Showing 42001 words to 45000 words out of 213309 words
sake haihuwar se Allah baiyiba.
Lamiɗo yarone kyakyawa dashegen shigarai tun yana dan kankaninsa and yet stubborn dankuwa tunda yafara rarrafe baka isa kashiga ɗakin Umma kaganshi fes fes ba,dan haka ze birkice ɗakin yakoma kamar na mahaukanta, yaɗale nan yaɗale can,yayi wurgi dawannan yayi wurgi da wancan. daya fara tafiya kuwa sema abunda yaƙaru akan nada. duk stubbornness ɗinsa kuwa bayida neman tsokana hakanan bazaka taba ji yayi faɗa da wani ba infact abokanansa sonsa sukeyi kamarmi,farin jini ne dashi tunyana ɗan kankaninsa. babba da yaro kowa sonshi yakeyi.
Sanda Lamiɗo yafara wayau akasaka shi a both islamiya da Boko wanda alokacinne Amina da Baffa sukaga typical darunsa dankuwa tunda yalura anfara kaishi makaranta da gari ya waye Umma tazo zata ɗaukeshi tamishi wanka zaifara zunduma ihu yana kuka har atafi makarantar dashi ahaka zaita kukan harlokacin tashi yayi. Lamiɗo yaƙi jinin zuwa makarantar boko abun mamaki kumase bayakin na islamiyyar
Amina dafari tashi hankalinta yayi ganin irin rigimar da Lamiɗon keyi,samun Mallam Yusuf tayi da batun kodai ahakura da makarantar ne tukunna harzuwa sanda zaikara waysu tunda Lamiɗon bayaso anma Mallam Yusuf yaƙi yace with time zaisaba. Sede fah Lamiɗo har aka gama first term baidaina wannan kukan banzan dayakeyi ba hakan kuma baisa andaina kaishi makarantar ba. Lamiɗo dayazo yaga kukan batayi mishi amfanin koma seya canza lauje. Duksanda yaji yanajin kashi ko fitsari seya ƙi faɗa ma nanny ɗinsu sede yayi a wando kokuma seya daidaici anfita break ko games seyazo yasamu kan table ɗin Auntynsu yatsuguna yayi yagudu abunsa and that'll keep her busy cleaning her table bazatayi musu lesson ba ranar wanda hakan bakaramin daɗi yake mishi ba,haka zai kwanta yayita baccinsa a aji,akumayi bincike amma ba'a sanin shiyayi sabida babu wani trace dayake bari,rana ɗaya dai Allah yatoni asirinsa yatsuguna kan table ɗin auntyn kenan segata tashigo class ɗin tayi mantuwa. ranar kuwa Lamiɗo yabugu ba kaɗan ba haka yayita kuka kamar zaiyi yaya. har ƙara Auntynsu takaishi gida inda Baffa yace "aibayason karatu ne makarantar ma dayaya akasamu yadaina kukan zuwa shiyasa ya fara wannan iskancin amma nan gaba inyasake shashanci irin haka ku basa kashi gobe bazai ƙara ba" and from that day onwards Auntynsu tazuba mishi idanu sosai,ta kulla mai,komai zata tambaya a class ɗin shitake tambaya inbai bada amsa ba kuwa yadinga shan punishment da bulala kenan wanda hakan yasa yake tsoronta sosai,intana koyar da abu dolenshi yake mayar da hankalinshi yakoya ahaka harya gama nursery school dan itake koyar dasu harsuka gama Nursery level. daman atsarin makarantar kowani set da da teachern dake coaching ɗinsu harsu gama leven ɗin dasuke ciki kafin takoma baya taɗauki wasu set ɗin kuma Toh Aunty chioma ita takoyar da set ɗinsu Lamiɗo a Nursery level and that was how yasamu good foundation dukda kuwa rashin son karatunsa. Lamiɗo sanda yashiga primary level harda murnarsa yarabu da alakakai anma da mamakinshi ranar dasukayi resuming primary one bayan an tashi daga school yana isa gida bayan yagama lunch sega ta tazo gida yimasa lesson wanda Baffa dakansa yanemi wannan request ɗin agurinta danyasan ita kaɗai zata ita dealing dashi indai aharkar karatune. Dole Lamiɗo yamaida hankali akan karatun primary school ɗinma sabida kullum tana zuwa zatace yaɗebo books ɗinsa yakawo daganan kuma yashiga uku da questions kenan inbai amsaba kuma duka.
