh baza
koma chan ba dole aka barshi ahakan.

yau Sakina keda sati uku da tarewa misalin karfe goma da wani abu na dare barowansu kenan
itada Safwan daga dakin Safeena safwan yana bayi itakuma tafito falo daukan wayanta sai
kawai taji nishi kuma daga dakin Safeena abun ke fitowa ai da gudu ta shiga dakin ta isketa
durkushe tana nishi gashi wani ruwa na biyota ai A sitti takoma daki tana kwalama Safwan kira
fitowarsa kenan daga wanka da sauri yazira jallabiya suka rankaya Suna zuwa kofar dakin
sukaji kukan jariri ai da gudu suna bugan kafadar juna suka antaya dakin shigansu yayi dai dai
da sawo kan dawani jinjirin yayi da sauri Safwan yasa hannu ya jawoshi Safeena takoma ta
kwanta tana maida Numfashi cikin farin ciki Sakina tadauki dayan tana fadin"Alhamdulillah Ala
kulli Halin Safwan yan biyu ne Safeena ta haifa shima bakinshi yaki rufuwa Safeena kawai yake
jerawa sannu harda hawaye da jinin da komai yahada da yayan ya rumgume yana zubamata
godiya sakina sai da tayi kwallah tana tuna da itama yamzu Safwan zai ma wannan rawan jikin.

cikin lokaci kankani suka gyara komai Safwan ya yankema yara cibi itakuma Sakina tagyara
wurin safwan dakanshi yadauki Safeena sai toilet yahadamata ruwan wanka yahau gasata
yabarta ciki saboda taji dadin jikinta,komawa yayi shida Sakina suka zage suka wanke yaran
tas suka sanya musu kaya suka jerasu kan gado suna kallo,safeena na fitowa suna rigen rigen
mata Sannu sakina tahadomata shayi mai kwauri tasha ...Kai in takaice muku nan suka kwana

suna dawainiya da Safeena sai da Safe da Safwan yadawo sallar asuba yashiga yake fadama
su momma safeena ta haihu cikin farinciki suka dumguma kan kace kwabo haihuwar Safeena
tazagaya dangi shida kanshi suka tafi asibiti yaduba da ita da yaran ya tabbatar da komai
normal kana suka dawo,mutane sai zuwa barka suke da ganin yara masu kama da ubansu
akuma haihuwarne hajiya kari da Anty mariya suka zo harda kwamishina da kayan arziki iri
Sunkoma washegari sai ga Anty laila itama harda amaryan da'a mata sunzo barka suna da
abun arzikinsu hakika safwan da su hajiya sunji dadi sunkuma yarda yanzu za'ayi zumunchi mai
tsafta sakina kuwa Allah kadai zai biyata domin tadaukema su momma hidima ita ke komai na
gidan ga dawainiyar mai jagejage Safeena tayi alkwari yadda Sakina take kokarin farantamata
ita sai ta faranta mata shikanshi Safwan tun bai sakin jiki da ita har yafara domin alkhairan
Sakina yadakushe sharrinta na baya,shikuwa Adil kuka yake dayaga Safeena da dauki yaran
sai yahau kuka wai a ijiyesu adaukesa sai Safeena ta mika sakina su tajawoshi ta rumgume
tace ya'yanta gaka ma nabata abunta akai kadaine dana ko"sai yahau murna yace"Mami ai
ya'yan Ummi ne ko ta gyadamai kai shikuma yana dariya.

Sai ana gobe suna suka samu damar komawa sabon gidansu tareda rakiyar yan"uwa da
abokan arziki ciki harda Aisha kawar Safeena da inna husai harda maman Aisha da matan
kawu isuhu momma da hajiya sun rakasu suma komai yaji baanda tsiya kowa yaga gidan sai
dai kaji ya furta masha Allahu dare nayi su momma suka koma gida su koma akabarsu nan da
masu shagalin suna.

