Showing 30001 words to 33000 words out of 52374 words

Chapter 11 - NA TAFKA KUSKURE COMPLET BY JANAFNANCY-1.pdf

addu"an mutuwa ce zata fitar dake"Gyada mata kai Safeena tayi
hawaye na kwaranyomata.


Hajiya mama data tsaya abaya saida taga kowa yashige kana ta kalli sakina dake tsaye dafe da
kirji tace"Ahayyyye....Rana bata karya sai dai uwar diya taji kunya,nasan kina tunanin mafarki
kikeyi ko? to kibude idanunki da kyau ba mafarki kikeyi ba da gaske Safiyanu yayi aure da
Amaryarsa safeena itace aka kawota yanzu wannan shine amsa abunda kika taba fadamun
watannin baya,kin manta ko? to bari in tuna miki kince in zan iya yima jikana maganin
matsalarsa nace miki bani da ikon yayesa masa mtsalarsa ammh ina da ikon kawo masa wacce
zata iya yayemasa"Hajiya mama ta dakata kan tacigaba da cewa"To yau shine ya tabbata....Ni
maryama duk wanda yaci tuwo dani miya sha Nasan ko ahaka na barki kingane kuranki"

Tana gama fadar haka tayi shigewarta dakin safeena tana fadin"ya banji guda na tashi bane
kudaina daga kafa fa" Ai sakina lokaci daya taji wani abu ya dira bisa kirjinta ya gangara har
sassan jikinta kafafunta suka hau rawa lokaci dayata zube akasa tana dafe kirji cikin karaji
tace"Na shiga uku nalalace ni sakina aure"Tafada da karfi to dayake hayaniya yayi yawa ba
wanda yajita sai yan aikinta dake kichen suka rugo suna tambayata lafiya abun mamaki sakina
ce ke hawaye idanu biyu tana girgiza kai tace"Never wlh it can happen...Kai haba bazai yuyuba
wlh sam"tana fadi hawaye na kwaranyomata masu zafi da radadi so take ta karyata abunda taji
kuma ta ganine ammh saboda dakiyar zuciya takasa yarda din.



Suna ta mata sannu ko kallonsu batayi ba tamike dakyar tana dafa bango tashige daki tana
fadin"Ina never 4ever wlh...Ni din kishiya tab wlh badai niba"tana fada tabuga kanta agaru ta
fashe da kuka mai tsuma rai tana bubbuga hannunta agaru tana ta surutai"Na shiga uku ni
sakina kardai ace da gaske ne sai kuma tayi shuru sai chan tace'kodai wasane wanine
adanginsu yayi aure"Sai kuma chan tace'to ai hajiya bazata min karya ba "Sai kuma chan
tace"Wlh da gaskene wayyo ni sakina na mutu na lalace tafada tana sulalewa akasa tana kuka
mai cin rai.



_Ho ho chai chai diz girl kinada hauka taurin kan sakina na burgeni don ubanki kiga amarya da
idanunki kiki yarda saboda muguwar taurin kai zaki yarda in kika ga Dr ya shige dakin amarya
Addabun Arab inji mrs ibrahim_

Adakin amarya kuwa anata yaba dakin sabida yadda ya tsaru kowa sai san barka yake nan fa
aka shiga shigowa da abinci kala kala da abunsha aka baje ana dibar girki ana hira safeena dai
ko kadan bata ciba domin har yanzu kuka take muryanta ya dishe sai wuraren sha daya suka
baro shashen safeena aka bar safeena da kawayenta sukuma iyaye suka koma barayin su
momma.




Su kuwa su Dr tahir suna ijiye tawagar amarya suka juya gidansu tahir suka wuce domin chan
suke daman suka iske ango na jiran dawowarsu sun tabbatar mai da amarya ta iso cikin aminci
da salama ajiyar zuciya ya sauke kan yace"Ina ta kiran wayarta tana ringing but no answer tahir
ne yace"To sai kayi hakuri gobe in mun kaika domin amarya harmuka zo kuka take"Kuka
safwan yafada yananuna damuwa Tahir yace"Eh...kukan rabuwa da gidamana Dr safwan
yakoma ya kwanta yana cewa"Allah yasa tabar kukan nan cos bani son ciwon kai yakamamin
ita'!shekewa sukayi dadariya Gaddafi yace"Shege nawa karka wani damu gobe zaka fanshe kaji
abokina"Kara fashewa sukayi dadariya shikuwa banza yayi dasu kusan kwana sukayi suna mai
shakiyanci.