Babu abunda Lamiɗo bema Aunty chioma ba danta baryimasa lesson anma taki,yasha sace takalminta yaje yajefa a shadda intazo gida lesson yace bashi bane ba anma hakan baihanata cigaba da zuwaba,akwai ranarda yasa su Hafiz suzo sucire mata attach din kanta intana cikin masa lesson su gudu dukdan de tayi zuciya tadaina zuwa anma duk abanza.
Dole Lamiɗo yahakura yacigaba dazuwa makaranta dukda kuwa har ransa baso yakeyiba hardai yasamu yagama primary school yayi junior secondary school duk itakemai lesson. Alokacin ne kuma akayi babban rashi amasarautar,Sarki da Mallam Yusuf dakuma wasu daga cikin fadawan masarautar Allah yakarbi ransu sakamakon hadarin mota dasukayi ahanyarsu nazuwa wani taro dazasuje a Nijar. anyi kukan rashi bama a masarautar kaɗai ba harma a faɗin jihar gombe baki ɗaya,bayan angama zaman makoki dadai sauransu lokaci guda kuma abubuwa suka canza a masarautar baki ɗaya sakamakon canjin mulki da'aka samu. Amina abubuwa suka rikiɗe mata,ga rashin mijinta abun kaunarsu itada ƴaƴanta gakuma responsibilities dayahau kanta wanda ada batasan komai ba inbanda akawo tagirka,suzauna itada ƴaƴanta suci toh haka suturama dan babu abunda Mallam Yusuf ya ragesu dashi,komai yimasu yake dede gwargwado dede karfinsa. Bayan kuɗin lesson dayake biya azo ayi musu agidama both islamiya da Boko duk private yasakasu,a Inda zasu samu ingantacciyar ilimi wanda itakanta bayan rasuwar mijin nata bataso ciresu amakarantun ba anma data dubs yanayin rayuwa dakuma halin dasuka tsinci kansu aciki dole seda tayi hakan,gashi ita ba aikin fari bare na baƙi. gashi basuda maiyi musu batun tace zata koma Kwami ma duk ba solution bane sabida daga ita har ƴaƴanta sunsaba da rayuwar birni and moreover insunje can ɗinma liability zasu zame ma family ɗinsu wanda dole daga ƙarshe tayi deciding tatashi tanemi abunyi dakanta kawai for the betterment of her children's future. Aminiyarta *Hajiya Hadiza* dasuke zuwa islamiyar manya tare ne tabata shawarar why not ta koyi ɗinki tunda taga masu yi suna samu sosai seta haɗa da kitson da ada takeyinshi for free tamaida shi na kuɗi for the time being kafin aga abunda Allah zaiyi. Aikuwa hakan Amina tayi dan acikin satin taje tayi register da makarantar da ake koyon ɗinki tafara zuwa while on the other hand kuma tanayin kitson kuɗi agida. Dake tamaida hankali sosai akan abun takuma maida shi priority ɗinta within no time takoyi ɗinki dan tunma kafin agama training ɗin tasayi keken ɗinkin tana practice dashi agida during her free time. Kan kace me Amina tazama chief tailor a unguwarsu harma wasu daga wani unguwannin sukan kawo mata ɗinki har gida gakuma kitso data haɗa duka tanayi lokaci guda. toh da wadannan sana'o'in Amina ke kula da iyalinta dede gwargwado dukda kuwa taso tayi fulfilling needs ɗinsu kamar yanda mahaifinsu kemusu abun ya faskara,dan kuɗin ma bawai koda yaushe akesamu ba in ansamu ɗinma akwai so many budgets akansu, shiyasa akullum suka zauna da yaran takan ce musu "kuyi hakuri da irin canjin dakuke gani a rayuwarku. wannan ɗin wata jarabawa ce daga Ubangiji,wani yana can dazai samu irinnamu halin rayuwar zuba ruwa zaiyi akasa yasha. kuzama masu gode ma Allah akodayaushe and if you want a better future dole sekun dage kunyi karatu"
