Showing 72001 words to 75000 words out of 213309 words

Chapter 25 - QADAR Book Complete Hausa Novels by Zeeneert.txt

Zeeneert   

09 Nov 2025

5875

yanda akeso anma karmu yadda mubarta agidanmu,inda so samune ma karmu zauna da ita agari ɗaya inbahaka ba akwai consequences. Dan akwai wanda already yana cikin rayuwarta yanzu haka and he can go to any length for her happiness,he's her soulmate,bashida burin daya wuce yafaranta mata hakanan babu abunda bazai iyayima wanda yace zai kuntata mataba kuma har tambayarshi nayi akan yaron anma seyace min daya duba fuskarshi is not visible hakanan ko iskanunshi sun kasa gane wanene shi. Kuma mahaifiyar sa a tsaye take wurin yimasa addu'a bare suce zasu iyayi masa wani abu shiyasama abunda bazai yuyu ba kar afarashi Baban Rabi'u" Kawu idrissa yace "ikon Allah toh wanene wannan yaron haka damu bamu sanshi ba?" Maman Rabi'u tace "Nima bansaniba Baban Rabi'u kuma in akwai wanda yakamata yasani aikune tunda kukuke ganin yarinyar kullum" Kawu idrissa yace "nidai ban taɓa cin karo da wani yaro daban dasunan yazo ganin Umar tahanyar Rukayya ba. Kuma shi bokan bece miki acikin dangi yaron yakeba?" Girgiza kai Maman Rabi'u tayi sannan tace "be faɗamin ba gaskiya" Kawu idrissa yace "toh shikenan zantambayi Adamu inji koyasan yaron" Maman Rabi'u tace "nifah duk wannan baya gabana Baban Rabi'u. damuwana shine asan yanda za'ayi acanza maganar Rukayya zatazo gidannan. kanadai gani tun ba'aje ko'ina ba har kaninka yafara nuna shine sama dakai sabida yafi ka kuɗi. Wai dan feleke da bushewar idanu har Sani ne zaka kawo shawara yace naka baiyiba nashine dede" ajiyar zuciya Kawu idrissa yayi sannan yace "toh yanzudai miye abunyi dan na riga na amince musu kan zanrike Rukayyan kuma gobe zanje in ɗauketa" Maman Rabi'u tace "kawai goben karkajeka,kosun kiraka kada ka daga" Kawu idrissa yace "ai wannan kuma ba solution baneba dan kobanjeba za'a iya kawota har gida" Maman Rabi'u tace "kadaiyi musu hakan insun kawota gidan seka fito barau barau kanuna kaifa bakason riketa sannan kaja Adamu kutafi kasuwa gobe kokaturashi Giyaɗe yimaka wani aiki yanda bazaisan me ake cikiba danshikam uban Ƴan tausayine yanzu seya ɓata mana budget bayan kuma kuɗin nan harda shi zai amfana in akasamu cigaban tunda kominku tare yake" Kawu idrissa yace "toh shikenan hakan za'ayi. Kawai ma zanturashi Kano sarin kaya gobe"

Aikuwa hakan akayi. daman da ɗaya daga cikin yaran shagonsu gobe zetafi Kano yi musu sari sekawai yakirashi yace yabari kawai zai tura wani inda bayan sunyi magana yakira Kawu Adamu awaya yacemasa ai yaron shagon nasu babu lafiya yanzu yakirashi sabida haka yayi hakuri shiya shirya yatafi kanon gobe da sassafe In Allah yakaimu darai da lafiya. Dukda tafiyar tazoma Kawu Adamu abazata beyi ma Yayan nasa complain ba,aganinsa ya Isa dashi shiyasa ya aikeshi barekuma ma da abun yazo da zancen cewa dukansune suke benefiting daga kasuwancin danhaka tun adaren yasanar da iyalansa yakuma fara shiri inda washegari da sassafe yakama hanyar Kano.


Sorry. I know it's short but insha Allah zakujini gobe.