abangaren su hajiya mama sunkwana cikin farinciki da Annushuwa haka bangaren ango da
abokansa bangaren Amarya ma sai dai muce Alhamdulillah domin kowa yakwana cikin murna
safeena ce ta kwana da ciwon kai saboda kukan data sha bangaren Sakina kuwa kwanan
zaune tayi domin barci sai da kwanciyar hankali gashi wayarta taki tashi balle takira hajiya kari a
idanunta aka kira sallah asuba idanunta sunyi ja sun kumbura saboda kuka ana shiga sallar
asuba tazare key din mota ko mayafi bata saba tafice tanajin hayaniya adakin amarya ammh ko
kallon gurin batayi ba tafice da sauri motarta tafada ta bata wuta afusace take dannah hon habu
megadi dake sallah sai da ya sallame saboda firgici ai yana ganin Sakina cikin halin kamar
mahaukaciya yayi saurin budemata tafice dawani mahaukacin gudu tsaye yayi yana dafe kai
kafin yarufe yakoma yakara tada sallah.



Katsina ta nufa da asubahin nan tana ta zuga gudu ahanya domin sam bata cikin hayyaacinta
itadai burinta ta isa ga mahaifiyarta ko ta fada mata cewa karyane safwa baiyi Aure ba.





Koda gari ya waye ba wanda yabi takan sakina balle yasan bata nan abun kari mai rai da lafiya
akayima bakin zurmi dakyar inna husai ta mtsama safeena taci abinci tasha magani ta kwanta

don ta huta karfe biyu nayi masu kidan kwaryan da hajiya ta hayo suka iso tuni suka baje
atsakar wuri suka fara sakin kida nan wuri ta hautsine hajiya mama ta shge fili tana tikar rawa
ana mata manni tayi shar cikin leshinta ciki da alaku🤣🤣🤣kai yan zurmi sunga rawan banjo ai
hajiya ta chashe iya chashewa momma na gefe tana dariya domin tasan yau ranar farincikin
hajiya ne, safeena da Aisha kadai aka bari adaki su kuwa sauran suna wurin kidan kwarya ana
cikin kidan ne saiga motar Dr Safwan tasawo kai cikin gidan shida tahir wanda tunda suka doso
get din gidan sukaji kida na tashi .



Da mamaki Dr Safwan ya bude murfin mota ya fito wuri ko yadau sowan ga ango nan ga ango
nan jin haka yasa hajiya mama tafito cikin fili ta nufi Safwan tanamai dariya.






*Janafty...*


Commet
And
Share
Vote
Like
[10/14, 20:02] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..!*

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty�_



*DEDICATED TO:My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*




*25*


"Tana isa kusa dashi ta rikosa tana fadin"Oyoyo safiyanu ango Safeenatu barka da zuwa..."

tana fadar haka tana jansa zuwa filin rawa jama'a nata rangada guda suna isa tsakiyar Filin
tace"Anchanza salon kida ga ango ya shigo flil baki safwan ya sake kan yayi mgana sunfara
kidan kwaryan tako ina yana tashi sunayi suna fadar sunanshi da safeena haj.Mama ta rikeshi
tana rausayawa shidai binta kawai yakeyi guri yadau ihu da sowa shikuwa Tahir manni yahau
zuba musu yana yi yana daukansu video ana tafi kai yan kida sunkwashi naira dakyar Safwan
ya yakice kansa Daga Wajen Haj.mama ya fice daga filin yana zufa yana jinjinama hajiya
mama daru to a ina tasan masu kidan kwarya _Niko nace kana wasa da hajiya mama_



sai alasar aka gama kidan kwaryan Haj.mama ta sallamesu suka tafi suna godiya da tarin
alkhairin dasuka samu suma yan biki suka fara shirin komawa yan zurmi mota guda Safwan
yasamo aka maidaasu bayan Safeena tasha kukan rabuwa da yan'uwanta da Kawarta Aisha
safwan yacikasu da kudi itakuma momma da hajiya mama sun cikasu da abun biki sun koma
suna labarta karamcin yan kaduna,Yan safana kadai suka rage sai gobe zasu tafi Safeena
momma ta rikota tun bayan tafiyar yan zurmi suka shga takaita har dakinta tana rike da Adli
safeena tasa hannu ta amsheshi bai mata kiyuya ba yako je gunta ta tsuramasa ido kaunarshi
na ratsata shima ita yake kallo yana bamgalamata dariya itama batasan sadda tayi dariyar ba
ga guntun hawaye a idonta ba.