Masalar Amina ɗaya ce "rashin son karatun Lamiɗo" duk dukan dayasha agurin Aunty Chioma abanza. dankuwa yanzu yakoma gidan jiya tun bayan data sallami Aunty chioma tun daganan kuma ya watsar da karatun agefe,makaranta ma seyaga dama yake zuwa wanda hakan ba karamin ɗaga mata hankali yakeyiba,barinma inta tuna irin burin da Mallam Yusuf yaci akan Lamiɗon nason yayi karatu yazama independent mutum bawai yadogara da wasuba, yazama head of the family tayanda zaikula da kannensa da itakanta mahaifiyartasa anma kwata kwata shi ta lura waɗannan ba sune dreams ɗinsa ba. Amina tarasa miyasa Lamiɗo ke ƙin karatun bawai kuma don bashida ilimin baneba. Sau tari takan zaunar dashi tayimasa wa'azi anma his only answer will be "Umma bakaratu ne kaɗai kesa mutum yayi kuɗi ba. ko masu kuɗin duniya ma ba tahanyar karatun sukayi achieving abunda suka zama yanzuba. Besides the way we're living our lives is quite okay,ni i'm not after money. I want to lead a simple life,munada wadatarzuci,munada abinci dede gwargwado and above all we love each other wanda inada yakinin wannan bond ɗinda ke tsakanin mu will always keep us going" Umma intaji Lamiɗo yayi irin maganarnan setace "Toh Lamiɗo inbakayi karatun ba mezakayi?kaida ba jarin kasuwanci garekaba,kaida ba fita neman kuɗin kakeyi ba ta'ina zaka iya gina kanka bare har kayi leading simple life ɗin? ni aidaman bacewa nayi seka zama bilget ko dangote ba,a'a kadai zama kanada rufin asirinka. nimadai kasan nafara tsufa koh? kuma yau in Allah yakarbi raina waye zaikulada ku inbanda kaidin?" Lamiɗo dayaji Umma tafara maganar mutuwa irin haka seyace "Umma Insha Allah you're going nowhere,insha Allah bazaki barmuba munanan taredake harsaikinga jikokinki" and she'll laughed setace "toh nadaina batun mutuwar da bakaso d6in anma fah batun karatu bazan bar yimaka itaba sabida azamanin yanzunnan inbakayi karatun ba wazai kalleka da idon daraja? wazaiyi dakai? kanadai gani mahaifinku ma dabadan masarauta yasamu yake aikiba da haryau munacan Dukku muna rarraba idanu" Lamiɗo se yace "karki damu Umma nima Inna girma I'll be lucky like Baffa,insha Allahu zansamu aikin dazanyi harya riqemu nida ku" Umma abudaya talura da lamido.
Shi mutum ne dabashida dogon buri,he just want a simple life. Shi mutum ne da abun duniya baidameshiba dankuwa tun yana kankaninshi ma baiyi halin kwaɗayi ba,yanada ɗauke kai akan abun wani hakanan duk abunda tadauka tabashi ko baiyi masa kyauba bazaiyi korafi ba,zai buɗi baki yayi godiya.
Sau tari zatadauki kuɗin break tabasu inzasu tafi makaranta kuma equally take basu dasu jidda anma still suda suke kanana sukanyi korafi anma banda Lamiɗo. ko naira biyar zata bama Lamiɗo bazaitaba cewa "Umma kuɗin nan bazai isheni ba" hakanan duk inda yaga abu maikyau na amfani kokuma kayan daɗi dayasan kanninsa naso koda kuwa da kuɗin break dinnasa ne zaisaya musu yakawomasu gida toh haka Umman ma indai yaga abu tana kuma son abun indai akwai kuɗi ahannunshi zaisaya yakawomata.
