Showing 12001 words to 15000 words out of 71593 words

Chapter 5 - Matar Dr Saiyadee Complete Book by Mhiss B~hal Ce.pdf

harta
kuma kwanciya ak'asa Ummunah wai gajiyar Ce haka kidaina kwanciya ak'asa ni banaso fah,
murmushi tayi tah tashi tace bacci nakeji neh shiyasa, tam bara nabaki abincin saiki kwanta
koh, nama yazuba matah acikin plate dah snacks yazuba matah nagari cikin mug sannan
yadawo kusa dah itah d'ago tah yayi ya kwantar ak'irjin sah, sannan yace, "haa Ummunah kiyi
Bismillah", uhm~uhm Allah ni nah k'oshi ya Saiyadee banci, Dan Allah kitaimaka min kici abinci
Ummunah bud'e kici koh kad'an neh, Ni a'a ya Saiyadee Allah am full, shikenan Ummunah
nagode, gani tayi baiji dad'i bah hakan yasa tace masa zansha milk din gobe zanci wannan
tafad'a kamar zatayi kuka, d'ago fuskan tah yayi ya k'ura matah ido sannan yace, "Ummunah I
love U, Ummunah ina sonki ina kaunar ki nagode dah kika aureni fuska tah saukar k'asa
murmushi yayi dan yasan kunya taji mug d'in yadauka yakai bakin tah ahankali tasoma sha
bayan tayi Bismillah, kallon tah yake yana maijin dad'in yanda takeshan hankali akwance, tasha
fin rabin mug sannan tacire bakin tah tace "tak'oshi", toh Ummunah hakan ma nagode sosai
Allah yayi miki Albarka wifey, Ameen tace, hanky tagani acikin aljuhun shi tace, " ya Saiyadee",
na'am Ummunah mekike so, handkerchief zaka aramin, kafin tah k'ara wani magana yajata jikin
shi ya lashe bakin tah tas,
wai ni Mhiss~B naga abu kaji iyayen soyayya, Toh Allah yabar kauna�,
ido tah zaro sannan tah rufe su gum, dariya yayi yace koh bah abinda zakiyi dah hanky bah
kenan, ai that's my job Ummunah remember u're my halal, shuru tayi sannan tace bacci nakeji
bacci zanyi, agogo yaduba yaga har 4am tayi it's almost time d'in tashiwar sah ma and she's
tired hakan yasah yayi tunanin k'in yimata komai kawai, toh muje ki kwanta d'agata yayi harkan
gado yakwantar dah itah bargo rufa matah zuwa k'irji sannan yayi matah rumfa yanah kallon
cikin idontah, kasa cigaba dah kallon shi tayi kawai tasaukar dah idanun tah, light kiss yakai
matah kan baki yace, "Ummunah kece murad'i nah ina sonki ina kaunar ki, kece abinda nake
nema Allah yabani kuma nagode masah, murmushi tayi kad'an tah d'auke kai, karan hancinta
yaja yace, "say something sweetheart, U keep on being silent, bargo taja kanta tace, "ya
Saiyadee ni bacci zanyi fah, gudnight sweetheart sleep well! Yace sannan murmushi yakoma

