Showing 84001 words to 87000 words out of 213309 words
da'ita kuma da Allah yataimakesu se Fadawan basu dawo ba tunda sukayi zuwa na biyu da azahar suka sanar dasu Lamiɗon yayi tafiya kuma bayau zai dawoba.
Ita Jidda daman haushin abunda yama Maimunatu ne yasata cewa zata fada ɗin.
Anshiga sallar maghriba Lamiɗo yashigo masarautar wanda hakan yasa dogaraye da Fadawa basu ganshi ba hakanan yafi mintuna goma abakin kofar gidansu yana kokwanton shiga ko kada yashiga sabida tunanin abunda zai iya tararwa acikin gidan.
Daƙyar dai yayi mastering courage daga karshe yashiga. irin rungumar da Salma tayi masa sanda taga yashiga parlourn nasu dakuma amsa gaisuwarsa da Umma tayi fuska ɗauke da fara'a ba ƙaramin mamaki abun yabashi ba. Amma seya ɓoye mamakin nasa yayi wucewarsa ɗaki donyin sallar maghriba ganin lokaci na kurewa. Lamiɗo befito a ɗakin nasa ba harsaida yayi sallar isha'i. Bayan yafito ɗinne kuma Umma tace Basma tazubo musu abinci suci.
Like a happy family sukayi dinner ɗinsu dukda kuwa Umma da Salma ne kaɗai keta surutansu. gaba ɗaya Lamiɗo yarasa farin cikin menene Ummar tasu takeyi,dankuwa by just looking at her face he can tell cewa tana cikin farin ciki da anashuwa yauɗin. Atunaninshi ko haryanzu batasamu labarin abunda yayi ba yakamata ta ɓata rai sabida tafiya dayayi baiyi mata sallama ba amma segashi yana ganin saɓanin hakan. Abunda baisani ba shine a gidan bikin da Umman taje yau wata kawarta dasuke zumunci tazo tabata labarin taga Lamiɗo a kasuwa yana aiki kuma harcutansa akayi yayi fighting for his right and the amaizing news is that bama kansa kaɗai yayi fighting justice ɗinba harga ma talakawan dasuke taking part a irin waɗannan ayyukan.
Wannan labarin ba ƙaramin daɗi yayi ma Umman ba yau shiyasama koda tadawo gida batasamu Lamiɗon ba ɗazu batanuna bacin ranta ba and besides tasan datana gida babu abunda zai hanashi yimata sallama and moreover aidama tun shekaranjiya yanemi izininta kuma tabashi izinin. Yes she might not have liked the idea of Lamiɗo going back to Bauchi amma ai bazatayi denying cewa adalilin nacin son zuwa Bauchin nasa ba yau for the very first time in his entire life yayi earning kuɗi da guminsa and for that she's grateful.
Ahakadai suka ƙarasa cin abincin nasu. Tashi Lamiɗo yayi yashige kitchen sannan yafito zaiwuce ɗaki cikin sauri Umma taƙira sunansa fuska ɗaukeda mamaki.
Juyowa Lamiɗo yayi sannan yace "Na'am Umma" Umma tace "Ba zaka fita yau baneba?" gyaɗa mata kai yayi alamar eh sannan yace "Umma na gajine. zankwanta inyi bacci kawai" murmushi Umma tayi sannan tace "toshikenan. Aikam kadebo gajiya gashi isowar dare kukayi. Jeka hutan gobe kazo kabani labarin mutanen Bauchi" Lamiɗo harya juya zaitafi ɗakin shi seya kuma juyowa yana kallon expression ɗin fuskar Umman,the way Umma is being nice abun yadameshi,yanason yasan dalili farin cikin nata don haka yakarasa inda take zaune shima yazauna agefenta tareda kallonta cikeda curiosity.