Kannenshi kuwa komi suka tambayeshi indai yana dashi zaibasu,zaikuma yimasu hakanan he's not strict on them, shakuwa ce sosai atsakaninsu wanda hakan kuma baisa sun rainashiba dan Amina batayi wasa wurin basu tarbiyya ba. in yace musu bari toh sunbari kenan,inyace yi kaza,take zasuyi batareda sunyi korafi ba.
Lamiɗo yana Ss2 aka kawo letter daga school ɗinsu kan ana neman parents ɗinshi dasuje makarantar akwai maganar da akeson yi dasu. Amina da taga letter daga makarantarsu Lamiɗo kuma magana ce za'ayi akan Lamiɗon bakaramin damuwa tashiga ba dantasan bazai wuce laifi Lamiɗon yayi ba,hakadai tadaure tashirya tatafi makarantar. har cikin office ɗin principal secretary ɗin principal ɗin taraka Amina mahaifiyar Lamiɗo inda principal ɗin yanuna mata kujera yace mata "Bismillah Madam ki zauna" zama Amina tayi tana gaida principal ɗin ya amsa kafin tasanar dashi itace mahaifiyar Lamiɗo da aka turama letter gida kan ana neman parents ɗinsa. Principal yace "Allah sarki. Ina mahaifinsa?" Amina sauke kanta ƙasa tayi jiki sanyaye tace "Allah yayi mishi rasuwa shekaru biyu dasuka wuce" Principal cikeda tausayinta yace "I'm sorry. Allah ubangiji yayi mishi rahama" Amina tace "Amin bakomai" daganan principal ɗin yashiga faɗa mata dalilin kiran nata yace "Daman munkirakine gameda Ɗan ki Isma'il" cikeda damuwa Amina tace "wani abun yamuku ne Sir?" principal yace "eyi wallahi. Isma'il yakoyi rashin ji kwanannan Madam. yana skipping classes akai akai,anyi test yayi missing har guda biyu kuma beje yanemi amasa makeup test ba haryau sannan yana soyayya da ƴan matan junior section bayan any sort of relationship a school ɗinnan is prohibited,last time da aka kawomin kararsa naduba record ɗinsa tundaga primary school haryagama junior secondary school anma ba'a taɓa kamashi da laifiba wanda wannan dalilin yasa nabashi suspension na one week kaɗai thinking that he'll mind ways after the suspension but instead of yadaina sema abunda yaƙaru shiyasa nayi requesting parents ɗinsa suzo. Is he under the influential of new friends? tunda dai da bayayi" Amina da hankalinta yagama kai kololuwa atashi tace "A'a abokanansa nada dasu yake tare haryanzu" principal yace "then why the sudden change from him?" Amina cikeda damuwa tace "wallahi bansani ba principal. Amma nayi maka alkawarin bazai sake ba Insha Allahu zanyi mashi magana" Principal yace "gwanda dai kimishi maganar kam kuma yakamata kijashi ajiki sosai sabida kinasanin in and out ɗinsa. yaran yanzu se ahankali, kahaifi Ɗa ne baka haifi halinsa ba" Amina tace "haka nekuma. nagode sosai principal" principal yace "bakomai kidaiyi ƙoƙari kiɗauki mataki dan inbai gyara halayensa ba we've no any Other option than mu koreshi sabida sabida in aka barshi other children might be influenced by him. Amina tace "insha Allahu zai gyara Principal" daganan tatashi tafita tabar office ɗin.