k'asa yasoma cin abinci ahankali, kad'an yaci yaji harya k'oshi milk d'in yasha shima yatashi,
komawa yayi danya duba tah sai yaji tanah shek'ar kuka ahankali, Ummunah yafad'a hankali
atashe bargon yayi saurin yayewa yaga fuskan tah sha'be2 dah hawaye, jikinsa yajawo tah,
Shhhhh baby it's ok, am here for U sweet, cikin tsananin kuka tace, "ni wajan Mummynah dah
Daddynah zakah kaini, ni gidanmu zanje bazan iya kwana anan bah, k'ank'ame tah yakuma yi
yanah shak'ar daddad'an k'amshin dake tashi ajikin tah, cikin kuka takuma cewa, "ni wlh kah
kaini ni gidanmu, ni banason nan wajan babu Mom nd Dad d'inah", kuka takeyi sosai sai
rarrashin tah yake yanah jijjiga tah ahankali, kamun yace, " Ummunah nifah? kinga Abbanah
dah Ummanah anan neh?, Ummunah wannan shine auren fah daman ai dole kirabu dasu kifara
sabon rayuwa, sauran kuma sakaiyar ki tanah gun Allah, ni bakya tausayi nah idan kika tafi kika
barni, koh bakya So nah bakya san zama dani? bazan iya rayuwa babu kebah Ummunah,
inazan saka kaina yau idan kika koma gida wlh nima bazan iya rayuwar nan gidan bah, kinga
sabon gida neh yau muka tare yazama wajan zaman mu inda zamuyi rayuwa kuma mu raini
yaran mu, Dan Allah kiyi hak'uri Ummunah muzauna lafiya, kidaina d'aga min hankali dah kukan
nan, I love U Ummunah, I love U so much, banasan kinamin asaran hawaye Dan Allah yafad'a
yanah k'ara rungume tah sosai, shuru tayi tanata haak'i, bayan tah yake bugawa ahankali
gamida yimata sannu akai2, shuru neh yabiyo baya sai saukar numfashin tah dayake ji
ahankali, gyara musu kwanciyar yayi sabida taji dad'in baccin sosai saidai shi yakasa baccin
kallon tah yake kawai yanajin kaunar tah aransa tamkar yamaida tah ciki!


Mhiss B~hal Ce
[15/10 07:22] 'Yar Gatan SadNaf Ce��: NoVelWriTter
☣Mhiss~B~hal‍♀☣

⌛13⏳

‍♀‍♀ ‍♀‍♀
☘Matar DR. Saiyadee☘

‍⚕ ‍⚕




(Love&Pain Story Based On Reality)

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
✍[P~M ~L]✍
www.mhissbhal.WordPress.com

Dedicated 2 Ol MATAN AURE round D globe, Ina kuke MATAN AURE Inayin Ku, ya aiki, ya
kula dah miji dah yara, ya d'iban lada kuma? toh ad'iba dayauwa fah dan samun tsira ranar

gobe, ya wanke2 dah shara, Allahu yabada lada yasaka da gidan Aljanna Mhiss~B tanah
gaisuwa