Yace "Umma wai meya faru yau kiketa farin ciki ne haka?" dariya Umma tayi sannan tace "shikenan se bazanyi farin ciki haka kawai ba? Ko so kake inta babbata rai Ina kumbura fuska?" girgiza kai Lamiɗo yayi sannan yace "bahaka nike nufi ba Umma na. I want you to always stay happy but atleast when the happiness is overload aiyakamata nima insan dalili intaya ki farin cikin koh?"
Wannan karan Jan cheeks ɗinsa Umma tayi tana murmushi sannan tace "Ina farin cikine sabida kai Lamiɗo. I'm happy because for once in your life kayi abun kanka" takarashe maganar smiling very widely sannan tabashi labarin yanda sukayi da kawarta a gidan biki yau kafin daga ƙarshe tajashi zuwa jikinta ta rungumeshi tana faɗin "hakan bakaramin daɗi yamin ba Lamiɗo. It makes me feel as if you're a grown up now,inafatan zaka cigaba dayin haka. If not for the family then for yourself. bakoyaushe bane zaka zauna kace komai se anyi maka. neman nakaima wani abune,kazama mai zuciyan nema abune mai matukar mahimmanci ga kowani Ɗa namiji"
Tariko fuskarsa da palms ɗinta tace "dagangan nahana ka kuɗin tafiya Bauchi sabida inason kaima kafara dogaro dakanka and alhamdulillah se gashi kagane hakan cikin gaggawa kakumayi amfani da basirar ka kasamo kuɗin dazakayi amfani dashi" Lamiɗo na murmushi yace "and this's the reason why bakiyi scolding ɗina ba for going without saying goodbye yauda safe koh?" Dariya Umma tayi sannan tace "Exactly. Amma hakan bawai yana nufin na kyaleka baneba. I'll surely scold you later innagama farin cikin nawa" rungumeta yayi ajikinshi still smiling sannan yace "A'a Umma kiyi min faɗan yanzu inhuta kawai gaba daya" dundu Umma takai mishi agadon bayanshi playfully sannan tace "bazanyiba. kaikasan laifin dakayi ai kuma Inka yarda kasake repeating irin wannan laifin karya kafafunka zanyi" Salma ce kawai tatayasu yin dariya wannan karan anma banda Basma da Jidda.
Sai da safe yayi musu sannan yawuce ɗakinsa yana tuna irin farin cikin dayabar Umma tanayi a parlour and then seya fara tunanin yanda zaiyi yatari mutanen Fadan batareda sunzo gida nemanshi ba dankuwa bazai taɓa so yayi spoiling mood ɗin Umma ba. Yes he desperately want to go out adaren nan anma inya tuna yana iyayin katari da dogaraye ko Fadawan masarautar seyaji bazai iya fitan ba shiyasama yacema Umma gajiya yayi ze kwanta yayi bacci a ɗaki but after Sharring a little moment with Umma dakuma irin farin cikin datake ciki seyaga babu amfanin buyan,dankuwa inyace zecigaba da buyan nema zesa suzo gida neman shi don haka atake yayi deciding gobe da sassafe zeje yayi summoning kansa a Fada and then he'll see what he can do wurin ganin maganar bata yadu a masarautar ba bare har hakan yasa maganar yazo kunnen Umma"
Yananan zaune bakin katifa yanata saka da warwarar abunda zece a Fadan gobe Jidda tashigo ɗakin nasa bakinta ɗaukeda sallama amma gaba ɗaya fuska babu walwala. amsa sallamartasa yayi and by just looking at her face yasan tasamu labarin abunda yafaru and may be ita dogarayen sukazo suka samu a gidan dasafe bayan Hafiz yabaro Fads. But still se zuciyarshi tashiga tambayarshi miyasa Jidda zatayi acting this way bayan tasan komai?why Jidda? In akwai wanda yake expecting yayi fushi dashi ko ya ɓata rai toh Basma ce anma ai Jidda he's always got her back akomi yakeyi arayuwarsa.
Tsayuwar datayi akanshine yasashi nuna mata gefenshi yace "zo zauna semuyi magana" babu musu Jidda takarasa gefen shi tazauna dukda kuwa mood ɗinta baicanza ba.