*Page Twenty Five*

***

Yau tunda garin Allah ya waye su Gwaggo Suwaiba keta aikace aikace acikin gidan. daga su kimtsa nan sesu kimtsa can,seda suka kalkale ko'ina agidan yayi tasss sannan suka tattara duka kayyakin dasukasan in an ajiyesu a afili zai iya ɓaci kosamun mishkila kafin suka fara shirin tafiya Giyaɗe kuma,kowadai jiki ba daɗi.

Nikuwa daman tundaren jiya nace muku sun kimtsamin kayayyakina hakanan bayan Gwaggo Suwaiba tayi wanka ta matsamin nima nayi,acewarta kada Kawu idrissa yazo ɗaukana banshiryaba. hakadai nadaure nayi wankan nashirya cikin wata kodaddiyar rigata da yawanci daman agida nake sakashi insha iska. Koda Gwaggo Suwaiba taga irin kayan danasaka taso tayi magana anma se Gogode ta kwabeta,tace tabarni inyi duk yanda nakeso,i'm not In my right self,abunda yadameni ma ya'isheni. Tace "zataji da rashin da akayi mata ne dakuma hanata binmu da akayi ne kokuma zataji da naki mitar ne? Kowani kaya tasaka kibarta tunda ba tsirara take yawo ba kumama inbanda abunki ba gida zatajeba? miye amfanin ace seta saka Kaya mekyau?" Itadai Gwaggo suwaiba batakuma cewa komaiba dan koni nalura tundaren jiya Gogode a hargitse take,gabadaya ita hukuncin da akayanke beyimata ba. Toh anma yazatayi?"
***
Lamiɗo da plans ɗinsa na tafiya Bauchi yakwana arai hakanan koda yaje sallar asubahi sedayi sporting sahun da Hafiz yazauna kafin shima yaje yajona nasa sahun abaya dan Hafiz ɗin yariga shi zuwa masallaci yau. Ana idar da sallah kuwa yadinga lura da sashin da Hafiz ɗin kezaune dankarya zo yatafi besani ba. Allah yagani kuma bayida niyar sake wahalar zuwa gidansu yauma danhaka yanaganin Hafiz ɗin yatashi yafice yayi sauri yabi bayansa.

Awaje suka haɗu suka gaisa sannan Lamiɗon yace masa sujesu gidansu,hararanshi Hafiz yayi sannan yace "kaman ya inje gidanku? Mezanje inyi maka?" Lamiɗo yamarairaice fuska sannan yace "about our deal mana Hafiz" Hafiz akafule yace "toh deal ɗin da asubahin nan za'ayi shi tsantsan jaraba da takura ne kawai irin naka? Ko angayamaka Sarkin saurarata zaiyi da asubahin Allahn Nan? Waikai miye matsalarka ne? Kabari karfe tara tayi ashiga fada mana tukun" Lamiɗo yace "Eh ai karfe Taran daman zakaje Fadan but before then Inason muje gida muzauna mujira lokaci yayi dannasan Inna barka katafi gida toh kafin kadawo ma wani aikinnne" Hafiz yasaki baki sannan yace "toh wallahi baka isaba. Ni bacci nikeji kuma bazan hana kainayin abunda raina yakesoba sabida kai" Lamiɗo yace "toh ni nahanaka yin barcinka ne? Muje gidanmu sekayi baccin acan" girgiza kai Hafiz yayi alamar beyarda ba yanashirin magana Lamiɗo yayi sauri yaja hannunshi yana faɗin "muje pleaseee! Inma katifata kakeson inbaka kakwanta akai kai kaɗai zanbaka for today dai kam" Hafiz yace "Aikuwa tunda kafaɗi haka toh bazaka kwanta akai ɗinba" Lamiɗo yayi dariya sannan yace "naji. nayarda. Mujemu" aikuwa kamar yanda Hafiz yace tunda Lamiɗon dakanshi yace zaibar masa katifar seya barmasa toh adole seda yasashi yabarmasa ɗin shikuma yakwanta akan sallaya. Aikuwa Hafiz yasha takura,dan minti minti Lamiɗo ke tashin shi yana cemasa suje su leƙa ko Sarki yafito fada.

Daga karshe dai dole Hafiz yahakura da baccin suka koma yin hira har taran safen tayi. Tashi Lamiɗo yayi yayi wanka yashirya sannan suka fita inda shi ya wuce tasha ayayinda Hafiz kuma yanufi Fada don aiwatar da plan ɗinsu.