*****
Kaduna....


karfe Tara da rabi Sakina ta isa gida saboda tayi gudu ahanya sosai shikanshi mai gadin gidan
nasu sai da ya firgita da irin hon din da sakina ta dinga saki shiya fito da kwamishna daga daki
wanda yaji abun yawuce misali yana saukowa falo yaci karo da sakina wurjajan bako mayafi
kamar mahaukaciya tana kiran"Hajiya....Hajiya safwan ya kasheni"kwamishina yadakamata
tsawa da cewa


"KE.....Sakina..."Yafada yana saukowa daga saman benen Hajiya kari dake daki taji kamar
muryan sakina nakiranta kuma taji muryan Kwamishina ai da hanzari ta sauko kasa zani na
neman faduwa abunda taganine yakusa sata faduwa sakina ce durkushe tana rafzan kuka ga
kwamishina yana ta tambayanta taki mgana ai da sauri hajiya kari ta karisa tana fadin"nashiga
uku ni karima sakina lpy meyake faruwane..?"Tafada tana rikota ai da gudu sakina tafada jikin
hajiya kari tana fadin"Hajiya safwan ya cuceni yaci amanata yamin kishiya"Tafada tana fashewa
dawani kuka haj kari ta zabura kamar taga abun tsoro tace Tana dafe kirji"na shiga uku wani
safwan din ne yayi aure..?


tafada tana kallon Sakinar sakina tace cikin kuka "Hajiya aure dakika sani kishiya yamin

bansaniba"haj kari tace"kan bala'i ammh safwan anyi tsinanne wlh....."


Kice tsinanniya mara tunani..."Kwamishina yafada ransa abace hajiya kari tayi zuru tana kallon
kwamishina kan tace"Ni ce tsinanniya kabiru...?yace"Kwarai kece Tsinanniya ba Safwan ba
inbanda rashin ilimi mutum yayi aure kice masa tsinanne.."

!Sakina ta shanye kukanta hawaye dai baidaina zubo mata ba, hajiya kari tayi tsam kawai tana
kallon ikon Allah yajuya ga Sakina yana fadin"Ke shashasha mara tunani don ubanki me na
fada miki kwanaki..?"Yafada rai bace sakina tace murya na rawa"kace karna sake dawowa gida
da sunan amun wani abun"Yace"to me ya dawo Dake ...?Tace"dady amanata fa yaci yayi aure
bansani ba"Kwamishina yace"ungo naki yamata dakuwa kan yace" dan gidanku ke amanarsa
nawa kikaci to billayil lazim ki ka kuskura kika kaso aurenki na rantse sai dai kinemi wani uban
bani ba"Yafada da kakkausan murya hajiya kari data daskare tun dazu tace"Haba Alhaji acuci
yarinya kuma ka hanata yin kuka ga dan iska chan.....shout up....!yakatseta da tsawa kan
yace"Na rantse karima kika kara samin baki cikin mganata saina ci mutumcinki"Haj kari ta rike
baki kawai tayi shuru saboda ganin yadda kwamishina ke huci.


Yajuya zai wuce yace"Ba wacce tatabamun yaji agidana sai ke saboda kece baki dauki aurenki
da daraja ba wlh saboda abun kunyan dakikeyi gidan mijinki kunyan yaron nan nakeji duk
sanda yakirani.....to ki bude kunnuwanki da kyau kjini kijirani yanzu zan shirya muje na maidake
dakin Aurenki wlh tallahi Allah daya ko inkika sake kika kashe aurenki sai kingane kurenki
sakarya wacce batasan meyakemata ciwo ba"yana fadar haka ya haura sama da Sassarfa
Daga ganin yadda yake Tafiya kinsan Ransa a bace yake.



Sakina ta fashe da kuka tace"Hajiya ki taimakeni kada daddy ya maidani wlh baran juri ganin
safwan da wata mace ba"hajiya kari ta jawo ta jikinnta tace"Bar kukan nan sakina kada kisa
nima nahau yi fa kimanta kece sakinar nan mai aji da kwalliya da dakiyar zuciya"!sakina takara
fashewa da kuka tana jin zuciyarta ta kusa bugawa kamar zata mutu kan hajiya kari tasamu
zarafin mgana Kwamishina ya fito cikin shirinshi na bugaggiyar shadda harda babban riga
yace"oya taso mutafi....Ke karima samamata mayafi bazan maidake a haka ba!sum sum
tashiga daki tadaukomata mayafi cikin mayafanta ta yafamata sakina na hawaye ta fice haj kari
tace"Alhaji....ya waigo yace"Bakiji ba kenan..?"Jin haka yasa tayi shuru har suka fice sunisu
direba ya tukasu suka kama hanyar kaduna.