Kallonta Lamiɗo yayi caringly sannan yace "meya faru Jiddodo na? Why are you burning your face?kowani laifin nayi miki?" Yayi maganar acting as if bemayi komaiba danya bugi cikinta.
Tura baki gaba Jidda tayi ayayinda take kallonshi cikeda tuhuma sannan tace "Yanzu Hamma Lamiɗo abunda kama Aunty Maimunatu ka kyauta kenan?" wara idanu Lamiɗo yayi hakanan cikeda mamakinta yace "Yanzu daman sabida Maimunatu kike fushi dani?"dankuwa baikawo hakan aranshiba kwata kwata,yes yayi mamakin fushin Jidda akanshi anma beyi tsanmanin it's something related to Maimunatu ba.
Jidda sake tura baki gaba tayi sannan tace "Eh mana Hamma Lamiɗo. Nifa na haɗaku kuma duk abunda zaishiga tsakaninku dole yayi affecting dina" murmushi Lamiɗo yayi sannan yace "toh naji. Yanzudai faɗamin menayiwa Maimunatun dahar kike fushi dani haka?" Jidda tace "Yaufah kwanan ka uku rabon da kaje kaganta kuma kayi mata alkwarin zuwa ranar da kuka rabu. baka ga yanda hankalinta yatashiba wallahi" Lamiɗo ɗan dafe kanshi yayi sannan cikeda mamaki yace "ita ta faɗa miki haka?" Gyadamasa kai Jidda tayi ahankali sannan tace "yauda safe take faɗamin a islamiya. harda hawayenta fah Hamma. Wai gani takeyi kotayi maka wani abunne shiyasa kadaina zuwa tunda baka taɓa yimata irin hakaba" Lamiɗo yace "she did nothing. Infact tana raina wallahi Jidda. Abubuwane suka shamin kai shiyasa banje naganta ba" Jidda sake tsuke fuska tayi sannan tace "wasu abubuwan ne suka shamaka kai dazai hanaka zuwa ganin Aunty Maimunatu for an hour daikan?" Lamiɗo yace "bakiji me Umma tafaɗa a parlour baneba? Ko bakiji tafaɗi irin aikin danayi kwanannan ba?" Jidda tace "naji. Anma ai aikin na kwana ɗayane kayi,you should've visited her the other days" ɗan ajiyar zuciya Lamiɗo yasaki Jin yanda Jidda taɗau abun seriously sannan yace "Toh Aunty Jidda. nayi laifi ayi hakuri. Ki tayani bama Auntyn ki Maimunatu hakuri,I'll surely go and see her tomorrow" tura baki Jidda tayi sannan tace "Kadaije yanzu Hamma. Wallahi tana cikin damuwa" wara idanu Lamiɗo yayi sannan yace "bakida hankali Koh? After All the situations so kike infita ayau ɗinnan?" Jidda tace "wani situation?" Hararanta yayi wannan karan sannan yace "My issue with Fadawa da dogaraye nasan kinsan komai" yakarashe maganar assuringly dankuwa in ita sabida Maimunatu take fushi dashi ya tabbatar Basma sabida abunda yayine yasa take babbata rai dashi tundazu sannan kuma babu yanda za'ayi Basma tasan batayi sharring da Jidda ba.
Jin ya ambaci maganar Fadawa yasa Jidda cewa "yauwa Hamma yanzu yazakayi tackling problem ɗinnan please? Kasan dai Umma batasani bakoh? Kuma bamwason tasani dan hankalinta zai iya tashi" Lamiɗo cikeda Jin dadin yanda Jidda takauda maganar yaje gurin Maimunatu lokaci guda yace "I don't want Umma to Know either shiyasa nayi deciding zuwa inje ingansu gobe dakaina kafin ma sudawo gidannan nemana" Jidda tace "toh mezaka cemusu?" Ware hannaye yayi alamun baisani ba sannan yace "inakan tunani dai" Jidda tace "toh Allah yadora ka akansu" Lamiɗo yace "Amin" sannan cikeda curiosity tace "anma abunda bangane ananba shine,why didn't you use the money dakayi aiki a kasuwa kasamo?" Lamiɗo yace "kuɗin bazasu isheni baneba Jidda and the most annoying thing now is that namaje Bauchin bansamu naga Rukayyan ba. ankaita gidan kawunnanta because her Father is death jiddahhh!" Lamiɗo yakarashe maganar in dismay.