Sanda ya'isa Fadan Sarki bejima da fitowa ba don haka Fadawa da dagoraye basu barshi yashigaba harsaida suka gama gaggaisawa atsakaninsu,suka ɗan tattauna akan al'amurorin masarautar sannan aka fara bama masu son ganin Sarki izinin shiga ɗaya bayan ɗaya har aka iso kan Hafiz. Hafiz jiyayi gabanshi yayi wani mugun faɗuwa Sanda wani dogari yazo yabashi izinin shiga yaga Sarki hakanan yakejin dama bezoba dan seyanzu yakejin kamar he's not sure of his decision tunda baisan mai hakan zata haifar ma Lamiɗo ba. Anma daya tuna irin alkawarin dayamishi kuma ya tabbata by now yanacan Tasha yanajiranshi yasa yatashi yashiga fadan kawai.

Da sallama ya ƙarasa kan shimfidar kafet ɗin da Fadawa ke zazzaune kai ayayinda Sarki ke zaune kan throne ɗinsa,har ƙasa ya tsuguna yagaida Sarki sannan yagaida Fadawa suma. ɗaya daga cikin Fadawan ne yace "Yaya sunanka Yaro?" Hafiz kanshi na ƙasa yace "sunana Hafiz Baba" bafaden yace "toh Hafiz,kozamu iya sanin menene matsalarka?" cikin sauri Hafiz yace "banida matsala Baba. Labari nakawoma Sarki" Bafaden yagyara zama tareda ɗan numfasawa sannan yace "toh munajinka. wace irin labari ne kakawo haka?" Seda Hafiz ya danyi Jim kamar bazaiyi magana ba sekuma yace "Labari akan wanda ya shigo masarautarnsn ranar da darene,naji kunce zaku bada kyautar dubu goma gaduk wanda yazo yafaɗa muku kowanene yashigo masarautar adaren ranan" cikeda zakuwa wani Bafade apart from wanda yake tambayar Hafiz ɗazu yace "kasan Barawon ne?" Hafiz yace "nasandai wanda yashigo ɗin anma ba barawo bane gaskiya" wannan karan Sarkine yayi gyaran murya sannan yace "Wanene shi? kuma kamarya ba barawo baneba bayan an tabbatar min da cewa tsallakowa yayi ta katanga?" Hafiz dahar lokacin kanshi na kallon kafet yace "Eh ba barawo bane Maimartaba. abokina Lamiɗo ne ɗan gidan marigayi Sarkin dawakai. Ranar daya diro ɗin anagobe zamuyi jarabawa ne,toh munjima a makaranta muna karatu bamumasan harlokaci yagota irin hakaba kuma gashi babu wayoyi ahannun bare musan lokaci harsaida muka baro makarantar sannan muka ankare da dare yayi sosai ganin babu movement acikin gari ahakadai harmuka karaso Masarautarnan mukasamu a rufe. Toh yasan kukuma dokace agurinku ba'a buɗema kowa gate in sha dayan dare yawuce sannan yasan ba lallai koyama dogaraye bayani sukarbi uzurinsa ba shiyasa yace zedira ta katanga kawai. Toh Kuma jiya senaji anabatun kunsaka kuɗi akan anemo wanda ya shigo daren ranar inda nikuma tsoron kada wani yaganshi ranar yazo yafada ayanke mai hukunci yasani zuwa in faɗi gaskiya. Kuyi hakuri don Allah" wani Bafade yace "wannan ba huruminka baneba tunda kazo kafaɗa shi Lamiɗon inya shigo hannu zeyi bayani" Hafiz nashirin sakeyin magana wani Bafade daban yace "tashi katafi" harya tashi ya Isa bakin kofa zaifita Sarki dakansa yakirashi yadawo sannan yasa ɗaya daga cikin fadawan yabama Hafiz kuɗi.