Hajiya kari tayi tsuru zaune afalo kan tace"komai ya dagulemin lokaci daya na shiga uku ni
karimatu.

*Ai komai ya gama kwabemiki haj.Kari sai dai hakuri...*




*Shakira...*


commets
Share
Vote
Like
[10/14, 20:02] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..!*

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_�


*DEDICATED TO:My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*




*26*


"Tafiyar yan zurmi ba dadewa su kwamishina suka iso wanda sakina tasha kuka a mota kamar
ranta zai fita kai tsaye shashen su momma ya Nufa shine agaba kana sakinar abayansa
haj.Mama na falo zaune itada iyami wacce sai gobe zasu tafi suna hira kwamishina yayi
sallama ya shigo sakina na biye dashi a baya da mamaki hajiya ta mike tana mai maraba cikin
mamaki sakina durkushewa tayi anan tana kuka mai tsuma wanda ke saurare hajiya mama
tace"kabiru lpy kuwa naganga a gaggauce haka..?


"Kwamishina yace"Lpy kalau hajiya wannan yarinyarnan ce tazo gidana tun safe tanama
mutane kukan banza,ina fatan safwan na nan..?Hajiya mama tarike baki tana kallon sakina kan
tace"Ikon Allah kabiru kaga muko ko fitarta bamu sani ba,bashi gida sai dai ka kirasa
awaya"Kwamishina ya ciro waya yana fadin"Iz ok hajiya yimin mgana da hadiza don Allah kuzo
mgana zanyi daku yanzu ina sau rine"Hajiya mama da iyami suka mike suka wuce cike da
mamakin sakina wacce ke durkushe tana kuka momma ma tayi mamaki da hajiya ke fadamata
zuwan kwamishina hakama safwan yaji lokacin da ya kirasa to daman bayan sungama

sallaman bakine suka wuce asibiti ahanzarce ya shigo mota ya taho



Afalon su hajya aka zauna da momma da sakina da hajiya mama sai Safwan wanda ke gefe
yana kallon yadda sakina tazama kamar tsohuwa saboda tashin hankali gyaran murya
kwamishina yayi kan yace"Don Allah hajiya kuyi hakuri da halin yarinyarnan nasani tana bata
muku sosai ammh kuyi hakuri mussanman kai Safwan don Allah kayi hakuri"Safwan ya
sunkuyar da kai yace"Daddy bbu komai wlh kaima kayi hakuri nayi aure baka sani ba abun ne
yazo agurguje"Kwamishina yace"Masha Allahu wannan ai karuwace ubangiji Allah yatayaka
rIko bbu komai safwan...Gatanan na dawo da ita hajiya ku shaida wlh in sakina tayi abunda
safwan ya saketa wlh sai dai ta nemi wani uban bani ba gabadaya yarinyarnan tafita zakka a
gidana halin uwarta kaf ta debe to billahil azim daga ke har ita inkukayi abunda kuka kashe
auren nan wlh dukkanku sai kun raina kanku" yana gama fadar haka yace"Hajiya dake da
hadiza gatanan nadawo da ita don Allah ku kara hakuri don Allah"Hajiya mama tace"Bakomai
kabiru Allah ya kyauta kawai"Yadakamata tsawa yace tashi kibani guri mutuniyar banza
kawai"Da gudu sakina tatashi tana kuka ta fice hajiya suka bita da kallo tana tuna rabon dataga
sakina cikin wannan yanayin lalle auren ya bugeta.




Kwamishina yasa aka kiramasa safeena ya hadasu da Safwan ya musu nasiha mai ratsa jiki
kan su zauna lpy yana tashi tafiya ya ijiyema su momma dubu hamsin ya wuce direba yaja suka
wuce ko takan sakina bai kara bi ba.