Duk yanda Jidda takejin haushin yanda Lamiɗon yadamu da Rukayya seda taji jikinta yayi sanyi lokaci guda ahankali tace "Allah ubangiji yayi masa rahama" Lamiɗo yace "Amin" sekuma ɗakin yaɗauki shiru naɗan wasu daƙiƙu.
Jidda ganin kamar Lamiɗon yafaɗa duniyar tunani yasata cewa "toh yanzu dai Hamma inma bazakaje gurin Aunty Maimunatun ba katura mata ko letter dazai ɗan sanyaya mata raine please" Lamiɗo dan kallonta yayi ahankali sannan yace "ta'ina zan tura mata letter ɗin? Kinsandai babu maibarin ku kufita a gidan nan dare yayi sannan banida wayar kiran Hafiz bare har inbashi sakon yakai mata. Yauda goben duk ɗaya ne ai in Allah yayarda. I'll go see her bayan nagama solving issues da mutanen Fada. I missed her too" yayi maganar sincerely and then se hakan yaɗan kwantar ma Jidda hankali atleast she now knows cewa haryanzu Hammansu nason Maimunatu bawai fita aranshi tafarayi ba.
***
Tunda nadawo parlour samun guri nayi nakwanta awata kusurwar da seka shigo tsakiyar parlourn sosai tukunnan zaka ganni. Yunwa nikeji sosai dankuwa rabona da abinci tun safe anma ko karen haukane yacijeni bazan tambayi kowa agidan abinci ba dankuwa for sure I know the outcome hakanan tsoro nakeji inje kitchen indiba dakaina yazame min wani matsalar kuma.
Kawai sena tsinci kaina Ina tunanin mutanen gidan baki ɗaya da halayensu ko Allah zaisa in iso kan me sassauci acikinsu and may be and may be I can rely on that person through out my stay in the house dankuwa zama da yunwa bazai yuyu ba.
Kawu idrissa mutum ne mesanyi hali da dattaku tun acan baya danasanshi daman. Sannan bayida nuna banbaci. Kulawar dazai nunama yaransa toh irinshi zai nuna ma Ƴaƴan yan uwansa shidai kawai kabarshi da ra'ayi tareda yin abunda yasaka agabansa. tunda kawunaina dasu Baba suka tare a Bauchi bada jimawa ba bayan kowa yafara kasuwanci Kawu Sani yafara furthering education ɗinsa. dafarko kwata kwata cigaba da karatu baya cikin yan kayanshi anma dayazo yafara sabawa da garin Bauchi,yake ganin yanda mutane kesamun cigaba, dakuma irin mutanen dayake interaction dasu,dakuma irin shawararwarin da abokanan kwarai suke bashi seyaji he needs to achieve something more,seyaji ba kasuwanci bane kadai goal dinshiba,Seyaji yanason yazamantoh ya kware akowani fanni,ma'ana a both kasuwancin dakuma harkar karatunsa tayanda zai nutsa cikin gwamnati sosai wanda hakan ne yasashi fara pursuing education ɗinsa. Daman diploma yayi tun asali,Kawu idrissa ne kaɗai yayi degree acikin su daman awannan lokacin.
DE yacika yanemi admission a ATBU Bauchi dayake result ɗinshi nada kyau babu wani ɓata lokaci suka bashi admission aji biyu(level 2). Bussiness administration yayi a diploma so daya cike DE ɗinma shiyasake nema and it turns out shiɗin suka bashi. priority sosai yabama karatun nashi dankuwa iyalinshi bakaramin takura sukayiba adalilin hakan dukdadai dede gwargwado yanayi masu kome,rashin godiyar Allah dakuma hangen nasama dasune yasa suke kallon kamar bayayi masu ɗin,suke ganin kamar kuɗinsa dana kasuwan cinsa akan karatunsa yafi tafiya.