Tunda Amina tafito a office ɗin principal tafiya kawai takeyi batareda tasan ina zatajeba,tasan Lamiɗo bayason karatu anma bata taɓa tunanin he'll skip classes sabida hakaba,bata taɓa tsanmanin har abun zekai ga batun yaƙi rubuta test ba, gameda batun ƴan mata kuma bazatayi blaming kowa ba sekanta dan dabakinshi yasha zuwa yasameta yace "Umma nayi sabuwar kamu" kokuma yace "Umma naga wata fara Ƴar kyakyawa yau kuma tayimin gobe zanje farauta" kokuma yace "Umma kinyi sabuwar suruka fah" anma bata taɓa ɗaukar maganar tasa da seriousness ba sede tayi dariya tace "Lamiɗo kaikam ba'a rabaka da shirme koh" wani sa'in kuma tace "yaro inzakayi karatu kayi karatu ka ajiye batun Ƴan mata agefe. There's time for everything inlokacin sa yayi sekayi amma bayanzu ba" aduk sanda yaji tayi maganarnan cewa yake "Umma kidai barni inyi lokacinane,akwai sanda za'ace inyima bazanyiba" ashedai duk maganar Ƴan Mata dayakeyi mata dagaske yakeyi?ashedai Lamiɗon ta yafara tsayawa zance batareda tasani ba wanda tanada tabbacin may be yana ɗaya daga cikin abubuwan dake hanashi karatu inda wata zuciyar kuma tashiga raya Mata "kodai dagaske he's under the influence of bad friends ne kamar yanda principal ɗin yafaɗa?" tasandai amsar tambayartannnan daga bakin mutum ɗaya zata sameshi "Hafiz" he's the only friend na Lamiɗo dayake zuwa har gida yagaidata kuma suna zumunci da mahaifiyarsa ma sauran abokanan shi kuwa sede taji labarinsu abakin Lamiɗon amma ai duka sunjima suna tare.
Daƙyar tayi karfin halin tsaida mai machine taɗale sannan tawuce gida wanda harta Isa gida tunane tunane kala kala aranta
*08147722806*
Vote
Comment
Share!
🌹 *QADR* 🌹
( _The story of Rukayya_ )
Written by *Zeeneert*💞
*Zeeneert*@wattpad
*Page Seventeen*
Bonus page **
Amina tana isa unguwarsu gidansu Hafiz tama mai machine kwatance yakaita. Tajima agidan suna hira da mahaifiyar Hafiz ɗin harsaida taga shabiyu takusa,su Lamiɗon sunkusa dawowa daga makaranta gashi batayi lunch ba sannan tamata sallama tatafi bayan tabar mata sallahu in Hafiz ya dawo daga makaranta yazo gida tana nemanshi don Allah.
Lamiɗo tunda yadawo daga makaranta yaga canji agurin Ummarsa,she's be acting weirdly kuma babu irin tambayar duniyar nan dabaiyi mataba amma ko cikanka batacemai ba wanda hakan yatabbatarmai dacewa fushin dashi akeyi bada kowaba tunda gashi tana harkokin gabanta da sauran Ƴaƴanta. ba ƙaramin damuwa yashiga ba hakanan abincin da tasa Basma takawomai ɗakin shi ma kinci yayi sabida kwata kwata ji yayi bashida appetite ɗin kuma. In akwai abunda yatsana aduniyar nan damuwar Umma da tashin hankalinta,in akwai abunda yake hanashi sukuni kwata kwata aduniyar nan toh yaga Ummarsa bata walwala dan gaba ɗaya se shima yaji duniyar tadainayi masa daɗi. koda ukun rana tayi daƙyar yashirya yatafi Islamiya bayan yabi ta ɗakinta yamata sallamarda batako kalleshi ba bare yasa ran zata amsa.