Asuba nayi Ummulkhair tah farka, ita tama manta duk tunanin tah tayi sallah tazo tah d'aura
breakfast kafin Daddyn su yashirya fita aiki, tunowa datayi ba agida take bah hakan yasah tah
tafashe dah kuka, wayan tah tadauka tah kira numban mahaifiyar tah bugu d'aya Mummy tah
dauka dasauri, Ummulkhair ya kike tafad'a cikin muryan kuka, kin kwana lafiya khairat? khairat
nakasa bacci babu ke acikin gidan! koh kad'an ban iyayin bacci bah, danma mahaifin ki
yakwace min wayana dasai nakira ki cikin dare sabida nakasa jurewa Khairiya, tafad'a tanah
hawaye masu zafi, kinga Daddyn naki ma baiyi bacci bah shima kasawa yayi tun yanah rarrashi
nah har shima saida yayi kukan, Affan mah kwana yayi idon sah biyu abud'e munyi kewar ki
Khairiya, we all miss U, Dan Allah kizauna lafiya dah mijinki Allah yayi miki Albarka, Ummulkhair
tunda mahaifiyar tah tafara magana take wani irin kuka wanda takejin zuciyar tah kamar wuta,
daman tasan hakan zai faru iyayen tah sun daura masu san duniya sabida subiyu kadai neh
kuma bayan an haife tah saida akayi shekara biyar aka haifi Affan so bah k'aramman shak'uwa
sukayi dah itabah ita cikin Daddy dah Mummy mah tarasa wanda yafi kaunarta, tasan dole
zasuji daban agidan jiya kuka take sosai, kasa cigaba dawayan tayi tah katse tafad'a band'aki
tayi alwala sallah tayi tah karanta Alkur'ani mai girma sannan tad'an samu nutsuwa, wayan tah
tadauko takuma kiran layin mahaifiyar tah, Affan neh yadauka, Sis yakike? kina lafiya ganinan
zuwa gidan ki, murna tayi sosai tanah sharar hawaye dake zubo matah toh Affan ina Daddyn
mu kabashi waya, gashinan yace sannan ya mik'a masa wayan, cike dah farin ciki Daddy
yakar'bi wayan, yace, "Khairiya Ce", uhm tah amsa sabida batason yasan kuka take, yakike?
kinanan klau koh? ya mijin naki Allah yabaku zaman lafiya, sannu koh sannu Khairiya Er Baba
yafad'a muryan shi atok'are saurin mik'awa Mummy wayan yayi ya kauda kai, khairat Mijin ki fah
jiya yashigo dawuri koh? cewar Mummy, eh Mummynah bayan ankawo ni bai jima bah
yadawo,toh fita fah, yau da gobe babu inda zaije koh? Zai zauna dake agidan koh? Ummulkhair
Eh tace, sannan tace, "Mummy harda jibi ma", toh shikenan naji dad'in hakan sosai, tun k'arfe
biyar nagama miki abinci yanzu Affan zaizo yakawo yace zai gane gidan naki, ogogon sama
takalla taga 6:15am tace Mummyn mu nagode Allah yabiya ki dah gidan Aljanna, Ameen khairat
Er Albarka, Mummynah, na'am khairat, Mummy Dan Allah kema kuci abincin dah Daddy sosai
naga kwana biyu bakwacin abinci yanda yakama tah, toh Khairiya Insha Allah zamuci, Allah ya
Albarkaci rayuwar ki Duniya dah lahira, Ameen tah amsa a nitse
Wayyo Allah nah Allah Sarkie UWA...UWA...UWA!!! Gaskia UWA tafi komai wanda baisan
darajar Iyaye bah especially Mahaifiya wallahi Allah ya kwashi Asaran Duniya, Allah kah
sakawa Iyayen mu dah gidan Aljanna, kah d'and'ana masu ruwan Alkausar cikin sauk'i! AMEEN
Sallama sukayi dah mahaifiyar tata saida taci kukan tah sannan tah tashi da nufin zuwa gaida
mijin tah, saidai taduba koh ina bata ganshi bah side d'inshi taje tayi knocking tareda yin
sallama nanma shuru hakan yasa tah murd'a k'ofan tashige ciki shuru babu kowa, d'aki
tak'arasa nanma shuru babu kowa, tayi tunanin koh wanka yakeyi, saikuma taji shuru, knocking
k'ofar bathroom d'in tayi taji alamun babu kowa, budewa tayi taji k'amshi fresh bath hakan
yatabbatar matah dacewar yayi wanka, toh ina yaje take tambayar kanta? koh breakfast yaje
dauko musu? toh amman ai akwai remnants d'in jiya basu cinye bah, ganin babu mai batah
amsa yasah tah fice harzata koma d'aki tah tuno bata duba main parlour bah, hakan yasa

tunanin tah yakarkata dah cewar yanacan yanah kallo, takawa tayi ahankali zuwa main parlour
sannan tashiga dah sallama shuru babu wanda ya amsa, wayam parlour'n babu kowa ciki, ruwa
tah hango kan dinning table tanufi wajan dan tasha kasan cewar every morning ruwa take
farasha kafin taci komai, bayan tasha cup d'aya harzata juya takoma d'aki idanun tah suka
sauka kan farin paper anyi folding d'inshi neatly!


Mhiss B~hal Ce
[15/10 07:22] 'Yar Gatan SadNaf Ce��: NoVelWriTter
☣Mhiss~B~hal‍♀☣

⌛14⏳

‍♀‍♀ ‍♀‍♀
☘Matar DR. Saiyadee☘

‍⚕ ‍⚕




(Love&Pain Story Based On Reality)

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
✍[P~M ~L]✍
www.mhissbhal.WordPress.com

Dedicated 2 ZAINAB YAKASAI (Shukrah Er Gatan Miemiebee, Er Autan Pure Moment)
marubuciyar RAYUWAR ABDULLAH gaskia banida abinda zan cemiki dear saidai kawai nace
Allah yahad'a mu a gidan Aljanna, U're Unique Love, I heart U so much deary��!