Kawu Sani nagama degree yajona Masters bayan yagama master ɗinne kuma yasamu aiki a bank of industry as a normal employee inda acikin hakan ne kuma yakeyi PHD ɗinsa. Yanda yakeda so much dedication da hardwork yasa yana gama PhD dinnasa bada jimawa ba aka bashi managing director na bank of industry din sakamakon retire da tsohon MDn yayi kuma shine yabada sunanshi as his candidate sekuma yaci sa'a da akayi bincike akanshi se akaga babu wanda yakaishi deserving wannan position ɗin.
Ayyuka sosai ne suka karuma Kawu Sani anma hakan kosau ɗaya be taɓa sashi Jada bayaba kokuma nuna gajiyawarsa and besides yana earning yanda yakamata, kuɗi suna shigo masa sosai fiyeda da gakuma uwa uba expenses na wasu abubuwan amfanin gida da bank ɗin ta ɗauke masa. Kamar irinsu NEPA Bill,subscription na TV, biyan kuɗin ruwa,petrol ɗin sakawa a generator dakuma man da akesama mota na zirga zirgan both aikin bank ɗin dana gida.
Sannan ko wata uku baiyi dafara aikin ba suka bashi dankareriyar gida anan cikin GRA dake cikin garin Bauchin wanda wannan dalilin yasashi parking shida iyalansa suka dawo gidan. Gidan da ko kwabonsa besaka acikiba danharta furnitures Bank of industry ɗinne suka saka masa aka kuma bashi sabuwar mota dal wanda hakan yasashi bama Fahad motar sa tada dayake fafutuka dashi inda Aunty kuma tasa Fahad ɗin yasaida wannan ɗin tayi masa ciko yasayi sabuwa. Dukda sudden canjin rayuwar da Kawu Sani da familyn sa suka tsinci kansu aciki hakan besa yamanta old self ɗinshi ba hakan kuma besa yasakar ma Ƴaƴansa maraba,acewarsa wahala yasha harya samu yazama abunda yazama yau ɗin toh sudinma hakan yakeso suyi,yanason sucigaba da rayuwa irinta talakawa kokuma yace middle class sabida koda sun tsinci kansu acikin wani hali in the future bazasu Sha wahalar adapting to new halin da suka tsinci kansu acikiba,aganinsa rashin shagwaɓa yaro dakuma rashin bashi complete Jin daɗin rayuwa shizaisa yazama abun kansa,yakumayi zuciya yayi abunda yadace shiyasa haryau Ƴaƴansa dake primary dakuma masu zuwa Islamiya da school bus suke zuwa su dawo islamiya kuma suje da napep sudawo da napep.
Waɗanda ke boarding ne kawai yafara bari akaisu da motar gida dawowan kuma Allah ne kaɗai yabarma kansa sanin zebari ɗin kobazai bariba tunda tun tafiyarsu haryau basuyi hutunba. Me aiki ma yahana a ɗauka aganinsa tunda yanada gandara gandaran Ƴan mata a gida babu amfanin masu aiki,they should learn,they should do it themselves tunda bawai karfin yi ɗinne basu dashiba bakumawai dama basu iya baneba tunda tunda daɗin su sukeyi. Abunda yasa yayi hakan kuma dukwai don tunanin irin gidan auren dazasu faɗa agabane,babu wanda yasan irin wanda zasu aurs hakanan babu wnda yasan karfin family ɗinda zasu tarda kansu aciki shiyasa yakeyi masu irin wannan tanadin. Shiyasa yakeson Ƴaƴansa su taso da tarbiya mekyau tayanda ko Ina suka shiga babu Mai aibatasu anma sede besan ainahin abunda ake toyawa agidan ba,bekuma duba yanayin iyayensu Mata ba dankuwa dukyanda kaso gayima ƴaƴanka tarbiya dole seda hadin kan iyayensu mata sabida sune closest to them.