Dayanma dasuka taso daga Islamiya Hafiz yace masa suje gidansu tare anma se Lamiɗon yace masa shiba gida zashiba,zeje gidan kawar Umma Hajiya Hadiza yagaisheta ne sunkwana biyu basu gaisa ba. Hafiz yace masa toshikenan nidai gidanku zani kafin inwuce gida sabida ɗazu Ummar ka tazo gida tabar ma Umma na sallahu wai tana son ganina inna dawo daga makaranta. Lamiɗo da harya fara raba hanya da Hafiz yayi sauri yadawo yace "Ummana taje gidanku nemanka kace?" Hafiz yace "Eh hakadai Umma tacemin ɗazu dana koma gida bayan munrabu a school. Shine tace Inna taso a Islamiya nabi ta gidan naku inji menene" cikeda damuwa Lamiɗo yace "ta tabbata nayi laifin kenan,ta tabbata fushin da Umma keyi dani sabida wani laifi danayine danikaina bansanshi ba" Hafiz yace "kayi mata wani abunne kafin katafi school?" Lamiɗo yace "haraam. wallahi lafiya lafiya muka rabu yauda safe,she even escorted us to the gate harsaida school bus yazo ya ɗaukemu sannan takoma gida" Hafiz yace "ikon Allah. toh dai kayi kokari katuna kasan fushin Uwa ba abun wasa bane" Lamiɗo yace "I've been thinking all day anma ni nakasa tuna menayi mata Hafiz,tunda nadawo na tadda condition ɗinta ko abinci kasaci nayi,bakaga a Islamiya yau seda Mallam yamin gyaraba da ina bada hadda? Wallahi I was just not in my right senses. anmadai yanzu mujemu gidan nizan tsaya ta window inji me Umman zatace maka kaga daganan zansan laifin danayi mata se inbata hakuri" Hafiz yace "a'a Lamiɗo kasandai babu kyau laɓe,mudaije kajirani a ɗakinka ko awaje Inna fito zanfaɗa maka yanda mukayi da'ita insha Allahu" Lamiɗo yace "zandai jiraka awajen dan intaga Ina cikin gida zata iya fasa yimaka maganar" Hafiz yace "toshikenan. Kafasa zuwa gidan Mama Hadizan kenan?" Lamiɗo yace "Kaiii kyaleta. daman nakwana biyu banje nagaisheta bane and nasan kona koma gidan yau I'll just make the atmosphere worst for Umma shiyasa nayi deciding najecan anma yanzu zuwa inji laifin danayi a gida inkuma bada hakurin laifin yafimin mahimmanci akan zuwa gidan Mama Hadizan,insha Allahu gobe zanje mata.
Hafiz yayi murmushi yace "toshikenan" inda daganan suka jera suka tafi gidansu Lamiɗon dake cikin masarautar. awajen gidan Lamiɗo yasamu wani dakali yazauna inda yakeda tabbacin ko Ummarsa taleko bazata ganshi ba sannan yacema Hafiz ɗin yashiga shiyana jiransa agurin.
Hafiz sallama yayi a kofar parlournsu Lamiɗo inda Basma da batajima dashigowa daga Islamiyaba ta amsamai danko shiga cikin gida batayiba tukunnan. ƙarasawa yayi cikin parlourn ayayinda Basma ke faɗin "A'aaa Yaya Hafiz kaine daman?" Yace "wallahi nine Basma" Basma tace "Ina wuni?" Hafiz yace "lafiya Lau. Ya karatu inafatandai yau bakisha bulalan hadda ba?" Hafiz yakarashe maganar cikeda zolaya Basma tace "aiyanzu nadage sosai bana bari ayimin dukan bada hadda danaga Uwar bari" Hafiz na dariya yace "toh Allah yabada sa'a" Basma tace "Amin" ananne Kuma suka jiyo muryar Umma daga ciki tana tambayar wayene yazo inda Basma tashige cikin tanacemata Hafiz ne yazo.
Umma tafito daga ɗaki tashigo parlourn tana kallon Hafiz tace "Hafiz ka'iso kenan?" murmushi Hafiz yasaki sannan yasamu guri yazauna yace "na'iso Umma. Ina wuni" Umma tace "Lafiya Lau ya Ummanka?" Hafiz yace "lafiyanta lau Umma tanama gaisheki" Umma tace "Ayya ai dazu ma nashiga gidannaku lokacin baka dawo daga makaranta ba" Hafiz kanshi na ƙasa yace "Eh itace ma take faɗamin kina nemana innataso daga islamiya inbiyo tanan" Umma tace "Allah sarki. daman tambaya zanyi maka akan Lamiɗo" Hafiz yace "Toh Umma" Umma tace "nikam wani abu yahaɗa ku faɗane kwanannan bana ganinku tare?" Hafiz yace "A'a babu