Su suka zauna akasa mai dauke da falo guda biyu da manyan dakuna guda hudu kowanne
yana dauke da falo da toilet sakina ta dau daya safeena ta dau dayan sauran biyun kuma daya
aka barma baki dayan kuma ba'a budesu ba


Commet
Share
Vote




*Shakira...*
[10/14, 20:02] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..!*

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_�



*DEDICATED TO:My Mommah Hajja Hadiza muhammed Ba"are*

*37*


"Hakika taro yayi taro domin yan'uwa da abokan arzuka sun hallata bbu laifi Safwan yabaza
bajintarsa awannan haihuwar domin sa guda yagada bayan ragunan da'aikata yankawa abun
sai wanda yagani.Safeena shiga kawai take tana cirewa domin akwatu guda Safwan yayimata
na fitan suna ita da babies sakina ma kala biyar yamata itama na fitar Sunan,baki sunzo tako
ina har hajiya kari sai tazo itada Anty mariya wanda suka zo da abun arzikinsu niki niki kafin su
wuce gidansu momma don suma achan suke nasu taron.



odar abinci kuwa Restaurant uku suka zo domin bawa jama"a abincin da sukeso,aikuwa anci
ansha harda masu guziri baki tako'ina sunzo ciki harda Yan Janaf fans,Hibbatullah fans,yarima
suhail fans1&2 da Na tafka kuskure fans,da yan kungiyata Interlligent writers suma sunzo
wannan wurin my Anty sis Naja'atu anci harda guziri ajaka my leema ma har ariga su Sahiba
kuwa anci kamar za"ayi amai bai isheta ba leda guda tasamu tana guziri,Anty sainah,Anty
hafsat,mummy zil,maman kausar,kuwa bayan angama nadan na gidan Dr ai suna ganin mota
zata koma gidan Hajiya mama suka shige suna Fadin bari suje suga kuma wata wainar ake
soyawa achan kuma....Oh ni jami,Yan sch dinsu wato yan faculty su sunmata kara domin
kwansu da karkwatansu su hallarta.





Anrarraba abubuwa irinsu Robobi botikai dinnerset kofuna da jakukkuna masu dauke da
hotunan yaran wa"inda sukaci Sunan Hajiya mama da mijinta wato MARYAM SAFWAN SALE
DA ABUBAKAR SAFWAN SALE...Hakika Safwan ya farantama Hajiyamama rai wanda
farincikinta yaki boyuwa kwatakwata harda kwallanta saboda murna.



Sakina itace kan komai domin tazage ana hidima da ita Anty laila tazo suna ita da amaryanta
itama suna zaman lpy abunsu basu kwana ba suka koma Sakina tasani cewa ta tafka kuskure
tun abaya domin fadar data ke dashi ada ayanzu banata bane domin safina tarigaya data
kamkame ko"ina Dr baya ganin kowa agabansa sai Safeena itadai kawai yana rakatane...Wani
lokacin in abun yadameta sai dai tashige daki taita kuka ita kadai gashi kwanakin nan tana ta
zubar jini tun abun nazuwa kadan har yafara yawa ada tazata period ne ammh daga baya tasan

abun ya wuce haka.





Anyi suna lpy an tashi lpy bakin Safana da na zurmi hardama na zamfara sunkoma gidajensu
Aisha ce kadai bata wuce ba wai Saita kara kwana biyu...dariya kawai Safeena ta mata kan ta
ce"munafuka wlh nasan meya tsaidake"Sakina ce tace"Ai Tahir wlh sai ya gundireki ne"Aisha
tace"Daman masoyi na gudinran masoyinshi ne"Dariya suka mata gabadaya.Tabbas soyayyah
mai zafi ta kulli tsakanin Dr Tahir da Aisha wanda suka sha tsiya gun Safeena da Sakina yan
tagwayen Dr.