Har Bafaden yafara korafin ai tunda ance ba sata yayi ba babu amfanin abashi kuɗin anma se Sarkin yace "Eh abashi tunda su sukayi alkawarin bama kowanene yazo yabasu labarin wanda yashigo masarautar adaren ranar" haka aka ɗauki dubu goma akabama Hafiz yayi godiya sannan yatashi yatafi hakanan yanajin sanda Sarki yake bada umarnin aje anemi Lamiɗo aduk Inda yake cikin masarautar a tahomai dashi.

Lumshe idanu Hafiz yayi yana tunanin ya Umma zata ɗauki labarin in akaje har gida akasameta da wannan labarin.

Ahakadai yatari napep yatafi Tasha,besha wahalar samun Lamiɗo ba dayake straight inda ake hawa motar bauchi yayi,nan yaɗauki dubu goman da aka bashi yabashi sannan yasanar dashi yanda sukayi da mutanen Fada.

Lamiɗo jiki sanyaye yace "thank You Hafiz and bakomai, karka damu I'll surely come back and see them. Yanzudai damuwana shine inka koma kasanar da Umma natafi bauchi tunda kaga sanda muka fito baswa gida suntafi islamiya dukansu kuma bamuyi sallama ba kafin suka tafi. And please kayi mata bayani kamar yanda kama Ƴan Fada indai har anje gida nemana. Anma karka nuna mata kaikakai karana please! Banason Umma tadinga kallonka da abun" Hafiz yace "toh shikenan. Safe journey" 5k Lamiɗo yacira yamika ma Hafiz yana faɗin karike wannan nakane.

Hararanshi Hafiz yayi sannan yabar gurin batareda yacemai komaiba, Lamiɗo murmushi yayi taredabin abokin nasa da kallo sannan yasaka kuɗin cikin aljihun wandonsa aransa yana faɗin "zama ka karba ne dole. baridai Allah yadawo Dani lafiya".

Karfe goma da rabi tagota sosai kafin motar su Lamiɗo ta daga zuwa Bauchi.
***

Har Sha ɗayan safe babu wanda yazo a tsakanin Kawu Adamu da Kawu idrissa dasunan ɗaukana hakanan basu turo wani daga can gidansu ba. Kawu Sani kuwa tun sassafe yazo ya sallami su Gogode yawuce office,acewarsa in Kawu idrissa ko Kawu Adamu sunzo zamu saukesu a tasha kafin muwuce gida. Gwaggo Suwaiba dahar tafara gajiya dazaman jira tace "toh wai meya hana Yaya Idrissan zuwa har irin wannan lokacin ne?" Gogode tace "Allah ne kaɗai masani. Kodai yamanta ne toh?" Cikeda mamaki Gwaggo Suwaiba tace "wani irin mantuwa ne haka ni Suwaiba? toh kodai kawai zamu tari adaidaita mubi mu ajiyeta acan gidan daganan mu muwuce Tasha kawai" Gwaggo Larai dake zaune gefe tun ɗazu batace komai ba tace "inmuka fita sukuma suka zofa?bagwanda mudan kara jiraba" Gwaggo Suwaiba tace "toh shikenan bari mu ɗan kara jiran mugani" anma har karfe ɗaya babu alaman ko ɗaya daga cikin su biyu. Ran su Gwaggo suwaiba bakaramin baci yayiba ayayinda nikuma daɗi abun yamin dankuwa nagama tsara plan ɗina kancewa zanyi convincing ɗinsu sutafi dani kawai anma semun shiga adaidaita.

Gwaggo Suwaiba tashi tayi daga zaunen datake tana faɗin "toh Larai. yanzudai kam bana tunanin zasu zo ɗin,kilan aikine yamusu yawa kokuma sunmnta din kamar yanda kukace. Muyi salla azahar kawai muje bakin titi mutari adaidaita sahu yakaimu can gidan su Yaya idrissan mu ajiye Rukayya semu wuce tasha"
Gogode tace "hakan ma yayi"

Su Gwaggo Suwaiba sun idar da sallah kenan zasufara fidda mana kayayyakin mu waje mukaji sallaman Yaya Fahad.