Gabanta neh yafad'i dan tasan tabbas Saiyadee neh yayi dropping note toh amman menene
aciki, kujeran dinning taja tazauna sannan takai hannun tah ahankali tadau paper'n cike dah
tsoro tafara unfolding d'inshi har tagama bud'e shi saidai tah runtse idon tah har saida tad'an
samu nutsuwa tabud'e su tasauke akan note d'in wanda yake kamar haka, Good morning sweetheart, finally U're awake & reading this, Ummunah bazan iya daukan
hutun kwana biyu bah due to wani aiki dah I must attend to, nayi signing Operation din wani
yaro tun last 2weeks kuma yaune ranar kinga dole nah naje nayi masa aikin, so sorry i just had
to leave, U slept well on my chest last night I miss U badly, I promise to pay back, Eat well baby
& lastly I hope U'll understand!
rasa abinyi tayi hawaye nah zubar matah tunani take yanzu da'ace abu yashiga tsakanin su last
night haka zatah tashi taneme shi tarasa saikace wanda yabiya tah yayi tafiyar sah, kuka take

by now wani zafi takeji aranta k'ofa taji ana bugawa tashiga share hawayen tah sannan tamaida
hijjab d'intah wanda tacire dan zafi taje dubawa, Anty bud'emin nine Affan dasaurin tah tabud'e
tanah dariyan murna sosai, tanah bud'ewa tah rungume sah tanah fad'in lilbro saikace jirgi neh
yakawo kah har yaushe Mummy tace min kanah tafe lallai kayi missing d'inah, wallahi naji
dad'in ganin kah sosai U juz don't kno hw happy I am, Sis ai jiya banyi bacci bah wlh naji gidan
duk babu dad'i koh kad'an nibanma san nafisan ki akan su Mom bah sai jiya, lilbro harda su
zak'in baki tace tanah dariya, muje ciki, gidan suka zagaye tah nuna masah ko'ina gaba d'aya
ya yaba dah gidan natah kuma yayi matah Addu'a sosai sannan sukayi zaman cin abinci,
serving d'insu takeyi tare, yace "laa Sis tare zamuci abinci"?, why not dear tare zamuci manah,
toh Sis naji dad'i, laa namanta ban tambaye ki yayanmu bah naga munzagaye gidan ban ganshi
bah kuma sabida yananan Mummy tace karna zauna, baya nan yatafi dauko min magani a
Asibiti dah zazzabi nakwana jiya Ummulkhair tayi k'arya, amman banason kah fad'awa Mummy
koh Daddy bansan hankalin su yatashi muyi zaman mu muci abinci muyi hira kawai, toh
shikenan Anty amman idan naci abinci anan idan naje gida fah Mummyn mu tayi fad'a, a'a kace
matah Abusaiyeed neh yayi insisting yace saika ci, toh shikenan anty wainar shinkafa neh dah
miyar agushi sai farar shinkafa dah miyan naman rago, sai drinks data aika masu dashi
Bismillah sukayi suka shiga ci tare cike dah farin ciki kai kace sunyi shekara basu had'u bah,
Ummulkhair kallon yanda k'anin tah yamaye gurbin mijin tah take tasan kamata ace dah mijin
tah sukecin abinci awannan lokacin wani hawaye mai zafin gaske neh yasauko matah saurin
gogewa tayi kada Affan yalura sannan tah godewa Allah daya bata d'an uwa ma, bayan sun
gama ya tattara plates yakai kitchen yawanke mata tas, yadawo yazauna suna kallo, har
shabiyun rana Ummulkhair ido tazuba koh zataga su Amal amman shuru babu labarin su ita tayi
tunanin zasuzo wajan tah sabida basuda nisa sosai, toh kodai sunsan Yayan nasu baya nan
neh, itah yanzu idan Affan yatafi yazata yi, haka kuwa akayi Affan yayi tafiyar sah sai itah kadai
kamar mayya, bak'i neh en unguwa suka soma d'an shishigo matah ciki harda zeesarkie daman
nasan za ayi hakan, zee Allah ya shirye ki! Lol
Kar'ba cikin mutunci dah k'ima tadinga wa bakin natah sosai tareda had'a masu dah kayan
marmari snacks dah drinks take tah basu sai ruwan sanyi,
Ahaka Ummulkhair tah dinga baki har saida akayi magriba suka daina shigo matah daganan
kuma tah tsaftace gidan tah tak'ara shiga wanka tayi kwalliya cikin atamphan tah mai kyau tayi
zaman jiran mijinta shuru taji hakan yasah tah dauki phone d'intah tasoma kiran numban
Saiyadee amman sam baya picking, saida tamishi missed calls goma sha sannan yayi matah
reply kamar haka,
Am busy we talk later pls!
bayan tah karanta tashi tayi kawai tayi sallah tah mik'a kukanta ga Allah,
Anan kan dadduma yakira akayi Isha bayan tayi sallan Isha neh bacci yadauke tah, bacci take
sosai kasan cewar tah jima batah samun bacci agida, chan wajajan to 12am taji anta'ba tah
kafin tah ankara taji anyi sama dah itah ido tabud'e atsorace zatayi k'ara taji yace, "shhh baby
its me, am the one so calm down OK U're safe", babu abinda tace masah kan gado yanufa dah
itah ya kwantar sannan yakwanta gafenta cikin idon tah yake kallo kafin yace Ummunah am
sorry, agogo taduba taga 12am saura juz 2mins tafashe masa dah kuka, jikin sah yajata yanah
fad'in shhh sweetheart I juz said m sorry ok tryna understand the situation pls, kuka take sosai
k'ank'ame tah yayi yanah fad'in it's OK Ummunah I love U OK, Inasan ki fiyeda rayuwa tah kibar