Safwan yadade tsaye har motar kwamishina tabace mashi kafin jiki asanyaye ya shige
barayinsu kai tsaye dakin sakina wacce ke kwance kan gado tana rafzan kuka mai tsaya
azuciya ya nufa yadade tsaye yana kallonta yauce rana ta farko da safwan yaji tsausayin
sakina ya tsirgamai asanyaye ya karisa kusa da ita yasanya hannu ya rikota tadago tana
kallonsa idanunta sunjajur dasu kurama juna ido sukayi na tsawon lokaci kafin ita ta janye
idanunta tayi saurin saukowa daga gado zata wuce yayi saurin riko hannunta tafada jikinsa ya
rumgumeta tadinga dukan kirjunsa ammh yaki sakinta dole tagaji tadaina tayi lamo tana kuka
shafa kanta kawai yake yana fadin"Srry....banyi wannan auren don na batamiki ba sakina kibar
kuka hakanan"Ina saima kara volume take shdai sai aikin lallashinta yake ammh tatafasa
batace maiba shiya yimata wanka ya shiryata saboda yadda tazama cikin kwana daya tal,Ita dai
kukan ta kawai take ko kallonsa batayi shiyaje shashen su momma yataho da safeena bayan su
hajiya sunkara musu Nasiha.

Dakyar da sodin goshi sakina tayarda ta fito falo inda safeena ke zaune tana jiranta tana zuwa
tazame daga kan kujera tana gaisheta zuramata jajayen idanunta kawai tayi ammh tak batace
mataba to shima kanshi Dr shirun Sakinar yafara batamasa rai haka dai ya musu nasihan su
zauna lpy yakuma fadama safeena cewa sakina ya take gareta kada yaji ko yagani ta rainata ita
kuma sakina yace takama girmanta itace babba kuma tasani in tazauna lpy to kamar ta
taimakeshi ne mganar raba girki kuma yace tafada kwana nawa za"a raba shuru ta musu kawai
idanunta na kallon kasa kwallah tataru a idonta kawai sai tatashi ta wuce dakinta wanda tayi
hakane kada kukan datake boyewa ya bayyana.



Dr Safwan yabi bayanta da kallo kafin yayi ajiyar zuciya yadawo da kallonsa kan Safeena
wacce ke durkushe kasa tana wasa da gefen hijabinta yayi shuru kawai yana kallonta jikinta ne
yabata ana kallonta shiyasa tadago karaf suka hada ido ammh me sai taga kamar ma
hankalinshi bai tareda ita sam tsuramasa ido kawai tayi tana jin badadi domin ta fahimci Antyna
nata bata karbeta amatsayin kanwarta ba.



Hada ido sukayi da ita yayi saurin sakarmata mirmishi kafin ya mike yace"Yan matana don Allah
ban minti biyu "yana fadar haka ya bi bayan sakina yana tura kofar yaganta zaune kan sofa ta
chusa kai agwiwan kafafunta kai tsaye yakira sunanta tadago da sauri idanunta na fitar da ruwa
tace"KA FITA SAFWAN KA FITA BANA SON GANINKA KA FITA NACE!!!tafada cikin karaji
idanunta na zubar da kwallah Safwan yayi jagale yana kallonta yabude baki zai yi mgana kenan
ta mike tace"KAFITA NACE KO!!!"tana zaremai ido kamar mayya ya lura tarasa natsuwarta dat
why yace"iz ok zan fita shikenan ko..?

"yafada yana kallonta juyamai baya tayi tana jin zuciyarta na zafi kamar zata fashe cikin
tsausayama sakina ya fice yajamata kofa yadade tsaye kafin ya karisa kusa da Safeena yasa
hannu yadagota kawai ya rumgume yana jin shima kamar ya kurma ihu Safeena tanajin yadda
zuciyarsa ke fat fat kamar wanda yayi gudun tsere,ahaka yakarisa dasu har dakin safeena
gafen gado ya zaunar da ita yana kallonta da shanyayun idanunwa wanda babukomai acikinsu
sai zallah desire yace cikin wata murya"yanmatana kidan jirani kadan yanzu zan dawo"Yafada
yana rikeda hannunta da kai ta amsa kan tace"Tom adawo lpy"Mirmishi yamata kan ya saketa
yafice da sassarfa,bayansa Safeena tabi da kallon tana jin tsausayinshi da wani sonshi na kara
shigarta tayi alqawarin bashi dukkan goyin baya wurin yaye damuwarshi.

*Anitha...*




Commets
Share
Vote
Like
[10/14, 20:02] Sis Janafty: *NA TAFKA KUSKURE..*!

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty�_



*DEDICATED TO MY:Mommh Hajja Hadiza Muhammed Ba"are*


*27*


" Yana fita ya shiga mota sai yahuza suya ya siyo gasassun kaji guda biyu yakamo hanyar
komawa gidane kiran Tahir ya shigomai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login