Anma se gashin shidin beyi sa'a ba. Dankuwa matan nashi biyu kowacce da nata biggest flaws ɗin.
Aunty itace first wife ɗin Kawu Sani,she came from an extended family kuma familynsu irin family ɗinnan ne dasuka yarda da dogaro dakai despite yawansu,babu wanda yake relying akan wani sede irin ɗan abunda ba'a rasaba. Kowannensu dayakai maturity age zakaga yana da abunyi na hanyar samun ɗan taro da kobo. Yes suna Boko anma neman kuɗinsu yafi bokon yawa,dan dayawansu kosunyi bokon toh zakasamu sun watsar da certificate ɗin sun koma harkar kasuwanci. Wasunsu kuma haɗawa sukeyi duka biyun suyi lokaci guda. Sanda Kawu Sani ya auri Aunty tana level 3 ma'ana zango nabiyun karshen gama jami'a kuma despite tafishi aji a bangaren boko hakan bekawo wani mishikila cikin aurensu ba sabida irin sonda sukeyi ma juna kuma Koda sukayi auren behanata cigaba da karatunta ba harta gama tunda daman tasha faɗa mishi tanayin bokon ne for reference purposes kawai. Data gama kasuwanci zata fara,Babban wansu dasuke ɗaki daya yayi mata alkawarin bata jari tayi kasuwanci. Hakan kuwa akayi dan tana karban certificate ɗinta da result ɗinta yayi kyau Yayan nata yabata makudan kuɗi takafa nata kasuwancin.
Bussiness ɗin atamfofi,laces,jakakkuna,takalma da gyalalluka tafarayi agida kuma kan kacemi seya zamanto tana samun albarkar kasuwancin,cikin lokaci kankani abun ya bunkasa sosai harma tafara da saida furnitures,gadaje dadai sauransu seyazamanto she's always busy,batasa komi agabanta ba inbanda kasuwancin ta. Intana gida zaka samu anzo duba kaya agurinta kokuma ita tafita dasu wurin masu saye danko kaɗan batayi yunkurin buɗe shago ba. Inkuma bata gida toh ka tabbata sari tatafi yi wani gari. Takanje cotounou,Lagos,Kano,Kaduna sarin kaya ayayinda inkuma tanason sayan kaya a kasashen sede tabama Yan uwanta dasuke fita su saro mata dankuwa ko kaɗan Kawu Sani bebata wannan damar ba itamakuma se bata damuba. Wannan rashin zaman nata shiyasa tarbiyan ƴaƴanta is somehow at stake,betafi yanda yadaceba,sukeyin duk abunda sukaga dama agida sabida ganin batanan wani sa'in ma kotana nan ɗin batacika samusu Ido a harkokinsu ba sabida kasuwanci data sa gabanta dukda kuwa indai taga wasu abun zata tsawatar atake.
Ko Kawu Sani yasan Aunty itace mace me hakuri tsakanin itada Ummi sannan kowani shawara zenema itayake consulting dankuwa akwaita da hangen nesa. Abudaya tayi lacking,rashin son zama guri ɗaya dakuma rashin bama iyalinta kulawa yanda yakamata wanda shida kanshi yayi iya bakin ƙoƙarin shi wurin ganin ta canza anma abun yaci tura dukda kuwa bahakan bane yasashi sake aure dafari,Ummin ma ganinta yayi yaji yanason kasancewa da'ita shiyasa ya aureta kuma daman tuncan yanada ra'ayin yin polygamy.
Mama Hadiza(Ummi) Macece kyakyawa son kowa ƙin wanda yarasa,she came from a simple and poor family. tayi karatu anma batakai matakin degree ba diploma kawai tayi wanda bayan tagama bada jimawa bane ta auri Kawu Sani. Ummi Macece meson hutu da