Inna zulai kanwatake ga Mallam Aliyu ita akabarma Safeena tana kula da ita Sakina ma ba'a
barta abaya ba tana iya bakin kokarinta wurin taimakawa domin in Safeena tatafi mkranta ita da
inna zulai suke wahala da yaran....Su momma kuwa kullum kwanan duniya in Safwan zai fita
aiki sai ya biya haka kuma inyadawo su Safeena kuwa indai basu dawani abu da zasuyi to haka
zasu saka yayan amota su kaima su momma wanda Hajiya mama tahana achanza musu suna
ana kiransu da Hajiya da Justice.






Babu wanda yataba lura da halin Da Sakina ke ciki sai Ranar da Safe weekend ne Safwan yana
Dakin Sakina yana kwance tundazu tashiga bayi ammh yajita shuru tashi yayi tsam ya bita
abunda yaganine yasa shi daskasrewa sakina ke tsungunne cikin bath jini yana zuba guda
guda Da Sauri Safwan yace"Sakina....Meye haka kuma jini nagani"Kallonsa tayi idanunta
sunkawo kwallah tace"Bansani ba Dr bansani ba wlh"Tafada tana bayyanan da Rauninta
kallonta yayi kan yace"Tun yaushe kika fara bleeding din"Sanda kai tayi tace"Bansani ba ammh
tun haihuwar Safeena ne".....What...Kina haukane Sakina ace kina zubar jini almost 4weeks
ammh kika kasa mgana what wrong wit u ne"Yafada ahasale sakina ta fashe da kuka tace"kayi
hakuri naji tsorone..."Juyawa yayi yana Fadin"Ki shirya muje asibiti kawai malama"Yafada yana
wucewa sulalewa tayi tana zubar kwallah domin ta tsorata daganin yanayin da Dr ya shiga.




Shiko dakin Safeena ya shiga yake Fadamata salati ta saka har inna zulai taji ta fito shine

Safeena take Fadamata ita fadan ta hau Sakina dashi tana cewa"Haba Sakeena wannan ai
sakarcine kina ganin halin dakike ciki ammh ki kasa mgana keda kike da likita agida....Haba don
Allah karki kara Sakarcin nan"Gyada kai kawai tayi tana hawaye har bakin mota suka rakasu
suna daga musu hannu.




Achan hosp.kuwa ba shi kadai ba harda sauran likitochin asibitin suka dukufa kan sakina domin
gano meke damunta Safwan tsurama abunda ya bayyana jikin yar"Na'urar datake haskomasa
cikin Sakina zuface ta yankomasa siririn gilashinsa ya cire yana share zufa kallon sakina yayi
wacce ta zuba mashi ido cikin rashin hayyaci kada kai kawai yayi ya fice shima Tahir binsa yayi
da sassarfa Runtse ido Sakina tayi aranta tana ayyana Abubuwa dadama.














commet
And
Share
Vote



*Shakira..*
[10/14, 20:02] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..*!

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_�


*DEDICATED TO:My mommah Hajja Hadiza muhammed Ba"are*

*38*




Yana shiga Office dinshi Tahir shima ya shiga yana Fadin"Dr Safana wai Sakina wata irin
macece...Ace kidinga ma kanki illar ammh kebaki sani ba kina haukar banza


"Yafada yana kallon Safwan dayake kokarin bude karamin fridge din dake kafe a office din
ruwan yadauko ya bude ya kafa kai sai daya sha fin rabi kafin ya dire ajiyar zuciya ya sauke kan
ya zauna yana cewa"I do'nt know Tahir....Sakina tagama illata kanta tana ganin kamar ni
tamawa ko..?Yafada idanunsa sunkawo ruwa Dr Tahir yace"Wlh bakai tamawa ba kanta tama
domin awannan stage din da mahaifarta takai masalaha shine fiddata kawai..."Zuru Safwan ya
mishi kan yace"A'a Tahir bbu wata dabara da za"ayi sakina fa danta dayane aduniyan nan kuma
sai aciremata mahaifa"yafada da jaddadawa Dr Tahir ya gyara tsayuwa yana cewa"Kafini sanin
illar cancer mahaifa Dr S S kuma kaganin ma idonka har ta kumbura saboda bayan tasa an
mata juyin mahaifa ta cigaba da shan pills cikin rashin akida wannan shiyasa basa zuwa cikin
mahaifan sai suka dinga taruwa guri daya suna mata illah shi ya haifarmata da zubar jini mai
yawa...Barinshi zuwa wani lokaci Dr zata Fashe ne da kanta kuma in ta fashe am srry to...."Iz ok
a shirya mata operation"Dr Safwan ya katsesa cikin rauni kafin yafice daga office din binsa da
kallo Tahir yayi kan ya girgiza kai yabi bayansa.