Kusan atare Gwaggo Suwaiba da Gogode suka amsa sallamar tasa. sanye yake da kananun kaya dasuka matukar amsar jikinsa hakanan tunda suka amsa sallamartasa yashiga taku cikin sassarfa har ya iso inda suke zazzaune kan tabarma,yatsuguna daga gefe, cikin nuna girmamawa yace "Ina wuninku?" Su Gogode suka amsa da "lafiya lau" sannan suka tambayeshi mutanen gidansu yace duk kalau suke daganan kuma se wurin yadauki shiru babu wanda yakuma magana hakanan babu wanda yakuma yunkurin daukan kayan daza'a fidda ɗin. da alamadai su Gwaggo suwaiba na tsanmanin wani bayanine daga bakin Yaya Fahad ɗin ayayinda shikuma yaƙi cewa komai inbanda shiru dayayi,yana wasa da car keys ɗinsa tahanyar gurgurzasu a ƙasa.

Nidaman tunda yashigo nasamu jikin gini na rakube araina Ina addu'ar Allah yasa ba ɗaukana yazo yiba. Gwaggo Larai ne dataga babu sarki se Allah kumadai da alama Yaya Fahad ɗin ko shekara zasuyi zaune bazai ce komai ba yasa tace "Fahad daga gida kakene?" gyaɗa matakai yayi ahankali.

Gwaggo Suwaiba tace "aikoh kayi sa'an samun mu dan harmuna shirin fidda kayan mu wajenema" se alokacin Yaya Fahad yabuɗi baki yayi magana,yace "Ai Abba yayita Ƙiran Kawu idrissa yaji kokun tafi baya daga wayarsa shine ya kirani yace inzo nan gida induba ko kuntafi tunda ku babu waya ahannunku" Gwaggo Suwaiba tace "Muna shirin fita kenan kazoka,Kawunanka kuwa babu wanda muka ga keyarsa tunsafe,daga Yaya Adamu har Yaya Idrissan. nicewama nayi tunda basuzo ba kilan sun mantane muje can gidan nasu mu ajiye Rukayya,muyi sallama dasu dakuma iyalansu daganan se mu wuce anma se Suwaiba tace mudan ƙara jira kada mutafi kuma su suntahonan muyi sabani. Toh kaji abunda yazaunar damu harwannwn lokacin inda daga karshe muka yanke shawarar tafiya can gidan kawai tunda haryanzu basu zoba" jinjina kai Yaya Fahad yayi sannan yace "toh yanzu muje inkaiku tashan koh? naga lokaci yanata kurewa kada kuyi dare" Gwaggo Larai tashi tayi tsaye tana gyara daurin zaninta tareda faɗin "aikuwa daka kyauta Fahad" Yaya Fahad bece komaiba sema tashi dayayi yanufi inda kayyakinmu suke yafara fitarwa yanasakawa cikin mota.

Muna shiga mota Gwaggo Suwaiba tacema Yaya Fahad yafara kaimu gidan Kawu idrissa suyi sallama dasu a ajiyeni seya kaisu tasha. Aikuwa inajin haka na fashe da kuka,take hankalinsu yatashi suka shiga tambayata kukan menene nakeyi. cikin gunjin kuka nace "Nima zan rakaku tashan" hakuri Gwaggo Larai tashiga bani ayayinda Gwaggo Suwaiba tacema Yaya Fahad muwuce tasha kawai inyaso inya ajiyesu mukayi sallama se yakaini can gidan Kawu idrissan tunda nace inason zuwa.

Shidai bece komai ba anmadai Naga yajuya kan motar tasa inda yaɗauki wani sabon hanyar,da alamadai da harya nufi titin dazai kaimu unguwar su Kawu idrissan ne.
Dakyar Gwaggo Larai ta banbareni daga jikin Gwaggo Suwaiba sanda motar su tacika,ita kuka ni kuka hakanan har motarsu tatashi tabar harabar tashan inanan tsugune inda motar tatashi ina kuka me tsuma zuciya wanda nikaina nasan bana tafiyarsu Gwaggo Suwaiba bane kaɗai harda na tunanin irin sabuwar rayuwar dazan tsinci kaina aciki. Yaya Fahad kuwa tun bayan dasukayi sallama dasu Gwaggo Suwaiba daman yakoma can inda yayi parking motarsa yajingina da jikin motar yana danne danne cikin wayarsa. ban ankara ba kawai sejin Karan mota nayi kusa dani wanda hakan yasani ɗago da kaina daga cusashi danayi cikin cinyoyina inason ganin wace motace tazo ta tsaya agabana and I saw Yaya Fahad.