min kuka banaso, nayi laifi kiyafe min Dan Allah kinji, shuru batace masah komai bah raba tah
yayi dah jikin sah yakalle tah yaga idon tah taf suke dah hawaye sosai yaji tausayin tah rasa
abinyi yayi hakan yasah yayi owning lips d'intah ahankali, ido tazaro masah sannan tayi saurin
rufesu, k'ank'ame tah yayi sosai yaci gaba dah kissing d'intah romantically!

Mhiss B~hal Ce
[15/10 07:22] 'Yar Gatan SadNaf Ce��: NoVelWriTter
☣Mhiss~B~hal‍♀☣

⌛15⏳

‍♀‍♀ ‍♀‍♀
☘Matar DR. Saiyadee☘

‍⚕ ‍⚕




(Love&Pain Story Based On Reality)

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
✍[P~M ~L]✍
www.mhissbhal.WordPress.com

Dedicated 2 all EN MATA round D globe, Ina kuke EN MATA ADON GARI IDAN BABU KU
BABU GARI IDAN KUNYI YAUWA GARI YA 'BACI�, ya samari, ya kyautatawa Iyaye kuma?
Toh adage fah bin maganar Iyaye bin maganar Allah! Allahu yahad'a mu A Aljanna yakawo
mazaje nagari masu Albarka dah rik'on amana AMEEN Mhiss~B tanah gaisuwa

Kissing d'inta yakeyi kawai dukda cewa yakula she's not comfortable hawayen dake tsiyaya
afuskar tah yake share wa idanun sah arufe, a hankali yayi patting lips d'insu yayi whispering
akunnen tah Ummunah m sorry kinji? shuru batace komai bah, Ummunah Dan Allah kiyi min
magana koh zanji dad'i, ya aiki sannu dah zuwa, kah gaji koh? tafurta ahankali, k'ank'ame tah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login