Safwan dakin da Sakina take yakoma tana ganinsa ta mike tana Fadin"Safwan...Meke damuna
ne..?Kallonta yayi kai tsaye yace"Abunda kika kullama kanki ne kina ganin nikika mawa to
dayake kinsan Allah ba azzalumin bawan sa bane sai abun yakoma kanki"yafada muryansa na
rawa cikin rudewa Sakina ta dirko daga gadon datake tana Fadin"Na shiga uku ni Sakina ashe
har yanzu bangama kwasan KUSKUREN DANA TAFKA BA"Safwan ya juya baya yana
Fadin"Wannan shine kuskuren dazaki Tafka na karshe Sakina domin Yau din za"ayi miki aiki a
fidda mahaifarki"Mahaifata....Tafada da karfi kan tasha gaban Dr tana Fadi cikin
kuka"Safwan...mahaifata to meyasamu mahaifan Tawa"Shima kallonta yayi kan yace"Bayan kin
Haifi Adil kin kara komawa an rufe miki bakin mahaifa ko..?"yafada still idanunsa na kanta
sunkuyar dakai tayi tana hawaye tace"eh...Yace kuma bayan nan kin cika gaba da shan pills
ko"nan ma tadaga kai wucewa yayi zai fita kana yace"Abunda kika aikata shiya jawo mahaifarki
ta kumbura har kikafara zubar jini nan da wani lokaci in aka barta zata fashe ne gabadaya kuma
ke zaki rasa ranki...Yadan dakata kafin yace"Kizama cikin shiri karfe biyar za"ayi aiki.Yana
gabama fadar haka yafita sulalewa Sakina tayi tana kuka harda kara wani tashin hankali wanda

ba'a samasa suna tashiga kuka take harda majina na nadamar abunda ta aikata domin ayanzu
itace ta kashe kanta bawani ba.




Shiko Safwan kai tsaye gidansu momma ya nufa yaje yafada musu sallallami kawai suketayi
Hajiya mama harda kwallanta na tsausayama Sakina nan da nan ta shirya tace ya kai ta Asibitin
taje ta zauna da ita domin awannan halin tana bukatar wani kusa da ita Haka Safeena dataji lbr
sai da takusa faduwa imani da tsoron Allah suka shigeta lokaci daya gabadayansu suka
dumguma zuwa asibitin koda suka je sun Sami sakina ba yarda take tasha kuka Da Gudu
Safeena ta isa ta rumgumeta tana kuka sakina fadi take"Abunda na shukane nake girba
Safeena kidaina min kuka ni najama kaina"Hajiya mama da momma ne ke ta bata baki da inna
zulai shiyasa tayi shuru duk mai imani yaga Sakina sai ya tsausayamata na halin data
ciki,safwan kuwa kasa zama yayi saboda yama rasa wani yanayi yake ciki.




Koda biyar din tayi angama kowani shirye shirye hatta kayan tiyatan asanyamata Dr Safwan da
Dr Tahir sai Dr Sainah sune zasuyi aikin suma sun kammallah komai lokacin da'aka gungurota
za'a shiga da ita ne ta rike Hannu Safeena tana hawaye tace"Hakika duk wanda yaki godema
ni'imar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login