Kallo ɗaya yamin tunda muka hada idanu yaɗauke kansa dasauri sannan yabuɗe kofar baya batareda yacemin komaiba. babu musu natashi nashige motar narufo taciki dukda kuwa harlokacin banbar kukan danakeyi ɗinba. Ko minti biyu baiyi da tada motar ba naji yatsaya kuma anma sai ban ɗago dakaina ba hakanan bantsaida kukan danakeyi ba don duk a tunanina wani gurin yatsaya zai karbi sako semu wuce yakaini Gidan Kawu idrissa da banki akoma kiran gidan da *Prison* ba. Yes prison! Because I know for sure ko wanda yake zama a prison seyafini Jin daɗi. Nanne nanne zanji Yaya Fahad yatada motarsa anma shiru,tun Ina shesshekar kuka har muryana yadashe yadaina fitowa nakoma ina sauke ajiyar zuciya tareda sakin hawaye anma still bamubar gurinba wanda hakan yasa nafara tunanin ko wani gun yatafi yabarni cikin motar nibanma saniba?. cikin sauri na ɗago dakaina daga cikin hijabina nakalli sashin mazaunin driver and then I saw him,babu inda yaje yana cikin motar kuma da alama ba yanzu zamu tafi ba tunda har mikar da seat ɗinsa yayi yakwanta yalumshe idanu fuskarsa na fuskantar saman cikin motar ayayinda muryar Sheik sudaiz ke tashi daga cikin radion motar yana karanta suratul Rahman.

Mamakin zaman me mukeyi nashigayi anma nasani ko karen haukane yacijeni bazanyi gigin tambayarsa ba. Toh ma kona tambayar amsa zaibani? mutumin da magana ma wahala take basa? danhaka nazame daga zaunen danake nakoma nayi mukus ajikin kofar motar inamai cigaba da zubda hawayena ayayinda wani irin kewan Baba ke azalzalan zuciyata.

Bayan mintuna kaɗan kuma se wayarsa tafara ringing inda naji yatashi zaune yayi picking yana communicating dawanda yakirasan inda ananne naji har kwatancen inda yayi parking motar tasa yakeyi ma wanda suke wayar and then I realized cewa zaman jiran wani mukeyi kuma da alama tare zamu tafi dashi wanda mukejira ɗin shiyasa sanda zanshiga motar Yaya Fahad yabuɗe min gidan baya instead of gidan gaba.
bayan sungama wayar badajimawa ba naji anbude kofar seat ɗin gaba wanda hakan ya tabbatar min dacewa wanda zamu tafi dashi ɗin ne ya'iso anma seban damu in san ko wanene ba harwanda yashigo ɗin yarufe kofar taciki.
Cikin sanyayyar murya naji Yaya Fahad na faɗin "How was the journey?" ayayinda yake ƙoƙarin tada motar.

Sejin muryar Yaya Salim nayi yana faɗin "Alhamdulillahi Yaya. nasaka zaman jirako? I'm very sorry motarmu tabaci a welcome to,seda aka nemo me gyara and i wanted to call and inform you wurin ba network kwata kwata"

"Don't worry" shine kawai abunda Yaya Fahad ɗin ya faɗa sannan yaja motar muka bar haraban gurin inajin Yaya Salim na sakeyi masa ta'aziyar rashin Baba da'akayi yakumayi mashi addu'a inda Yaya Fahad ɗin ya amsa da Amin,nima na amsaa da Amin ɗin acikin raina hakanan inason ingaida Yaya Salim ɗin dankuwa he's my only favourite acikin cousins ɗina na garinnan anma sena kasa danayi tunanin ai bangaida Yaya Fahad ba dazu dayajeshi gida toh yanzu Inna gaida Yaya Salim kuma mezaiyi tunani kenan? Don haka naja bakina nayi shiru dukda inamai cigaba da tararradi nikadai dukda kuwa wata zuciyar na rayamin aiko hausawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login